Showing 222001 words to 225000 words out of 250533 words
Chapter 75 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.
ɗabi’unka da halayanka, shiyasa nake alfaharin mallakarka da nayi a matsayin mijina” lumshe idanuwanshi ya ɗanyi kalamanta ba ƙaramin faranta mashi suke Yi ba, tamkar tana ƙarfafa mashi gwiwane.
Zame hannunta tayi daga kan sumar shi zuwa gefen fuskarshi idanuwansu cikin na juna
“Kamar yadda ka sani, duk abunda kakeso nima inason shi, koda bana son shi saina yi kokarin koya ma kaina yadda zanso shi saboda mijina yana son shi, don haka nima ina goyan bayanka akan Yaron, Allah ya baka sa’a mijina ya cika maka burinka na ganin yaron ya samu lafiya, A shirye nake dana bada gudummuwata wurin ganin mun inganta rayuwarshi”
Murmushine ya bayyana akan fuskar prime minister, kallonta kadai da yake yi natsuwa yake samu, musamman idan tana ƙarfafa mashi gwiwa da daɗaɗan kalamanta.
“In sha Allah zamuyi nasara, yaushe zaka bani iznin zuwa ganin yaron”?
“Na yanke shawara idan yaji sauƙi, zan gayyace shi zuwa gidan mu, zamu shirya mashi dinner.”
Tsantsar farin cikine akan fuskarta”naji dadin jin hakan mijina, wallahi har na ƙosa naganshi, duk na kagu gashi bazamu daɗe a ƙasar ba, kwanaki kadan suka rage mana” ta fada tana 6ata fuska alamar bataso hakan ba.
Damƙo hannunta yai da take kokarin shafa wuyanshi, fari sol dashi, ga wani shu’umin kamshi dake fita sako da lungu na jikinta, sumbatar tafin hannu yai, ba tare da ya sake shi ba ya dago da reddish eyes dinshi akan fuskarta”yaron marayane bashi da kowa, Owais ne ke kula da su, zan nemi alfarmar yabar min shi mu tafi canada atare, inaso ya maye min gurbin abunda narasa” sai yanzu ta fahimci damuwarshi.
Tausayinshi ne ya kamata, tuntuni tasan yana da burin samun ɗa Namiji, yaso ta ƙara haifa mashi ƴa’ƴa sai dai shiru babu alamun zasu sake samun ƙaruwa, kuma lafiyarta ƙalau saboda shi yasa bata yin tsarin Iyali, Allah ne bai nufa zata ƙara haihuwar ba.
Kafin ta buɗe baki tayi mashi magana, wayarsa dake ajiye cikin aljihun shi ta soma yin ringing, ya riga da yasan wanene Ya kirashi.
Da sauri Ya saki hannun Gimbiyarsa, Ya zura hannu ya zaro wayar picking call din yai tare da karata a kunnanshi, gimbiya mujeedat ta kura mashi ido tana kallon shi
“Alhamdulillah, Allah ya kawo ku lafiya,” iya abun da taji ya furta kenan, zame wayar yai daga kunnanshi yana dubanta yace”sun sauka lafiya”
Gimbiya mujeedat tace’shiyasa naga farin ciki akan fuskarka, sheik imam yaƙaraso kenan, bari nayi magana da masu aiki su shirya maku breakfast dinku”
Ta fada tana kokarin daukar phone dake ajiye on nightstand da sauri ya ruƙo hannunta, ta dago da ido suka kalli juna
“An shirya mashi breakfast dinshi, tun acikin jirgi, ina da tabbacin babu yunwa ko gajiya atare da shi, nafi buƙatar idan ya ƙaraso mu tafi gidan Owais din”
“Amma kaifa? Baka ci komai ba, Yakamata kayi breakfast dinka, zaka fi samun kuzari”
Girgiza mata kai yai”Bana buƙata, saboda bani da natsuwar cin abinci, Idan har yaron nan bai dawo dai dai ba, nafi son idan Ya samu sauƙi, muci abincin atare da shi”
Tsantsar mamakin kalamansa ne ya daure mata kai, bata ta6a ganin ƙauna kalar wannan ba, Ko a shirin film.
“Amma kasan bana iya yin breakfast ba atare dakai ba, idan har baka ci ba, nima bazan ci komai ba, har sai ka dawo gidan” cikin tausasa harshe tayi maganar.
“Yau kawai, Kiyi hakuri kiyi breakfast tare da su Yazrin, bazan jima ba, in sha Allah atare zamu yi lunch dinmu”
Kwa6e mashi fuska tayi hadi da marairaice mashi tamkar zatayi mashi shagwa6a ta furta”bazan takura maka ba, Na kar6i uzurinka”
“Ki tashi ki shirya inaso ku gaisa da shekh imam kafin mu wuce gidan owais” amsa mashi tayi da toh, kafin ta sauko daga saman gadon, shima ya miƙe yana bin bayanta da kallo, har ta 6ace ma ganinsa, jim kadan ta fito sanye da Abaya launin Maroon tayi rolling mayafi akanta, ruƙo hannunta yai acikin nashi, suka nufi kofar fita daga dakin.
Lokacin da suka shigo babban katafaren palourn gidan, masu yi masu hidimane suke ta gudanar da aikace aikacen su, kowan nan su sanye da uniform baƙin wando da farar shirt, matasan ƴan mata, duk inda Suka gifta jiki na 6ari suke gaishe dasu cikin girmamawa, yayin da su kuma suke amsa masu da fara’a.
Yanke shawarar zuwa bedrooms din Ƴa’ƴan su suka Yi, kafin ƙarasowar Ya sheikh, Yana da buƙatar suma su kasance cikin shiri donsu yi mashi kyakkyawar tarba.
elevator suka hau ta daukesu zuwa upstairs, bayan ta sauke su suka fito batare da sun saki hannayensu da suka ruƙe acikin na juna ba, kaitsaye suka nufi bedroom din ƴan matan su.
Gaba ɗaya ta tattara hankalinta akan Apple laptop din dake agabanta, yayin da take zaune a tsakiyar katafaren gadonta dake acikin hamshaƙin ɗakin kwananta daya gaji da haɗuwa, ko dakin sarauniya Albarka, farace sol kamanninta sak dana Mahaifinta Hateem, yadda kasan ta macen aljanna saboda kyanta da dirinta, kamanninta sun 6aci dana Hateem, tamkar yayi kakinta, Hasken fatarta ne kadai ta dauko na mom mujeedat da doguwar sumar kanta, mace ce mai aji, mai ji da ƙasaita da izza, bakowa bace wannan face NAZLI, itace first born dinsu, a ƙalla zata kai shekara ashirin da takwas a duniya, tana asanye da lace Camisole daga sama ta ɗaura silk robe launin hot pink, a tsanake take operating laptop dinta cikin ƙwarewa, yayin da kyawawan idanuwanta dake a manne da farin glass suke akan screen din laptop nata, daga gefen gadon ƙayataccen round table ne daga saman shi china tea set ne, jefi jefi takan kai hannu ta dauki cup ta kur6i coffee din dake aciki, Nazli agogo sarkin aiki bata gajiya tana da hazaƙa da ƙwarewa a 6angaren Iya kasuwanci, Company guda take juyawa na mahaifinsu dake a ƙasar Canada, ƙamshin turaren jikinta ya buɗe ko’ina na room dinta, hatta sumar kanta kamshin turaren data turara ma gashinta ne ke fita, kullum ne sai ta turara jikinta da gashin kanta, Nazli badai tsafta ba.
“Assalamu alaikum” Muryoyinsu ne suka janyo hankalinta ga duban ƙofar shigowa room dinta dake a kulle, daga inda take tana Iya hangen su ta cikin kofar, saukowa tayi daga saman gadon, sumar kanta ta rufe bayanta tamkar hijabi tayi mata, daura idonta tayi akan cashmere slippers dinta dake ajiye saman lallausan carpet, ta zura su cikin kafarta, kafin ta nufi kofar cikin takun izza, ta sanya hannu biyu ta ruko handle din kofar ta buɗe ta.
Fuskokinsu dauke da murmushi suke kallonta, sai dai ita babu alamun murmushi akan fuskarta, haka take bata da fara’a, taji dadin ganinsu amma bazaka Iya gane hakan ta yanayinta ba saboda tsabar ji da izzarta,
Cikin harshen turanci tace
“Good morning, Mom and Dad! I’m so glad to see you, yau kun riga ni zuwa room dina, yanzu nake koƙarin kammala aikin da nakeyi a laptop....”
Ta ƙare maganar tare da matsawa ta rungume daddynta, hannu biyu ya daura saman bayanta”barka da safiya daughter, Ina fata kin tashi cikin koshin lafiya”
Muryarta ƙasa ƙasa ta amsa mashi da cewa”
“I’m doing well, Dad. I’ve been thinking about you since yesterday. I’ve missed you.”
Gimbiya mujeedat tace”oh shi kaɗai ki ka gani shiyasa kika rungume shi ko? Da zolaya tayi maganar.
Ɗagowa Nazli tayi tare da miƙa hannu zata rungume mujeedat, da sauri gimbiya mujeedat taja da baya tana fadin”nayi fushi, ba tun yauba na lura kinfi ji da daddynki, shiyasa nima nafi ji da Yazrin daboda tafi nuna damuwa akaina”
Marairaice mata fuska Nazli tayi haɗi da kama kunnanta”agafarce ni sanyin idaniyata, mahaifiyata abun alfaharina”
Sakin fuska mujeedat tayi”nayi hakuri amma kada ki ƙara yi min hakan, Daga yau ni zaki fara hugging kafin daddynki” ta faɗa tana kallon Hateem dake kallonsu, fuskarshi dauke da murmushi yace”na fahimci kishi kike yi dani akan Nazli, Yarinya tafi son ubanta, da ni da ita ƙaunace mai ƙarfi, baki ga kamannin fuskarmu ba? Shiyasa take ji dani, ke kuma kije da Yazrin itace take kama dake”
Farfari tayi mashi da ido batare datace komai ba, ta rungumo nazli ajikinta tana ɗan bubbuga bayanta da hannu tace”sannu agogo sarkin aiki, tun da sassafe ko breakfast bakiyi ba kin fara danna laptop, Ina fata na same ki lafiya”?
Ɗagowa tayi da kanta tana fadin”Ina lafiya mommy, bana so aiki yai min yawa shiyasa nake ragewa” ta fada tana dubansu.
“Naji dadin ganinku, duk da ni yakama naje na sameku, ban samu damar yin hakan ba,”
Prime minister yace”bakomai daughter, muma munji dadin ganinki, Inaso ki shirya Zanyi baƙo Ƴan mintuna suka rage su ƙaraso, daga sudan zaizo, gaisawa zakuyi da shi,”
Batare da ta tambaye shi wanene zaizo ba tace”in sha Allah daddy, yanzu zan sauko down”
Amsa mata yai da toh, kafin ya dubi mujeedat, muje ko” ya runƙo hannunta suka juyawa zuwa dakin Yazrin,
A lokacin Yazrin tana daga kwance cikin bathtub dake a bathroom dinta, ta jiƙe jikinta da ruwan kumfa mai ɗumi, ta lumshe idanuwanta yayin da take shaƙar ƙamshin bath soft dinta daya karaɗe toilet din tamkar an fesa turare, A kalla zata kai shekaru ashirin da biyar, Yazrin ƙarshe ce afagen haduwa bata baro komai na mahaifiyarta mujeedat ba, launin fatartane kadai kalar na hateem, haskenta bai kai na mujeedat ba, daga ita har Yazrin babu wanda yafi wani kyau, ta inda suka banbanta Yazrin tafi Nazli sauƙin Kai da iya mu’amala da mutane, Ita Nazli bata son bare, ƙiwuya gareta kamar ƙaramar yarinya ga ji da izza, magana ma wuyar furtata take ji.
Sautin ƙarar door belt ne ya katse mata jin daɗinta, A hanzarce ta ɗaure jikinta da ruwan dumi, kafin ta fito ta ruƙo towel dake sagale jikin hanger ta ɗaure qugunta da shi,
Shigowa Bedroom din tayi da sauri ta nufi wardrobe dinta, shaf shaf ta zura jallabiya a jikinta, ko tsane jikinta bata samu damar yi ba, sumar kanta duk ta nannaɗe saman kafadunta.
Buɗe kofar ɗakin tayi fuskarta dauke da kayataccen murmushi, dimples dinta biyu sun lotsa
Su kansu da sukayi tozali da ita saida suka saki fara’a, Yarinyar akwai shiga rai, da wuya kaga fuskarta adaure, kafin su bude baki suyi mata magana ta ware hannayenta biyu ta hadasu ta rungume tana fadin”Mom dad, tunkafin nazo gaishe ku kun riga ni zuwa, kunsa naji nauyin hada ido daku”
Ta faɗa tare da ɗagowa da kanta tana faman kare fuskarta da tafin hannunta
Dariya kowan nan su yasaki, Prime minister yace”barka da safiya daughter, fatan mun same ki lafiya”? Jinjina mashi kai tayi”lafiyalou daddy, amma ni baku kyauta min ba, maimakon ku bari ni in fara zuwa gaishe daku” ta fada tana bubbuga ƙafafuwanta da shagwa6a.
“Ladar da nake kwaɗayin samu, Kun rigani kwashe ta” dariya mujeedat tasaki tana fadin”Wato ke har yanzu baki girma da shagwa6a ba”
Hateem yace”barta tayi abunta, don bata da ƙanine shiyasa take yi mana shagwa6a”
Nuna kanta tayi da yatsanta”saboda nice auta mommy, dagani babu ƙari, kunga kuwa dole nayi shagwa6a” ta fada tana ruƙe masu qugu,
Ba ƙaramin nishaɗi take basu ba, Hateem yace”baki fada mana ya kika wayi gari ba,”
“Na tashi lafiya daddy, tun safe nasha coffe, yanzu haka wanka nakeyi a toilet naji ƙarar knocking dinku shiyasa na fito”
“Kina nufin baki ƙarasa wankan ba”? Acewar mujeeda.
Yazrin tace”tun ɗazu fa na kammala, kawai inajin daɗin kwanciya acikin ruwane”
“Okey, Ki koma ciki ki shirya muna jiranku a downstairs, daddynku ne zai yi bako daga kasar sudan, yanaso ku gaisa dashine”
Yazrin tace”okey mom, bari na shiga ciki in shirya”
Ta fada tare da kallon Daddynta, harta buɗe baki zatayi mashi magana, sautin ƙarar dirar motocin dake shigowa gidan nasu ya katse mata hanzarinta, muryarta tamkar tame yin raɗa ta furta”bakon ya karaso kenan, bari nayi sauri naje na sanya kayan mutunci” ta juya da sauri ta shige cikin dakin
Murmushi kowan nan su yasaki, mujeedat tace”yazrin kenan, tana bani nishaɗi, sai dai narasa gane halin wa ta dauko atsakanin nida kai”
Nuna ta yai da yatsa”ke mana, har sai an fadi, ni dai kin san ba haka nake ba, idan kika dubi ɗabi’un Nazli sak kalar nawane”
Hararar zolaya ta yi mashi”nazli fa hada izza ta sarauta ke ɗawainiya da ita, kai ina kaga sarauta? Nice na gajeta, sai dai ta 6angaren siyasa nan kafi karfi, kuma shi ɗan siyasa da fara’a aka sanshi, hakan na nufin halinkane yazrin ta dauko bani ba”
“Gorin sarauta zaki yi min”? Ya faɗa yana kanne mata ido.
Tana dariya tace”ni dai bance ba, ai kafi ƙarfin ayi maka gori, dani dakai babban gorone magogin ƙarfe”
Ta fada tare da ruƙo hannun shi”muje kada su jimu shiru, ina tunanin sune suka ƙaraso” atare suka nufi down stair.
Adai dai lokacin zungureriyar motar da ta ɗauko Sheikh imam daga airport, ta karaso bakin entry hall nagidan Prime minister a hankali tayi parking, gaba da bayanta motocin sojoji ne da suka dauko shi domin bashi tsaro, fitowa sukayi daga cikin motocinsu, wani ƙato daga cikinsu ya buɗe mashi murfin mota, A hankali sheikh Imam malik Ya zuro kafarsa ta dama dake asanye cikin takalma na alfarma, kafin Ya ƙarasa fitowa, masha Allah, magadan annabawa, kallon ɗaya zakayi mashi ka shaida maluntakarsa, yayi shiga ta alfarma shiga ta larabawan saudi arebiya, farar throbe ce, daga sama ya daura wata shara sharar riga, kanshi yana asanye da kufi ƴar karamar hula ta malamai, an nannaɗeta da black turban, Yana da godon gemu, babban mutunne ya manyata don harya fara tsufa gashin gemunshi hada furfura ta manyantaka, duhun fatarsa mai kyau ne, kai daga ganin shi baida wasa irin malaman nan ne masu zafi akan addini, babu tsoro a idanuwanshi, mutunne mai cikar kamala, ya shahara a 6angaren wa’anzartawa da yin da’awa ta addinin musulunci, yayi gwagwarmaya a kasashe daban daban babu inda bai shiga, kuma yana cin nasara akan da’awarsa, shaidanun aljanu kansu tsoronshi suke Ji, Suna jin shakkar zama a inda shekh imam malik yake, mutunne shi mai koyi da sunna ta manzon Allah SAW, Ya ruƙe Allah ɗaya azuciyarshi, kainuwane shi dashen Allah, badai mutun ba sai Allah, ta ko’ina jikinshi ƙamshin turarensa ne mai dadin shaƙa a hanci, hannun shi na dama ruƙe da cazbaha.
A hankali Yake bin ko’ina da kallo, Yayin da yake shaƙar kamshin iskar data gauraya da ƙamshin turarensa.
“Ya mu’allim, mu ƙarasa shiga ciki,” ɗaya daga cikin Sojojin ne yai mashi magana haɗi da nuna mashi kofar shiga babban falon, ɗaga kafarshi yai atsanake yake yin tafiya, suna gab da zasu shiga falon, Prime minister ya fito tare da gimbiya majeedat, Murmushin dake kan fuskokinsu ne ya ƙara faɗaɗa, da sauri hateem Ya mika mashi hannu suka gaisa cikin girmamawa”Marhaban bika babana, barka da sauka, ya gajiyar tafiya” ya fada tare da rungumeshi, bayan sun raba jikinsu daga na juna Sheikh imam yace”ai ni babu gajiya atare dani, ni da aka gatantani kamar wani basarake haka aka daukoni a privet jet, hankali akwance naci na koshi na cika tumbina” Ya fada yana nuna tumbinshi da cazbahar hannunshi, gaba daya suka sanya dariya gwanin ban sha’awa, sheikh imam mutunne mai son barkwanci amma fa sai idan yaso.
Prime minister yace”Akara makallah ai kafi karfin basarake awurinmu, ku fa magadan annabawane, kunfi duk wani mai muƙami a karkashin tafin kafarku Yake”
Murmushi Shekh imam Yasaki, Tare da daura idanuwanshi kan fuskar Gimbiya mujeedat, kafin yayi magana tayi saurin gaishe shi cikin harshen larabci.
Da zolaya yace”Hateem dama ana ganin fuskar matarka? Ya akai yau baka rufe lu’u lu’un ka ba”? Koba ita bace matar nan da ake yi mana 6oyanta ba? Kodai Ƴarce”? Kunyace ta rufe gimbiya mujeedat, Ta sanya hannu ɗaya ta kare fuskarta
Hatta jami’an dake a kewaye da Ya shekh Imam saida suka saki murmushi .
Dariya prime minister yasaki a fakaice ya harari Jami’an dake atsaitsaye suna kallonsu, jiki na 6ari suka juya kowa yakama gabanshi, don sun fahimci me yake nufi, wato suna kalle mashi matarshi.
“Ya sheikh Mu ƙarasa cikin falon, mun barka atsaye gashi ka kwaso gajiya” prime minister ya fada tare da ruƙo hannun shi, Suka nufi babban falon Gidan, Gimbiya mujeedat tana abiye da su.
“Hateem Irin wannan daula haka? Anya kuwa kuna tunawa da mutuwa? Ka ajiye lu’u lu’u agidanka ga kuma kayan alatu ta ko’ina, maimakon ku bari sai mun shiga Aljana muji daɗi” Ya faɗa yana Jijjiga cazbahar hannunshi, Dariya suka sanya gaba dayansu, A saman Royal sofa kowan nan su Ya zauna, suna fuskantar juna da sheikh imam, sai faman jinjina kai yake yi yana bin gidan da kallo, duk maganar da sheikh imam zaiyi yanayin amfani da harshen turanci saboda mujeedat yasan bata jin hausa sai dai turanci da larabci.
“Yanzu kai hateem, Har kake iya kwana acikin daular nan? Wannan haɗuwa haka ai sai mutun ya manta da tur6aya aka halicce shi”
Murmushi suka saki suna dubanshi
Sautin takun takalman Yazrin da Nazli ne Ya janyo hankulansu ga dubansu,
Hannunsu ruƙe cikin na juna suke yin tafiya suna tunkarosu, kowaccensu ta yafa mayafi akanta,
Bayan sun ƙaraso, Cikin girmamawa suka gaishe da shekh Imam, Abunda Ya burgeshi da yaran tarbiyarsu, A saman lallausan carpet din dake a atsakankanin Royal sofa din suka zauna kowaccensu ta nade kafafuwanta
“Masha Allah, Matan hurul aini har a duniya, Hateem, wacce zaka bani acikinsu in cike sunnah”? Ya faɗa yana duban faces din Yazrin da Nazli, Yazrin sai famam sakar mashi murmushi take Yi, Nazli kuwa tunda ta gaishe dashi ta sunnar da kanta ƙasa.
“Duk wadda ka za6a malam, zamu baka Ita” acewar mujeedat,
Shekh imam yace”Uwargida maganarnan taki bata kai zuci ba, ni nasan kin faɗine kawai, taya zaku ba yarinya auran dattijo? Mai jan cazba, balle ƴan matan zamani basu son auran malamai”
Murmushi kowannansu yasaki, banda Nazli.
Biyu daga cikin masu aikin gidanne suka nufo falon, hannunsu ruƙe da faɗaɗan farantai daga sama an jera drinks masu sanyi da snacks.
Tunkafin su karaso sheikh imam yace”waɗannan fa? Badai