Showing 51001 words to 54000 words out of 250533 words
Chapter 18 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
ƙoƙarin zubewa saman gwiwowinsa da sauri ta ɗago da shi ta rungume shi tana ɗan bubbuga bayanshi da yatsun hannayenta, Farin ciki duk Ya cikata, ta manta when last ta ji ɗumin shureim a jikinta, saboda rashin jituwar dake a tsakanin su.
Muryar shi da alamun karaya ya furta mata”Mommy, ana ‘uhibuk kathiran” Hawayen da suka taru acikin idanuwanta ne suka soma gangarowa saman kuncin ta, still ba su raba jikinsu daga na juna ba, martanin maganarshi ta mayar mashi”i love u too My son, ba zan Iya misalta farin cikin da nake a ciki ba, Shureim ka faranta min rai,” ta yi maganar tare da raba jikinsu daga na juna, fuskokin su ɗauke da murmushin ƙauna
“Idan har dagaske mun shirya inaso daga yau ka goge duk wasu hotunanta dake a cikin wayarka, kallonsu baida amfani shureim, saboda suke fama maka raunin dake a cikin zuciyar ka”
Shiru yai yana kallon fuskarta, har sai da ta kai ƙarshen maganar, Har ga Allah bai jin zai Iya goge hotonta a wayarshi, don ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya suke yi ba aduk lokacin da ya kalle su, Allah ya jarabce shi da ƙaunarta, Yafi sonta akan kowa na duniyar nan, duk da bata araye.
Gudun kada ta zarge shi, yasa shi yin saurin cewa”saboda farin Cikin ki mommy zan yi deleting ɗinsu, ni kaina bana son abunda zai ƙara shiga tsakanina da ke,”
Gyaɗa kai ta yi “Shureim ka ɗauko wayar ka goge su agabana In gani” tuni yasha jinin jikin shi, ba don yaso ba ya amsa mata da toh, slowly ya juya ya nufi gadon shi ya ɗauko wayar, Kafin Ya kai mata, wayar ta hau ruri, hakan ba ƙaramin daɗi yai mashi ba, Waiwayowa yai still tana a tsaye tana kallon shi”who’s calling u”? Ta jefa mashi tambayar, Nuna mata screen ɗin wayar ya yi sunan Daddy ne Ya bayyana akai” Umarni Ta bashi ya ɗaga kiran Ya kara wayar a kunanshi, Muryar Alhaji Ubaid ce ta ratsa kunnuwanshi”Shureim Uncle ɗin ka na son ganin ka, gamu nan zamu shigo cikin gidan” muryarshi A sanyaye ya amshi mashi da toh, takaicin shi ɗaya layla taƙi tafiya, ta tsare shi da ido, adan dole sai ya goge hotunanta awayarshi.
A hankali ya zame wayar daga kunnan shi, matsawa yai kusa da ita, Bayan ya cire password Na wayar Ya miƙa mata adai dai kan Gallery ɗinshi, Ta kar6i wayar tana duba hotunan, Ta yi mamakin ganinsu kamar hauka, hada wanda ya ke a rungume da ita saman ƙirjinshi, ta6e baki layla tayi, hankalin shureim ba ƙaramin tashi yai ba ganin zata danna delete all, jikin shi har tsume ya ke yi.
“Assalamu alaikum”! Muryar zainab ce ta katse mata hanzarin ta, a sukwane ta juya tana binta da kallo, a bakin ƙofa ta tsaya”Alhaji ne ya shigo tare da kawun shureim, Shine yace nayi maki magana...” yatsina fuska layla tayi”Naji, ga ni nan zuwa” Miƙa wa shureim wayar tayi”ka tabbatar ga goge su, sannan ka fito ku gaisa da kawunka,” Amsa mata yai da toh, Bayan ya kar6i wayar, fitar ta keda wuya Ya cire memory ɗin wayar, Ya 6oye shi a cikin rigar pillow, Ajiyar zuciya ya sauke Ba ƙaramin daɗi yaji ba, don ji ya ke kamar za’a raba shi da ranshi idan akace ya goge hotunanta.
Toilet ya shiga ya wanko fuskarshi, Ya futo Ya nufi dressing mirror, cikin jerin turarurrukansa ya ɗauki ɗaya ya feshe shi a jikin shi, bayan ya ajiye ya fito daga ɗakin Ya nufi babban palourn.
*GIDAN ƊAN IYA*
Tun da ta fito daga cikin toilet ta ke a tsaye bakin wardrobe, daga ita sai Towel ɗaure a ƙirjinta, Ya sauko har saitin gwiwarta, a ƙalla Tafi ƙarfin mintuna goma, ba tare da ta motsa ba, idanuwanta na akan Jerin suturarta da ke a ninke sun sha guga, ba komai ne ya tsaida ta ba fa ce neman kayan da zasu dace da tarban Manyan baƙin su da zasu Yau, Ruwan ido take yi, duk kayan da ta ɗauko sai taga kamar ba zasu dace da ita ba, Wayarta dake a jiye saman drawer ce ta soma ringing, nan ta ke taji gabanta ya faɗi fatanta Allah yasa basu bane suka ƙaraso, Da ɗan saurinta ta nufi wayar tare da kai hannu ta ɗauketa, ko da ta duba screen ɗin wayar, babu sunan wanda ya kira, Baƙuwar number ce, kokwanto ta shiga yi akan ta ɗaga ko karta ɗaga? Don ita a tsarinta bata ɗaga baƙuwar number in dai ba wadda ta yi saving akan wayarta ba ce, kusan sau uku kiran nashigowa Yana yin rejecting ba tare da ta ɗaga shi ba, tayi kasaƙe kamar an dasa mata Aya,
Shigowa Cikin ɗakin Zahra ta yi, bakinta ɗauke da sallama, turkish gown ce a jikinta launin pink ba ƙaramin kyau tayi mata ba, tayi rolling veil saman kanta. Ganin Aneelerh a tsaye yasa tace”lafiya? Ya akai naga baki shirya ba? Ko kin manta cewa suna a hanya? Sun fa kusa isowa, Na rasa meke damunki, Ko har yanzu kewar baby junaid ɗin ce bata sake ki ba”? Harara Aneelerh ta ɗan jefa mata, Ba tare da tace koma ba, ta ɗaura wayarta saman mattress, kafin ta juya ta nufi wardrobe din Kayan da ta bari a buɗe.
“Zahra zo Ki tayani zabar kayan da zan sanya, Ruwan ido Ya hana ni ɗauka tun ɗazu” murmushi zahra ta saki yayin da take tunkarar wardrobe ɗin”Aunty aneelerh, shiga za ki yi ta mutunci, ta kece raini, Lace ko shadda su zasu fi dacewa, “ Ta yi maganar tare da Kai hannu cikin wardrobe ɗin kayan ta janyo mata wani haɗaɗɗan lace launin golden colour, ta miƙa ma Aneelerh, Fuskarta ɗauke da murmushi ta kar6i Kayan da zahra ta miƙa mata”na yadda ke ƙwararriyace a6angaren iya zabar kayan da zasu dace da mutun, nafi karfin 15 mins ina neman wanda zasu dace dani na kasa, sai da ki ka zo” Zahra tace”kada ki manta aikina ne, burina kiyi kyau auntyna, surukanki su ganki a mutuncenki, bari naje na ɗauko maki sarƙar da zata dace da kayan, ‘ amsa mata Aneelerh tayi da toh, Wuce wa zahra tayi agaban drawer chest Ta zuƙunna ta dauko mata jewelry box dinta, Ta buɗe ta lalubo mata necklace da earrings launin Lace ɗinta, maida box dinta tayi kafin ta miƙe ta daura mata su gaban mirror.
“Aunty aneelerh, Ga su nan saman mirror, Pls Ki shirya da wuri, Ni zan je na taya su mami shirya masu abincin”
Amsa mata ta yi da toh ta ƙara da yi mata godiya, Bayan fitar zahra, Aneelerh ta shirya tsaf cikin Lace ɗinta, riga da skirt, sun yi bala’in yi mata kyau, sun ɗan kama jikinta, shape ɗinta ya fito sosai, Kamar a jikinta aka ɗinka kayan, a gaban mirror ta zauna tana yin make up, lip gloss ta shafa ma la66anta, Ta ɗan shafa hoda, ta ɗauki brush tana gyara jagirarta, ‘ Sumar kanta Ta sauko har saman bayanta, ƙarar Shigowar text a wayarta ne yasa ta ɗan kalli 6angaren da wayar take ajiye saman gado, sai lokacin ta tuna da baƙuwar number da ake ta kiranta ɗazu, sai da ta fara Ɗaura dan kwalin leshin Kafin ta miƙe ta nufi wayar ta ɗauke ta, Da yatsan hannunta ta janyo sakon A hankali ya buɗe, Ta yi mamakin ganin Sunanta da aka rubuta da manyan haruffa, menene ma’anar sakon? Just Aneelerh? Wanene wannan? Kiran number ta soma ƙoƙarin Yi sai dai taƙi shiga, A ƙarshe ta hakura ta daurata saman pillow, Gaban Mirror ta koma ta ɗauki jerin turarurruka tana feshe jikin ta da su, tunawa da baby junaid ɗinta yasa ta ɗan saki murmushi, tayi missing ɗinshi sosai, yau tun da safe Mahboob Yaje kai shi school, Bayan ta haɗa da shi da kuɗin fetur, kusan sati biyu da fara zuwanshi makarantar, kullum da fara’a yake tafiya, yana zumuɗi, da zarar an kaishi Ya ke saka masu rigima sai sun dawo dashi gida, Har atashi daga school ɗin Yana yin kuka, Fuskarshi jawur ake dawo mata da shi. Malaman makarantar har sun canza mashi suna daga Junaid zuwa babyn mommy, saboda sunanta da yake yawan kira masu.
Daga waje tajiyo muryar Zahra tana kwaɗa mata kira”Aunty Aneelerh! “ girgiza kai tayi aranta tace”Ko yaushe ne zahra zata daina Yi min irin wannan kiran talaucin kamar zata ƙararmin da sunana”
Zahra na shigowa ɗakin ta Waro ido waje tana fadin”Wow!!! Tabarakallahu Ahsanul khaliqin Aunty aneelern kinga yadda ki kai kyau? Kamar wadda zata shiga gasar miss world,” harara Aneelerh ta jefa mata fuskarta asake tace”Naji na gode Da yabo, ni dai yanzu faɗa min Kiran menene kike yi min”? Watsa hannu Zahra Tayi”dama ummi ne ta aiko ni zaki ci abinci yanzu ko sai anjima idan sunzo”?
“Yunwa nake Ji zahra, ba zan Iya jira sai sun zo ba, ki samu plate ki zuba min dambun shinkafa, Ki haɗo min da lemu mai sanyi, “
“Toh, Amma kafin nan mu ɗanyi selfy mana” ta yi maganar tare da Kunna camera din iphone nata, ta ɗaga Wayar Tare da ɗaura kanta saman kafaɗar Aneelerh, gaba ɗaya suka saki murmushi, ‘ kusan hotuna Biyar tayi masu atsaye kafin Ta nufi hanyar fita ɗakin tana faɗin”Idan surukan naki sunzo zamu ƙara yin wasu hotunan tare, Hakan Yana ƙara danƙon zumunci,” fuskar Aneelerh ɗauke da murmushi ta ke bin Bayan Zahra da kallo, gefen gadon ta zauna tana Jiran dawowarta.
*EVIL FOREST*
Tun da garin Allah Ya waye Masu a cikin ƙurmin dajin, Kowan nan su Ya farka, Da wata irin matsiyaciyar yunwa, suna zazzaune abakin bishiya sun jingina bayan su, Sai hamma suke Yi, Jiya basu ci abinci da yawa ba kafin Kwanta, sauran Kayan marmarin da suka rage ne su ka sha, dan ma suna da jumurin yunwa, Hankalin su ba akwance Yake ba, Danish Yaƙi farkawa daga bacci, tsawon awanni tun daren Jiya da Angel ta sanya shi yin bacci yake ta yi, Ko motsi Ba ya yi numfashinsa ne kaɗai ke fita, tun suna sa ran zai farka har sun fara tunanin Anya kuwa Lafiya? Baccin ya wuce na hankali, domin kuwa tuni safiya ta jima da wuce wa sun shiga tsakar rana. Sun tsare shi da ido suna kallon shi, A saman shimfiɗar da Angel ta yi mashi, ya ke a kwance sun ƙudundune shi da bargo, tuntuni su ka so su tada shi daga bacci amma Angel ta hana su, ita aganinta bai kamata su takura mashi ba, tsawon wata ɗaya baya runtsawa kullum shine yin gadinsu, Na yau kawai Ya samu ya runtsa ai bai kamata su katse mashi hutun shi ba.
“Angel Yunwa mu ke Ji” Parveen ce Ta yi maganar, Fuskarta A kumbure ga miyan bacci a gefe da gefen bakinta, sumar kanta A haukace take babu gyara kamar Ƴar mahaukaciya, Angel da ke Fuskantar su tana zaune daga gefen shimfiɗar Danish, fuskarta sam babu walwala, abun ya fara damunta ganin yaƙi farkawa fatanta Allah yasa baccin lafiya ne ya ke yi.
“Genie we are feeling hungry, pls cikina kukan Yunwa yake mini” Jemimah ce tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka, idon Angel akan fuskokinsu, Batul sai hamma take Yi, tana faman yamutsa fuskarta.
“Ki jaraba Tada shi mana, wata’ƙil Ya farka, Tun da kinga mu bamu san kan dajin nan ba, balle mu ce zamu shiga ciki mu nemo abinci” Naufal ne yai maganar muryarshi da kasala.
“Ni zan Iya zuwa na nemo mana abincin sai mu ci” Gabriel Ne yai maganar, hannunshi ɗaya asaman sumar kan Azeeza da ke kwance saman ƙirjin shi.
Girgiza kai Angel ta yi”A’a Gabriel, ba sai ka je ba, Danish ne kaɗai zai Iya shiga dajin nan Ya dawo ba tare da wani abu ya same shi ba,” bubbuga ƙafa jemimah tayi cikin shessheƙar kuka tace”wai genie Ya ki ke so Mu yi ne mu fa yunwa muke ji, Ki tada shi ki tada shi Kin ƙiya so kike mu mutu ko”?
Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan jemimah dake Yiwa angel faɗa, ita kanta Angel kallon nata take yi, ganin yadda ta 6ata fuska, Kumatuntu sun yi jawur da su tsabar fusata.
“Angel ku tada shi mana” Da sauri suka kalli Haris Da yai magana, Tun da su ka baro kurkuku, baya magana daga Eh sai a’a, su kaɗai ne abunda Yake iya furtawa, amma yau sai gashi yayi masu magana, sun ɗanyi mamaki kuma sunji daɗi ga dukkan alamu sauƙi ya samu
Saboda maganar Haris yasa ta kai hannu ta bubbugi kafadar Danish, Muryar ta ƙasa ƙasa take furta sunanshi”Danish wake up! Ka tashi suna jin yunwa,” shiru bai motsa ba, Kusan sau biyar tana yi mashi magana har acikin kunnanshi takai bakinta
Nan fa gabanta ya fara faɗuwa, Parveen tace”ki buge shi mana wata’ƙil ya farka” Ba tare da ta kalli parveen ba tace”bazan Iya ba” ta ambaci hakan tare da cigaba da kwala mashi kira.
“Angel nauyin bacci ne da shi, Ba haka yakamata Ki tayar dashi ba, let me help u, “ Gabriel ne ya ambaci Hakan, Sai da ya fara janye azeeza daga jikinshi, tukunna Ya matsa gaban shimfiɗar Danish, bubbuga kafadarshi ya yi Da ƙarfi haɗi da ambaton Sunanshi”Danish! Danish!” yadda yake kware murya hatta su kansu sautin Ya cikasu, amma wani iko na Allah Danish ko girgiza Bai yi ba, Zuciyar Angel a jagule ta ɗaura Kunnanta saitin ƙirjinshi Bayan ta yaye mashi bargon, jin heart beat ɗinsa yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya sai dai ta yi mamakin dalilin rashin farkawarshi, Hankalin sauran ƴan uwan Yaƙi kwanciya, Gaba ɗaya suka dawo kewaye da shimfidarshi Kowa Ya zuƙunna
Su Azeeza har sun fara shessheƙar kuka suna faɗin Wayyo Allah Danish ɗinmu meke damunka, dan Allah ka farka ka yi mana magana ko hankalin mu ya kwanta, Mu mun haƙura ma da abinci kai kawai muke so ka tashi.
“Ko dai suma ya yi ne? Ku duba cikin gorar ruwan mu idan akwai sauran ruwa ku ɗauko Mu yayyafa mashi” Gabriel ne yai maganar cikin rashin kwanciyar hankali, Angel tace”a’a kada ku watsa mashi ruwa, Zuciyarshi fa tana bugawa, bacci ya ke yi, kunsan Danish da nauyin bacci, Balle kuma da ya ɗauki tsawon kwanaki bai runtsa ba,’ ɗaya bayan ɗaya suke jogana kunnansu saman kirjinshi don su ji idan zuciyarshi na bugawa, Hankalinsu Ya ɗan kwanta da jin sautin heart beat din nashi.
“Nasan nan bada jimawa ba zai farka, Mu ɗan ƙara haƙuri” Miƙewa Jemimah tayi tare da bubbuga ƙafarta, abunka ga yaro ba haƙuri, Yunwa ce ta addabeta, Juyawa tayi gaba ɗaya suka bi bayanta da kallo, agaban korayen ciyayen dake shimfiɗe a wurin ta tsugunna, ta soma tsigowa tana turawa abaki tana ci, hakan da tayi ne ya tuna masu da Ganyen da ake basu a prison, aiko da sauri batul da Parveen da azeeza suka mimmiƙe agaban jamimah su ka zuƙunna kamar akuyoyi haka suke cizgar ciyawa suna ci, tsawa Angel da daka masu”Meye haka dan Allah? Kunsan wani irin ganye ne ku ke ci? Ku daina” a tsawace ta ƙarasa maganar, ta mike ta bi su ɗaya bayan ɗaya tana kwace ciyawar da suka damƙa a hannun su, Fashe mata da kuka Parveen da jemimah su ka yi Nan take taji zuciyarta ta karya, cikin shessheƙar kuka suke faɗin ba za su iya jurewa ba, yunwa ce ta addabe su, ta taimaka tabar su su ci ganyen, suna jin daɗin shi ahaka.
Idanuwanta acike tab da ƙwalla tace”Is ok, Bari na shiga cikin dajin in nemo mana abincin da zamu ci,” miƙewa Gabriel yai”Zan bi ki Angel” girgiza mashi kai tai”A’a gabriel, Ka zauna ka kula da su Azeeza, Yanzu zan dawo” ba don yaso ba ya amsa mata da toh, Kallon sauran Ƴan uwan nasu tayi”Javed Naufal, Ku kula da su Azeeza, Yanzu zanje na dawo,” Naufal yace”meyasa zaki tafi ke kaɗai, bayan kin faɗa mana mu yi takatsantsan da dajin nan akwai mugayen halittun da zasu Iya cutar damu, why angel? Gaskiya ni ban goyi bayan ki tafi ke kaɗai ba, sai dai mu tafi mu duka,” Yai maganar tare da miƙewa, Javed ma Ya miƙe, haris ne kaɗai Ya rage a zaune yana sauraronsu.
Ita kanta gabanta faɗuwa yake yi gani ta ke yi kamar wani mugun abun zai iya faruwa da ita
Murmushi ta ƙaƙalo akan fuskarta duk don ta kwantar masu da hankulan su yasa tace”Bawani abu fa, da zarar nayi addu’a Allah zai tsare ni har inje in dawo lafiya, ku kwantar da hankalinku” girgiza kai Gabriel yai”bazai yiwu ba Angel, bana so wani abu ya same ki ta silar mu, idan har ba zaki bari mu bi ki ba, To ki bari Danish Ya farka Ya je da kanshi ya samo mana abincin....” tunkan ya ƙarasa maganar Angel tai saurin katse shi da cewa”su Azeeza yunwa su ke Ji, Na yadda Gabriel Ka raka ni mu tafi, ku kuma ku zauna yanzu zamu dawo” Hankalinsu ya ɗan kwanta, Atare da Gabriel Suka nufi Cikin dajin, Hannunta ruƙe da ƙaramin kwandon su, komawa su azeeza su ka yi abakin bishiya suna zaman jiran dawowarsu.
Cikin dajin suka kutsa suna tafiya suna dan tattauna fira a tsakaninsu, ta ko’ina bishiyoyine masu tsayi Da faɗi, Rassansu sun lullu6e wurin da inuwar su.
“Hankalinka ya kwanta ka biyo ni, ni ban san ma ina zamu dosa ba, Ka ta6a shiga daji”? Ta jefa mashi tambaya, girgiza mata kai yai alamar a’a”bazan Iya tunawa ba Angel, na manta da komai na rayuwata, amma inaji araina koda ace ban ta6a shigowa daji ba, zai iya yiwuwa na ta6a kallon shi a waya, Ni yanzu burina mu fita daga Cikin Dajin nan, Ko mun samu mu tona asirin zaluncin da ake yi a cikin kurkukun ƙaddara, Angel na damu da rashin ƴar uwata, ina tsoron kafin mu yi nasara su kashe min ita” yayin da yake yin maganar yanayin fuskarshi ne Ya canza, abun ba ƙaramin ta6a zuciyarshi yake yi ba duk in ya tuna da ƴar uwarshi Gabriellah.
Cikin nuna jin tausayin shi angel tace”ka kwantar da hankalin ka, Idan Allah yasa mai tsawaicin kwanace