Showing 159001 words to 162000 words out of 250533 words

Chapter 54 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.

18 Feb 2025

116500

zama ga jerin Throw pillows launuka daban daban saman kowace sofa, daga tsakiyar Katafaren falon wani faffaɗan Glass table ne daga saman shi an ɗaura flowers Vase, Furannin har ƙyalli suke Yi masu launi daban daban, bayan haka a kowani sofa hand din akwai Round glass table, mai dauke da kayan ƙyale-ƙyale na ado, daga saman jigunan ceilling din falon wasu ƙayatattun Crystal chandeliers ne masu girman gaske, An ƙawatasu da ado, kusan guda Uku ne a saman silin din, Haskensu Ya mamaye ko’ina tamkar da rana, Idan ka kalle su sai ka yi tsammanin zasu rubzo maka saman kai, sobada girman su, ga wata faskekiyar flat screen tv wadda idan kana kallo da ita sai ka yi tsammanin mutanan ciki zasu fito waje saboda girmanta, Bayan sofas din falon akwai hamshaƙan armchairs har guda biyu, hatta saman floor din falon Kayan adone aka ɗaura samansu, sparkling floor lamps ne ajiye a kasa suna bada nasu hasken mai ƙyalƙyali, akwai Kayan jin sauti, Ga Dogayen labulaye dake kewaye da falon an zuge su, A ƙalla Part din Yana ɗauke da Faluka sun kai Uku, bayan wanda na zayyana ma ku, daga cikin falon farko kana Iya hangen furniture din da ke a cikin falo na biyu ta hanyar Glass window, komai zaka Iya gani, Gidan fa Ya haɗu Ga glass elevator gefen twins stairs din dake a falon, ta ko’ina sanyayyan sanyin A.c ne ke ratsa fatar jikin bil’adama mai ni’imar gaske, bayan haka ta cikin glass din falon zaka Iya hango Sashen da tanƙameman swimming pool din gidan Yake, ruwan dake acikinsa launin sky blue ne, da wasu kujerun shaƙatawa a gefenshi, da sauran ababen more rayuwa, Idan muka koma Dining room wato ɗakin cin abincin gidan abun ba’a magana, shima a kewaye yake da floor-to-ceilling glass windows, kana Iya hangen abubuwan dake wakana daga wajen ɗakin cin abincin, An ƙawata shi da haɗaɗɗun dining tables, na farko zungureren table ne mai mazaunin mutun goma sha biyu, da me mazaunin mutun shidda, da kuma tabur mai mazaunin mutun uku, kowan nan su saman shi an ƙerashi da zallar glass, ƙafafuwansu kuma wooden legs ne, wasu haɗaɗun gujerune kewaye da tables din, daga saman ceilling din ɗakin cin abincin ƙaton kwan fitila ne ke haskaka cikinsa, ga kuma Zungureriyar floor lamp, Itama nata hasken Daban Yake, agurguje zamu leƙa Cikin Bedrooms din dake a part din, A ƙalla ɗakunan kwanan dake a cikin part din sun kai goma sha biyar, Just for one part, ƙofar shigar kowani ɗaki ta glass ce sai dai baka Iya hangen abunda ke ciki idan har na cikin ɗakin ya zuge curtain dinsa ba, ƙofar da kanta take zugewa da zarar mutun Ya kusance ta take sliding a hankali, Idan ka shiga ɗakin idanuwanka zasu fara Yin Arba da wallpaper ta bango mai matuƙar jan hankali, kowani room Yana ɗauke da hamshaƙan king-side beds masu tausasan Katifu kalar wanda ko mutun bai jin bacci idan Ya hau su sai dai aji sautin minsharin shi, saman gadon shimfiɗe yake da tausasan bedsheet, da jibgegen bargon lullu6a kafi mage laushi, ga jerin matassan kai daga gaban gadon.

Gefe da gefen gadon nightstands ne, wadanda ke ɗauke da bedside lamps, daga bakin gadon faffaɗan wooden table ne mai ɗauke da drawer chest a jikin shi, ga wani haɗaɗɗen rag carpet shimfiɗe ƙasa mai dumbujejen gashi gashi ajikinshi tsaf mutun zai Iya kwanciya saman shi saboda laushinshi, ga wani ƙayataccen dressing mirror gabanshi haɗaɗɗiyar kujerace, daga can cikin ɗakin akwai dressing room, aljannar duniya kamar ka shiga company saboda haɗuwar Large walk in closet din daya mamaye kowani bango na dakin sanya suturar, suturun sanyawa ne an jera su, daga waje zaka Iya ganin kayan dake a cikin closet din, 6angaren Kayan bacci, dana Dogayen riguna, 6angaren english wears dana atamfofi ga laces, da jerin coat, ga 6angaren takalma kala kala, dana jakkuna, kai komai fa an zuba shi babu ce kaɗai ke babu, shima ɗakin Yana da nashi dressing table, mai ɗauke da oval-shaped mirror, Mai Kyan gaske.

Ataƙaice Idan fa nace zan tsaya zayyana daular Owais sharafudden tabbas zamu ƙare littafin akan bayyana kyawunsa, sai dai mun shiga cikin labarin sannu a hankali zan ƙarasa zayyana maku haɗuwar wasu 6angarorin na gidan.


*CHIEF OWAIS✊*


Gajiyar tafiya ta hana shi ta6uka komai, ga6o6in jikinsa sunyi mashi nauyi, tun da ya fito daga bathroom yake a kwance saman katafaren king bed dinsa, ya lullu6e surar jikinshi da Cashmere robe launin dark navy, Iya gwiwarsa rigar ta tsaya mashi, ya ɗaure igiyarta daga saiting flat waist dinsa, mutumin fa akwai ƙirar ƙarfi, Kyawawan idanuwanshi A lumshe suke tamkar maiyin bacci, Yalwatattun eye lashes dinsa sun kwanta luf, a hankali Yake motsa soft thin lips dinsa tausasa launin pink, dogon hancinsa Yayi tsaye babu lanƙwasa Yayin da yake fitar da numfashi cikin kwanciyar hankali, ya zagayo da hannun shi ɗaya ta saman yalwatacciyar sumar kanshi, ba za ka ta6a gane a wani yanayi yake aciki ba, ya tada kansa asaman tattausan pillow.

Alert ne ya shigo wayarshi, tamkar baisan motsawa A hankali ya miƙa ziraran yatsun hannunsa na dama ya janyo wayar dake ajiye saman nightstand, daƙyar yake iya buɗe eyes dinshi akan screen din wayar, Doorbell alert ya gani alamar wani yana son shigowa room dinsa, unclock button ya danna, a hankali ƙofar room ɗin ta zuge, mutun biyu ne sanye cikin kakinsu, baƙaƙen kaya, dogon wando tare da black shirt, daga sama sun ɗaura long coat, kowannansu ya 6oye fuskarshi da face mask, idanuwansu ne kaɗai zaka Iya gani, suna da faffaɗan ƙirji, agaban gadon shi suka dakata da yin tafiya, cikin girmamawa suka haɗa baki wurin furta

“Barka da safiya Yalla6ai, fatan ka tashi lafiya, Ya gajiyar tafiya” tun da suka fara magana basu ɗago da ido sun kalle shi ba, saboda a ƙa’ida shi ba’ayi mashi magana ana kallon cikin idon shi, hakan babban laifi ne.

Bai da niyar yi masu magana, bai kuma buɗe idanuwanshi ba tun da ya lumshe su, aran su su ka ayyana yau qasaitar tashi ce ta motsa, kamar gumaka Ya shanyasu a tsaye suna jiran amsar shi, sai da ya mula yasha iska kamar baison motsa la66ansa Ya furta”Lafiya” muryarshi tamkar ana busa sarewa.

Big Guy yace”Sir, is there anything you need?” ya tambaye shi ne don shi a ƙa’ida ba’ayi mashi abun da bai ce yana so ba, ko da kuwa abinci ne ka kawo mashi duk mun yunwar da yake ji in dai bashi yace yana so ba to zai ce maka ka koma dashi inda ka ɗauko shi sai in yaga dama ya ke kar6ar shi”

Jin yayi shiru yasa Big Guy kuma cewa”yalla6ai zamu Iya yin magana ta waya”? Sai lokacin Ya ɗaga mashi kai alamar eh, ajiyar zuciya Big Guy ya sauke tare da kallon mutumin dake a gefen shi wanda suke kira Boss Man, murmushi su ka sakar ma junan su, sun ƙwammace su yi magana dashi ta text message saboda wahala yake basu in dai a baki zai furta masu magana.

Slowly ya ware reddish brown eyes dinsa akan screen din iphone dinsa, a tsanake yake yin typing.

Jin ƙarar shigowar message ta wayar Big Guy ne yasa shi yin saurin curo wayar daga cikin aljihun coat dinsa Ya duba abun da Chief ya rubuta mashi

_I need My breakfast right now_


cikin girmamawa big guy yace “I’ll bring it to you immediately,”

Ya faɗa tare da Juyawa ya fuce daga ɗakin, Boss Man daya ya rage a tsaye ya natsu yana jiran jin me zai ce.

A lokacin da bai yi tsammani ba, muryar Chief ta katse shi”Have a seat” wuri ya samu saman doguwar sofa din ɗakin Ya zauna
“Check your phone, I sent you a message.”
Ya bashi umarni.
Da sauri Boss Man Ya zaro wayarshi daga aljihu ya soma karanta saƙon chief din nasu.

“Ya kake fatan ka tashi lafiya” murmushi ya saki har saida ya ɗago dakai Ya kalli fuskarshi, Yana matuƙar yin mamakin girmama shi da yake yi duk cikin waɗanda ke aiki a ƙarƙashinsa shi kaɗai Owais Yake gatantawa, suna mutunci da juna.

“Lafiyalou Alhamdulillah, Ina fata kaima lafiya, don na lura kamar gajiyar tafiya bata sake ka ba” abaki Ya furta mashi maganar, shi kuma Ya bashi amsa ta text message.

“Nagaji sosai, amma alhamdulillah, lafiyata ƙalou, Ina fata ka leƙa wurin Ƴar taka, “

Still fuskar Boss man da murmushi yace”ban kaiga zuwa ba, Yanzu nake shirin shiga na duba ta”

Text ya rubuta mashi”Make sure you give her a big hug. I know you’ve missed her for a long time.”

Idanuwan shi ne suka cicciko tab da ƙwalla, tuni jikinshi yai sanyi, cikin sanyin murya ya furta”in sha Allah, zanyi hakan, daren jiya ko runtsawa banyi ba saboda jiran ƙarasowarku Nigeria, duk don saboda Inyi tozali da ita, sai dai ban samu damar Yin hakan ba, saboda Bayan nayi sallar asubahi a masallaci bacci Ya dauke ni, saida na shigo gida nake jin labarin ƙarasowar ku......” dakatawa ya ɗanyin da yin maganar, ganin text din da owais Ya tura mashi.

“Don’t let the tears fall from your eyes, Otherwise, I won’t let you see your daughter.” fashewa yayi da dariya jin abunda yace mishi, har saida ya ɗago ya dubi fuskar Owais, Hankali kwance sam idanuwanshi basa akan fuskar Boss Man ɗin.

“Kana da mutunci, shiyasa muke ƙaunarka, wallahi tunda nake arayuwata ban ta6a ganin matashin saurayi mai wadatar arziƙi, da kyau da asali, mara girman kai irinka ba, saboda kowa naka ne, babu ruwanka ka ji daɗin rayuwarka, bazan ta6a mantawa da alheran da kayi mun ba, nasan bazan Iya biyanka ba amma ina fata Allah Ya wadatani da abunda zan faranta maka da shi”

Tunda ya fara magana Chief owais Ya natsu yana sauraron shi, idanuwanshi akan screen din wayarshi.

Tambaya ya jefa mashi”What’s her full name?”

cikin girmamawa Boss Man yace”UNAISAH ZAHEER TAJUDDEEN” lumshe idanuwanshi yayi, ƙamshin turaren jikinsa yana ƙara daɗaɗa hancinsa.

“She looks like you” dariya Boss Man ya saki yana duban fuskarshi Yace”tayaya akai ka sani? Kaida baka kallon mutane, Ni nasan baku haɗu da ita ba”

Kafin Owais Ya furta magana, alert Ya shigo wayar shi, unclock button ya danna, door room din ta zuge, Big Guy ne ya shigo da food trolley, Ya gunguro shi zuwa gaban wooden table din gadon Owais, a saman shi Ya jera mashi kayan Lafiyayyan breakfast dinsa, Bayan ya gama da zolaya Boss man yace”Big Guy, mutumin fa yau baya iya cin abinci da kanshi, ko zaka mashi abaki”? Big Guy na murmushi yace”If he gives me the opportunity to do that, I’ll do it har wanka zan dinga yi mashi....”daƙyar Ya ƙare maganar ganin yadda Chief owais Ya ɗago da sexy eyes dinsa akan fuskarshi, cikin jin kunyar maganar daya furta ya sunnar dakai ƙasa Yana faɗin”afwan Sir, su6ul da baka nayi”

Fuskarshi a ɗaure Ya furta”If you ever repeat this mistake, you’ll spend the rest of your life in prison.” Dariya Boss Man yayi jin abunda chief yace, Big Guy na murmushi aranshi Yana fadin”Ai bazan ma ƙaraba, Yanzun ma albarkacin boss man naci”

Ajiye wayarshi yayi saman nightstand, Ya yunƙura Ya miƙe Yana faman Yamutsa fuskarshi, Big guy dake satar kallon damtsen hannun shi sai faman jinjina kanshi Yake Yi, dawowa yayi end bed din Ya zaune gaban glass table din dake shaƙe da abinci.

Serving dinshi big guy Ya fara Yi, Ya miƙa mashi mug na coffee, Kafin Ya fara sha sai da Ya fara fadin”Boss bismillah” Man na murmushi Yace”A’a yalla6ai, Ni ina na isa In haɗa Kafaɗa dakai wurin cin abinci, kaima ka sani bamai yiwuwa bane, sannan Ni a ƙoshe nake, Madam ta girka min abinci na cika ciki na”

Ta6e baki Chief Owais Yai, ba tare daya ƙara furta komai ba.

“Yaran fa har Yanzu bacci suke Yi yalla6ai, na lura ba ƙaramin gajiya suka yi ba, musamman Kyakkyawan matashin nan dake acikinsu, mai kama dakai,’ yamutsa fuska owais Yai jin ance mai kama da shi.

Fresh fruit ya soma ɗauka Yan sha, duk wani motsin shi akan idon Boss Man, Yaron ba ƙaramin burgeshi Yake Yi ba, ƙaramin mutun da halin girma, Idan kaji shekarun chief owais zaka sha mamaki, girman jikine kawai dashi da kuma babban matsayi da Allah Ya bashi, uwa uba Ya iya dattako.

Boss man Yace”An kammala shirya masu breakfast dinsu, masu aiki suna can suna aikin jera masu, Yanzu su kaɗai muke jira su farka don su ci” ya faɗa yana duban fuskar chief, Jinjina kanshi ya ɗanyi batare daya ɗago da idona ba ya furta”hakan Yayi kyau”

Miƙewa Boss Man Yayi”Ni zan shiga Cikin gidan, Ka ci abinci Lafiya our chief” Ya ambaci hakan tare da Juyawa Ya fuce daga ɗakin, Ya rage saura Big guy dake saving dinshi.

*🤍EX-PRISONERS❤*

Kwance take saman katafaren gadon ɗakin Danish, tun daren Jiya da suka ƙaraso kowannansu aka ware mashi ɗakin shi, mutun biyu ɗaki ɗaya, Danish ne kaɗai Aka mallaka mashi bedroom ɗaya saboda shine babbansu, Angel da Batul ɗakinsu daban, Azeeza da jamima ɗaki ɗaya, Parveen da Hanna suma nasu daban, Gabriel da Naufal room ɗaya, Javed da haris a ɗaki ɗaya.

Saboda Rashin lafiyar danish yasa ta gudo daga ɗakinsu ta dawo nashi tana matuƙar jin tausayinshi batasan wani abu ya same shi, gani take kamar idan tayi nesa dashi wani abu zai faru da shi, gown din Jiyace a jikinta red colour, tayi uban squeezing, hatta sumar kanta a haukece take babu gyara sunsha bacci kamar ba za su farka ba, daɗin lumbutsetsiyar katifar gadonne Ya sanya suka shagala, daga ita har shi garkuwan, ya cire suit jacket din jikinshi Iya farar shirt dince Ya bari, da gajeran wando fararen laps dinshi kamar ka ta6a jini ya ɗago tsabar hasken fatar, ya ɗaura kanshi saman wuyanta, yayin da hannayenshi biyu ke a ruƙe da waist dinta, zafin jikinshi ya daidaita bakamar da suna acikin jirgi ba zazza6i ya lullu6e shi, Yanzu ya samu sauƙi numfashinshi na fita cikin kwanciyar hankali, Sanyin A.c din dakin ya ƙara masu ƙaimi wurin Yin baccin nasu kamar matattu.

Mutsu mutsu ya soma yi alamar zai farka, wata irin matsiyaciyar yunwace ta addabe shi, tun Jiya baici ko mai ba, ko ruwa bai gifta maƙoshin shi ba, Dogon numfashi yaja idanuwanshi sunyi mashi nauyi Ya gaza buɗe su, da wata irin kasalalliyar murya ya soma ambaton sunanta”My Angel! My Angel” badan la66ansa na akusa da wuyanta ba da kuwa zaiyi wuya ta iya jin muryarshi.

Kamar an zungureta, a firgice ta farka tana faman zare gray eyes dinta haɗi da ambaton sunanshi”Danish are u okey? Ko jikin ne”?

Daƙyar Ya iya janye head dinsa daga saman wuyanta Ya daura shi saman tattausan pillow, a hanzarce ta yunƙura Ta miƙe zaune tana faman mutsistsike idanuwanta da hannunta donta samu damar ƙare mashi kallo.

“My man, yunwa ko”? Tun kafin ma ya faɗa mata abunda Yake Ji ta riga shi faɗi.
Ɗaga mata gira yai alamar eh, murmushi ta ɗan sakar mashi har dimple dinta Ya lotsa”Danish banga ka yaba kyan ɗakinka ba, ko da yake baka acikin hayyacinka, saboda kana Jin Yunwa, bari naje naga ko zan samo maka abunda zaka ci, kafin in dawo ka shiga toilet kayi wanka, sai ka canza kayan jikinka” kamar ƙaramin yaro haka takeyi mashi magana.

Wurga eye balls dinshi yayi akan katafaren ɗakin nashi, kamar na ɗan shugaban ƙasa tsabar haɗuwarshi.

Saukowa Angel tayi daga saman gadon, tana tafiya tana waiwayon shi, daɗi kamar ya kashe ta, haƙika taji daɗin canjin rayuwar da suka samu, har ta fara tsara masu irin rayuwar jin daɗin da zasuyi, sai dai ta ɗan shafa’a da zancen kurkukun ƙaddara.

Tun da ta fito daga ɗakin take faman ƙwala ido tana kallon haɗuwar katafaren falon, Cikin sanɗa take Yin tafiya kamar 6arauniya, fararen ƙafafuwanta babu takalma, bata nufi ko’ina ba sai ɗakin su Azeeza a hankali ta zuge ƙofar ta faɗa cikinsa, tayi mamakin ganinsu a tsaitsaye saman bed mattress kowacce ta ruƙe pillow a hannunta, sai tsalle suke Yi suna fadin”gamu agidan daddyn Genie” dariyace ta kusa kubce mata da sauri ta toshe bakinta da tafin hannunta, wato su duk a tunaninsu gidan daddyn Genie ne aka kawo. yara sun zama ƴan hutu. Fitowa tayi daga ɗakinsu ta nufi ɗakin Parveen tana shiga ta sameta a zaune tsakiyar gado, bacci yaƙi sakinta ga yunwa tana ji sai faman yin hamma take Yi, sumar kanta kamar ta mahaukaciya duk ta yamutsata, ta gimtse eyes dinta, hannah na akwance gefenta sai sharar baccinta take Yi.

Ƙumshe dariya Angel tayi da sauri ta fito ta nufi ɗakin su Haris don ta duba su, lokacin data shiga ɗakin gaba ɗayansu bacci suke yi daga shi har javed duk sun cire suit jacket dinsu sunbar shirt da gajeran wando.

Fitowa tayi dakinsu ta nufi, ɗakinsu Naufal, adai dai lokacin Gabriel Ya fito daga wanka, daga shi sai short, Ya ruƙe short toilet Yana tsane sumar kanshi, Naufal kuma yana zaune saman mirror chair Ya ƙura ma madubin ido da alama gabriel din Yake jira ya fito daga wankan shima Ya shiga.

Gaba ɗaya basu lura da Angel ba, da zolaya gabriel Yace”mutumin kyau kake kallo a madubi naga tun ɗazu ka tasa shi agaba ko ƙyafta ido baka Yi”

Ba tare daya juyo ya dube shi ba yace”Kai nake jira ka fito daga toilet din nima wankan nake son Yi”

Gabriel Yace”amma dai kasan toilet din nan ba kalar na prison bane, akwai ruwan zafi dana sanyi kada kaje ka ƙona fatarka, kazo in nuna maka Yadda zakayi amfani da shi”

Harara Naufal Ya watsa mashi”bana buƙata, nima zan Iya dakai na” gabriel na dariya yace”bana so ka yi danasani” miƙewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login