Showing 219001 words to 222000 words out of 250533 words
Chapter 74 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
cikin bargon idanuwanta sunyi luhu luhu, ƙoƙari take tabar dakin duk don kada ta ƙara haɗa ido da ummi, tayi tsammanin zata ganta asaman gadon sai ganinta tay kwance saman carpet, ta lullu6e half body dinta da bargo, tafi ƙarfin ta haɗa shimfiɗa da su shine ta dawo kan carpet ta kwanta.
Muryar batul kasa kasa ta ke ambaton sunan parveen,
Daƙyar ta samu parveen ta farka daga bacci, tana faman yin miƙa haɗi da yin hamma, juyawa tayi 6angaren su Jemimah ta soma tada su daga bacci ɗaya bayan ɗaya suka farka suna faman mutsustsuke idonsu.
Cikin muryar rada take yi masu magana”ku tashi mu tafi ɗaki, lokacin sallar asuba yayi,” ruƙo hannun jemimah tayi ta sauko da ita daga saman gadon, Parveen ta ruƙo hannun Azeeza suka sauko.
“Bana so ta farka ta ganmu, kada ku yi surutu mu lalla6a mu bar mata ɗakinta” ta faɗa tana dubansu, Jinjina mata kai su ka yi alamar toh.
Cikin takun sanɗa suka nufi ƙofar fita dakin, sai da suka fita Batul ta tuna da kayan ummi dake a jikinta, dafe kai tayi da hannu ɗaya”nashiga uku ashe ban cire mata kayanta ba, Parveen ki ruƙe hannun Aziza dana jemimah ku tafi ɗakin mu zan biyo ku daga baya”
Maƙe kafada jemimah tayi”ni tsoro nake ji, idan abun nan ya ganmu fa”?
“Kada ki damu, babu shi ai, waɗannan mutanan sun kashe shi” daƙyar batul take Yi masu magana
“Batul baki lafiya? Idanuwanki sun kumbura jawur, muryar ki kamar ba’aji sosai” Azeeza ce tayi magnar.
Kafin batul ta bata amsa parveen tace”sanyine ya kamata, sai da na hana ta kar6i rigata amma ta kar6a tasaka”
“Amma ai aunty ummi ta bani kaya na saka, Kawai bana jin daɗine bawani abu ke damuna ba, Ku tafi ɗaki zan biyoki” Ta faɗa tare da juyawa ta nufi ɗakin.
A tsananin tsoroce suke tafiya suna tunkarar benan, parveen tana aruƙe da hannun azeeza dana jemimah, har yanzu basu daina jin fargabar macijin ba.
Bayan batul ta koma dakin Ummi cikin sanda take tafiya, harta ƙarasa gaban gadonta, ta cire mata kayanta, ta ɗauki doguwar rigar parveen data jefar ƙasa, ta zura a jikinta, Juyawar da zatai keda wuya, taji sautin datse kofar ɗaki, rass taji gabanta ya fadi ganin ummi atsaye bakin kofar ta goya hannayenta kan ƙirjinta, fuskarta a murtuke babu annuri, idanuwanta sun ƙanƙance.
Hankalin batul ya tashi matuƙa, agigice ta furta”aunty ummi ina kwana”
Harara ta galla mata”daban kwana ba kin ganni atsaye? Kilbabba uwar iyayi”
Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace”Ai na cire maki kayanki, gasunan kan gado, Ni dakinmu zan tafi, wajen unaisah”
“Idan kinga na ƙyale ki kin fita daga dakin nan, to kuwa kin gyara sautin muryarki ne, wallahi baki isa kija min bala’e ba, Har kayan sanyi na baki, na kuma kashe sanyin a.c, saboda baƙin hali irin naki saida kika bari mura tayi maki mugun kamu duk don kija min masifa ko”?
Hawayene suka soma wanke fuskar batul, muryarta na rawa tace”ba haka bane aunty ummi, nima bayin kaina bane, bansan mura ta kamani har haka ba, dan Allah kibarni in koma cikin ƴan uwana”
Shu’umin murmushi ummi tayi mata,
“Zan barki ki tafi, amma kafin nan saina fara kawar maki da murar nan, don haka mu shiga toilet inyi maki wanka da ruwan zafi”
Zazzare ido batul tayi hadi da girgiza kanta”dan Allah aunty ummi ki ƙyaleni, ai ni ba yarinya bace, da zaki min wanka, ni kawai ki rabu dani nayi maki alƙawarin babu wanda zaisan ina yin mura”
Ɗaure mata fuska ummi tayi zaki wuce mu shiga toilet ko saina 6ata maki rai”?
Cikin jin ƙunar rai, batul ta maƙe mata kafaɗa”ni bazan shiga ba, Na fada maki banaso, ki ƙyaleni,” atakure take Yi mata magana, makoshinta radadi yake yi mata.
Ganin ummi na tunkarota ne yasa ta soma ja da baya tana kuka, kokarin kubce mata tayi da sauri ummi ta damƙo sumar kanta, tajata ta ƙarfi ta shigar da ita toilet tana fadin”Ke har kin isa ki kufce min, ƙaramar ƴar shila dake, me zan gani a jikinki? da har kike fadamin ke ba yarinya bace” sautin kukan batul ya cika dakin ummi, gigitacciyar tsawar data kwatsa matane yasa tayi saurin jan baki tayi shiru, hawaye na cigaba da bin fuskarta.
Ummi tafi ƙarfinta, da girmanta da komai, Tayi mata wanka da ruwan zafi, tamkar zata sale mata fatarta, fitowa ummi tayi daga cikin toilet din, ta nufi closet din kayanta, tana faman sakin murmushin mugunta, riga da wando ta dauko masu kyan gaske, na saƙa launin pink, waɗannan kayan tsohuwar ajiyace tuntana ƴar shekara sha bakwai a duniya take 6oyansu, tana matukar son kayan, rigar tana da hula hannunta dogone.
Komawa toilet din tayi kamar yadda tabar batul haka ta sameta, ta ƙanƙame kanta jikin bango, dan pant ne ajikinta, hannunta biyu tallabe da kirjinta ta kakkare boobs dinta.
Jefa mata kayan ummi tayi da sauri ta kar6esu.
“Ina jiranki aɗaki, salon kuma ki daɗe, idan kika ƙara mintuna wani wankan zan sake yi maki” cike da isa ta furta maganar, kafin ta juya ta fuce daga toilet din, abakin ƙofar ta dakata tana jiran fitowar batul.
Jin motsin buɗe toilet door dinne yasa ummi kai idonta ga dubanta, har saida taji gabanta ya fadi, ganin kyan da kayan sukayi ma batul, rigar tayi mata daidai, wandonma haka, kamar don ita aka saƙa kayan, bata sanya hular ba, yalwatacciyar sumar kanta ta sauko har gadon bayanta dark brown.
Sai faman ƙanƙame jikinta take yi, ganin yadda ummi ke kallontane yasa ta duƙar da idanuwanta ƙasa, duk tasha jinin jikinta.
Batasan ya akai ta tsinci kanta dayi ma fuskar batul kallon sani, sai dai tarasa tuna dawa take yi mata kama.
Matsawa tayi kusa da ita, takai hannu ta ruƙo hular rigar ta sanya mata ita, sai taga ta ƙara yi mata kyau.
“Ki daina ganin ina kallonki, ba kyau kikayi min ba, Munin fuskarki nake kallo” shiru Batul batace mata komai ba, bayan ta kammala gyara mata hular rigar, ta nuna mata gado”ki koma ki kwanta, har zuwa time da muryarki zata dawo dai dai kinji ko”?
Maƙe mata kafaɗa batul tayi”ni bazan kwanta ba, dan Allah kibarni in tafi daki wajen ƴan uwana, Inason ganin Unaisah” muryarta shaƙe ta furta maganar.
“Wato saboda kinga makwancina shiyasa kika fara rainani ko? Har kina da bakin fadin Bazaki yi abu ba idan nasaka ki, Dalla ni wuce ciki ko inyi ball dake”
Ƙin matsawa Batul tayi, gani take kamar ummi zata iya kasheta, furucin da tayi mata jiya sun firgitar da ita, sun kuma tsaya mata aranta.
Zabura tayi da niyar ta nufi kofa don ta gudu, ai kuwa azafafe ummi ta damƙota kamar ɗiyar roba haka ta ɗaga ta sama, ta nufi gado ta jefar da ita, ta kuma janyo bargo ta lullu6eta tana fadin”idan kika kuskura kika leƙo koda kankine saina murƙusheƙi”
Muryar batul da shessheƙar kuka take fadin”aunty ummi dan Allah kibarni in tafi, banason kwanciyar, ni wajen ƴan uwana zanje” ummi dake tsaye tana kallon bargon tace”idan kina son fita daga dakin nan to ki fara gyara muryarki”
“Ai ni bansan yadda zan gyarata ba, ki bani magani in sha”
Ta cikin bargo batul take Yi mata magana.
Tunani ta somayi aranta, ina zata samo mata maganin mura? Tasan ba’a rasa dakin ajiye magani a gidan tun da na jami’ae ne kuma yaran an tanadar masu komai da zasu buƙata saboda rayuwar kullece aka shirya masu.
Boss man kadai take da contact dinsa, awayarta, daukar wayar tayi dake ajiye on bedside drawer ta danna ma Boss kira, cikin sa’a ya ɗaga kiran.
Cikin girmamawa ta gaishe da shi”barka da asuba yalla6ai”
On the other hand muryar boss ta amsa mata da cewa”wa’alaikum salam, ummi barka da safiya”
“Yawwa barka, Allah yasa dai ban katse maka baccinka ba”
“Kada ki damu, idona biyu yanzu nake shirin zuwa cikin gidan, ko akwai wani abu da kike buƙata”?
“Taimako nakeso kayi min in ba takura, maganin mura nake buƙata”
“Wanene ke baida lafiya”? Da sauri tace”nice zan sha, Yaran dake atare dani lafiyarsu ƙalau’ amsa mata yai da okey, idan zan shigo gidan zan taho maki da shi”
“Nagode” katse kiran tayi tana faman sauke ajiyar zuciya, Batul dake a ƙumshe cikin bargo, abun duniya ya isheta.
Muryarta shake tace”aunty ummi banyi sallar asubaba, kuma ina jin yunwa”
Guntun tsoki ummi taja”kiyi min shiru malama, ni ma ai banyi sallar ba, kuma ina jin yunwar bawai bana ji ba”
Ta fada Tare da samun wuri daga gefen gadon ta zauna tana gadin Batul, hannunta ruƙe da wayarta, chatting ta kama yi, batul tayi shiru cikin bargo tana faman matse ƙwalla.
A katafaren Villa Mallakin Hateem Obinna, haddadiyar daula kuma aljannar duniya wadda idan ka zura ƙafarka acikinsa sai ka yi tsammanin ƙasar dubai ka shiga, Hamshaƙin Gidanshi a kewaye yake da Jami’ae sojoji da ƴan sanda, mugun tsaro ake yi mashi, babu wanda ya isa ya ƙetare gidan hateem cikin sauƙi idan ba Mahaifinsa ba da yayyansa, amma bayan wadanda kafin mutun ya samu iznin shiga ciki sai ya ci baƙar wahala don kuwa daga ƙasa har sama zasu bincike ka da na’ura, har ƙwara mutun ya shiga masarauta yafi mashi sauki, akan Gidan prime minister, tsaruwar ginin gidan kuwa da haduwarshi ba’a magana, gaba ɗaya Obie estate babu gidan da yakai Na prime minister In ka cire Villah din Owais.
*Gimbiya Mujeedat👑*
A kishingiɗe take saman Katafaran gadonta na alfarma, kalar na sarakuna waɗanda suka gaji Arziƙi, gadon a kewaye yake da labulaye launin royal blue, an ƙawata shi da lallausan zanen gado fari ƙyal, haɗi da matassan kai launin blue and white, gefe da gefen gadon bedside drawers ne suma launin royal blue, daga saman su Fitilune masu bada haske launi daban daban, an zuba mata tsadaddun furniture a ɗakinta, ya ƙawatasu sosai da kayan alatu.
ta ɗaura kanta saman pillow, Rigar dake a jikinta Silk robe ce launin ice blue, tabi shape dinta ta bayyana dirarran dirin jikinta, A halitta Gimbiya Mujeedat doguwace, fara sol tana da dogon wuya, hutu ya zauna mata ta ko’ina Allah Ya hore mata, Kyau kamar ita ta zana kanta, fararen idanuwanta tamkar an ɗiga masu zaiba, launinsu dark black ne, ga tarin ziraran eye lashes dinta da suka ƙawata kewayen idanuwanta sun yi mashi rumfa, dogon hacinta a tsaye yake babu lanƙwasa, siraran la66anta launin ja tamkar na jarirai tsabar ƙarantarsu da laushin fatarsu, tana da yalwatacciyar sumar kai baƙa wulik mai santsi da silbi, har gadon bayanta, Tabarakallahu ahsanul khalilin Gimbiya mujeedat maƙurace afagen kyau, uwa uba ta fito daga tsatson masarautar daular larabawa, bugu da ƙari First Lady ta ƙasar Canada, ajin farko ce ita, zan iya cewa baba Hateem Ya more mata 😉
Ziririyar sarƙar wuyanta ta zallar diamond ce, haka zalika Ziraran yatsun hannunta na dama suna sanye da Ring set na Gold komai nata me tsadane ita kanta lu’u lu’un ce.
Yanayin yadda ta kwanta da alamun kasala atattare da ita, ta ɗan lumshe idanuwanta, fuskarta sam babu walwala, kamar akwai wani abu dake damunta.
A lokacin da bata yi tsammani ba, muryar prime minister Hateem ta karaɗe kunnuwanta, sallama ce yai mata yayin da yake shigowa dakin, Cikin shiga ta jallabiya launin maroon, daddaɗan ƙamshin turarenta dana ƙamshin turaren wuta ne Ya daki hancinsa Har saida Ya lumshe idanuwanshi, mutunne shi ma’aboci son ƙamshi, sai kuma Allah Ya haɗa shi da mace ma’abociya son kamshi da son ado, shiyasa a kullum take ƙara shiga ranshi, soyayyarsu bata tsufa, Idan suna atare da juna daukar kansu suke Yi tamkar sabbin ma’aurata.
Bata samu damar amsa mashi sallamar shi ba, daƙyar ta iya buɗe idanuwanta da sukayi mata nauyi, launinsu ya rikiɗa zuwa ja, saboda rashin baccin da batayi ba adaren jiya kuma shine sila, Ya hanata sukuni, bai ta6a burkice mata ba irin Na jiya, Ƙiri ƙiri Ya takura kanshi, Ya hana kanshi runtsawa, kuma yaki fada mata abun da ke damun shi, daga ita har shi jiya babu wanda ya runtsa, saboda ta maida damuwarshi tata.
Koda ya shigo dakin, a hankali ya daura idanuwanshi kan fuskarta, sai yaji ba daɗi har cikin zuciyarshi yasan bai kyauta mata ba, tunda ya riga da yasan halinta na damuwa da damuwarshi.
Daga gaban gadon Ya dakata dayin tafiyar, ya goya hannayenshi on his broad chest yana fuskantarta.
Ba zato ba tsammani, yaga ta galla mashi harara haɗi da murguɗa mashi ƙaramin bakinta.
Nan take ya fahimci fushi take yi da shi, ranta ya 6aci.
Cikin harshen turanci tace”Sannu da dawowa”
Ta inda gimbiya mujeedat take burge shi, duk mun fushin da zatayi dashi hakan bai hanata kula da shi
“Yawwa, fatan na same ki lafiya”
Yamutsa fuska tayi fuskarta babu annuri ta soma magana tamkar bata son furtata.
“Mijina baka kyauta min ba, ka hana kanka runtsawa nima kuma ka hanani runtsawa, nayi koƙarin faranta maka duk don na kawar maka da damuwarka amma babu abunda ya canza, Ka jefa ni cikin wani hali daga daren Jiya zuwa yau, meyasa ba zaka fadamin meke damunka ba? Ko ban isa nayi maka magani bane? Nasan ka yarda dani, sannan baka 6oye min komai, sirrinka nawa ne amma meyasa jiya kaƙi fadamin damuwarka” sautin muryarta tamkar ana busa sarewa tsabar daɗinta.
Idanuwanta aruntse take yi mashi magana, don ta fahimci idan tana kallon cikin idanuwanshi bazata samu ƙwarin gwiwar yi mashi magana ba”
Sauke hannayenshi yai daga saman kirjinshi, ya zagayo ta gefen da take a kwance Ya zauna, yana duban fuskarta
Ƙayataccen murnushine kwance kan la66ansa, yasan ta kan mace, idan ranta ya 6aci cikin sauƙi yake faranta mata
“Uwar gida sarautar mata, Gimbiyata, Ina neman afwarki ranki shi daɗe, bai kamata gimbiya tana fushi da bawanta ba, Ni fa a karkashin inuwarki nake, da taimakonki nake samun natsuwa da kwanciyar hankali, taya zanso na 6ata maki rai? Bayan kece linzamin dake sarrafa ni....”
Tun da yafara gaya mata daɗaɗan kalamansa, ta fara sassauta fushin fuskarta,
A hankali ta buɗe idanuwanta kan fuskarshi, da sauri ya kama kunnuwansa Yana fadin”Am sorry My wife, na gane kuskurena”
Ta6e mashi baki tayi”Ni so nake ka fadamin meke damunka? Da har yai silar hanaka runtsawa, kalli fuskarka duk ta yamutse, idanuwanka sun ƙanƙance saboda rashin baccin da baka yi ba” ta faɗa tana faman 6ata fuska, yayi shiru yana kallonta batare daya furta mata komai ba.
“Kai nake sauraro! Meke damunka? Sannan naji kana waya ɗazu, akan za’a tura da jet zuwa sudan, wa za’a ɗauko”? Ta jefa mashi tambayar cike da son jin amsar shi.
Ya rasa amsar da zai bata, Ta kafe shi da ido.
Gyara muryarsa yadanyi kafin yafara magana a tsanake.
“Sheikh imam nake son gani, baya a ƙasarne ya tafi sudan, Ina buƙatar ganinsa da gaggawa akwai taimakon da zaiyi mani”
Fuskarta da alamun mamaki ta furta”meyasa kake son ganin shi? Wani kalar taimako zaiyi maka”
“Wani matashin yarone yake fama da aljanu sun hana rayuwarshi sakat, jiya ina zaune tare da baba muna yin firar yaushe rabo, a lokacin da bamuyi tsammani ba, yaron ya faɗo falon gwanin ban tausayi, duk mai imani idan yaji irin jarabtar da yaron yake fuskanta sai ya tausaya mashi.....” tun da ya fara magana gimbiya mujeedat ta yunƙura ta miƙe daga zaune tana dubanshi, Ya fayyace mata komai sai dai bai faɗa mata da suffar da ya ga yaron ba.
“Na yanke shawarar yin magana da sheikh Imam akan halin da yaron yake aciki, Ina da tabbacin zai taimaka mashi In sha allah, yanzu haka da nake yi maki magana, sheikh imam Yana akan hanya, Ina tsammanin nan da ƙarfe goma jirgin daya ɗauko shi zai yi sauka a nigeria.
Yanayin fuskartane Ya canza, yayin da take kallonshi, Ya rasa gane kallon menene take yi mashi, har dai yagaza jurewa jin shirun yayi yawa yace”baki fahimci abunda nake fadi bane? Ko bakiji dadi bane”?
Girgiza mashi kai tayi”ko ɗaya mijina, wani abune yadan bani mamaki, nasan halinka ne yin taimako, indai abune daya shafi aikin Allah kana akan gaba, amma tunda nake arayuwata ban ta6a ganin tausayi da ya kai wannan ba atare dakai, saboda yaron jiya ba ka yi bacci ba, aduk lokacin da ka dawo gida a yanayi na damu nasan yadda zan shawo kanka in kwantar maka da hankalinta harma kayi bacci, amma adaren jiya saboda damuwar halin da yaron yake, waɗannan dabarun nawa basuyi maka aiki ba, bayan haka ka tura da jirgin da zai dauko malamin da zai duba shi daga Sudan zuwa Nigeria, saboda kana buƙatarshi da gaggawa don ya duba yaron....” ta faɗa fuskarta da alamun ruɗani, yayin da Hateem ya natsu yana sauraronta abunda bata sani ba ayanzun ma da take yi mashi magana hankalin shi yafi karkata kan agogon dake sanye a wrist din hannun shi, burinshi goma ta buga.
“Abunda yafi ɗaure min kai mijina, wanene yaron? Menene alaƙarka da shi? Yanayin yadda ka nuna damuwa akanshi ko ɗan cikin ka sai haka”
Jim ya ɗanyi kafin ya furta”bani da alaƙa da shi, bansan shi ba! Kuma ban ta6a ganin shi ba, kamar yadda na faɗa maki adaren Jiya idanuwana suka fara yin tozali da shi, tun daganan sai naji ƙaunarsa ta kama ni, har naji ina son na taimaka mashi, sai nake jima kamar nike da alhakin ciwon shi, idan har ban taimaka mashi yaji sauƙi ba Allah zai iya kamani da laifin ƙin tallafa masa da banyi ba”
Murmushin gefen fuska Gimbiya mujeedat ta sakar mashi har fararen hakoranta suka bayyana.
“Kai din na dabanne mijina” ta faɗa tana matsawa kusa dashi, ta ɗaura hannunta na dama saman sumar kanshi.
“Samun miji kamarka a duniyar nan abune mai wuya, kana da tausayi da jinƙan na ƙasa dakaina, sannan kowa naka ne, burinka ka faranta ma wanda yake acikin kunci koda ta silar hakan kai zaka rasa naka farin cikin, ni kaina ina ilmantuwa da kyawawan