Kurkukun Kaddara 3 Original Document Takun karshe
Chapter 13 of 19
sai an ƙaru da baiwar da Allah yayi mashi na iya tsara kalami, ga farin jinin dake gare shi, gidajen jaridu basu da abin yaɗawa daya wuce ziyartar national assembly da prime minister yayi, komai daya tattauna da shawarwarin daya bama shuwagabannin Nigeria, saida ƴan jarida suka yaɗa shi a social media, duk aranar ya ziyarci gidajen marayu da gidan Yari, yayi masu kyaututtuka naban mamaki wanda ya gigita mutane zunzurun kuɗi ya bayar da za'a tallafi rayuwarsu da shi, aranar talata yabar garin abuja shi da Iyalan shi da ƴan uwan shi tun daga kan senate lateef his excellency deen and his excellency abdul razak tare da Sharafudden da hajiya saratu, Sir mubarak da kuma muƙarrabansa na ƙasar canada, Chief of staff, national security advisor, 6angaren masu ba su tsaro Royal canadian mounted polices and Nigerian Soldiers.
kasancewar A privet jet din mai girma sharafuddeen suka yi tafiyar basu jin wahalar zuwa ko'ina, arana ɗaya sai suje har sama da gari uku, ƴan mintuna jirgin yake sauke su suje inda zasu je, kafin marece su lula zuwa wani state din.
Wuri na farko da suka fara ziyarta bayan barin su abuja, masauratar yarbawan jihar lagos suka fara sauka an mutuntasu an kuma karramasu sanin matsayinsu a ƙasar, kafin suka Wuce Garin Kano, anyi masu kyakkyawar tarba, kwana ɗaya su ka yi awashe garin ranar da zasu baro garin saida suka biya kasuwannin kano da gidajen tarihi da gidan gwamnati, daga bisani suka ziyarci jihar bauci, a katafaren wurin shaƙatawar nan me suna Yankari anan suka yaɗa zango tare da gwamnan jihar, haƙiƙa Prime minister ya mori lokacin shi a Nigeria, yaji dadin yawon buɗe idon da suka je tare da ƴan uwanshi, sai dai abu ɗayane bai goge ba a tunanin shi wato Danish, da shi yake kwana da shi yake tashi, ko abinci zaici saiya tuna da shi, aranshi ya ayyana inama ace hada shi suka taho yawon nan da Allah ne kaɗai yasan irin farin cikin da zai yi.
A ranar Alhamis suka dawo Birnin Abuja amatuƙar gajiye, friday za'a shirya mashi family dinner, Ranar sataurday Hateem zai bar Nigeria agurguje zasu koma Canada.
____________________________✍️
Idan muka koma 6angaren su Unaisah cikin ƴan kwanakin nan wata irin shaƙuwace ta shiga tsakaninsu da ummin america, musamman Batool sun kulle da ita, Har karatun kur'ani ta fara ƙoƙarin koya masu ranar da suka ji ta yi masu ƙira'a tsantsan mamaki ne ya kama Unaisah, don ita bata ta6a tsammanin ummi ta iya karatun kur'ani ba sai gashi tana yi mata ƙarin karatu cikin suratul baƙra, har tambayarta tayi aunty ummi dama kin iya karatu, sai tayi dariya tace mata hadda gareta ai, tun tana ƴar shekara goma sha bakwai ta haddace alkur'ani mai girma, Unaisah ta jinjina mata aranta ta ayyana amma ya akai take aikata sa6on Allah bayan ita din mahaddaciyar alƙur'ani ce, wata kil kuma wata jarabtar ce ta ubangiji Allah wa'alamu.
Damuwarsu ɗaya ayanzu Ɗan uwansu Danish yaƙi dawowa dai dai, Har yau babu wani cigaba kamar kullum yana akwance idanuwanshi arufe wanka da cin abinci su boss ne ke taimaka mashi, da kuma salsabeel dake zuwa dubashi kusan kullum sai yazo, tare da shi ake ɗawainiyar kula da garkuwa, haka zalika sheikh imam kusan agidan yake wuni, wurin yi mashi addu'o'in da zasu bashi kariya, Hatta Ƴan uwan shi su Sajeed sai da Imam malik Ya koya masu addu'o'in da zasu dinga yi mashi hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, sau uku suke zuwa duba shi a ɗakin shi don suyi mashi addu'a safe rana da dare, Ita unaisah har tsakar dare tana zuwa ɗakin shi ba tare da sanin kowa ba, duk ta ƙagara ya yadawo hayyacin shi, akwai abubuwa da dama da take son yi mashi albishir, na farko tana so ta faɗa mashi dangane da prime minister Hateem dake kama da shi na biyu abun arziƙin daya fara fito mata a ƙirji, ta riga ta yanke shawarar fada mashi idan ya dawo normal, ta hana kowa yagansu a 6oye take ɗaure su da mayafi ta matse su don karsu bayyana agani, abunda bata sani ba, batool tuni ta ganota duk in zata shiga toilet tsakar dare don tayi masu kallon ƙurulla sai batool tayi mata la6e, ta dinga tiƙar dariya kamar cikinta zai ƙulle.
Tun ranar da ummi tayi tozali da sheikh imam bata ƙara bari sun haɗu ba, da zarar yazo gidan take komawa ɗaki ta zauna ko bakin ƙofa bata fita har sai ta shaida tafiyar shi tukunna take saukowa down stairs.
A 6angaren su Benazir, since last week taso zuwa gidansu Aneelerh Allah bai nufa ba, saboda rashin samun layin Abie din Aneelerh, Alhaji ubaid yayi trying layin shi baya shiga, kuma shi kaɗaine dama yake da numbar shi, Adole Benazir ta haƙura da zuwa gidan su tun da bata da hanyar da zata samu address din su, bata ji dadi ba gashi har Mamie tafara yi mata zancen komawarsu Jos, don ma alhaji ubaid yace ba yanzu ba sai sun cike wata ɗaya ai da tuni sun jima da komawa, mamie bataso hakan ba, saboda ita bata son suna zama gidan Alhaji musa, badan bata jin daɗin gidan nashi ba sai don saboda ranta dake raya mata cewar ba don Allah yasanya suka zo gidan shi ba, don kawai yaji daɗin juyasu son ranshi shiyasa yake son su zauna masa agida, taci alwashin indai Alhaji ubaid bai basu damar komawa joss ba cikin watan nan to zata kama hanya ta tafi ne koda ita kadaine! Sauƙinta ɗaya Hajiya sarah tana janta ajiki matar tana da mutunci duk in tadawo daga office sai ta ware masu lokaci sun shiga garden ita da mamie donsu tattauna kan abunda ya shafi rayuwarsu da ta ƴa'ƴan su, ba ƙaramin ɗebe mata kewa take yi ba.
Haka Itama zeenatu bata da matsalar komai ayanzu, Benazir ta zama tamkar ƙawarta, har gyara mata gashi takeyi tayi mata kwaliya, dr shureim ne yake daukarsu a motarshi su fita yawon shaƙatawa, kullum sai sun fita yawo ko gajiya basayi. To meya fi ransu? Nima da zan samu mai fitar dani yawon binshi zanyi.
A 6angaren Pravin kuwa, Takaicin duniya Ya ishe shi, tun da yaji cewar baba obie ya amince yaran su cigaba da zama a estate dinshi duk irin wahalar dayasha wurin ganin ya tunzurasu donsu ƙi amincewa da shi amma abanza, baƙin ciki da hassada ne ke damun shi, Ranshi ya 6aci matuƙa ya kuma ci alwashin sai ya raba alaƙar yaran da chief owais, burin shi kawai su bar estate din. Ko ita hajiya saratu a yanzu tadaina damuwa da zancen yaran tun da taji hukuncin da baba obie ya yanke sai ta sanyama zuciyarta salama, idan pravin yai yunƙurin tunzurata don taje ta tada maganar a wurin baba obie, sai tace mashi itafa yanzu bata su take ba, tun da ba'a kanta suke zaune ba, Owais shi zai kula da komai.
Idan ta faɗi hakan sai yaji tamkar ya rufe ta da bugu.
Kullum tunaninshi ta wace hanya zai 6ullowa lamarin???
Alhamdulillah Jikin dr. Jazz yayi sauƙi, da taimakon ƴan uwanshi da suke bashi kulawa, har gida yake shiga don ya gaishe da Baba Obie, sannan yaci gaba da zuwa gidan su khadeeja kamar yadda ya saba zuwa domin duba lafiyarta.
Idan muka koma wurinsu Aneelerh, shiru har yau zahra tana zaman jiran sakon Hajiya saratu harta fara tunanin kodai dama wasa take yi mata ne? Ko kuma tayi mistake ne wurin tura mata hotunansu twins don ta za6i ɗaya? Tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi ta riga data ƙwallafa rai akan su twins shiyasa duk ta damu kanta, kullum ne saita duba chat dinsu da hajiya saratu har tsakar dare duk don taga kota tura mata amsar maganarta amma shiru kake ji har yau, ganin yadda ta ɗaga hankalintane yasa Aneelerh kwantar mata da hankali tace taci gaba da addu'a idan rabonta ne zata samu, sannan tayi mata uziri watakil tamantane ko kuma ta shiga busy a aiki shiyasa bata samu damar bata amsa ba,
Aneelerh Ba ta jima da fada mata hakan ba, Sai ga mahboob yazo masu da labarin tafiyar da sukayi zuwa wasu states din nigeria, Jin hakan yasa taji sauƙi acikin zuciyarta.
Hajiya adama tun bayan da suka kawo baby junaid, kusan kullum saita kira donsu gaisa dashi har video call suke yi, ta jima tana mamakin yadda junaid yake yi mata surutu idan ta kira shi awaya, amma lokacin da aka kai masu shi kamar wani salihin bawa baya surutu sai in yana son cin wani abu tukunna yake buɗe baki yace abashi, nan take ta fahimci yafi son zama wurin mommynsa, yanzu tasama ranta dangana bazata ƙara raba shi da maman shi ba, idan tana son ganin shi ita za ta je gidan ko kuma ta gayyaci aneelerh tazo mata da shi, yanzu haka Aneelerh ta fidda masu lokacin da zasu je gidan ita dasu mami da ummi hada su uncle ɗan Iya gaba dayansu zasu je kai masu ziyara, tun da ta sanarma hajiya adama farin ciki kamar ta zuba ruwa ƙasa tasha, taji dadin zancen zuwansu................
Atakaice kenan abubuwan da ke faruwa atsakanin family din kowani 6angare.
*💋BABE UNAISAH ANGEL❤*
fitowa tayi daga toilet, Jikinta asanye da bathrobe fara ƙal ta ɗaure igiyoyin rigar saitin waist din ta, fatar jikin ta da alamun lemar ruwan wankan da tayo, A hankali take tafiya tana tunkarar Dressing Mirror, ta wutsiyar ido take kallon Batool dake akwance saman gadon su, tana fuskantar ceilling tamkar maiyin bacci, alhalin nan kuwa idonta biyu....
On mirror Chair Unaisah ta zauna, fuskarta babu annuri babu walwala, kamar bata da ƙoshin lafiya ko wani abunne ke damunta wanda yayi silar canzawarta.
Body lotions din su ta ɗauko ta buɗe murfin, ta soma bin ko'ina na jikinta tana shafe shi da mai.
Bayan ta gama shafa man, ta feshe sako da lungu na jikinta da turare, ƙamshin shi ya buɗe room din, hatta Batool sai da ƙamshin Ya ziyarci Hancinta.
Sumar kanta ta soma gyarawa, ta busar da ita tabi da smoothing serum ta cuccuɗata, tunkafin ta kammala kunnuwanta suka Jiyo mata sautin knocking ƙofar room dinsu da ake Yi daga waje.
"Batool, nasan idonki biyu, je ki leƙa ki ga wanene ke yi mana knocking, may be ko aunty ummi ce,"
Fuskar Batool Ayamutse ta buɗe idanuwanta, ta sauko daga saman gadon tana miƙa haɗi da yin hamma ta nufi ƙofar, ƴar rigar dake a jikinta bata wuce gwiwarta ba.
Buɗe ƙofar ɗakin tayi, tare da leƙawa ganin big guy ne yasa tayi saurin zuwa ta dauko Mayafi ta lullu6e kanta kafin ta dawo bakin ƙofa ta kuma leƙawa tana fadin"Barka da safiya Ina kwana"
Kamar kullum da face mask a fuskarshi ya amsa mata da lafiyalou, yakike fatan na same ki lafiya' bayan sun gama gaisawa yace"ina Jari "?
"Tana a ciki, Yanzu ta fito daga wanka, ko in kira maka ita"? Ɗaga mata gira yai alamar eh, juyawa tayi da sauri ta shiga dakin, A lokacin Unaisah ta koma gaban Closet dinsu, tana laluban Suturar da zata sanya, Jin motsin shigowar ta yasa ta juyo tana kallon Batool
"Wanene"?
"Big guy ne Yake son ganin ki"
"Ni kuma"? ta faɗa da alamun mamaki"ni nama yi tsammanin boss man ne, Ko me zai faɗa min bari dai naje naji dame yazo"
Ta faɗa tare da ɗaukar Hijab ta zura ajikinta, Ta nufi ƙofar dakin cikin girmamawa ta gaishe da shi ya amsa mata da fara'arsa
"Batool ta fada min kana nemana, gani toh" yadda tayi maganar taso ta bashi dariya.
"Kina wani abune"? Girgiza mashi kai tayi"a'a, ba abunda nake yi"
"Yawwa My baby Girl, Kin tuna maganar da muka ta6a yi dake last week"? Shiru tayi tana faman ƙyafta ido a ƙoƙarinta nata tunano maganar da sukayi
"Namanta, ka tuna min mana"
Numfasa yai kafin yace"ba kince kinaso kiyi ma chief namu godiya ba game da alkhairin da yake yi ma ki" murmushi tasaki tare da cewa na tuna.
"Good, Yanzu abun da nake so dake, Kinga ni ke ɗawainiyar kai mashi abinci har ma da gyara mashi room din shi, saboda bai yarda da kowa ba Yana da wuyar sha'ani, Nima don ya aminta dani shiyasa ya yarda ina masa aiki a part dinsa, abun da Yakamata Yanzu ke nakeso Ki cigaba da zuwa part dinsa kina yi masa hidimar kai mashi abinci, breakfast lunch and dinner, sannan yana yawan shan coffee, a rana sau shida nake kai mashi, gyaran daki kuma sau biyu ne safe da dare before ya kwanta bacci, sai kuma gyaran falo dinsa da toilet dinsa da dressing room din shi hada gym room dinsa......" tunda yafara kora mata jawabi, ta zaro mashi idanu waje tana kallon shi, ganin kamar ta ruɗene Yasa shi sassauta muryarshi yace"Ko ba ki Iya aikin mata bane"? Murmushin yaƙe ta sakar mashi tare da cewa"Na Iya, amma naji kace Yana da wuyar sha'ani kuma bai yarda da mutane, Tayaya zai yarda Ina zuwa part dinsa yi mashi aiki"? Ta jefa mashi tambayar tana duban shi.
"Kada ki damu, zai yarda da ke, abun da yasa kika ga Na baki wannan aikin saboda ta hanyar kyautata mashi ne kaɗai zaki Iya biyanshi da ɗawainiyar da yake yi maku, tun da shi ba'ayi mashi godiya baiso,"
Jinjina kai tayi kamar tana fahimtarshi,
"Shikenan, Yaushe zan fara zuwa yi mashi aikin"?
Murmushi yasaki jin ta amince fatan shi Allah yasa Chief Ya yarda da ita.
"Yanzun nan zaki fara aikin, Gyara mashi Room dinsa, baya aciki daga sallar asuba ya nufi gidan kakansu Obie, kafin Ya dawo please ki tabbatar kin gyara mashi ko'ina na part dinsa, before ki gama ni kuma zan kawo maki breakfast din shi, duk idan nakai mashi abinci sai na tsaya nayi serving nashi kema haka za ki yi, nasan kina da natsuwa chief baison mutun mai ƙazanta yana son mai tsafta, kullum ki tsaftace jikinki da suturar ki kafin ki shiga part dinsa.... " wani kallon take bin da shi a fakaice.
"Baka da matsala dani, In sha Allah zanyi komai yadda ya dace,"
Har cikin ranshi yaji daɗin maganar data furta mashi,
"Mu je in nuna maki ɗakin" da sauri tace"Ai ban gama shiryawa ba, ka bani mintuna yanzu zan dawo" amsa mata yayi da toh, da sauri ta koma ɗakin a lokacin batool ta shige bathroom tana wanka.
Shaf shaf ta nufi glass wardrobe dinsu, ta shirya kanta cikin Turkish gown launin Yellow, rigar tayi mata kyau ta kuma bi shape din jikinta, tana da belt a tsakiyar ta, tayi rolling mayafi akanta, kafin ta ɗauko Cashmere slippers mai gashi gashi launin yellow ta zura a ƙafarta.
Bayan ta kammala kimtsawa, Ta fito daga ɗakin, Shi kanshi Big guy daya kalle ta sai da gabanshi Ya faɗi ganin kyan da tayi, satar kallonta ya dinga yi batare data ankara ba.
Tafiya suka soma Yi, tana abiye da bayanshi, tayi tsammanin upstairs zasu hau amma sai taga Ya nufi elevator, Zaro idanu tayi ganin inda zasu shiga, tunda take arayuwarta bata ta6a hawa elevator ba sai yau, wani irin daɗi take ji, musamman da suka shiga daga ciki, tayi sama da su A hankali ta sauke su a second floor, kofar ta zuge, fitowa yai daga ciki da sauri tabi bayanshi, abakin kofar ɗakin nan data ta6a zuwa kwanaki taga wani mutun Yana motsa jiki nan yakaita nan take ta gane cewa shine ɗakin kuma mutumin da tagani shine chief dinsu.
Abakin door room din suka dakata da yin tafiyar,
"Ƙofar tana da password, ba zaki Iya shiga ciki ba tare da kin sanya password din taba, sai kuma idan shine ya baki iznin shiga" ɗaga mashi kai tayi alamar toh.
"Amma yanzu babu security din ƙofar zaki iya shiga, sai dai ki kula please banda 6arna" dariya tayi tana fadin"6arna kuma sai kace wata ƙaramar Yarinyar"
"Nasan ki da ƙiriniya, shiyasa na faɗi hakan"
Yamutsa mashi fuska tayi batare da tace komai ba, Ya buɗe mata ɗakin Yace ta shiga ta fara aikin idan ta kammala yana s falo Yana jiran ta" amsa mashi tayi da toh, sai da taga Ya bar part din tukunna tayi sallama ta shiga daga ciki.
Kamar yau ta fara ganin dakin, dama time din farko data fara shiga bata samu damar ƙare mashi kallo ba, har mamaki takeyi idan ta tuna mai rai ne ke rayuwa a dakin, Kamar baza'a mutu ba, komai ka kalla mai tsadane da inganci furniture din dakin har daukar ido suke yi idan ka kalle su, tsabar haɗuwarsu.
Ga wani sanyin A.c mai haɗe da ƙamshin room freshner har cikin hancinta take shaƙar shi.
A ƙalla ta 6ata tsawon mintuna, kafin ta soma tambayar kanta, meya kawo ta dakin? Don ita bata ga abun da zata gyaraba, babu datti ko kaɗan komai a gyare yake kamar yau aka fara amfani da ɗakin, har ƙwara bedsheet dinsa Ya tattare alamar anyi amfani da shi.
Ɗaura idanunta tayi akan Toilet dinsa, daga inda take tana kallon komai dake aciki ta jikin glass din bangon , atsaftace yake komai na cikinsa fari ne ƙal.
Ruƙe qugu tayi da hannu aranta tana fadin"Ikon Allah, To ni meye amfanin zuwana part dinsa? Me ake so nayi! Bayan babu wani abu da zan gyara, ni wannan dakin ma in nawane ai say yayi sati kafin in gyara shi"
Ta jima atsaye ba tare da ta ta6uka komai ba, tunawa da big guy dake jiranta a falo, ne yasa tayi saurin nufar gadon chief, Ta soma gyara shi, bayan ta gama ta koma tana jera mashi turarurrukansa da body lotions dinsa da yayi amfani da su da safe, cikin ƙanƙanin lokaci ta gama gyara ko'ina na part dinsa..
Fitowa tayi daga part dinsa ta sauko down, Babu kowa A falon, Ƴan uwanta duka suna a bedrooms dinsu.
"Kin gama gyaran"? a hanzarce Ta juya Baya jin muryarsa, Big guy ne ya nufe ta hannun shi ruƙe da haɗaɗden wooden tray madaidaici daga saman lafiyayyan breakfast ne.
"Na gama,"
"Madallah sannu da ƙoƙari" tace mashi yawwa,
"Yanzu ki