Showing 189001 words to 192000 words out of 250533 words
Chapter 64 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
rasa madafa sam bayason suyi kuskuren shiga gidan mutane, don ya fara kokwanto.
Army yace”yakamata mu fara dudduba ɗakunan nan wata’ƙil mu same shi aciki” Ya furta hakan tare dakai hannu Ya buɗe ƙofar ɗaki Ɗaya, karaf idanuwanshi suka sauka akan matasan Ƴan matan dake akwance saman bedmattress, cikin shiga ta kayan bacci”a matuƙar ruɗe ya juya yana kallon Sir mubarak Ya furta”yalla6ai ƴan matane kwance saman gado, Anya kuwa bamuyi kuskure ba”! Matsawa sukayi zuwa bakin ƙofar da Army yake a tsaye, kowan nan su Ya leƙa Sun yi mamakin ganin kyawawan ƴan mata kwance suna sharar baccinsu farare tass dasu kamar jinsin larabawa.
Rai amatuƙar 6ace sir mubarak ya dubi Major”kace min nan jazz ya shigo to yana ina? Waɗannan ƴan matan alamace dake nuna cewa Gidan wani ne muka faɗo”
Tuni major yasha jinin jikinshi, Muryarshi adabarbarce ya furta”yalla6ai wallahi da idona naganshi Ya shigo gidan nan, Ga army nan ka tambaye shi, ai tare dashi muka shigo, kuma shima yaga jazz din” Yai maganar yana nuna army da hannun shi
Kallon Army sir Mubarak Yai, da kakkausar murya ya furta”idan har kukasa naji kunya wallahi zakuji ajikin ku ne” hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, Jin abunda yace masu, Guntun tsoki Yaja tare da juyawa da niyar Ya fuce daga gidan, kwatsam ba zato ba tsammani, kunnuwansu suka soma Jiyo masu shessheƙar Kukan mace cikin murya mai ƙaraji take fasa ƙara tana fadin”Bana so! Ka ƙyaleni Nace maka banaso, Ni ka ƙyaleni, ka sake ni ka rabu dani....” sautin gigitacciyar ƙarar data fasa gaba ɗaya Ya cika ginin, Kallon juna sojojin sukayi kafin da gudun gaske suka nufi Hanyar da suke jiyo sautin kukan Yarinyar, Sir mubarak kamar zai yi tuntube, cikin zafin nama suka haɗa ƙarfi wurin bangaje ƙofar ɗakin, A tsiyace ƙofar ta bude, Hankalin sir mubarak Idan yai dubu to ya tashi, A matuƙar gigice sojojin suke kallon abun da ke faruwa, Lamarin yai matuƙar ɗaga hankulansu, musamman Sir mubarak Ya gaza yadda da abunda idanuwanshi suke nuna mashi, Tuni zufa ta soma wanke fuskarshi,
Sam baiji motsin shigowar mutane ɗakin Ba, Ya duƙufa akan abunda Yake aikatawa, Rigar shaddar shi da wandonshi gaba daya suna asaman floor, Singlet ce kaɗai a jikinshi sai gajeran wando Fari, Ya haɗa uban gumi, matashiyar yarinyar daya danne saman gado sai kuka take Yi, tana bugun bayanshi da hannayenta, A wahalce take harba ƙafafuwanta cikin fitar hayyaci kamar ranta zai fita, ta gama galabaita, tuntana kukan neman agaji har muryarta tafara disashewa, wani irin kukan kura sir mubarak Yai cikin zazzafan taku Ya kutsa kai Cikin ɗaki, da hannayenshi biyu ya damƙo wuyar singlet din Jazz da ƙarfin gaske Ya wurgar dashi kasa gaba ɗaya ya kife kanshi ya daki tiles, Jiki na kerma ya ɗago yana dubansu ɗaya bayan ɗaya kafin ya tsayar da idanuwanshi akan fuskar Sir mubarak dake tsaye kanshi tamkar mayunwacin zaki, hankalinshi yai matuƙar tashi da ganinsu duk yabi ya ruɗe ya susuce, jikinshi ya hauyin kerma, sai faman zazzare idanuwanshi yake Yi, Muryarshi na kakarwa ya furta”daddy....” bai ƙarasa maganar da zaiyi ba, Sir mubarak Ya damƙo wuyanshi ya ɗago dashi tsaye cikin rauni na murya ta wanda ya karaya yake fadin”Jazz ka kasheni, Ka cuceni, dama abunda kake aikawata kenan? Ƴan mata kuke tarawa acikin gida, donku lalata rayuwarsu sannan ku kashe su? Nasha kama ka kanayin waya kana fadin kaji ashe mutanene kajin, Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un” cikin jin ƙunar rai yace”Wallahi baka isa ka ɗaura min hawan jini baa, Kafin ka kasheni ni zan fara kasheka don ubanka, Mugu azzalumi fasiƙi, Jazz ka bani mamaki, ka cuce ni kuma ka cuci mahaifiyarka,’ Cikin shessheƙar kuka Sir mubarak Yake furta maganar, Ya shaƙe wuyan Jazz sai faman mutsu mutsu yake Yi, don ya ƙwaci kansa.
Yayin da sojojin suke a kewaye da gadon da yarinyar take, duk tabi ta tsorata jikinta sai kerma yake Yi, short gown ce a jikinta, yalwatacciyar baƙar sumar kanta duk ta rufe gefe da gefen fuskarta, tamkar wadda tasha gudu sai faman yin haki take Yi.
Sautin ƙarar da jazz Ya fasane Ya janyo hankulansu ga duban shi, wani irin radadin azabane Ya ziyarce shi sakamakon buga kanshi da sir mubarak Yai jikin Mirror din dakin, gaba ɗaya madubin Ya zube, Jini Ya wanke fuskar Jazz hatta gaban farar shirt din jikinshi Yayi ca6a ca6a da jinin shi, daddafe kanshi yai da hannu bibbiyu cikin mawuyacin hali Yake sambatu “Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Daddy ka kashe ni, Na shiga uku na bani na lalace, daddy ka rabani da rayuwata”
Yarinyar dake zaune saman gadon, ganin yadda suka raunata shi yasa ta fasa ƙara da ƙarfi ta furta”yaya Jazz, Wayyo Allah na kun kashe min shi, mugaye azzumai baiyi maku laifin komai ba amma kuna cutar min dashi” Da gudun gaske ta duro daga saman gadon ta kife ƙasa, sam babu natsuwa atare da ita, da rarrafe ta ƙarasa gabanshi, Ta sanya hannu biyu ta ɗago dakanshi ta daura saman laps dinta, Cikin shessheƙar kuka take fadin”Wallahi Allah bazai barku ba, Ku baku da burin daya wuce ku cutar da rayuwar waɗanda basu ji ba basu gani ba, Sai Allah ya saka mashi, ku dukanku sai kun shiga wuta” ta fada tana nuna su da yatsan hannunta, kallon juna sojojin sukayi, sunyi matuƙar girgiza da jin kalaman Yarinyar, sun fara kokwanton Anya kuwa Zargin da sukeyi mashi gaskiya ne? Tayaya yarinyar da ake cutar da rayuwarta, kuma take fada don an ta6a mutumin dake ƙoƙarin rabata da mutuncinta!! Fashewa tayi da kuka Hannayenta tuni sun 6aci da jinin dr jazz tana kuka tana ambaton sunanshi”yaya jaz dan Allah kada ka mutu kabarmu, wallahi idan ka mutu nima saina kashe kaina”
Zuciyar sir mubarak ce ta soma harbawa da ƙarfin gaske, Jiri ya soma ƙoƙarin kwasarshi, Gaba ɗaya ya gama rikicewa, Hankalinshi atashe Yake kallon Kwalaben alluran dake ajiye saman bedside drawer tare da sirinji, hada magunguna, Adaddafe Ya nufi drawer din da niyar Ya duba kwalaban don ganin na menene, sautin ringin wayar Jazz ne Ya dakatar da shi, da sauri ya daura rinannun idanuwanshi inda yake jiyo sautin daga cikin aljihun wandon shaddarshine, Major ne yai saurin daukar wandon Ya binciko wayar cikin aljihun, Ya miƙa ma sir mubarak, yatsun hannun shi na kerma ya ruƙe wayar, batare daya duba sunan mai kira ba Yai picking call din Ya sanya kiran handsfree.
Sautin muryar mutumin dayaji tayi matuƙar gigitar dashi, har baisan sa’adda Ya saki wayar jazz ta fadi saman floor, sojojin dake atare dashi duk sun sha jinin jikinsu, kallon kallo suka soma Yi a tsakaninsu, cikin matsanancin tashin hankali, sautin shessheƙar kukan matashiyar ya cika dakin, dr jazz tuni Ya jima da sumewa.
*EX-PRISONERS💔*
Gaba ɗayansu sun hallara a dining room, domin cin abincin Dinner dinsu, mutun ɗaya ne ke babu acikinsu, Yana can dakin shi, mazan suna fuskantar matan, sunyi shiga kala ɗaya wandon jeans da farar shirt,matan kuma dogayen rigunane a jikinsu, Aunty ummi ce kaɗai ta banbanta dasu, riga da skirt ne ajikinta sun matseta, shape din jikinta Ya bayyana muraran, babu mayafi akanta, sa6anin su Batul da sukayi rolling veils.
tunda suka zauna Unaisah ta kasa samun sukuni, yanayinta tamkar na mara lafiya, sai faman jujjuya spoon take Yi acikin plate din gabanta, da ke shaƙe da abinci, damuwar duniya ta isheta, sam babu sukuni akan fuskarta, A hankali ta ɗago da ido tana duban fuskokin Ƴan uwanta, tun daga kan Sajeed dake fuskantar Azeeza, suna cin abinci suna kallon juna, har zuwa kan Haris dake fuskantar Hannah, kafin ta kawar da idonta daga kansu ta maida su kan fuskar Naufal da javed, sun natsu suna cin abincinsu, hasken musulunci ya fara shigarsu, komai nasu cikin natsuwa suke yin shi, mayar da idanuwanta tayi akan face din jamimah, bakinta duk ya 6aci da maiƙo, ta samu cinyar kaza saici take Yi kamar tsohuwar mayya, ta cinye tsokar naman, Ƙashin take gwaigwaya kamar babu sauran naman alhalin gashinan saman tray guda aka jera masu chicken legs, girgiza kai tayi kafin ta mayar da dubanta kan Batul dake gefenta, ita dai duniya babu abunda ke burgeta irin taliyar indomie, tun ranar farko data fara cinta, kullum ne in zasu ci abinci saita ci ta, sam bata gajiya, da hannu take nannaɗota kafin ta tura abaki, rantane ya raya mata ana kallonta, dai dai time dinda ta tura taliyar abaki ta ɗago da ido suka kalli juna ita da Angel, da sauri ta haɗiya taliyar, cikin muryar raɗa ta tambayeta lafiya take kallonta? Ko tayi ƙauyancine”? Girgiza kai Angel tayi babu komai kawai burgeni kikeyi idan kina cin noodles da hannu”
Gyaran murya ummi tayi masu atare suka ɗago suna kallonta.
“Unaisa tun ɗazu na lura kamar bakya jin daɗi, meke damunki ne”? Murmushin yaƙe ta sakar mata”babu komai aunty ummi, ko kinga wani abu ne” ɗaga mata gira tai”ƙwarai kuwa, tun da gashinan kin kasa cin abincinki”
Kafin unaisa ta ƙara furta wani abu, Muryar Haris ta katse su
“Kodai Danish bashi da lafiyane? Tun jiya da rana ban ƙara ganin ya leƙo waje ba, naso naje na duba shi sai dai karatu Ya mantar da nayi yin hakan”
Cikin nuna damuwa Sajeed yace”wallahi yana araina, tun ɗazu da muna awurin kar6ar karatu nake ta tunaninshi, bansan dalilin dayasa baya son zuwa cikin mu cin abinci ba, naga dazu da rana ke kika kai mashi lunch dinshi a dakin shi” ya faɗa yana nuna Unaisah da spoon din hannunshi.
Naufal Yace”to me zai hana mu tashi muje ɗakin nashi mu duba su? Ni abunda ke damuna da danish baya son sakewa cikin mutane” Yai maganar fuskarshi dauke da damuwa.
Javed yace”ai halinshine tun fil azal, kaima kasan Danish bai cika son zama cikin mutane ba, baison surutu kuma baison ana kallon shi”
Gyaran murya Ummi tai masu, Hankalinsu Ya dawo kanta sun natsu suna jiran jin me zatace
“Koda ace halinshi ne hakan bai kamata ku ƙyale shi ba, cos barinshi acikin ɗaki zai Iya haifar mashi da wata damuwar, duk da naga Unaisah tana ƙoƙarin dubashi, amma a ƙalla yakamata kuma kuna zuwa wurinshi kodan ku dinga ɗebe mashi kewa, kafin zuwa lokacin da zai saki jikinshi, nasan rashin sabone ke damun shi”
Jinjina kai sukayi alamar gamsuwa da bayaninta, Sajeed yace”ku tashi muje dakinshi Inyaso sai mu tafi da kayan abincin mu ƙarasa ci acan” Yai maganar tare da miƙewa, da sauri Unaisa tace”a’a basai mun tafi mu duka ba, Ku zauna ni zanje in taho da shi” amsa mata sukayi da toh, da sauri ta miƙe ta nufi ƙofar fita daga dining room din
Miƙewa Batul tayi Ummi tace Ina zuwa? Cikin sanyin murya tace ina so zanbi Unaisah ne”
“Ki koma ki zauna, ai tace zasu dawo atare dashi ko”? Amsa mata tai da toh jiki asanyaye ta koma ta zauna.
Shiru suka ɗanyi, abincinma sun dakata da cin shi, hakanan suke jin zuciyoyinsu na bugawa, Jemimah kadaice ke cin abinci ta cika masu kunnuwa da sautin taunar abincinta, da gangan take yi duk don ayi mata magana.
Harara Azeeza ta watsa mata”dan Allah ya isa haka, ba zaki Iya ci a hankali bane”? Hanna tace”ki daina wahalar da bakinki, dagangan take yi duk don ayi mata magana” tuntsirewa tayi da dariya tana fadin”Eh din kuma gashi kunyi min maganar ba” girgiza kai ummi tayi fuskarta dauke da murmushi take dubanta, hankalinta kwance take yin magana. Kallon da naufal ya jefa matane yasa tai shiru tana ƴan ƙunƙuni.
“Kuna burgeni, gaba ɗayanku” ta fada tana nuna su da spoon din hannunta.
Batul tace”aunty ummi, kina nufin kina sonmu”? Jinjina mata kai tayi”haka nake nufi,” murmushi su naufal suka saki jin abunda tace,
Parveen na faman siɗar hannu tace”Aunty ummi ke baki haifi ƴa’ƴa bane, kamar yadda daddyn unaisah ya haife ta? Ko kuwa ita mace bata haihuwane sai maza”? Da mamaki Ummi ta dan zaro ido tana kallon parveen da tayi maganar, sam babu wasa akan fuskarta ita bilhakki take Yin maganarta.
“Amma baki da hankali parveen, Kin manta labarin da unaisa ta ta6a faɗa mana ne? Macace take haihuwa ba namiji ba, itama Mommyntane ta haifeta ta jefar da ita cikin wannan abun kalar na toilet din gidan nan, namanta sunanshi” Batul ce tai maganar,
Azeeza tace”eh kuwa hakane, Macace ta haifi unaisa ba namiji ba, to aunty ummi ke kin ta6a haihuwa”? tayi tambayar tana kallon ummin america wadda mamaki da al’ajabi suka cikata, sai kallonsu take Yi ɗaya bayan ɗaya, sajeed Ya duƙar da kanshi ƙasa sai faman sakin murmushi yake Yi jin wautar parveen.
“Aunty ummi kinyi shiru baki ce komai ba, kina ta kallonmu” Hanna ce ta jefa mata tambayar, ta ƙura masu ido tana binsu da kallon mamaki,
“wai kuna nufin bakusan komai ba, game da zamantakewar aure?
Atare suka haɗa baki wurin furta”Aure kuma”? Gudun kada suyi wata 6aran 6aramar yasa Sajeed yin saurin cewa”aunty Ummi, Yakamata mu maida hankali akan abunda muke Yi yanzu,” Ta6e baki taɗanyi kafin ta furta”okey, “ ta fahimci baison maganar dama ta lura yafi su hankali shida Unaisah, bata ta6a ƙagara da sonjin labarinsu ba sai yau, tabbas tana son tasan tarihin rayuwarsu! Ya akai har suka kai wannan shekarun basusan komai dangane da zamantakewar aure ba? batun Yauba ta lura da ƙarancin wayewarsu, kamar babu ƙwalwa akansu, basu iya komai ba, In banda cin abinci da kwanciya bacci sunfi ƙwarewa a 6angaren nan.
_(Ummin america batasan su wanene prisoners ba, Mutanan da suka juri rayuwar kulle tun suna jarirai, basu ta6a ganin hasken rana ba, dare da rana basu da abunyi daya wuce idan ankawo masu abinci sau ɗaya suci sai kuma idan lokacin baccin su Yayi su kwanta, badan Allah Ya ƙaddara zuwan unaisah kurkukun ƙaddara ba, da kuwa abunda zasu aikata sai yafi hakan saboda su din tamkar baƙine a duniyar mutane, basusan komai ba, unaisah itace ta wayar masu da kansu dangane da mutanan duniya da wasu abubuwan da suka shafi rayuwar ɗan adam shiyasa ma har suke Iya sakin jiki suyi rayuwa acikinsu)_
Shin meya faru bayan Unaisah ta fita daga Dining room?
Cikin sauri ta nufi upstair, tunkafin ta ƙarasa ƙofar ɗakin danish ta dinga jin faɗuwar gaba, tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, jiki na rawa ta nufi ƙofar room dinshi, zura ƙafarta keda wuya cikin ɗakin, taga babu kowa wayam har saman gadonshi babu mutun, sai faman baza ido take Yi tana faman ambaton sunanshi tamkar makoshinta zai 6allo”Danish! danish! my Man! Kana ina”? Shiru babu alamun zai amsa mata, ƙofar toilet dinshi ta tunkara lokaci ɗaya taji sautin gurnaninshi mai matuƙar firgitarwa ya cika ɗakin, cikin jin faɗuwar gaba ta sanya hannayenta biyu da ƙarfi ta ingiza ƙofar ta buɗe, tun daga bakin ƙofar toilet din ta ci karo da singlet dinshi, A hankali take bin ko’ina da kallo har tayi nasarar cin karo dashi kwance acikin kwamin wanka, wanda ke akewaye da glass, ya ƙunshe kanshi cikin kwamin, jikinshi sai kerma yake yi, faɗawa cikin toilet din tayi, Cikin sanyin murya take fadin”My man meke damunka? Meyasa kake yin gurnani? Baka da lafiyane” idanuwanshi dake a lumshe ya buɗesu sun kaɗa jawur dasu tamkar an wanke ƙwayar a cikin jini, Hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, sam bata damu da yanayin da zata riske shi ba, Jiki amace ta shiga inda kwamin yake ta zuƙunna agabanshi tana dubanshi, fatarshi tayi wani irin haske naban mamaki, Ya cika kwamin da ruwa mai sanyi, amma saboda tsabar zafin jikinshi yasa ruwan ya koma na zafi.
Idanuwanta tuni sun cicciko da ƙwalla muryarta na rawa ta furta”My man dan Allah kayi min magana meke damunka? Meyasa ka shigo toilet ka kwanta cikin bathtub”? Ta faɗi hakan ne donta fahimci ba wani uziri bane ya shigo dashi toilet dinba, saboda bai cire short dinshi ba, Ahaka ya shiga cikin ruwan duk don ya sassauta zafin da jikinshi yai mashi.
Da wata irin kakkausar murya ya furta”Kiyi nesa dani, zan iya cutar dake, bani bane, Ki tafi ki ƙyaleni, bana so in ta6a lafiyar jikinki” zazzare idanuwanta tayi waje tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, muryarta adabarbarce ta furta”me..meyasa kace haka danish? Idan bakai bane to wanene? Nashiga ukuna! dan Allah kadaina furta waɗannan kalaman, Ni nasan bazaka Iya cutar.....” kasa ƙarasa maganar tayi sakamakon ganin sa6ar macijin dake tsastsafo mashi saman fatar wuyan shi, Kafin ƙyaftawar ido danish ya rikiɗa ya zama Giant snake fari sol, Jikinsa yana da tsayi da kauri, mai santsi, Ya nannaɗe kanshi cikin kwamin wankan, Wani irin narkeken maciji danƙareran gaske yana da doguwar jela da siraran harshe, tsabar firgici da ruɗanin ganin abunda bata ta6a ganiba Ya hanata motsawa, jikinta ya hauyin kerma zufa ta wanke fuskarta, ko amafarki bata ta6a ganin mutun ya rikiɗa ba sai yau da Allah Ya nuna mata Danish ɗinta Ya canza halittarshi zuwa maciji, girgiza jikinshi yai nan take kwamin wankan da yake acikin shi Ya tsastsage Ya tarwatse, Ya faɗo ƙasa, aikuwa da gudun gaske Unaisah ta fito daga dakin, ta fasa razananniyar ƙara, tana gudu haɗi da yin tuntu6e, a matuƙar gigice ta fado saman bene, Mayafin kanta tuni yajima da barin jikinta, Sumar kanta duk ta rufe fuskarta, cikin tashin hankali take tattaka matakalar benan, tana kuka haɗi da ambaton sunan ƴan uwanta
Adai dai lokacin Chief Owais Yana saukowa down ta cikin glass elevator, ya kimtsa cikin Dark jeans, daga sama ya sanya button-down shirt, yayin da ƙafafuwanshi ke asanye cikin patent leather shoe, gefenshi Big guy ne hannunshi ruƙe da car key, karaf idanuwan big guy suka sauka akan unaisah dake Faman zumbula gudu tana tunkaro down, ta cikin glass elevator din yake kallonta, kafin yai yunƙurin buɗe baki Yai magana, unexpected danƙareran macijin Ya kunno kai daga ɗakin ya daka tsalle Ya haura ta saman handrail din benan Ya rigata saukowa ƙasa, da buɗar bakinshi sai cewa yai”yalla6ai anya ban fara samun matsalar gani