Showing 156001 words to 159000 words out of 250533 words
Chapter 53 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
ƙayan hadi sai ƙamshi Yake Yi, a tsanake Yake cin abun shi.
Kasa zama shureim yayi idanuwanshi akan fuskar Alhaji musa Yace”uncle barka da safiya” kamar bazai amsa mashi ba ya furta”lafiya” da ido Hajiya sarah tayi alamar yayi haƙuri da halin uncle din nashi, murmushi shureim ya sakar mata yaɗan jinjina mata kai
“Ko zaka Bari idan Ya gama cin abinci sai ku yi magana, don bai cika son yana cin abinci ana yi mashi magana ba” hajiya sarah ce ta fada,
Kafin dr shureim ya bata amsa muryar Alhaji musa ta katse mashi hanzarinshi”Shureim ina jin ka, faɗi abunda ya kawo ka”
Ba ƙaramin daɗi Yaji ba, da fara’arshi ya fara magana”uncle bansani ba, ko daddy ya kira ka awaya ya sanar dakai abun farin cikin daya faru a daren Jiya” sai da ya ambacin hakan tukunna alhaji musa Ya ɗago da ido yana dubanshi alamar yana son jin ƙarashen zancen
“Ƴar uwata Benazir ta dawo gida a daren Jiya ƙarfe goma sha biyu na dare!!!”
Tsantsar mamaki da al’ajabi ne Ya bayyana akan fuskar alhaji musa, sai dai babu alamun zai furta magana sai faman jinjina kanshi yake yi.
Hajiya sarah kuwa Tsabar farin ciki mikewa tayi tsaye tare da ɗaga hannyenta sama tana ambaton”ALHAMDULILLAH!! wayyo Allah shureim Allah Yasa ba wasa kake Yi min, dagaske Benazir ta dawo gida da ƙafafuwanta ko kawota akayi”?
Shureim na murmushi yace”da kanta ta dawo gida, kuma abun mamaki tana ta sambatu tana ambaton sunan daddy da mommy da mijinta da ƴarta, kuma muna hasashen kurciya ne akayi mata da har ta gudu tsawon shekaru bata dawo gida ba, shiyasa nake so inje jos din Yanzu.......”
Hawayene suka wanke fuskar Hajiya sarah, Muryarta na rawa ta furta”shureim nima zan bika muje jos din, nasan shima uncle din naka zai je sai mu tafi atare...” kafin ta ƙare maganar Alhaji musa ya dakatar da ita ta hanyar cewa”Ya isa haka? Kinsan bana son shouting” shiru suka yi gaba ɗayansu, duk suka sha jinin jikinsu.
Kallon shureim yayi”ina zaka je da safen nan, naga ka shirya ga key din mota a hannu”?
Cikin sanyin murya yace”jos zan tafi, Inason ganin benazir”
Ta6e baki Alhaji musa yayi, tsawon mintuna ɗakin yai tsita, saida ya mula yasha iska tukunna yace”zanyi waya da yaya ubaid din, basai kaje jos din ba, zansa su zo nan abuja...” har saida gaban shureim Ya faɗi jin abinda Yace, bashi ba hatta Hajiya sarah arude take duban fuskarshi, kallon mara hankali take binshi da shi don wanna Yafi ƙarfin a kira shi da izzah, Tayaya zai nuna ƙarfin iko akan Yayanshi? Waye ya dace yazo gidan wani? Almost 16years yarinya ta 6ace sai Jiya ta dawo ƙarfe sha biyu na dare ko kaɗan bai nuna danuwarshi ba, kuma babu alamun zai je ya taya yayanshi murnar ganin yarsu da suka yi?
Muryarta na rawa ta furta”am..amma hakan bai dace ba, nayi mamaki daka furta wannan maganar, kodai baka ji abunda shureim Yake faɗi bane? Ƴar wurin Yayanka benazir ce data 6ace tsawon shekaru ta dawo gida a daren jiya ƙarfe goma sha biyu na dare Yakama ka tashi ka shirya mu tafi” da buɗar bakinshi sai cewa yai”Umarni kike bani”? Da ƙarfin hali Ta furta”A’a kawai ina ƙoƙarin faɗa maka abunda Ya dace ne” tamkar zaki Haka ya yunƙura ya miƙe Ya dubi fuskar shureim da mamaki Ya gama kamashi
“Nace bazaka je jos ba, ka koma ɗaki ka zauna, zansa Iyayen naka su zo tare da ƴar uwar taka abuja” gyaɗa kai dr shureim yayi jiki amace yace”toh uncle, na hakura, zan jira su zo ɗin” ƙwalla ce ta ciko idanuwanshi da sauri Ya juya ya fuce daga dakin.
Bayan fitarshi Alhaji musa Ya nuna Hajiya sarah da Yatsan hannunshi”koda gigin wasa kada ki kuskura ki ƙara shiga tsakanina da shureim idan muna magana, abune da ya shafeni da dangina banaki ba, don haka ki kiyaye” yana gama fadin hakan a fusace yakai hannu ya yago tissue ya goge bakinsa ya nufi cikin dakin.
Jiki asanyaye hajiya sarah ta zauna saman sofa din, lamarin Ya ɗaure mata kai, wannan rashin adalcin har ina? Meyasa zai dinga iko da yayanshi? Ko dan Yana da dukiya ne? girgiza kai tayi ahankali ta furta”wannan ba adalci bane” ta faɗa haɗi da miƙewa ta nufi hanyar fita daga ɗakin.
Bawan Allah dr shureim abun duniya ya isheshi, Uncle musa Ya bashi mamaki, bai ta6a jin haushinshi ba sai yau daya nuna ƙarfin iko akan iyayenshi, Ya fahimci ma bai damu da dawowar benazir ba saboda babu annuri akan fuskarshi duk da yasan halin shi ne hakan, amma yaji ɗaci aranshi, don me zai dinga juya mahaifinshi son ranshi bayan shine agaba dashi, ko a shekaru Alhaji ubaid Ya zarce Alhaji musa nesa ba kusa ba saboda shi ba wasu shekaru gare shi ba, shiyasa ko a jam’iyarsu ake kiranshi da ƙaraminsu babbansu. Abun ya ɗaurewa Dr. Shureim kai, har ya fara tunani kodan Yana da dukiyane shiyasa yake sarrafa kowa yadda yake so? In banda rashin ta ido har zai Iya buɗe baki yace zai kira iyayan nashi suzo abuja maimakon shi ya tattara iyalansa suje can jos din su tayasu murnar dawowar ƴar su, Anya kuwa Uncle musa bai fara shan ƙwaya ba”? Saƙe saƙe zuciyar shureim take Yi mashi hakanan ya samu kanshi da kokwanton uncle din nasa.
“Shureim dan Allah ka yi hakuri da abunda uncle dinka Ya faɗa maka, wallahi banji daɗi ba, bai kyauta ba, wannan ai ba adalci bane, bansan meyasa yake yin haka ba”
Muryar Hajiya sarah ce ta katse mashi zancen zucin nashi, har ya kusa shiga ɗakin shi Ya ci burki tare da Juyowa baya yana dubanta
Damuwace ƙarara akan fuskarta, kamar yadda shima tashi fuskar damuwarce
Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi da karyayyar murya ya furta”kada hakan ya dame ki mommy, da ace bansan halin uncle din nawa bane, amma nasani, shiyasa nake yi mashi uziri, bakomai zan jira su zo din kamar yadda ya fada”
Gyaɗa kai hajiya sarah tayi har cikin ranta bataji daɗin abin daya faru ba
“Bari na kira maka zeenatu, nasan zata ɗebe maka kewa, kafin isowarsu” still da murmushi akan fuskarshi Yace toh, zan jirata
Bayan tafiyarta, Ya shiga dakin shi, asaman gado ya jefar da key din hannun shi, Ya tu6e arab tur6an dinsa Ya jefar saman gado, Ya zauna daga gefe hannu bibbiyu ya zabga uban ta gumi takaici Ya ishe shi, mahaifinshi Yafi 6ata mashi rai saboda shine silar komai, da ace tun farko bai bari uncle musa ya raina shi ba da duk hakan bata faru ba.
Yayi zurfi acikin tunanin shi muryar Zeenatu ta katse shi
“Yaya shureim ɗina” a hanzarce ya ɗago da ido yana dubanta, ta zumbula dogon hajibi har ƙasa Yake ja, ta ruƙo round plate mai ɗauke da mug, sai faman sakar mashi murmushi take yi, kwata kwata babu natsuwa atattare da ita, kafin shigowarta ɗakin mommynta ta faɗa mata xancen ganin benazir shiyasa take ta yin farin ciki, ita fa tun da take bata ta6a ganin benazir ba a hoto kaɗai tasanta saboda kafin guduwar benazir tana ƴar jinjirarta.
Ganin yadda take tafiya babu natsuwa yasa shin saurin motsa la66ansa da niyar ya dakata da ita, sai dai ina kafin yai yunƙurin yin hakan tuni tayi tuntu6e da takalmanshi daya cire a tsakar ɗakin, Mugs din data dauko yai tsalle sama Ya dira daman ƙafarta ruwan coffee mai zafi Ya ɗalli ƙafarta, zafin da tajine yasa ta jefar da plate din hannunta, ta duƙe saman floor tana kuka, da sauri Ya miƙe ya ƙarasa gabanta, ya zuƙunna tare da kai hannu ya damƙi ƙafafuwanta Ya soma tottofe su da addu’o’i, ta dage sai kuka take yi mashi, abunka ga farar fata wurin da ruwan coffeen Ya ta6a yayi jawur kamar zai fashe.
Kukanta duk Ya cika mashi kunnuwanshi, a hankali ya ɗago Yana dubanta, hawaye sun wanke fuskarta, lokaci ɗaya ya soma tariyo sambatun benazir tuni yaji jikinshi yai sanyi, haƙiƙa Yana matuƙar tausayin rayuwar ƴa mace, fuskar benazir ce ta dinga yi mashi gizo akan fuskar zeenatu, har baisan sa’adda Ya rungume ta a kirjinshi Ya zagoya da hannanyeshi saman bayanta, Yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi, ƙanƙameshi zeenatu tayi kamar zata koma cikin cikinsa, daddaɗan ƙamshin turarenshi ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba, tuni ta haɗiye kukan da take yi, tayi kwance abunta sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, dr. Shureim sam ya manta dawa ya rungume a jikinshi, kewar benazir duk ta addabe shi, Ya jefa zeenatu cikin yanayi najin shauƙin shi, yayin da shi hankalinshi nacan wani wurin daban...............
Idan muka koma 6angaren zahra, tun wuraren ƙarfe shidda Mahboob Ya shigo mata da jakar kuɗin motarta da wayar da aka saida mata, shaf shaf ta shirya cikin jallabiya ta yafa mayafi akanta, tace da mahboob ya taimaka ya kaita gidan Hajiya falmata, yace zai kaita amma bisa sharadin zata bashi nashi kason, tunda ai yayi mata ƙokari, a lokacin taƙagara da taje tace mashi ta amince su tafi kawai, kafin su bar gidan saida ta fara cire miliyan ɗaya ta ajiye su cikin drawer, ya rage saura 3m dai dai kuɗin da zata bata.
Tana zaune a back seat na motar mahboob, yayin da shi kuma yake zaune a mazaunin driver, a tsanake yake yin driving har Allah Ya kawo su gidan Hajiya falmata.
A parking space mahboob yai parking din motar yace da ita ta shiga yana jiranta, ta amsa mashi da toh, ta buɗe motar ta fito ta nufi ƙofar shiga babban falon gidan”
Murmushin gefen fuska Mahboob ya dan saki yayin da yake bin Bayan zahra da kallo, ya zuro ƙafarshi daga cikin motar daya bar murfinta abuɗe
Wayarshi ce tayi ringing daga cikin aljihu da sauri Ya zura hannu ya duba mai kiranshi sunan Aunty Aneelerh ne Ya bayyana
Picking call din yai ya kara wayar a kunne”Babbar yayanmu, mun karaso gidan fa, Yau zahra zata sha mamaki, wallahi bakiga yadda take ta zubda uban gumi ba, kamar wadda tayi ma sarki ƙarya fadawa suka kamo ta” tuntsirewa yayi da dariya,
Muryar Aneelerh da sautin dariya tace”baiwar Allah, ina fata yau hankalinta zai kwanta, naji daɗi da nasarar da muka samu, ubangiji Allah Ya ƙara tsare mata ita” ya amsa mata da ameen
Ta kuma cewa”Idan kuka dawo gida, ka faɗa mata cewa motarta da wayarta jingina ka bada su, idan tanaso ta baka kuɗin za’a dawo mata da su, sannan please bana so tasan cewa jiya munje gidan hajiya falmata, ya amsa mata da toh, daga haka sukayi sallamar.
Tun da zahra ta shiga gidan, takasa zama, tana a tsaye tana jiran fitowar hajiya falmata don ta miƙa mata kuɗinta, mai aikin gidan ce ta fito daga part din dakin nata ta dubi zahra”ki zauna mana gatanan fitowa” galla mata harara zahra tayi’ba zama nazo yi ba” murmushi mai aikin tasaki kafin ta wuce ta nufi kitchen
Jim kaɗan, Hajiya falmata ta sauko down stairs, sleeping dress ne a jikinta riga da wando ta yafa mayafi akanta.
Fuskarta babu walwala ta dubi zahra”zauna mana” tayi maganar tana nuna mata sofa
Harara zahra ta watsa mata”ba zama nazo yi ba, kuɗinki na kawo maki” tayi maganar a fadace ta ajiye mata jakar gaban kujerar da take a zaune
Har ta juya zata fita muryar hajiya falmata ta katse mata hanzarinta
“Zahra! Dan Allah ki zauna inaso muyi magana badan halina ba”
Batayi mata gardama ba tace”dan kin haɗani da Allah, shiyasa zan zauna badan haka ba wallahi ko kallo baki ishe ni ba” murmushi hajiya falmata tasaki.
Bayan zahra ta zauna tana faman haɗe rai tace”ina sauraronki sauri nake yi in tafi”
“Nasan zakiyi mamaki zahra, kuma ba lallai ki yarda da abunda zan faɗa maki ba, abunda Ya faru a tsakanina dake badagaske bane, jarabaki nayi saboda wani dalili nawa....” da mamaki zahra take dubanta, jinjina kai hajiya falmata tayi”tabbas ba halina bane, nayi ƙoƙarin jan ra’ayinki ne don insan dawa ƴata take tarayya”
Tunkan ta kare maganar zahra tasaki dariyar rainin wayau tana fadin”dallah malama dakata! Banason zancen banza, harni zaki raina ma wayau? Ki gama zubda mutuncinki agabana kuma ki dawo kina fadin jarabani kikayi akan me kenan? A tsiwace ta furta hakan
Numfasawa hajiya falmata tayi”zahra dalilin dayasa nayi maki hakan, Mun samu sabani nida wata aminiyata hajiya naja’at akan ƴarta dake bin mata, ta laƙafa mun sharrin cewa ƴata fatima ce ta koya mata, saboda ita kaɗaice suke tarayya, sannan ita taba yarta tarbiya tasan bazata ta6a aikata hakan ba, faɗa sosai mukayi da ita, ta zageni taci mutuncina, damuwar duniya ta isheni, lokacin dana dawo gida narasa ya zanyi in tuhumi fatima saboda nima ina tsoron ace ƴata tana aikata kalar abunda Yarinyar aminiyartawa take yi, nasan zaiyi wuya fatima ta faɗa min gaskiya, kinji dalilin dayasa na yanke shawarar yi maki hakan saboda nasan ke kaɗaice aminiyar fatima, duk wani abu da zatayi saida shawararki, atare kuke yin komai, Ni a tunanina ta hanyar dana 6ullo maki zan samu abunda nake nema na gano abunda ƴata take aikawata ashe ba haka bane nayi babban kuskure zahra, dan Allah Ki yafe min” fashewa tayi da kuka hawaye nabin fuskarta, baiwar Allah zahra tuni zuciyarta ta karya, sam bata kawo komai aranta ba, ta yadda da kalaman hajiya falmata, cikin shessheƙar kuka tace”Amma meyasa zaki yi jarabawar dani? Kin hanani bacci kin hanani cin abinci, kin jefa rayuwata cikin matsanancin tashin hankali, babban abun takaicina shine karya min zuciya da kikayi saboda na ɗauke ki tamkar mahaifiyata ina ganin girmanki, ashe dama duk plan ne kika shirya min”?
Hajiya falmata na matsar ƙwalla tace”kiyi hakuri zahra nasan ban kyauta maki ba, dan Allah ki rufe min asiri kada kowa Yaji maganar nan, saboda banaso ayi tsammanin nima ina aikatawa ne sannan, maganar kuɗin da nake binku ni tuntuni na yafe maku, wallahi na bar maku su babu abunda zanyi dasu, sannan maganar yin order na kaya daga dubai in sha Allah gobe zasu iso Nigeria, inaso kuci gaba da gudanar da aikinku a companyna ke da fatima, don bazanso in rasa mace mai nagarta da tawakkali irinki ba, komai kuke so zanyi maku zahra, ni dai fatana ki manta da duk wani abu daya faru a tsakanina dake, Ki cigaba da daukata tamkar mahaifiyarki”
Rushewa zahra tayi da kuka, kamar ranta zai fita, bata ta6a tsammanin komai zai zo mata da sauƙi ba, harta fidda ran cigaba da aiki a companynsu da kuma damar zuwa obie estate ashe da rabon mafarkin ta ya zama gaskiya.
Cikin shessheƙar kuka tace”In sha Allah mommy babu wanda zaiji maganar nan, komai Ya wuce amma dan Allah kada ki ƙara yi min wasan nan, ni kaɗai nasan raɗaɗin da naji acikin zuciyata”
Jinjina kai hajiya falmata tayi da karyayyar murya tace”bazan ƙaraba zahra, nima nayi danasani, dan Allah ki tsaya mu yi breakfast atare kada kice zaki tafiya”
Zahra tace”sauri nake yi wata rana zan dawo, Ina fatima take”? Hajiya falmata tace”bata nan, jiya ta tafi gidan uncle dinta amma yau zata dawo saboda aikin da zakuyi tare” murmushin farin cikine Ya bayyana akan fuskar Zahra, sai faman washe bake takeyi harta fara tunanin irin rashin mutuncin da zatayi ma Aneelerh idan ta koma gida,
Godiya sosai hajiya falmata tayi mata, itama zahra tayi mata godiya da fara’a suka rabu.
Ta ruƙo jakar kuɗinta a hannu, tana fitowa daga falon da gudu ta nufi motar mahboob tana dariya haɗi da yin rawa tana jujjuya,
Mahboob tamkar baisan komai yace”zahra kin haukace ne? Lafiya kike dariya kamar wadda ta zauce ga hawaye akan fuskarki” da sauri ta share hawayen da gyalen jallabiyarta
Tace dashi”bro ka tayani murna yau ina cikin farin ciki, amma fa kada ka tambayeni meyasani shiga yanayin nan”
Mahboob na murmushi yace”shakuruminki aini ba ɗan jarida bane da zan tsareki da tambaya, Yanzu dai shiga mota muje gida muyi magana akan haƙƙina,”
Da farin ciki tace”ai mahboob kamar yadda Allah Ya rufa min asiri kaima zan rufa maka asiri, kai dai muje gidan” ta faɗa haɗi da shiga motar, ya tada suka nufi Hanyar komawa gida.
*EX-PRISONERS🥳*
*At abuja Nigeria🛬*
Alhamdulillah Matafiya sun samu damar sauka Lafiya basu wayi gari ba sai acikin Katafaren Luxury Villa Mallakin Chief Owais sharafuddeen Obinna! haɗaɗɗiyar Daular arzƙi ce wadda zamu Iya kiranta da Aljannar duniya saboda Kayan alatun dake acikin ta, Katafaren gini ne mai girman gaske ta 6angaren tsayi da faɗi Yana ɗauke da Sassa Uku acikinsa, a ɗaya daga cikin Part din gidan aka yima Prisoners masaukinsu, A hankali nake bin ginin da kallo domin in ƙarasa ga cikinsa, ta ko’ina na kalla ƙyalƙyalin gilassai ne suke kashe min idona da kyawunsu, wasu irin haɗaɗɗun floor-to-ceiling Glass windows ne masu mamaye bango, daga ƙasa har sama glass ne, Kana Iya hangen Katafaren Main falo din dake acikin sashen ta glass windows din, Ga wasu sliding doors ƙofofi masu zuge kansu da zarar sun gama tantance mutun saboda gidan Yana da mugun tsaro ba iya mutane ba hada na’urori ke sarrafa shi, ba za ka ta6a Iya ƙetare Gingirimeman entry way din gidan ba tare da An tantance ka ba, daga ƙasa har sama, bana tunanin ko aljani zai Iya shiga salin alin ba tare da na’ura ta haska shi ba, salon kuma ace nayi karya (😂)
Dafa ƙofar glass din Nayi da hannuna ɗaya, Na’ura ta tantance ni aka bani iznin shiga ciki, Slowly glass din Ya soma zugewa, Na baza ido ina kallon tsaruwar Falon da kallon shi kaɗai zai Iya faranta zuciya, launukan painting cikinsa black, gold and white, An ƙawata shi da manya manyan sectional Chersterfield sofas, saiti biyu ne a palourn, Ƴan ubansu masu numfashi masu tafshi da daɗin