Showing 186001 words to 189000 words out of 250533 words
Chapter 63 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
wa ta ta6a yin aure ba, kamar budurwa saboda babu abunda ya canza a jikinta, dama bata ta6a shayarwa ba.
Wani irin kallon so da ƙaunar ƴan uwantaka suke jefa ma juna tsakanin ta da shureim, idanuwan kowannansu ya ciko tab da ƙwalla, La66anshi na kerma ya furta sunan ta”be.. Nazir! Yar uwata rabin raina, Jinin jikina Dagaske ke ce idanuwana suke nuna min? Fashewa tayi da matsanancin kuka, gaba ɗaya ta faɗa saman chest dinshi, ya zagayo da hannayenshi biyu ya rungumeta tamkar zai mayar da ita cikin cikinshi, Zeenatu dake tsaye tana kallonsu hawaye tuni sun wanke fuskarta, tsananin tausayin benazir ne Ya kamata, Fitowa Alhaji ubaid yai daga cikin motar shida Hajiya layla, ya dauki wankan shadda, itama layla Atamfar ce ta sanya sunyi anko da benazir hatta daurin dan kwalinsu da mayafin da ta daura a kafaɗa iri dayane dana benazir, idanuwansu na akan dr shureim da benazir, sun ƙanƙame juna sai kuka sukeyi kamar waɗanda suka rasa mafaɗi a duniya, zagayawa zeeenatu tayi ta 6angaren da su hajiya layla suke koda sukayi arba da ita, Hajiya layla ta buɗe mata hannu da fara’a akan fuskarta take fadin”Zonan My daughter zeenatu” kamar jira take yi da sauri ta ƙarasa ta faɗa jikin Layla, rungumeta tayi sosai, tana dan bubbuga bayanta ta furta”kin ƙara girma daughter, tsawon lokaci bamu haɗu ba, Daddynki Ya hanaki zumunci da ƴan uwanki, baison kina taka wajen mu, gashi mu kuma muna ƙaunarki” ta faɗa tana raba jikinta da na zeenatu, fuskokinsu dauke da annurin farin ciki, kallon Alhaji ubaid tai”sannunku da zuwa daddy” miƙa mata hannu yai da sauri ta ƙarasa gare shi, Yai hugging dinta yana fadin”fatan mun same ku lafiya,” ɗagowa tai da kanta tana fadin”Lafiya lou daddy mu shiga daga ciki”
Drivern daya daukosu Yana daga tsaye ya jingina bayanshi jikin motar, Yace”yalla6ai ku ƙarasa shiga gidan, za’a shigo maku da kayan naku” amsa mashi sukayi da toh, layla tace da su shureim ayi haƙuri adaina kukan ya isa haka mu shiga cikin gidan inyaso kun ƙare kukan naku acan” Alhaji ubaid na murmushi yace”ke ko kibarsu mana, An daɗe ba’a haɗu ba, Jini ɗaya ba wasa ba, mundai godema Allah daya bayyana mana ita da ranta da lafiyarta ubangiji Allah Ya ƙara tsare mana ita, layla da zeenatu suka amsa mashi da ameen,
Gaba suka fara Yi, Ya rage saura zeenatu data ƙura ma benazir da shureim ido.
Ta kwantar da kanta saman kafadarshi, yayin da hawaye masu ɗumi suke cigaba da wanke fuskarta, cikin muryar kuka take fadin”yaya shureim nayi danasanin duk wani abu daya faru arayuwata, wallahi nayi danasani mara amfani, bansan meke damunaba, hakanan na tafi nabar dangina nabar mijina, babban takaicina ƴar jinjirar dana bari cikin jini, na haura ƙafa na tafi nabarta saboda rashin hankali irin nawa, bansan meyasa na aikata hakan ba” cikin jin ƙunar rai ta ƙare maganar.
Ɗaura hannunshi yai saman bayanta cikin rauni na murya ya soma magana”kiyi haƙuri benazir, wallahi ba laifinki bane, ni nasan duk rashin jin maganarki bazaki ta6a iya aikata hakan ba, Ina yi maki kyakkyawar zato, ki kwantar da hankalinki My sister” cikin kwantar da murya yake lallashinta
Shessheƙar kukan zeenatu ne Ya janyo hankalinsu ga kallonta, idanuwanta sunyi luhu luhu, da mamaki akan fuskar benazir ta furta”yaya shureim a ina muka samu kyakkyawar matashiyar baturiya”?
Fuskarshi dauke da murmushi yace”zeenatu ce, nasan ba lallai kisanta ba, saboda ba’ajima da haihuwarta ba ki ka tafi, ɗiyar uncle dinmu ce, ki kalli fuskarta dakyau”
Farin cikine Ya lullu6e benazir, Yarinyar ta burgeta, Gata ƴar kyakkyawa da ita, miƙa mata hannu tai zonan ƴar uwata, Ina fata an fada maki wacece ni, idan ma ba’a sanar dake ba toh nidai sunana benazir, Ƙanwar dr.shureim” fashewa Zeenatu tayi da dariyar farin ciki, Hawaye nabin fuskarta.
“zonan In rungumeki ajikina, Nima yau inji ɗumin ƴar uwata” jiki Na rawa zeenatu ta nufi benazir suka rungume juna kamar zasu koma mutun ɗaya
Cikin shessheƙar kuka Zeenatu take fadin”Aunty benazir munyi kewarki sosai, Mommyna tana bani labarinki, najima ina son ganinki arayuwata, duk da bamu ta6a haɗuwa ba amma kullum idan nayi sallah sai nayi maki addu’a Akan Allah Ya bayyanar mana dake idan kina araye, Idan bakya araye Allah Yajiƙanki yakai rahama agareki, ashe da rabon zamu haɗu....”dakyar ta ƙare maganar saboda kukan daya cimmata, daga ita har benazir din kukan sukeyi, Kalaman zeenatu sunyi matuƙar ta6a mata zuciyata, tayi mamakin irin ƙaunar da take Yi mata, ita da bata ta6a ganinta ba, labarinta kaɗai aka bata, haƙika taji dadi mara misaltuwa, kaunar zeenatu ta shigeta, tayi fatan Ace itama ƴarta data bari tana yi mata addu’a.
“Aunty benazir dan Allah kada ki ƙara tafiya kibarmu, wallahi muna kaunarki nida mommyna” sosai benazir ta fashe da kuka tana fadin”in sha Allah bazan ƙara tafiyaba, nadawo kenan zeenatu, naji dadin kalamanki agareni, ƴar uwata rabin raina”
Dr.shureim Ya natsu yana kallonsu, idanuwanshi sun kaɗa jawur, hawayen dake gangarowa saman kuncinshi sai ƙara ninkuwa sukeyi.
Cikin sanyin murya yace dasu’Mu shiga cikin gidan” amsa mashi sukayi da toh, hannun benazir acikin na zeenatu suka dunguma zuwa babban falon gidan.
Lokacin da suka ƙarasa ciki, Alhaji ubaid da Hajiya layla suna a zaune saman sofa mai mazaunin mutun biyu, a yayin da Hajiya sarah ta zauna saman 3 sita, Alhaji musa yana daga zaune gefenta, kamar kullum fuskarshi babu annuri, kamar wanda akayiwa albishir da ranar mutuwarshi, shaddar jikinshi ta zauna mashi launin blue sky, daddadan kamshin turarenshi Ya karade hancin kowa, Hajiya sarah Lace ne ta sanya kalar shaddarshi, head dinta kalar takalman ƙafarta, sunyi kyau abunsu kamar sabbin ma’aurata
Jin takun tafiyarsu yasa hajiya sarah ta ɗago tana dubansu, wani irin farin cikine ya lullu6eta ganin benazir, Jiki na rawa ta miƙe tana faman sakin fara’a fararen hakoranta tarr dasu ta nufi benazir tana fadin”ashe rai kanga rai? Benazir dagaske kece idanuwana suke nuna min? Wayyo Allahna, Idan ma mafarki nake Yi toh kada atadani abarni in tayi dan Allah” Rungume juna sukayi, Benazir ta fashe da wani sabon kukan bata ta6a tsammanin zata samu kyakkyawar tarba a wurin ahalinta ba, Tabbas sun bata mamaki tayi tunanin kamar yadda ta gudu babu wanda zai saurareta donta dawo gare su.
Hajiya layla sai faman sakin murmushi take Yi ita da Alhaji ubaid hankalinsu na akan Hajiya sarah data rungume benazir, Shi kuwa Alhaji musa ko kallo bata ishe shi ba, tamkar baisan sun shigo falon ba.
“Allah sarki benazir, Ashe da rabon zamu sake ganawa a duniyar nan! Tsawon shekaru sai yau Allah Ya nufa zan ƙara Yin tozali dake” ta fada tana duban benazir da hawaye suka gama wanke fuskarta
Cikin shessheƙar kuka tace”Aunty Sarah nayi danasani, naji haushin kaina, naji na tsani kaina saboda komai ya faru arayuwana laifina ne, tunda nida kaina na gudu na tafi batare da nayi shawara da kowa ba, Dan Allah ku yafe min, nasan na 6ata maku rai”
Idanuwan hajiya sarah tuni sun cicciko tab da ƙwalla, kasancewarta mace mai tausayi.
Cikin karyayyar murya ta furta”dan Allah ki daina fadin hakan, Komai ya riga daya faru kuma ya wuce”
Kafin benazir ta kuma yin magana muryar Alhaji musa ta katse masu hanzarinsu
“Idan kun gama jimamin, ku ƙaraso ku zauna” cikin isa Ya furta hakan, sai lokacin Benazir ta ɗago da ido tana dubanshi, Ya haɗe rai babu annuri sam a fuskarshi, gani take kamar baiyi farin ciki da dawowarta ba.
Ruƙo hannunta Hajiya sara tayi acikin nata, suka ƙarasa tare da samun wuri kowannansu ya zauna, zeenatu da dr shureim suna zaune saman lallausan carpet, Benazir kuma tana agefen hajiya sarah, ta ƙankame hannunta.
A tsanake Alhaji musa Yasoma yin magana batare daya ɗago da ido ba
“Da farko, Inayi maku barka da zuwa, yayana da kuma hajiya layla,’ kwa6e fuska layla tayi aranta tace”dallah jibarshi ɗan rainin wayau”
Numfasawa yai tamkar bayason buɗe baki Ya furta”benazir,” amsa mashi tayi da na’am.
Dawo nan ki zauna” yai maganar yana Nuna saman carpet daga gefen hannun sofa din da yake zaune, jiki asanyaye ta miƙe ta dawo inda ya bata umarni ta zauna.
Kowa ya natsu yana jiran jin me Alhaji musa zaice da ita.
“Meyasa kika gudu daga gidan auranki har na tsawon shekaru baki nemi kowa ba”? Kafin benazir ta bashi amsa hajiya layla tayi saurin cewa”Bai kamata kayi mata wannan tambayar ba, kodai mu da muke Iyayenta bamu tambayeta komai ba, duba da halin da tadawo gidan”
Ranshi a matuƙar 6ace ya dago da ido Yana binta da matsiyacin kallo batare daya furta komai ba
Sai Alhaji ubaid ne yace”wannan maganar bata shafeki ba, tsakaninshi da ɗiyarshine don haka ki daina sanya masu baki” harara ta wurga ma Alhaji ubaid”kaima ka sani bazan ta6a rufe baki na ba, akan me zai tambayeta meyasa ta tafi? Lokacin da ta gudun ya nuna damuwane akanta? Ko kuwa ya bada gudummuwar da za’a nemota ne eye? Daga zuwanmu gidanshi zai tsareta da tambaya? Dama ya kira mune don Ya tuhumi ƴar mu badan Ya tayamu murnar ganinta ba” tunda tafara zazzaga masifa hankalin hajiya sarah dana zeenatu ya tashi haiƙam, shi kanshi shureim jikinshi yai sanyi laƙwas, benazir dai ta saddar da kanta ƙasa hawaye na cigaba da wanke fuskarta.
Lallashinta Alhaji ubaid Ya soma Yi, Alhaji musa kuwa sai faman jinjina kanshi yake Yi, Yama rasa bakin magana
Hajiya sarah na faman yarfa hannu tace”dan Allah kiyi haƙuri aunty, idan ranki ya 6aci, nasan ba’a kyauta ba, Ni tun farko banso yace kuzo nan ba, har magana nayi mashi akan mu yakamata mu taka muje tayaku murna amma ya hanamu zuwa....” daƙyar ta ƙare maganar ganin irin kallon da Alhaji musa ke binta dashi, ba arziƙi taja baki tayi shiru
Jinjina kai yaɗanyi kafin ya ɗaura da cewa”Allah Ya huci zuciyarki Hajiya layla, Naji bazan ƙara tambayarta ba,” tayi mamakin jin abunda yace, har saida ta kalli cikin idonshi, murmushin gefen fuska yasakar mata afakaice, kafin Ya maida dubanshi ga benazir”ina yi maki barka da zuwa My daughter, naji daɗi da kika yi tunanin dawowa gida, ki kwantar da hankalinki, kuma ki share hawayenki, abunda ya faru ya riga daya wuce”
Ajiyar zuciya benazir tadan sauke, cikin sanyin murya ta soma magana”nagode uncle, sannan idan na 6ata maka rai, kayi hakuri, nasan komai ya faru laifinane, dana kama hanya na tafi”
Lumshe idanuwanshi yadanyi kafin ya waresu akan fuskarta”kada ki damu ni ban ruƙe ki araina ba, kawai dai banji dadin guduwar da kikayi bane na tsawon shekaru batare da kin tuntu6emu ba, amma yanzu tunda kin dawo da ranki da lafiyarki falillahil hamdu, sai dai fatan Allah ya kyauta gaba, In sha Allah zanyi ƙoƙari dan ganin na inganta maki rayuwarki, duk wani abu da kike buƙata ki sanar dani zanyi maki shi, kada ki ƙara yunƙurin guduwa saboda muna buƙatarki, zaifi ki sanar damu idan ma wani abune ya 6ata maki rai a tsakaninmu zamu Iya sama maki solution, Ina fata kina jina”
Ɗaga mashi kai tayi alamar eh, lamarin Alhaji musa ya ɗaurewa hajiya layla kai, bata ta6a tsammanin ya iya tsara kalami irin haka ba, hatta Alhaji ubaid yai mamakin yadda ya sakar ma benazir fuska yana yi mata magana cikin lallami, aranshi ya ayyana wata’ƙil tsananin tausayinta ne Ya kamashi, yaji dadin hakan, hankalin hajiya sarah ya kwanta dana zeenatu, sai faman sakin murmushi suke Yi, haka zalika dr.shureim shima murmushi ne akan fuskarshi.
“In sha Allah uncle bazan ƙara yunkurin guduwa ba, duk runtsi duk wuya zan zauna atare daku, nima nayi danasanin abunda na aikata,
Gyaɗa kanshi yai,
Hajiya sara tace”tun ɗazu fa na sanya masu aiki sun shirya maku lafiyayyan abinci, yakamata muje muci kada ya huce” da fara”a akan face dinta ta furta hakan,
Miƙewa sukayi atare suka dunguma zuwa dining room, benazir ta girgiza da ganin daular uncle musa, Gidan Ya tafi da imaninta.
Saman dining chairs suka zazzauna, ga kayan abinci an jera masu saman table,”
Tani da lami ne suka zo domin yin serving dinsu, Bayan sun gaishe da alhaji ubaid da hajiya layla, suka soma zuzzuba ma kowannansu abunda yake ra’ayin ci, hankalinsu kwance suke ci baka jin sautin komai saina ƙarar cokulansu.
Jefi jefi zeenatu take satar kallon benazir da zarar sun haɗa ido sai ta sakar mata murmushi, Ta fahimci yarinyar ba ƙaramin so take Yi mata ba, Dr shureim na kallonsu, shima murmushine akan fuskarshi, Hajiya layla dai taƙi sakewa, itafa har yau har gobe bazata ta6a yadda da alhaji musa ba, gani take yi kamar akwai wata manufa atare dashi, abincin ma daƙyar take cin shi”
Bayan sun kammala cin abinci, Hajiya sarah ta rakasu zuwa masaukinsu da zasu zauna, Hadaddun bedrooms aka ware masu, Zeenatu ta hana benazir sakat, tsabar Iyayi hada ɗauko bargonta da pillow ta dawo down stair dakin benazir donsu dinga kwana atare, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi mata ba,
*SIR MUBARAK✊*
Yana acikin dangi suna ta yin firar yaushe rabo tare da Ƴan uwanshi, Wayarshi dake acikin aljihunshi ta soma Yin ruri, kusan sau uku kiran na shigowa yana yin rejecting batare daya ankare ba, saboda hayaniyar ƴan uwan shi da suke Yin fira a tsakaninsu, a babban katafaren falon gidan, a kira na huɗune, Senate lateef dake zaune gefenshi ya ankarar dashi ta hanyar yi mashi magana ka duba wayarka tun dazu nake jin sautin ringing ɗinta, amsa mashi yai da toh, sai da ya fara curo wayar ya duba sunan mai kiran nashi tukunna ya mike yai masu sallama Ya nufi ƙofar fita daga babban falon, bayan ya fitone Ya dakata da yin tafiya, Yabi kiran da aka yi mashi, bugu ɗaya aka ɗaga kiran
“Major, ince dai lafiya? Naga miss call dinkane”
On the other hand major yace”yalla6ai yaron nan na wurinka jazz Ya fita daga gida Yanzu haka da nakeyi maka magana munbiyo bayanshine muna asaman titi,”
Cikin saurin murya sir mubarak yace”gani nan zuwa, kubi a hankali kada ku bari yaganku yaron wayau ne dashi, yanzu zamu biyo diddiginku” tunkafin maijor ya amsa mashi yai saurin yin rejecting call din, Ya dannawa driver dinshi Kira bugu ɗaya ya daga”Ina jiranka abakin entry hall na gidan baba, kazo da mota ka daukeni”
Ya ƙare maganar tare da kashe kiran, Jikin shi har tsuma yake yi fatan shi Allah ya basu nasarar kama jazz don ganin menene yake aikatawa,
Badajimawa ba baƙar mota ƙirar Range rover ta shararo da matsakaicin gudu bata nufi ko’ina ba sai bakin entry hall adai dai nan Tiger Yai parking dinta, Jiki na rawa sir mubarak Ya buɗe front seat na motar ya shige tare da bashi umarnin su tafi, reverse yai kafin ya karya kwana Ya nufi tanƙameman gate din fita daga estate din dake a kewaye da jami’ai, tunda suka hango sir mubarak ta tagar motar basu yi gigin dakatar dasu ba, kaitsaye motarsu ta haura saman titi, da gudun gaske tiger yake driving dinsu tamkar zasu tashi sama, sir mubarak yai amfani da phone dinsa wurin bin diddigin su major, cikin sa’a suka samo location din da suke, dare ne tamkar da rana saboda hasken street light daya gauraye ko’ina, hanyar da suka biyo kwata kwata babu mutane, sababbin gine gine ne a unguwar, wani ginin ma ba’a kammala shi.
Rage gudun motar tiger yai ta hanyar glass din motarsu suka hango motar major tana tafiya a hankali ga dukkan alamu sun ƙaraso inda dr jazz Yake shiyasa suka rage speed din motar, bayan major yai parking din motarsu, kusan atare suka fito shida wani matashin saurayi dukansu suna asanye cikin kakinsu na sojoji, daga bayan motarsu Tiger yai parking din tasu motar, fitowa sukayi atare shida Sir mubarak, koda su Major sukayi arba dashi a hanzarce suka buga ƙafa tare da sara mashi, Jinjina masu kai Yai yayin da yake bin gine ginen da kallo Ya ce”ina ku ka ga jazz din Ya shiga”? Ya jefa masu tambayar cikin ƙagara da sonjin amsarsu.
Major yace”Wancan gidan mai jan gate Ciki Ya shiga” yai maganar yana nuna wani katafaren gida, Da sauri Sir mubarak Ya nufi gate din, Major da Army din da suke atare kowannansu Ya zaro bindigarshi, shima Tiger Ya curo tashi pistol din, gefe da gefen sir mubarak Suka Jera sun saita bindugunsu saboda tsaro gudun kada akawo masu hari tunda basusan adadin miyagun da yake mu’amala da su ba, Cikin sanɗa suke tafiya suna bin ko’ina da kallo, ta ƙofar jikin gate din da aka bari abuɗe suka shiga, babu kowa abakin gate din tamkar anyi shara, Sir mubarak yace”Anya major akwai mutane acikin ginin nan? Naji shiru babu motsin komai, kodai kunyi kuskurene”? Girgiza kai major yai”Yalla6ai tabbas cikin ginin nan ya shigo, ba mu yi kuskure ba, akan idonmu ya fito daga cikin motarshi Ya buɗe gate kafin Ya koma ciki Yajata zuwa cikin gida”
Gyaɗa kai sir mubarak Yai”okey mu ƙarasa ciki” kaitsaye suka nufi katafaren ginin da suke tsammanin zasu samu hanyar shiga cikin gidan, adai dai bakin wata ƙofa, suka dakata A hankali Major Ya turo ƙofar cikin sa’a suka sameta abuɗe, ɗaya bayan ɗaya suke shiga, Hadadden palour ne An ƙawata shi da furniture, ga sanyin A.c ta ko’ina mai ratsa fatar jikin mutun.
Sunyi mamakin ganin babu kowa a palourn, ko motsin mutun babu, daga cikin falon akwai bene da zai kai mutun up stair, yanke shawarar haurawa saman benan sukayi, Cikin sanɗa suke tafiya kowa ya saita bindigarshi saboda tsaro, a second floor suka dakata da yin tafiyar suna bin ko’ina da kallo, ƙofofin ɗakunane ta ko’ina, Sam sun kasa motsawa saboda sunfara kokwanton anya akwai mutane agidan
Tiger yace”shirun yayi yawa, kada fa ace tarkone aka ɗana mana don mu afka”
Major yace”ai shi soja da kasada akasanshi, Idanma tarkon ne suka shirya mana to bamu bane zamu rufza aciki ba, sune zasu afka, wata’kil watan tonuwar asirin su ne Ya kama”
Sir mubarak Ya natsu Yana sauraronsu, ya