Showing 18001 words to 21000 words out of 250533 words
Chapter 7 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
yi nasara akanta, Faɗa da aljani ba riba maganar da zafreen ta furta a yayin da take miƙewa ta nufi wuƙar da batul ta yi amfani wurin yi mata Illah, Jinin da ke a jikin wuƙar ta lashe kafin ta juyo ta dawo kan tsohuwa Tamira, Ta zuƙunna tana Shafa Jikinta da tsinin wuƙar”Na jiye maki baƙin Ciki, domin kuwa ayanzu ɗin nan zar farke Cikin ki, In kwashe ƴan hanjin dake a cikin ki In cinye su, idan kin isa Ki kwaci Kanki, ƙazamar banza har ni za ki kalli idona Ki gaya mini magana kamar bakisan wacece ni ba.....” ta ambaci hakan tana mai sakin murmushi
Yunƙurin caka mata wuƙar ta yi ba zato ba tsammani taji an buge kanta da wani abu mai nauyin gaske tamkar dutse kafin ta yi yunƙurin juyawa don taga wanene taji an ƙara buga mata shi akanta, nan ta ke kanta ya juye Ta kife ƙasa,.
Batul ce a tsaye Tana haki, Hannunta ruƙe da sandar Zafreen da ta jefar ƙasa, ƙarfin sihirin da ke a jikin sandar ne yasa har ta yi nasarar kwaɗeta da ita, daddagewa tayi da ƙarfi taci gaba da buga mata sandar, Jijiyoyin wuyan ta duk sun furfuto waje saboda tsabar 6acin rai, babu sassauci atattare da ita tun tsohuwa zafreen na motsi har ta kai ga idanuwanta sun Juye, Jefar da sandar Batul ta yi ƙasa tare da ɗaukar wuƙar da zafreen ɗin ta jefar, Saman ruwan cikinta ta haye ta daddage ta dinga luma mata wuƙar Jini yadin ga ambaliya kamar an kunna fanfo harta saman fuskarta, Kacaca tayi mata sai da ta farketa, A ƙarshe dai Baful ta yi nasarar kashe tsohuwa Zafreen ko shura wa ba ta yi ba nan ta ke rai yai halin shi, harta mutu batul bata daina farke jikinta da wuƙar ba, saboda bata acikin hayyacinta, kuka ta ke yi tamkar ana zare ranta.
Farfaɗowa tsohuwa Tamira ta yi a hankali ta buɗe idanuwanta da suka ruƙida su ka yi jawur dasu, ta wurga su kan Batul da ke a zaune saman Zafreen tana aikin fiɗa.
Muryarta na rawa ta ambaci sunanta”Ba..tul..” Sai lokacin ta jefar da wuƙar hannunta, jiki na rawa ta sauko daga saman jikin zafreen ta rarrafo Zuwa gaban tsohuwa Tamira.
Fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina, taci gaba da yin kuka tana faɗin”Ta zalunce mu ba mu yi mata laifin komai ba, ta kashe mana ƴan uwan mu ta gama da rayuwar mu.....”
Hannun tsohuwa na kerma ta ɗaura shi saman sumar kan Batul da ke a tarwatse daƙyar take iya yi mata magana”Batul babu wasu kalmomi da zan iya yin amfani dasu wurin baku haƙuri akan irin jarabtar rayuwar da kuka fuskanta, Ku yi haƙuri kuyi haƙuri Allah yana atare da ku.......” Da numfashinta na ƙarshe ta ƙarasa maganar nan ta ke rai yai halin shi, A matuƙar kiɗime Batul ke Fuskarta.........
*Boss Bature✍️ Mu haɗu Gobe Idan Allah Ya kai mu da rai da lafiya don jin yadda zata Kaya Game son cigaban littafin kurkukun ƙaddara 500 ne zai tura ta acct number dina Ga bank details da za ki tura kuɗin*
First bank
3196407426,
*Bature Hafsat Muhammad, za’a tura evidence of payment ta phone number ɗina 08103884440, Banda kira whatsapp kawai*
_~*BossLadiesWriters*~_
_*KURKUKUN ƘADDARA*_
_The Prisoners E4🔥💫_
*Daga alƙalamin Hafsat Bature*
~Middle step~
_A heart-wrenching story of love, romance, and redemption, set against a backdrop of betrayal and cruelty💔._
wani sabon kukan ne ta kuma fashewa dashi ga matsanancin ciwon kai da ya takura mata, saboda tsabar kuka shatun jijiyoyin wuyanta sun fito ruɗu ruɗu kamar zasu fasa fatarta, hatta saman fore head ɗinta jijiyoyin ne....
A 6angaren su Haris kuwa da ke a cikin ɗaki, tun suna kuka har sun fidda rai da ƴan uwan su zasu rayu, Tun suna iya jiyo sautin shessheƙar kukansu har ta kai ga yanzu basu Iya jin komai, A bakin ƙofar ɗakin tsohuwa Tamira suka zuzzuƙuna, Zuciyoyin na tafarfasa Gabriel yasha kuka Idanuwanshi har sun ƙafe, Haka zalika Naufal da javed babu sauran mai walwala akan fuskokin su, Mubeen kuwa Dama ba ƙoshin lafiya ce da shi ba tun lokacin da aka dawo dashi kamar mutun mutumi ko magana bai Iya yi, Daƙyar ne yai tsawaicin kwana.
A firgice su ka ɗago Da idanuwan su Jin Dirar mutun a Cikin ɗakin su, jiki na kerma suka miƙe suna kallon shi ba su san wanene shi ba, ganin su da Salsabeel ya yi ba ƙaramin karya mashi zuciya su ka yi ba, tausayin su ne ya kama shi, Cikin sanyin murya ya soma yi masu magana.
“Ku kwantar da hankalin ku, Ba cutar da ku nazo yi ba, Nima ɗan uwan ku ne nasan ba ku ta6a gani na ba, Sunana Salsabeel Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira”! Duk da basa acikin hayyacin su sai da suka zazzaro idonsu akan fuskarshi.
Cikin shessheƙar kuka Haris yace”ƴan..uwan mu suna a cikin ɗakin tsohuwa Tamira, Zafreen Ta kashe mana su, Muna jin sautin kukan su sai dai mun gaza ceton su saboda ta datse ƙofar.....” tun kan ya kai ƙarshen maganar, Salsabeel Ya wuce da wani irin sauri Ya sanya hannu Ya daki Jikin ƙofar Nan ta ke ƙofar Ta buɗe.
A fujajen Ya faɗa Cikin Ɗakin Hankalin shi a matuƙar tashe Ya ke binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, tun daga kan su azeeza dake kwance cikin Jini saman gadon Tamira har izuwa kan su Parveen da ke a sume ƙasa Babu kaya a jikinsu, Ga Uniform ɗin su yashe a kasa da ta Cire masu, Da ƙarfi Ya ambaci kalmar Inna lillahi wa’inna ilaihirraji”un runtse idon shi yai sosai tare da bugun iska da hannun shi daya dunƙule, Tsabar ƙunar da zuciyar shi ke yi mashi zafinta tamkar zai fasa ƙirjin shi, Zafafan hawaye ne su ka soma wanke fuskarshi Kamar ya haɗiyi zuciya ya mutu haka ya ke Ji.
“Ya Allah ka ɗauki raina In huta Idan ba haka ba zan kashe kaina ne” Muryar Batul ce ta janyo hankalin shi ga Kallonta, wa’iya zubillah Wani mugun bugu Zuciyar shi ta yi ganin mahaifiyar shi kwance cikin Jini, Kunnuwanta Biyu babu su Ga kuma gawar tsohuwa Zafreen A can gefe ɗaya, tangal tangal yai kamar zai kife ƙasa Da sauri ya tsayar da kan shi Yana faman fitar da huci mai ɗumin gaske, Ba dan Zuciyar Imani ba wlh da ɗaya daga cikinsu baƙin ciki ba zai bari Ya rayu ba. Daga Salsabeel ɗin har su Haris Allah ne bai nufa zuciyar su zata buga ba, Amma tashin hankalin da su ka fuskanta a wannan baƙar ranar baya misaltuwa. Batul sam bata lura da shi ba, Ta zama mahaukaciyar ƙarfi da ya ji kamar ma ta zauce, Agaban gawar mahaifiyarshi ya zuƙunna cikin rauni na murya ya furta”ya za ki yi mini haka mommy na? Meyasa za ki mutu ba tare da mun cimma burin mu ba, why ki ka tafi ki ka barni ni kaɗai a cikin wannan Duniyar mai cike da ruɗani”? Daƙyar ya ke iya furta maganar, cikin rauni na murya yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman kuncin sa, tun da ya soma magana Batul ta ɗago da runannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu ta ƙura su akan fuskarshi ba ta Iya gane wanene ba saboda batasan shi ba, A halin da ta ke a ciki bata Iya Fahimtar Kalaman shi.
“Hada kai Aka kashe min Ƴan uwana ko! Kai ne ka kashe su wlh kaine”! ɗago wa yai tare da kallonta, Kafin yai yunƙurin furta magana, Batul ta daddage ta Haye saman jikinshi tare da dunƙule hannunta tadinga kai mashi bugu ta ko’ina tana faɗin Mugaye azzalumai wlh ba zamu ta6a yafe ma ku ba, Kun cutar da rayuwar mu, kun kashe mana ƴan uwa, wai laifin me muka aikata ma ku ne....? bata ƙarasa maganar ba kuka Yaci ƙarfinta, Rashin sani yafi dare duhu, sam bai ji komai da abunda ta yi mashi saboda hankalin shi ba akanta Ya ke ba, Yana akan gawar mahaifiyar shi, Bawan Allah Ya ji mutuwarta Fiye da tunanin mai tunani, Ya yi danasanin irin rayuwar da su ka ɗaukarwa kansu yanzu gashi ta mutu tana aikata sa6on Allah, Sai dai shi Allah gafurirrahim ne mai rahama mai Jin ƙai, Maganar su ta ƙarshe ya soma tariyo acikin kanshi.
“Salsabeel ko bayan ba raina inason yaran nan su ku6uta daga KURKUKUN ƘADDARA! Ka yi min alƙawarin nan, ka taimaka masu ko dan su isar da saƙon mu zuwa ga mutanan duniya, Bana so acigaba da aikata zalunci agidan kurkukun nan Ina mai jin takaici da baƙin Cikin ganin yadda ake tauye wa ƙananun yara haƙƙinsu na rayuwa, basu ji ba basu gani ba, An hana su more rayuwar su ta duniya, Ana kashe masu rayuwa a lalatasu A ƙasƙantar dasu kamar dabbo bi, sannan a kashe su, kuma su mutu a wulaƙance! Ka faɗa min Laifin me suka aikata da su ka cancanci Yin irin wannan rayuwar? Idan har kana so In yi alfahari da kai a matsayin ka na Jini na to ka cika min burina, Bana so Ganin mutuwa ta yasa zuciyarka ta raunata nafi so a lokacin da ka yi tozali da gawata ka ƙara Jin ƙwarin gwiwar aiwatar da umarnin da na baka, idan mutuwa ta risƙe ni a gidan kurkukun nan bana so kabar gangar jikina a gidan kurkukun ƙaddara Ka yi nesa dani kafin ka binne ni.........” lokacin da tsohuwa Tamira ta yi mashi maganar sosai ya fashe mata da kuka yana faɗin zai yi duk abunda take so amma tadaina maganar zata mutu, ya ta ke so ya yi da rayuwar shi? Bashi da kowa a duniyar nan bayan ita, murmushi ta yi tare da ce mashi Kana da Allah sannan bayan shi ga ƴan uwanka nan suma basu da gatan daya wuce Allah da kuma kai, Don haka ka daina tunanin cewa sai da ni zaka Iya aiwatar da komai. Ni dai fatana Ku tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara, Azzaluman shuwagabannin da suka ƙirƙire shi ku tabbatar tun agidan duniya sun ɗanɗani kuɗarsu kafin su koma ga mahaliccin su bana so kubar hukuma ta hukunta su saboda duniyar nan acike take da marasa gaskiya idan kunga ba zasu baku goyan baya ba ku yi amfani da ƙarfin ikon da ku ke dashi wurin yi masu mummunan kisan da sai sun yi danasanin haihuwarsu da uwarsu tayi acikin duniyar nan, Kafin su mutu ku Azabtar dasu ta yadda zasu manta da duk wani jin daɗi da su ka yi a duniya, Idan har ku ka yi min hakan to zan jin daɗi, zan yi kuma alfahari da ku, Bayan ta yi mashi wannan maganar salsabeel yana kuka ya roƙe ta alfarma ɗaya kafin faruwar duk waɗannan abubuwan yace mata yana so ta kar6i musulunci akaro na biyu ta yi imani da Allah, Numfasawa tayi tare da ce mashi”Ba zai yiwu ba saboda Allah ba zai ta6a kar6ar tubanta ba ko da ta musulunci saboda ɗumbin zunubban da ta aikata sun yi muni sosai, Salsabeel ya yi ƙoƙarin fahimtar da ita ta hanyar Yi mata nasiha ya nuna mata cewa shi Allah gafurirrahim ne yana son bayinsa waɗanda su ka aikata zunubi suka gane kuskuran su kuma su ka tuba zuwa gare shi, daƙyar ya samu tsohuwa Tamira ta sake kar6ar shahada maganarsu ta ƙarshe data furta mashi”Zan je wurin Yaran can inaji araina wani abu yana faru a ɗakin su, Kafin na isa wurin su inaso ka yi gaggawar zuwa Ɗakin Madubin sihiri Ka canza ganin su ta yadda ba zasu fahimci abunda ke faruwa ba......wannan itace magana ta ƙarshe da tsohuwa tamira ta furta mashi kafin tabar wurin shi, akan hanyar shi ta zuwa ɗakin madubin sihiri Ya ga duk wani abu da ya faru da Angel kun ji yadda akai har yaje gare ta.
Cakumar Batul ya yi da hannun shi tare da janyota ta dawo saman faffaɗan ƙirjin shi, Rungumeta yayi da hannayenshi tamkar zai mayar da ita cikinshi, Hakan da yayi mata ne yasa ta sassauta kukan nata......
Tsoro da fargaban abunda idanuwansu zasu nuna masu ya hana su shiga Cikin ɗakin, Bayin Allah suna atsaitsaye Bakin ƙofar suna sauraron gunjin kukan da Batul ta ke yi.
Idan mu ka koma 6angaren Angel kuwa tun bayan tafiyar Salsabeel tana zaune cikin matsanancin tashin hankali, Da fargaban farfaɗowar Danish, Ba zato ba tsammani ta ga yatsun ƙafarshi na motsi, A gigice ta yunkura da niyar ta miƙe Sai dai kash ƙafarta ta ƙi bata haɗin kai, Wani irin tsami ta yi mata, a tsananin tsoroce take ja da baya tana kallon shi jikinta nata 6ari
A hankali Ya ware kyawawan idanuwanshi Akan ceilling ɗin ɗakin na tsawon daƙiƙa talatin kafin Ya yunƙura ya miƙe zaune.... Ta wutsiyar idon shi ya ke hango kamar mutun na motsi, hakan yasa shi yin saurin kai idon shi gare ta, unexpected idanuwan shi su ka sauka acikin nata, da wani irin kallo ya ke bin ta da shi, gani ta ke yi kamar bai dawo hayyacin shi ba.
Ya kasa tantance wacece ita? Saboda daskararren jinin da ke a jikinta, ta koma mashi kamar aljanna, ranta ne ya bata cewar ko dai ya dawo hayyacin shi? Wata’ƙil saboda munin da ta yi ne yasa bai gane ta ba, Cikin jin shakkar shi muryarta na kerma ta ambaci sunan shi”Da..nish..its me ur Angel” Ware fareren idanuwan shi yai sosai akan fuskarta, jin muryar da ya daɗe yana mararinta, ba zai ta6a mantawa da muryarta ba, A ruɗe ya motsa la66ansa tare da furta sunanta”Angel? Is that you”? Ita kanta batasan ya akai ta iya miƙewa ba, Tsabar farin Ciki da gudu ta nufe shi tana ƙarasawa gaban shi slowly ta zube saman gwiwowinta tare da faɗawa saman faffaɗan ƙirjinshi sosai ta rungume shi tana ku ka, Bai damu da ƙarnin jinin da ke a jikinta ba, sai dai zuciyar shi ta rikice ya shiga ruɗanin ganin canzawar da ta yi, Jikinta duk raunuka ta yi muni kamar ba Angel ɗinsa ba, Tunawa da Ƴan uwanta da kuma ƙurarren lokacin da ke gare su yasa tace mashi”Ka tashi mu tafi Danish ka kaini ɗaki, na bar su Azeeza suna jiran mu” shiru bai motsawa ba saboda ya rasa tunanin shi.
Bugun bayan shi ta dinga yi da hannunta Cikin shessheƙar ku ka ta ke faɗa mashi Ya tashi ya ɗauke ta suje ɗaki ƴan uwan su na acikin haɗari, “ daƙyar ta samu Danish Ya miƙe ɗauke da ita saman faffaɗar kafaɗar shi, daga ina ya ke a tsaye Ya 6ace bai dura a ko’ina ba sai A cikin ɗakin su, Tunkan ya sauke ta ta riga zame jikinta, Su Haris da ke a tsaye bakin ƙofar ɗakin tsohuwa, a ruɗe su ke kallon shi Musamman Gabriel yasha ruwan mamakin ganin Danish da idon shi Garas.
Muryar Angel na rawa ta soma ambaton sunayen su”Ha..ris..Mubeen..Naufal..Javed..”! akace labarin zuciya a tambayi fuska, Tun kan ma su yi mata bayanin abunda ya faru da gudu ta faɗa cikin ɗakin tsohuwa Tamira da ke a buɗe, Idanuwanta Azazzare take kallon Ƴan uwanta dake kwance ƙasa ba numfashi, Wata irin gigitacciyar ƙara ta saki ta fitar hayyaci wadda tayi silar faɗowar Danish dasu Haris cikin ɗakin sai lokacin su ka ga mummunan abunda tsohuwa zafreen ta aikata ma ƴan uwan su. Silar ƙarar da Angel ta fasa ne yasa Batul raba jikinta daga na salsabeel fuskarta jaga jaga da hawaye ta ɗago idanuwanta, tana yin tozali da Angel da gudu ta nufota tare da faɗawa saman ƙirjin ta suka ƙanƙame juna suna yin kukun zuci, Cikin shessheƙar kuka Batul ta labarta mata duk abunda ya faru bayan tafiyarta, Tasha kuka kamar ba gobe, ta yi fatan ace dukkan su ne suka mutu hada ita, gaba daya shirin su ya tarwatse taya zasu iya barin kurkuku Bayan ƴan uwansu duk sun mutu, Alƙawarin data ɗaukar masu bata samu cika shi ba, Ga danish ɗin ta ci nasarar dawo dashi sai da kash Ta faru ta ƙare, ƙaddara ta riga fata, Cikin raunatacciyar murya ta wanda ya gama sarewa da rayuwar duniya ta furta”Nashiga Uku na bani na lalace! Ya Allah zunubin me muka aikata mu ke fuskantar irin wannan mummunar jarabawar daga gare ka? Idan ba ka son mu, ka ɗauki ran mu mu huta, Mun gaji mun gaji Wayyo Allah na Na rasa Azeeza na rasa jemimah na rasa Deeja da sauran Ƴan uwana, To ni zaman uban me zanyi acikin duniyar nan wlh bazan rayu ba dole in kashe kaina......” Cikin fitar hayyaci ta furta kalaman, kamar mahaukaciya, ta juya da niyar ta je nemo makamin da zata halaka kanta dashi, Cikin zafin Nama Salsabeel Ya damƙi hannunta, tare da juyo da ita ta yadda zata fuskance shi”Meye ribar ki idan kin kashe kan ki? Dama ba sai da na faɗa maki Ba lallaine ku rayu ku dukan ku ba, Yanzu idan kika mutu Kinsan adadin rayukan da za’a cigaba da 6arin jinin su a gidan kurkukun nan? Idan har bamu lallashi zukatan mu ba mun kawo ƙarshen Azzaluman da suka cutar da ƴan uwan mu Duk wani ƙoƙarin mu ya tashi abanza kenan! Ya ku ke so inyi da raina ne? saboda ku na rasa mahaifiyata Ni kaina ashirye nake da in rasa raina in dai akan ku ne, Don haka kada wanda Ya ƙara Yi mana kuka Ya isa haka !! Mutuwa dole ce ko muna so ko bamu so, Kuma mutuwa sauƙi ce agare su saboda rayuwar duniyar bakomai bane acikinta face ruɗani, cike take da ƙalubale iri iri, ni banga amfanin yin kuka don wani ya mutu a cikinmu ba, Saboda Allahn daya halicce su wanda yafi mu sonsu shine ya kar6i abunshi, Sai sunfi jin daɗi fiye da na duniyar nan......’ sosai Salsabeel ya yi masu nasiha har saida yaga sun dawo hayyacin su tukunna Yace dasu babu isasshen lokaci su wuce su tafi, Danish Zai buɗe masu ƙofa, shi zai kula da gawawwakin Ƴan uwansu da suka