Showing 15001 words to 18000 words out of 250533 words
Chapter 6 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
dukan mu zamu Mutu bayan azabtarwa da zasu Mana.”
Baiwar Allah duk da raɗaɗin da bakinta ke yi mata ahaka ta daure ta cije ta soma Yi mashi magana muryarta araunace daƙyar sautin ma yake fita
“Sun cire min uniform ɗina, Ruwan zamzam din Yana a cikin aljihun wandona bansan Ya zanyi ba” cikin ƙunar rai ta ambaci hakan
“Zanje na ɗauko maki Uniform ɗin ki, cikin minti ɗaya” Yana ambaton hakan ya 6ace ma ganinta.
Yunƙurawa ta yi daƙyar ta miƙe zaune, Ƙarnin Jinin jikinta ya addabi hancinta, bargon da ke shimfiɗe saman gadon ta janyo ta yafa ma jikinta, Zuciyarta acunkushe take da damuwar halin da ƴan uwanta su ke a ciki, Ita ba ta damu da kanta ba, sune damuwarta. Fatanta Allah yasa tsohuwa zafreen bata cutar dasu ba kamar yarda ta faɗa mata.
Durowa Cikin ɗakin salsabeel Yayi hannu shi ruƙe da uniform ɗinta, Jar vest ɗinta da wandon ta Ya miƙa mata su, yatsun hannayen ta na kerma ta kar6e su, Agaban shi ta zura kayan bayan ta kammala sanya su ta zaro ƴar ƙaramar robar zamzam daga cikin aljihun wandonta, Idanuwanta acike tab da ƙwala ta kalle shi tare da cewa”Ta ya ya zan Iya ganin Danish har in bashi ruwan zam zam ɗin”?
“Bamu da isasshen lokaci, A saman bayana zan goya ki in kai ki inda Ya ke kuma zan taimaka maki mu bashi ruwan, ya kai ƙarshen maganar tare da Juya mata baya ya zuƙunna daga bakin gadon, matsowa ta yi tare da kama bayan shi ta haye, Ya yunƙura Ya miƙe, Daga inda ya ke goye da ita Ya 6ace 6att....
Ba su dura a ko’ina ba sai A wani katafaren Ɗaki mai tsawo da faɗi komai na cikin shi launin Ja ne, hatta dogayen labulayen da ke a kewaye dashi red colour ne. wani irin sanyi ne ke ratsa sassan Jiki acikin ɗaki kamar sanyin A.c, daga gani special room ne na kurkukun ƙaddara, Tsadaddun furniture ɗin da ke a cikin ɗakin kaɗai abun kallo ne.
Jin shiru bata motsa daga saman bayan shi ba yasa shi yi mata magana muryarshi cikin raɗa ya furta” Mun ƙaraso, Ki tashi ki ga ɗan uwanki” yanayin yadda ya yi mata maganar ne yasa taji gabanta Faɗuwa shi kanshi Salsabeel ɗin A tsorace Ya ke da abunda zai Biyo baya balle ita kuma da ta ke Ƴar ƙwaruwa wadda bata taka kara ta karya ba. Tsoro ya hana ta ɗago ta kalli inda Danish ɗin Ya ke duk irin kewar shi da ta yi, Sosai ta runtse idanuwanta Hannayenta ƙanƙame da Salsabeel.
“Na faɗa maki bamu da isasshen lokaci ki sauka mana” yai maganar tare da zuƙunnawa don ta sauka, Kamar wadda ƙwai ya fashe mawa akai jiki na kerma ta sauko daga saman bayanshi, sai lokacin ta samu damar Ware idanuwanta sosai Tana ƙarewa ɗakin kallo tun daga kan labulayen dake a cikin shi har zuwa kan shimfiɗaɗen Carpet ɗin dake a ƙasa Ga wani ƙayataccen table mai ɗauke da Dinner set, plate ta gani na tangaran mai ɗauke da kayan marmari, ga wani apple da aka datsi saman shi, hada sawun haƙoran mutun, Ga wani glass cup mai ɗauke da wani abu acikinsa ruwane amma launin shi yayi bright red kamar an surkashi da wani abu. Duk fa wannan kalle kalle da ta ke yi ba ta yi tozali da shi ba, saboda ta hana idonta kaiwa gare shi, Har sai da Sabsabeel yai mata gyaran murya tukunna ta soma Juyar da ƙwayar idanuwanta a hankali ta ɗaura su kan katafaren king sized bed ɗin da ke kafe a cikin ɗakin, Gado ne irin na sarakuna launin shi Golden Colour an shimfiɗe shi da lallausan Bedsheet launin Ja, slowly ta sauke idonta akan dogayen ƙafafuwanshi wa’iya zubilla tsabar ruɗu yasa ta dabarbarce saboda ta kasa yadda cewa shine, Halittar Jikin shi gaba ɗaya ta canza, Ya zama jibgegen ƙato, Samun Namiji mai irin ƙirar ƙarfin shi zaiyi wuya, ƙira ce mai matuƙar tsoratarwa, rikitarwa da kuma jan hankali, Ga dukkan alamu bacci ya ke yi a giant ɗin ma bai bar halin shi na yin bacci ba, Dogon wandone Baƙi A jikin shi, Sai Jar t shirt ta matse jikin shi, ta bayyana ainihin surar shi, musamman damtsen hannayen shi tamkar zasu fasa rigar saboda tsabar ƙarfi.
Sun canza shi sosai Farar fatar wuyan shi hada zanen tattoo launin baƙi da Ja wanda ya kasance Tambarin kurkukun ƙaddara ne duk wani Giant yana da Zanan a wuyan shi, sun rage mashi tsayin sumar kanshi, Anyi mashi kitson zane guda shida, wutsiyar kitson ta sauka har saman Broad-shoulders ɗin shi, Ya koma kamar ƴan iskan turawan nan, waɗanda tun daga suffarsu zaka shaida cewa, ba bu Ɗigon Imani A zuciyar su.
Zafafan hawaye ne su ka wanke fuskarta a yayin da ta ke ƙare mashi kallo, Ta gaza yarda da abunda idanuwanta su ke Nuna mata, Wai Danish ɗinta ne Ya koma haka? Hankalin shi kwance ya ke sharar bacci babu alamun damuwa atattare da shi, duk irin kewar shi da ta yi shi baisan ma da zaman ta ba balle sauran ƴan uwan shi, saboda zalunci na mutanan nan sun rabasu da ɗan uwansu.
Cikin shessheƙar Kuka Ta furta Sunan shi”Da..Nish..” walking nervously ta nufi bakin gadon ta zauna daga gefe tana ƙare mashi kallo, Ya yi wani irin haske mai kyan gaske, tsabar kyan fuskarshi tamkar zai kashe mata ido, la66ansa sun yi jawur dasu kamar na Jinjiri, Dogon hancin shi ya tafi tsaye ba lanƙwasa, kwarin idon shi ta zuba ma ido, dogayen eye lashes dinshi masu kyau da tsari.
“Don’t waste Our time! Mintuna kaɗan suka rage mana,” Muryar Salsabeel ce ta fargar da ita, Ji ta ke kamar ta faɗa mashi ta rungume shi a jikinta ko ta samu sassauci a cikin zuciyarta.
Matsawa kusa da ita sabsabeel yai “Ki buɗe murfin robar, Ni zan hau saman gadon In ruƙe shi gudun kada ya farka ya ham6are ki, naushin giant yana da haɗari sosai Bugu ɗaya su ke Yiwa mutun ya mutu In ba wani iko na Allah ba’ Wannan maganar da ya yi ta ɗaga mata hankali, ta ƙara jin tsoron shi.
Yatsun hannunta na kerma ta soma ƙoƙarin buɗe murfin, tana dab da zata Ƙarasa cire shi, Kamar An ce ta kalli fuskarshi taga ƙwayar idon shi na motsi ta saman kwarin idon shi, da ƙarfi ta furta”Ya farka”
Sautin miryarta ne ya daki dodon kunnanshi, Aiko kamar an zungure shi Ya ware manyan idanuwanshi launin russet brown akan fuskarta, wani irin ƙwar jini yai mata a furguce Ta miƙe daga gefen gadon Tana ja da baya, idanuwanta azazzare, Salsabeel da ke yunƙurin ruƙe kafaɗun shi don Ya hana shi miƙewa A zafafe Yai wurgi dashi tun daga saman gadon Ya ƙundumo ƙasa Ji ka ke tummm, Hankalin Angel fa ya ƙara tashi ganin yarda ya jefar da babban mutun kamar Salsabeel yadda kasan kallon tamola haka ya jefar dashi wanda a haife salsabeel zai Iya haifarshi, Durowa yai daga saman gadon Yana huci Kamar mayunwacin zaki, breast ɗin shi har motsi su Ke yi, Wani matsiyacin kallo da taga yana binta dashi yasa ta haɗiyi yawu mai zafin gaske, kallon da Danish ke yi mata kamar ma baisan wace ce ita ba, Tunkararta Ya soma yi Yana gurnani har wani jijjiga jikin shi ya ke yi, babban abunda ta ke ji ma tsoro kada Ya rikiɗa Ya canza halitta don ta fahimci abinda ya ke shirin Yi kenan, Juyawa ta yi da gudu tana neman inda zata 6oye kanta don kada ya cimmata, saida ta gama shan wahalar kewaye ɗakin Kwatsam taga Ya bayyana agabanta. Ɗagowa ta yi a tsananin tsorace ta ke kallon shi tana girgiza mashi kai haɗi da marairaice mashi fuska don Yaji tausayin ta amma ina ai ko kallo arziƙi bata ishe shi ba, Muryar Salsabeel ce ta karaɗe kunnuwanta a kausasace ya ke bata Umarnin ta gudu daga gabanshi kada ta bari ya Damƙe ta.
kafin ta yi yunƙurin Canza hanya Cikin rashin sa’a ta ji Ya damƙi qugunta Kamar ɗiyar roba Ya ɗaga ta sama Muddin kuwa Ya bugata da kasa sai qugunta Ya 6alle saboda ƙarfin dake gare shi bana Mutun bane na baƙin shaiɗanin aljani ne, Yana ƙoƙari makata Da ƙasa Salsabeel ya cimma shi Gaba ɗaya yai wurgi da ita ƙasa ta kife robar zamzam ɗin da ke a hannunta tuni ta gangara ƙarƙashin table ɗin da ke a ɗakin gashi murfinta ya fara zamewa zai cire saboda buɗeshin da ta fara Yi, ruwan da bai wuce Kur6a ɗaya ba Ya kare idan ya zube shikenan sun rasa damar da su ke da ita.
Faɗane ya kaure a tsakanin Salsabeel tsohon ƙashi da Danish garkuwar kurkuku, Yadda Danish Ya ɗaga salsabeel Ya buga shi da kasa ba ƙaramin gigita Angel yai ba, lamarin ya tsoratar da ita babban abunda take jima tsoro kada Ya kashe shi da bugu, da ko ta shiga uku, ƙarfi ba ɗaya ba Danish ya zarce salsabeel Nesa ba kusa ba saboda shi matsayin babban giant ke gare shi masu haɗarin gaske, Salsabeel Kuwa Ko star ɗaya bai da ita a muƙamin Giant, ta inda Allah ya taimake shi ƙwarewar da ya samu A fannin sarrafa tsafi, ba don haka ba da tuni Danish ya jima da karkarya ƙasusuwan jikin shi, Bugun da ya ke yi mashi da ace Lafiyayyan mutun ya yi mashi wanda baida sihiri a jikin shi da tun a bugun farkon, ga6o6in jikin shi zasu daina aiki.
Ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji daɗi faɗansu ya yi matuƙar ta6a ƙwaƙwalwarta, Ku ka ta dinga yi hannayenta daddafe da kanta, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya farmata, muryar Salsabeel taji a raunace ya ke faɗa mata ta ɗauko zam zam ɗin, da sauri ta rarrafa ta nufi table ɗin har ta kusa ƙarasawa Taji an Janyo ƙafarta da ƙarfi Yai wurgi da ita gefe ɗaya har saida kanta ya bugu da bango tsabar raɗadi Yasa nan ta ke ta sume. Sai faman huci ya ke yi yana gurnani, gaba ɗaya ya gama naƙasa ƙwarin gwiwarsu , shi kanshi Salsabeel Yana durƙushe ƙasa kanshi Ya bugu sosai ga6o6in jikinsa sun rauna, akan idon shi Danish Ya jefar da table ɗin da ƙafarshi, Kayan marmarin da ke asaman shi duk su ka tarwatse ƙasa, Ashe yana sane da robar Zam Zam ɗin hannunta, Kafarshi Ya ɗaga da niyar ya ta ke ta don ta fashe, A kiɗime Salsabeel Ya fasa ƙara tare da Miƙewa Yana jan kafarshi Ya nufi Danish.
Shu’umin murmushi ne Ya bayyana akan fuskar shi hada juyowa ya kalli Fuskar Salsabeel Ya ɗaga mashi gira muryarshi tamkar ta mashayin giya ya furta”What?”
“Kada ka fasa ta na roƙe ka ko dan saboda ƙaunar da ke a tsakanina da kai danish, Nifa ne Ya yan ka, Yau da hannun ka ka ke buguna kamar zaka kashe ni? Sai ka ce baka sanni ba? Laifin me muka aikata maka? Kalli kaga yadda ka Bugi ƴar uwarki Angel kamanta irin ƙaunar da ke atsakaninka da ita”? Ta6e la66ansa yai”who is she”? Tambayar daya jefa mashi kenan
Muryar Salsabeel tamkar zai fashe da ku ka Ya ce “Ka kalle ta da kyau yar uwarka ce Angel, Ba ka yi kewarta ba? Idan bazan manta ba lokacin da ka ke rashin lafiya saboda matsalar da idon ka ya samu sunanta ka ke faɗi acikin sambatun ka ko ka manta ne”? Kwa6e fuskarshi yai Alamar bai tuna komai ba.
Salsabeel sai Jan hankalin shi ya ke yi da surutu A yayin da ya ke tunkararshi duk don ya samu damar ɗauke robar zamzam ɗin da ya ke Yunƙurin fasawa.
“you’re trying to deceive me” Danish Na ambaton hakan Ya dire ƙafarshi saman robar, kukan Kura Salsabeel Yai tare da cakumar Wuyan shi Da iya ƙarfin shi na ƙarshe Ya daddage Ya janye Danish gefe ɗaya, A gaban robar Sabsabeel Ya zuƙunna Yana Kallon Yadda ruwan Cikin ta ya tsiyaye ƙasa, Tsabar takai Ci yasa shi Fashewa da kuka kamar ƙaramin Yaro, ƙululun baƙin ciki ne ya addabi zuciyar shi, Damar da su ke da Ita ta ƙare, zaiyi wuya su tsira.
Jikin Salsabeel na tsuma Ya yunƙura tare da miƙewa Ya ɗaura idanuwanshi akan Bayan Danish wanda ke ƙoƙarin Tunkarar Angel don Ya ƙarasa kasheta, A hankali ya ɗaura yatsun hannun shi saman rigar jikin shi ta kakin Giant, For the fast time da yai nufin bayyana ainihin suffar shi, Cire Rigar jikin shi yai tare da jefar da ita ƙasa, Faffaɗan ƙirjine dashi Irin na sadaukan Ya ƙi, 6an6are mask ɗin da ke akan fuskarshi Yai tare da jefar dashi saman rigarshi.
Namijin Duniya Kyakkyawan gaske, fatar jikin shi Jawur ta ke, Ya fito a baturen shi, Idan ka kalli fuskar shi ba za ka ta6a yarda cewa shi jinin tsohuwa Tamira ne, saboda ita mummunace tsufa Ya 6oye kyanta.
“Na bika ta lalama ka ƙi banin haɗin kai yan zu zan yi maka ta tsiya, Danish ko ni ko kai A yau ɗin nan” Jin miryarshi yasa Danish dakatawa da yin tafiyar, cikin Takun Qasaita Ya waiwayo yana kallon shi, ganin ya tu6e rigarshi yasa ya fahimci shirin faɗa Ya yi, jijjiga jikin shi yai nan ta ke ya rikiɗa ya koma Jibgegen zaki ƙosasshen gaske sai gurnani ya ke yi yana wage bakin shi.
Hankalin Salsabeel Yai matuƙar tashi ganin ya rikiɗa, saboda shi sihirin shi bai kai ƙarfin da zai Iya rikiɗa ya canza halitta ba, ganin yadda ya ke tunkaro shi a fusace Yasa shi ja da baya ya soma tunanin me yakamata yayi don Ya dakatar dashi, idan ba haka ba A kashe zai kashe shi har lahira.
Waige waige ya dinga yi yana bin ɗakin da kallo har idon shi ya sauka akan Wuƙar yanka kayan marmarin da ke yashe saman floor, Ba zai iya ɗaukarta ba don bai son Ya cutar dashi, Lallashinshi ya soma yi yana faɗin”Am sorry Danish ni ba faɗa zanyi da kai ba, Pls ka saurare ni Danish dan Allah ka canza halittarka zuwa ta mutane ina son yin magana da kai.....” Magiya ya dinga yi mashi amma ɗan tahalikin nan yaƙi sauraron shi, Juyawa yai da gudu ya nufi saman gadon ɗakin Ya daka Uban tsalle Ya haye saman shi tare da sanya hannu ya rarumo bargon dake nannaɗe saman shi, dai dai lokacin da Danish Yai kukan kura Ya daka tsalle da suffar Zaki Zai kai mashi hari Yai saurin Rufe shi Da bargon Ya nannaɗe shi a ciki, Allah ne ya taimake shi Ya bashi ƙarfin da shi kanshi yasan bana shi bane, a saman floor suka faɗo, Sosai Ya matse Danish Acikin bargon, ruƙo bana wasa ba kamar zai kashe shi, tun yana jin sautin gurnanin shi har ta kai ga yai shiru babu motsi alamar ya suma.
Tsabar farin Ciki yasa shi sakin dariya yayin da hawaye ke bin fuskarshi, tunawa da lokacin su da ke shirin ƙarewa saura Mintuna 30 ya rage masu kacal, A hanzarce Ya zame bargon da ya lullu6e shi a ciki, har ya koma suffar shi ta mutane a ƙasa ya kwantar dashi, Miƙewa Salsabeel yai da sauri ya nufi robar zam zam ɗin da ya tsiyaye, Ya ɗauko ta a tsakiyar tafin hannun shi ya dawo ya zuƙunna agaban Danish, a hankali ya buɗe mashi ƙaramin bakin shi ya dinga matsar robar ta ƙarfi kamar zaiyi hauka daƙyar ya samu ɗigon Ruwan Ya faɗa bakin shi, Ɗigo ɗaya kacal, Gani ya ke kamar ba zai isa ya dawo hayyacin shi ba, hakan yasa shi cigaba da matsa robar duk don ya samu ruwan ya ƙara ɗigowa a ƙarshe da ya gaji ya jefar da robar ƙasa, ya dafe kanshi da hannu biyu zuciyar shi na harbawa da matsanancin sauri.
faɗuwar da gaban shi ke yi ya tabbatar mashi da cewa wani mummunan abu na faru da wani nashi ko dai mahaifiyar shi, ko kuwa yaran da ya ke ƙoƙarin taimakon rayuwar su, Miƙewa yai a zabure Jiki ba ƙwari ya nufi Angel da ke yashe ƙasa tun ɗazu da Danish ya jefar da ita ta sume bata ƙara motsi ba, hannu biyu ya sanya tare da ɗaukar ta, Ya dawo ita gefen Danish Ya kwantar da ita, kafin ya ƙara miƙewa Ya nufi Kayan saman table da Danish Ya watsar dasu ƙasa, A cikinsu ya samu robar ruwa, ya ɗaukota tare da dawo wa gaban su Ya zuƙunna yana faman fitar da huci Shi kanshi a raunace ya ke daurewa kawai ya ke yi duk don ya samu ya ƙarasa taimakon su.
A Saman fuskar Angel Ya watsa ruwan a Firgice ta farka haɗi da miƙewa tsaye tana Faman zazzare idanuwanta fuskarnan jawur ta kumbura suntum.
“Unaisah” Cikin sanyin murya Salsabeel ya ambaci sunanta ko da ta kalle shi a tsoroce Ta furta”wanene kai”! Ras Ya ji gaban shi ya faɗi, Can kuma sai ya tuna da fuskarshi daya cire, shiyasa bata gane shi ba.
“Salsabeel ne” kallon shi ta dinga yi kamar yau ta fara ganin shi, ita kanta ba haka ta yi tsammanin zata ga fuskarshi ba.
“Ga ɗan uwan ki nan, Na yi ƙoƙarin ɗiga mashi ruwan zamzam ɗin sau ɗaya abakin shi bansani ba ko zai farka acikin hayyacin shi ko kuwa akasin hakan, Ba zan Iya jiran farfaɗowarshi ba, hankalina ba akwance yake ba, Ina tsoron wani abu ya sami mahaifiyata Don haka zan tafi wurin ƴan uwanki nasan tana atare dasu” Angel na ƙoƙarin buɗe ba ki tace mashi ya tafi da ita kada yabarta anan gudun kada Danish ya farka a matsayin Giant ya kasheta sai dai kash kafin tayi maganar Salsabeel tuni ya 6ace ma ganin ta...
A 6angaren Su tsohuwa zafreen kuwa Dambe su ka yi bana wasa ba, Saboda tsabar zalunci sai da ta cire mata kunnuwanta duka biyun ta cinye su, Jini duk ya wanke jikin tsohuwa tamira, duk yadda taso ta ƙwaci kanta ta kasa saboda rashin ƙwarin Jikinta, har sai da zafreen ta kwantar da ita ƙasa ta dinga buga kanta Ga ƙasa tuntuna motsi har ta kai sumewa.
Mahaukaciyar dariya zafreen ta saki ganin ta