Karfe A Wuta

Chapter 103 of 167

akwai haɗarin gaske, amma yanzu burikana biyu ne, bayan ganin bayan Bunkure foundation, sai wanke Viper daga zargin da ake yi masa"

Da sauri ya ce "Kamar yaya?"

"Kamar yadda nake gaya maka, bana nufin na sanyaka a matsala, kamar yadda ka taimakeni kwanaki a kansa, yanzu ma ina neman taimakonka, dan Allah"

"Nabila, wannan wasa da rai ne fa, ke ya aka yi ki ka san ba shi da laifi? Tayaya zakinkare mutumin da hukuma take nema ruwa a jallo?"

Nabila ta numfasa ta ce "Zaka ga ta yadda zan yi, ni dai haɗin kanka nake buƙata da taimakonka"

Ya girgiza kai ya ce "Nabila matana biyu fa da yara uku, haka kurum ki saka su zama zawarawa da marayu, na gaya miki case ɗin sa yayi involving manya haka kurum ki ja mana fitina muna zaman lafiya"

Cikin marairaice wa ta ce "Dan Allah yaya habib, ba zan bari sunanka ya fito ba, dan Allah copyn file ɗin sa nake so, da aka yi masa shari'a shikaɗai nake buƙata"

Ya ce "Taɓɗijan, ke kin san uban process ɗin da na bi, aka baki ki ka gani wancan lokacin, balle yanzu kicw copy ki ke so"

"Dan Allah ka taimake ni barrister Habib"

Yayi shiru sannan ya ce "Gaskiya sai kin bani lokaci, dan wanan aiki ne da yake buƙatar ɓoyayyiyar gwagwarmayar "

Cikin farinciki ta ce "Zaka nemo mini ɗin?

"Zan jarraba ne na gani idan zai yiwu, ba alƙawari nayi miki ba"

Ta miƙe cikin farinciki ta ce "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi ya raya zuriya"

Ya amsa mata da Amin.

***

Ramma tana ta gogewa Abdul labcourt ɗin sa, ya daɗe a tsaye yana kallonta, wani irin matsanancin tausayinta ne ya mamaye zuciyarsa.

Ya ƙarasa ya zauna ya ce "Rahama" ta ɗago ta kalleshi.

"Ina da masu gugu fa, kaiwa nake yi ayi mini, ki ke wahalar da kanki"

"Ka ce zaka yi tiyata, shiyasa nake goge maka"

Yayi murmushi ya ce "Ai ba da labcourt muke shiga tiyata ba, kayan tiyata daban suke"

Ta ce "Ok, duk da haka ka saka wani lokacin"

Ya jinjina kai ya ce "Rahama menene babban burinki a rayuwa ne?"

Ta sunkuyar da kai ta ce "Ka mayar da ni wurin mamana"

"Na san da wannan, zan mayar da ke, burinki na rayuwa?"

Ta ɗago idanu ta kalle shi ta ce "Babu"

Ya ce "Kamar yaya? Kowane ɗan Adam yana da buri da yake son cimma a rayuwarsa"

Rahama ta kashe socket, ta kalleshi ta ce "Wace rayuwar? Rayuwar da ka gama kassarawa wane buri ne yayi mini saura? Ka mayar da ni wurin mahaifiyata na ƙarasa rayuwata shikaɗai ne roƙona a gareka, amma ba ni da wani sauran buri da nake da shi, gaba ɗaya rayuwar ta fita daga raina, babu abun da yake burgeni yake bani sha'awa".

Abdul ya koma kusa da ita ya zauna, ya ɗan tsura mata ido, ita kuma ta kawar da kanta gefe ɗaya.

"Dukkanin mai rai baya fitar da rai, da cimma burikansa na rayuwa, na san ni ne musababbin rushewar naki, amma haryanzu ina dana sanin abun da na aikata, amma zan cika miki burinki Rahama, zaki koma makaranta kiyi karatu mai zurfi in dai muna tare in sha Allah, makaranta mai kyau zan mayar da ke, na gyara makarantun garinku, kuma an karɓi ƙudurin gyaran hanyarku, aiki yayi nisa na yi muku boreholes kamar yadda nayi miki alƙawari, idan aka kammala zan nuna miki"

Maimakon ta yi magana, kawai sai ta fashe da kuka.

Cikin damuwa ya ce "Rahama menene kuma?"

"Ni duk bana son wannan abubuwan, kawai na koma gidanmu na ƙarasa rayuwata, babu wani abu da zan zama a rayuwa da zai katange ni, daga tsangwamar da zan fuskanta a cikin al'umma, wannan ɗabi'a ce ta hausawa"

"Ina tabattar miki da idan muna tare, babu wanda zai tsangwame ki, wasu shirye shirye nake yi ne, da sun tabatta in sha Allah zamu je ki ga mama, amma babu maganar rabuwa tsakaninmu, ba sai na bar ki a tsakanin hausawan ba ma zau yi miki, ki daina damuwa Please bana so"

Wayarsa ce ta fara vibrating, ya ɗaga ya ce "Yeah Salim ya ake ciki ne?"

"Wai ina ka shiga ne? Mummy ta kira saifu a waya, wai an nemeka a waya an rasa, ya ce mini shi ma baya samunka a waya, ni kaina kwanana biyu kenan ina nemanka yanzun ma ban zaci zan sameka ba, nace bari na jarraba kiran wannan layin naka"

Abdul ya numfasa ya ce "Akwai damuwa ne Salim, mu haɗu a gidana na by pass"

"To shikenan, ka san nina har ta gaji da nemanka ita ma, har clubs ka daina zuwa, gidanka da take samunka ma yanzu baka zama, kuma ta daina samun wayarka, na ce mata kayi busy ne da shirye shiryen siyasarka"

Abdul ya ce "Manta da ita, zan je asibiti zan yi tiyata da daddare, idan na kammala ko kafin na tafi, sai mu yi magana sai mu haɗu"

"To shikenan, sai na ji ka"

***

Walid ne ya ƙarasa in da Viper yake a zaune a kan dutsen nan, yayi shiru yana nazari.

Ya zauna a kusa da shi ya ce "Sannu da hutawa"

"Yauwwa sannu da zuwa"

"Yauwwa, tunanin me ka ke yi ne?"

Viper bai ba shi amsa ba ya ce "Meye labari?"

"Labari, yan unguwar su madaki, sun addaba wa yan unguwarmu, naji ɗan mama ya ce zai shiga unguwar, sai kuma na je maɓoyar madaki, na tarar baya nan, ko dai ya tafi wani wurin bamu sani ba?"

Viper ya ɗan kaɗa kai ya ce "Kar ka damu na san in da yake"

Cikin mamaki ya ce "Ka san in da yake kamar yaya?"

"Kamar yadda na ce" ya faɗa a taƙaice.

Shiru ya wanzu na wani ɗan lokaci, Viper ya ce "Jibi yarinyar nan zata shiga kotu, ta kuma ce a kwankin nan zata fara shari'ata, i need to assist her, a haka ma rayuwarta na cikin hatsari, muddin ta shiga case ɗin nan matsaloli zasu ninku fiye da baya, akwai buƙatar na taimaka mata sosai"

Walid ya ce "Haka ne, Allah ya tabattar mana da alkhairi, ya bamu dukkanin nasara, ka yi yanci mai zamani, ka daina wannan zaman ɓuyan"

Viper ya dafa kafaɗar Walid ya ce "Mai laya"

"Na kiyayi mai zamani"

"Mu huta wannan zaman ɓuyan zaka ce, idan Allah ya bamu nasara, in ga kun tsaya da ƙafafuwan ku, na aurar da kai, da wancan sarkin faɗan"

Walid ya ce "A'a, ka yi yanci, muga farincikinka da walwalarka sun dawo dai, mu dai mu cigaba da gurgura rayuwa"

Viper ya girgiza kai ya ce "Aure yana da daɗi mussaman idan ku ka yi dace kamar yadda na yi. Ni na taɓa yi na more shi, kuma yakamata ku yi, idan na bari ku ka ƙarar da rayuwarku a kan hidimata kawai ban yi wa kaina adalci ba muhsin"

Walid ya ce "Taɓ anya na taɓa jin ka kira ni da ainihin sunana kuwa?"

Viper ya yi murmushi ya ce "Ka tuna mini da watarana, da 'yar madara ta sakani a gaba, ta ce sai na gaya mata ainihin sunayenmu, na ce mata ni Muhammad Al'amin, kai Muhsin, liti Abdullahi. Ta rafka salati, ta ce kalli yadda duk kuka mayar da sunayenku wani iri, har ma ɗan gara yaya walid, duk da shi ma wataran mai laya kake ce masa, gaskiya ku canza hali, sunayenku masu daɗi, amma duk kun canzawa kanku suna. Na ce ;Sunan waye yafi daɗi, tayi murmushi ta ce na mijina, na ce yauwwa ke ma sunanki mai daɗi an saka miki wani iyayi daban. Muhsin ku yi aure akwai alfanu a cikin aure, haryanzu na kasa manta rayuwar cikin aure, na san abu ne da ba zai bar ƙwaƙwalwata ba. Ina son naga kun samu cigaba a rayuwar ku, ba zan yi alfahari da ku ƙarar da rayuwarku a kaina ba"

Walid ya kalli Viper ya ce "Al'amin, ko mai muka yi maka a rayuwa ka cancanta, ai duk ɗan halak baya manta alkhairi, idan kai ka manta ni ba zan manta ɗawainiyar da ka yi da ni da mahaifiyata ba, haka zalika mutuntawar da matarka tayi mana"

"Muhsin, mahaifiyar ka, mahaifiyata ce, ka daina saka wannan a lissafi"

Walid ya ce "Na daina, amma dai sai mun fara aurar da kai tukuna, farincikin ka da walwalarka su dawo, sannan mu san abun yi mu ma"

Viper ya girgiza kai ya ce "Bani da ra'ayin kuma yin aure a rayuwata, wancan ma tsautsayi da ƙaddara ne ya saka aka yi shi"

Walid ya yi murmushi ya miƙe ya ce "Wannan kuma, ƙaddarar tausayi da soyayya zai saka a ayi shi" har Walid ya yi gaba, Viper ya miƙe da sauri ya ce "Ina ba zai yiwu ba, jauhar ce kawai a zuciyata" kawai walid ya ɗaga masa hannu ba tare da ya waiwaya ba ya yi gaba yana dariya.

***
Salim ya kalli Abdul da ya shigo a gajiye, ya zauna ya ajiye labcourt ɗin sa a gajiye.

"Yaya ne mutumina, na ganka a wahale"

"Aiki na sha yau ɗin nan, na je asibiti ya kai huɗu, na duba wanda na yi wa tiyata, sannan na yi wa wasu aikin sai godiyar Allah"

Salim ya yi murmushi ya ce "Sannu, ko in ɗaukko maka abar ne, ina da ita a mota?"

Abdul ya girgiza kai ya ce "Rahama ta san warin giya, faɗa zamu yi da ita"

Salim ya ce "Wow, to ko abinci zamu je ka ci?"

Nan ma ya girgiza kai ya ce "Ina da special cook a gida, yarinyar nan dar ce" yayi maganar yana kashingiɗa.

Salim ya kwashe da dariya ya ce "Allah mutumina, ta saduda kenan?"

Abdul ya yi murmushi.

"Ina jinka, bani labari"

"Salim, kai ka san komai, tun da ka tafi fa babu labarin mahaifiyar yarinyar nan, gashi ta matsa mini na mayar da ita gida, ni ba mayar da itan ne ya dame ni ba, na fara yi wa daddy bayani ko zai fahimce ni, ya hau ni da faɗa da zagi, kuma wai lallai sai na kai masa ita, sai an kaita kotu ta bayar da shaida, ni fa na yanke shawarar zan ɗauke ta mu ƙara gaba, har takarar ma bana so. Wallahi Salim ban taɓa dana sanin aikata wani abu a rayuwata ba, irin yi wa rahama fyaɗe ba, kuma ban taɓa jin so da ƙaunar wani abu a raina ba, kamar yadda nake jin son ta, ya mamaye zuciyata ba, Salim wallahi ba zan iya rabuwa da rahama ba, ba wai ina sonta da jikinta ko wani abu ba, ita ɗin nake so"

Salim ya ce "Ƙarya ne malam, mun san komai fa"

Abdul ya yi murmushi ya ce "Ita ta sani ai, ba zan yi maka ƙarya ba"

Salim ya ce "Kar ka damu, na fahimta maganar ka ɗauketa kayi gaba bai taso ba fa, ka zauna ka yi wa daddy cikakken bayani"

"Salim na san waye mahaifina ciki da bai, muddin na fito da rahama, zai iya salwantar da rayuwarta, ita kanta mahaifiyarta ina tantama a kan bashi ne ya ɗauke ta ba, ni kuwa a kan rahama sai dai ayi duk wadda za ayi"

Salim ya waro ido ya ce "Da iyayen naka? Abdul yaushe ka koma haka ne? A cikinmu duk rashin nan da kai da Saif kun fi mu mutunta iyaye ma da jin maganar su mussaman kai, meyasa ka ke son canzawa saboda mace?"

"Kamar yadda take yawan faɗa, na riga na ɓata rayuwarta, dan haka ba zan bari a sake tagayyara rayuwarta ba, ina son rahama irin son da nake son na ƙarasa rayuwata da ita, idan Daddy ya cigaba da matsawa, ba zan yi wancan auren ba"

Ya girgiza kai ya ce "Ba za ayi haka ba, ka je ka fara maganar da mahaifiyar ka, ko zata fahimceka"

Ya ce "Taɓ ayi sha'ani kawai, zan je zanji kiran da yake yi mini amma in fito da rahama dai, gaskiya ban ji zan iya ba"

"Amma fa Abdul mun tafka shirme a gaban uwar yarinyar nan, anya zata yafe maka kuwa? Ga tsiyar da ka je ka kuma yi daga baya"

Abdul ya numfasa ya ce "Sharrin giya ne, da gigin arziki da nake ji da shi, nake jin kamar zan iya taka na ƙasa da ni, ni komai zata yi, mini tayi mini amma ban da raba ni da yarinyar nan".

Salim ya ce "Lallai ka faɗa da yawa mutumina"

"Rahama, akwai haƙuri, duk da ina cin zagi a wurinta da tsinuwa, amma da ta ganni cikin rashin lafiya, ko damuwa hankalinta yake tashi, ita take dafa abincin da zan ci, yau har da yi mini guga. Nifa yarinyar da aka ce za a haɗa ni da ita, gaba ɗaya bata yi mini ba buɗaɗɗen ido ne da ita, gara a bar ni da rahaman dai, na san koma menene ni ne sila"

Salim ya jinjina kai.

***

Nabila ce a tsaye a gaban court, tana ƙoƙarin fara gabatarwa da mai shari'a appeal ɗin su, ta kalli barrister Habib, ya jinjina mata kai alamar bata ƙwarin gwiwa, ta tsaya ta gabatar da kanta cikin harshen turanci, tare da fara karantowa kotu koken su.

Na kotun ta yi duba da rubutaccen jawabin da suka gabatar, a kan hukuncin da kotun farko ta yi, bisa ga wasu kurakurai da suke ganin an tafka a wurin yin shari'ar, na rashin bayyanar wadda abun ya faru da ita a gaban kotu, da rashin gabatar da medical report ta hannun ɗan sandan da kuma likitan da ya tabattar da yin laifin ba.
Hakazalika a hujjojin da suka gabatar a kotun farko, akwai sautin murya, na mahaifiyar ramma tana koken a kawo mata agaji, domin kuwa wanda ya yi mata fyaɗe ya dawo ya ɗauke ta, idan kuwa haka ne, wanda ake zargi ba shi ne ya aikata wannan laifin ba, sannan kuma wanda ake zargin ya amsa laifin ne, a sakamakon barazana da aka yi masa, da haka take roƙon kotun ta bibiyi shari'ar da kotun baya tayi, ta tabattar da adalci"

Ta miƙa file ɗin aka miƙa gaban mai shari'a.

Suna tafe a mota tare da barrister Habib ta ce "Yaya, gaba ɗaya jikina a sanyaye yake, gani nake wannan karon ma, ba zan yi nasara ba"

"Bana son saurin karaya dan Allah, kin manta wadda ki ke ƙoƙarin tunkara ta fi wadda ki ke yi yanzu? Kuma yanzu hankalin mutane da yawa ya dawo kanki, ba common mutanen gari ba, har da ma'aikatan shari'a"

"Idan Allah ya sa na yi nasara, akwai gagarumin tonin silili fa" tayi maganar tana murmushi.

Barrister Habib ya kalleta ya ce "Na me fa?"

"Zaka gani kai dai, ya batun case ɗin Viper, samo mini copyn shari'ar da na ce?"

"Ai na gaya miki ba aiki ne mai sauƙi ba, ina nan ina ƙoƙartawa, yanzu idan aka san ina ƙoƙarin samo file ɗin ma, rayuwata na cikin hatsari"

Ta jinjina kai ta ce "Haka ne, Allah ya ba da sa'a"

***
"Inadabo, wallahi akwai matsala muddin Abdul bai kawo yarinyar nan ba, tun da ya ce maka tana wurin sa ya fito da ita mana"

"Naja duk wani ƙoƙari ina yi, bai taɓa bujirewa umarnina ba sai a wannan karon, yama daina zuwa in da nake gaba ɗaya, bana samun wayoyinsa"

"Ka san kuwa me nasararta a appeal ɗin nan yake nufi? Yarinyar nan fa ba zata zuba mana ido ba, dole ka yi ƙoƙari fa a kai"

"Kar ki damu, zan ga alƙalin da kaina"

Bunkure ta girgiza kai ta ce "Ƙoƙarin ka ba a kan alƙali kawai zai tsaya ba, har da wannan yarinyar, dan ni na yi iya yi na"

Inadabo ya katse kiran, ba tare da ya sake yin magana ba.

****
Babu tsammani, indabo ya shiga falon mai ɗakinsa, ya tarar da ita tana yi wa Abdul faɗa. Yayi turus, sannan cikin tsananin ƙuluwa ya ce "Ai dama na sani, ke ki ke goya masa baya, yake rashin mutunci"

"A'a nima fa yanzu na ganshi, nake tambayarsa ba'asin ina ya shiga, kar ma ka ɗora mini wannan zargin"

"Wato Abdul ban isa da kai ba kenan ko? Nayi maka magana sai ka ɗauke ƙafarka gaba ɗaya daga gidan ka daina zuwa, ina yarinyar take?"

Abdul ya yi shiru ya ƙi magana.

"Ka gaya mini in da take, tun ban tattaka ka ba, yau an yi appeal ɗin shari'ar yarinyar, kuma muddin aka wanke mutumin nan, babu lallai ka tsira ba tare da asirinka ya tonu ba".

Abdul ya ce "In dai hakan yana nufin na cigaba da rayuwa da ita, shikenan ni ba komai asirin nawa ya tonu, dan Allah Daddy ka yi haƙuri, wallahi ba zan iya fito da rahama gaban duniya ba, ban san iya abun da zaka yi mata ba, kuma bana fatan abun da zai ƙarasa zubar da mutuncinta, dan kuwa fito da ita gaban kotu kamar cigaba da yayata abun da ya faru da ita ne"

Tamkar shashasha indabo ya tsaya yana kallon Abdul, babu kunya babu tsoron Allah Abdul yake gaya masa wannan maganganun.

Ya numfasa ya ce "Babu laifi, ni na san matakin da yakamata na ɗauka".


***
Nabila ta shiga office ɗin ta, ta zauna ta janyo drower zata ɗauki biro, ta ga file, ta ɗaukko file ɗin ta buɗe, kawai taga copyn shari'ar Viper ne a ciki, sai da ta razana ta ja da baya, tana waige-waige.

A razane ta ɗauki waya, ta kira barrister Habib, ya ɗaga ya ce "Hello Nabila"

"Barrister ka samo file ɗin nan ne?"

"A'a, ina ta ƙoƙari dai a kai, ki yi haƙuri"

"Barrister, file ɗin na gani a office ɗina"

Ya ce "Wane file ɗin?"

"Na shari'ar Viper"

"Iyee, waye ya baki?"

"Nima ban sani ba, a office ɗina na tarar kamar yadda aka ajiye mini na Bunkure"

"Kar ki gaya wa kowa, gani nan zuwa"

Ta ajiye wayar tana sake dudduba file ɗin.

Ji ta yi an buɗe ƙofar office ɗin ta razana da sauri tana ɓoye file ɗin,

Download complete TXT · Novel page