Karfe A Wuta
Chapter 104 of 167
ya rufe ƙofar office ɗin, ya ƙaraso.
Ta ce "Yau ma kai ne da kanka?"
Ya ce "Eh, ko in koma ne?"
"A'a, bisimillah zauna"
Ya samu wuri ya zauna, kamar yadda a wancan karon, tayi masa hidima, haka ma a wannan karon, ta haɗa masa tea, ta bashi abincinta da ta zo da shi, ta bashi" wannan karon babu gardama ya karɓa ya ci.
Ta ciro file ɗin ta ajiye masa ta ce "Yau da safe aka kawo mini shi, ban san kuma wanda ya kawo ba"
Ya karɓa ya bubbuɗe, yana dubawa.
"An fitar da sanarwar cigaba da nemanka jiya, wai yaranka sun je sun yi faɗan daba, jami'an tsaro na ta cigaba da yayata nemanka"
Ya girgiza kai ya ce "Ni ma na ji, sai dai ni bani da masaniyar hakan, na samu labarin faɗa tsakanin yan unguwarmu da yan unguwar su madaki, ban san ma me ake ciki ba"
"Zan je kotu, na nemi kotu ta hana kama ka, kafin na ɗauki mataki na gaba"
Viper ya jinjina kai yana kora shayin hannunsa.
Ya ce "Bani system ɗin ki"
Ta ɗaukko, ta bashi ya ciro tab ɗin sa, ya ɗan jima yana danne-danne, yayin da ita kuma take satar kallonsa kamar yau ta fara ganinsa.
Kamar kar ya tafi ta daina ganinsa, wani irin shauƙi da farinciki ya din ga ratsa zuciyarta.
"Ki shirya, zamu je ki ga shaidar da nake da shi, idan da abun da ki ke buƙatar sani"
Ta ce "To shikenan, ka sanya lokaci sai mu je, sai kuma mu yi ta addu'a".
Ya ɗan daddana tab ɗin hannunsa ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Barka da wannan lokaci, kana magana da mai zamani ne.
Babu buƙatar yin doguwar magana, na san zuwa yanzu ka san labarin haɗuwata da ɗanka, zuwa yanzu na san duk wani motsinsa, duk in da yake zuwa na sani, amma ba wannan ba, akwai buƙatar ka bibiyi case ɗin ɗanka da ka ke musayar sa da ni, a lokacin da yake Nigeria yake aikata laifuka, ina da babban albishir gareka, Mexico na shirin miƙawa amurka shi, ya fuskanci shari'a, kuma ina mai sanar da kai kisan kai ne hukuncin abun da ya aikata.
Na san zaka yi mamakin yadda aka yi aka kama Jafar, akwai buƙatar mu haɗu fuska da fuska nayi maka bayani" ya katse wayar, tare da tashi tsaye ya ce "Ka zan bar wurin nan"
Ita ma ta miƙe ta ce "Amma....
"Amma me?"
Sai ta tsaya tana kallonsa "Ina son mu yi magana ne, ina da tambayoyi"
"Ba yanzu ba, am not safe here"
Ta ce "To muje, na raka ka gate nima fita zan yi" ta tattaro file ɗin, da jakarta suka fito.
Tun kafin su ƙaraso, ya zuba masa ido, duk da fuskar Viper sanye yake da facemask, amma hakan bai hana shi gane ko waye ba.
Suna ƙarasowa yayi murmushi ya ce "Barrister, wurinki na zo, ina Abuja aka ce mini kin samu accident, sai dai na samu labarin da sauƙi jikin, duk da haka na ce bari na zo na ganki, kuma na ganki da baƙo. Assalamu alaikum" yayi maganar yana miƙawa Viper hannu.
(Ayi mini afuwa ji na shiru, bani da lafiya ne)
Ayshercool
08081012143
71
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Viper ya tsaya ƙyam yana kallon Alhaji mu'azzam da ya miƙo masa hannu.
A rikice Nabila ta ce "Amm eh, ai na ma warware na ji sauƙi, ka shiga, ka jira ni a office ɗina, yanzu zan dawo"
Viper ya kalli Nabila ya ce "Koma ciki" sai ta tsaya tana rarraba ido, tana kallonsa tana kallon Alhaji mu'azzam wada.
Wani irin kallo Viper ya yi mata, da ya tilasta mata barin wurin, tana waiwayawa.
Viper ya saka hannunsa a hannun Alhaji mu'azzam, ya sauke facemask ɗin sa yana kallon cikin idonsa.
"Dama ana ganinka, ka yi wa hukuma wuyar kamawa? Ya aka yi na ganka tare da yarinyar da nake so, kuma nake fatan na aura?"
Viper ya tsananta riƙon da ya yi wa hannun Alhaji mu'azzam ya ce "Ka gaya mata wani abu ne?"
"Kamar me fa?"
"Ka san abun da nake nufi" yayi maganar yana ƙara tsare shi da ido.
Alhaji mu'azzam ya ce "Kana tsoron wani abu ne?"
"Ba maganar tsoro bane ne ko akasin haka, gargaɗi ne nake yi maka, idan baka furta ba kar ka fara, nike da alhakin kai ƙarshen wannan lamarin, idan ka yi wani yinƙuri da zai kawo tangarɗa ga abun da nake tsarawa, ka san abun da zan iya aikatawa".
Alhaji mu'azzam ya yi murmushi ya ce "Da fari jauhar, na bar maka ita, a wannan karon kuma Nabila, kar ka zama mai......
"Jauhar ta wa ce, haka zalika Nabila, muddin zan cigaba da ganin fuskar jauhar a cikin ta Nabila ta haramta a gareka, ba kai ba kowane mahaluki ma" ya fizge hannunsa daga na Alhaji mu'azzam ya mayar da facemask ɗin sa ya bar wurin.
Nabila kuwa kai komo ga din ga yi a office ɗin ta, cike da fargaba da tsoro.
Kankarofi ya turo ƙofar office ɗin Nabila ya shigo, ta tsaya tana kallonsa yayi mata murmushi ya ƙarasa ya ce "Madam ya na ganki a tsaye ne?"
Murmushin ƙarfin hali ta yi ta ce "Bisimillah zauna mana"
Ya zauna ya ce "Ashe tsautsayi ne ya kuma afkuwa haka, ya ƙarfin jikin?"
Ta ce "Jiki da sauƙi Alhamdilillah"
"Amma dai babu wani mummunan rauni ko?"
Ta ce "Eh, gocewar ƙashi na samu a hannuna, amma Alhamdilillah da sauƙi"
"To Alhamdilillah, na ji daɗi ƙwarai, ya shari'a kuma?"
Tayi murmushi ta ce "Mu na ta fama, sai fatan Ubangiji Allah ya iya mana"
"Allah ya yi jagora, kin ga kamata yayi ace har gida na je dubiya, daga nan na miƙa buƙata ta ga Abba, ayi komai a kan lokaci, kin ga babban mutum ne ni, amma soyayya ta saka sai wahalar da ni ki ke yi, kina sakani sintiri, sai dai na yi ta biyoki office"
Ta ɗan shagwaɓe fuska ta ce "Wahalar da kai kuma?"
Ya kwantar da murya ya ce "Eh mana, ko ba ayi na ne, ya sanya ake ta bani wahala"
"Matanka fa biyu, ni gaskiya...
"Ba kya son mai mata ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.
"To meyasa?"
"Wahala ake sha, kuma nan da nan ake sakin wadda ta zo daga baya, impact ni fa tashin hankali ne ba na so, gidanmu ma uku ne, ina ganin tashin hankalin da ake yi"
Yayi dariya ya ce "Barrister, dabarar mutum ba ta sanyawa ya kaucewa ƙaddararsa. Da dabara da wayon mutum na sanyawa ya kaucewa ƙaddara, da wataƙila haryanzu fatima tana raye da ni ta aura"
"Wacece hakan?"
"No kar ki damu, kawai dai misali nake yi miki, wata yarinya ce da na taɓa ƙallafa raina a kan aurenta, Allah bai yi ba"
"Baka aureta ba, sai ka auri mata biyu, yanzu da sai ka yi ta uku da ita ni ta huɗu?"
Sosai ta bashi dariya, saboda yarinyata da kishinta da suka gaza ɓuya.
"Karki damu, labarin ne akwai sarƙaƙiya, idan ya zo ƙarshe zan baki. Amma matana ba matsala bane. Uwargidana tana Abuja, amaryata kuma na kano, ke kuma sai in da ki ke so zaki zauna"
Noƙe kafaɗa tayi, tana ɗan tura baki, har ya gama yi mata hirar, bai yi mata magana akan Viper ba, duk da ta so ta tambaye shi ko ya san shi, amma ta ja bakinta tayi shiru, dan da Viper yakamata su tattauna wannan maganar.
****
Naja'atu Bunkure ce zaune a office ɗin Abdul yasar, ya hakimce a kan kujera yana saurarenta.
"Abdul, yarinyar nan fa dole ka fito da ita, even for your own safety, idan fa aka wanke mutumin nan, akwai cakwakiya, bamu san ya shari'ar nan zata kasance ba, taurin kan nan da kake yi, babbar barazana ce gareka da mahaifinka Shari'a saɓanin hankali ce"
Abdul ya ce "Ba wata barazana, ai ba yau ki ka saba goge laifi ba komai girmansa, wannan karon ma ki yi wani abu"
"Nayi iya yi na, da kai da mahaifinka ne kuka ɓata komai, Abdul idan lamarin nan ya kwaɓe fa, zaku shiga matsala mussaman ma kai. Kuma an gaya maka shaida kawai zata bayar a kotu shikenan ba wani abu ba"
Abdul ya yi murmushi ya ce "Naja'atu Bunkure, na sanki fa, na kuma san waye mahaifina, na san abun da zaku iya na san wanda ba zaku iya ba. Idan aka kuma cutar da yarinyar nan a karo na biyu, ba zan yafewa kaina ba, ke da kanki kin san kura tayi lafiya, duk da a duk lokacin da zan shiga Asibiti ina ajiye duk wani iskanci a gefe, in shiga a nutse, amma ke kin san yanzu na nutsu sosai da sosai, albarkacin rayuwa tare da rahama"
Naja ta tafa hannu ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Abdul kidnapping fa kenan, bayan fyaɗe ka saceta kana rayuwa da ita, wani laifin fa kake aikatawa a kan wani"
"Babu wani laifi da nake aikatawa, da na barta to da tabbas kun yi mata wata illar, barinta a wurina shi ne zata zauna safe"
"Shikenan, zamu ɗauki duk wani mataki da hukuncin da muke ganin ya dace"
Ya ɗage kafaɗa alamar ko a jikinsa.
***
Indabo kuwa gaba ɗaya ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rasa abun da yake yi masa daɗi, tun yana ƙirga adadin shigarsa banɗaki, har ya sare lissafi ya ƙwace masa.
Gudawar tsoro da fargaba kawai yake yi, tun bayan da Viper ya kira shi a waya.
Embassy ɗin Nigeria na Mexico ya kira, domin a bincika masa da maganar da Viper ya kira shi ya gaya masa, idan gaske ce.
Ya ma rasa wa zai kira ya gaya wa maganar, ashe da gaske yana sane da cewa, da shi yake sakawa ayi exchange a duk lokacin da jafar ya aikata laifi, to ko da sanya hannunsa aka kama masa ɗa? Amma ya za ayi common ɗan daban gari, ya saka a kama masa ɗa a ƙasashen ƙetare?.
Waya ya ɗauka ya kira IG, ya din ga masifa, a kan jan ƙafar da ake yi, wurin kama Aminu Viper, tare da jadadda idan har ba za su yi abun da yake so ba, zai shiga ya fita a ɗauke shi daga garin kano, a canza wani IG. Tun da suka kasa kama mutum ɗaya, alhalin yana yawonsa a gari, da aikata abun da yake so.
Yayi ta bashi haƙuri, tare da bashi tabbacin suna iya ƙoƙarin su, amma komai ya kusa zuwa ƙarshe. Ya ajiye wayar yana mamakin ya za ayi, ace senator guda ya tayar da hankalinsa haka a kan ɗan daba guda ɗaya tal har haka, ya din ga ɓata lokacinsa a kansa.
Yadda indabo ya kira shi, ya tayar masa da hankali, haka shima ya kira Nasir a waya, ya ce masa nan da kwanaki talatin, idan babu improvements a aikin nan, zasu karɓi aikin daga hannunsa su bawa wani, kuma hakan ka iya janyo masa demotion, da rasa wasu damarmaki.
Shi ma haƙurin ya din ga bayarwa, tare da bada tabaccin zai kama Aminu Viper.
***
Abdul da la'asar ya koma gidansa,ya tarar rahama na wanka, ya kwanta ya yi ɗai-ɗai a kan gado.
Ta buɗe ƙofa ta fito, ta tarar da shi ta ɓata fuska ta ce "Abdul meye haka?"
Ya buɗe ido ya kalleta.
"Na gyara gadon, kawai ka hau ka ajiye mini shirginka, wata uwar jaka kamar wanzami, kalli takalmi har bedroom ba a wancan ɗakin nake ajiye maka ba?
Lumshe idanunsa ya yi, ta ƙarasa ta kwashe kayan, ta hau kan gadon ta kwance agogon hannunsa, dan ta san ƙarshe ya cire, ya yar da shi a wani wurin, ya zo ya isheta da nema.
Ya kai hannu ya fara shafa bayanta, tayi masa banza, tana cikin ɓalle masa labcourt ya cigaba da shafa gashin kanta, sai da ya kai hannunsa kan towel ɗin ta, ta buge hannunsa da ƙarfi ta ce "Tashi kayi sallar la'asar na san baka yi ba" ya buɗe idonsa ya kalleta.
"Eh kana wani manne ido, ka tashi kayi sallar la'asar"
"Zan yi in anjima, yanzu na gaji"
Ramma ta buɗe baki ta ce "Wace anjiman? Kai ke da anjiman? Waye ya baka guarantee kai wa anjiman? Abdul wallahi wutar duniya ma ba zaka iya da ita ba, balle ta lahira, kai a wuta kala nawa kake so a saka ka ne? Saƙara fa, wutar marasa yin salla, ita ka ke so ka shiga ko? bayan ta shan giya da neman mata. Ba shiri ya tashi ya ajiye labcourt ɗin ya ce "To naji, ai dama ban ce ba zan yi ba, zan yi Astagfirullah in sha Allah ba zan shiga wuta ba, shan giya da neman mata ai kin san na daina" yana maganar ya nufi banɗaki.
Sai da tayi dariya, Abdul ga tsoro ga iskanci, ta tabatta da ya samu kyakkyawar tarbiyya, da isashshen ilimin addini, da bai aikata wasu abubuwan ba.
Taje gaban mudubi ta zauna, mudubin fal da turaruka, da kayan gyaran gashi da na fata, wasu abubuwan duk shi ya koya mata amfani da su, har wasu supplement yake bata tana sha. Ita kanta ta san tayi ƙiba ta yi kyau. Tayi ajiyar zuciya ta fara shafa man.
Ya fito ya tayar da salla, ta ce "A kyautata niyya da nustuwa idan ana salla, yadda ka yi ta haka zata zo maka a kabari" ta shirya cikin doguwar riga, yana idar da sallar, ta ɗaukko masa azkar ta ce "Ungo, ka san shi yawan ambaton Allah, yana hana mutum aikata alfasha, abu ne mawuyaci kaga wanda yake da kusanci da Allah, yana aikata ɓarna kala-kala" haka ta saka shi a gaba, ya idar suka je ya ci abinci.
Gaba ɗaya rayuwa da ramma ya sanya ya ji tamkar an canza shi, zuwa wani na daban, haka kurum yake jin wata nutsuwa a tare da shi.
Mussaman saita shi da take yi a kan ibada, da yawan tsoratar da shi a kan yin ta, haka yana saka masa nustuwa da kwanciyar hankali, kuma ya rage aikata tsageranci da rashin ta ido. Hakan ya sanya yake ƙara jin raba shi da ramma, tamkar raba shi da rayuwar sa ne.
System ya kunna ya ce "Your excellency zo ki ga wani abu"
"Wanke-wanke zan yi na ɗora abincin dare"
"Karki damu, zan yi mana takeaway"
"Sai dai idan zaka yi wanke-wanken"
Abdul ya ce "Na ji zan yi"
Ta ƙaraso ta zauna, ya rungumeta a jikinsa, sannan ya buɗo wani form ya ce "Kin san na menene wannan?"
"No"
"Form ɗinki ne na makaranta"
Ta kalleshi ta ce "Makarnta kuma?"
Ya ce "Eh mana, ko ba kya so?"
"Ina so, amma gida zaka mayar da ni?"
"Eh, zaki je ki ga gida, daga nan sai school, boarding ce, mai kyan gaske, saboda sonake ki nutsu ki yi karatu da kyau, yadda babu wanda ya ganki, balle yayi miki gori, da kin gama karatu kuma, ƙasar waje zaki tafi jami'a, shiyasa nake tambayar ki me ki ke son zama, na biya komai, na yi rubutu, yadda ko bayan raina ba zaki tozarta ba in sha Allah, ko bana raye karatunki ba zai tsaya ba sai kin kammala in sha Allah"
"Yar uban wace ni da zaka yi mini duk wannan hidimar haka?"
"Ba yar kowa ba ce, amma komai zan yi miki, ba zai kai nauyin laifin da nayi miki ba, ba zai biya budurcinki da na karɓa ta ƙarfin tsiya ba, da kuma rashin darajar da naje gidanku nayi ba, ba zan gaji da cigaba da neman afuwar ki ba rahama" ta sunkuyar da kai ta yi shiru, hawaye na zubowa daga idanunta.
Ya saka hannu yana share mata hawayenta ya ce "Ki yi haƙuri, na san na cutar da ke, dan Allah ki yafe mini rahama, soyayyar nan kawai da Allah ya jarabbe ni da ita, ta isheni, baki san tarin ƙalubalen da yake a gabana nake ta ƙoƙarin karewa a waje ba, amma dai ki yi haƙuri dan Allah" a hankali ta zare hannunta daga nasa, ta tashi ta bar falon tana kuka.
***
Nabila kuwa da file ɗin Viper ta tafi gida, ta kai shi ɗakinta, ta cigaba da duba shi daki-daki, tana picking ɗin kurakuran da aka tafka a cikin shari'ar ta sa. Kai da ganin fasalin shari'ar ka san cewa cike take da mugunta da zunzurutun zalunci.
Zafi ne ya isheta, babu wuta, ga solar sai ƙara take yi, kasancewar ranar ba ayi rana sosai ba.
Ta ɗaukko system ɗin ta, da wayoyinta, ta fita gareji, ta shimfiɗa sallaya, da kayan ciye-ciyenta, ta zauna ta cigaba da aikinta.
Nasir ne ya fito yana waya, ba ta san da wa yake yin waya ba, sai dai yanayin yadda ya fito yana wayar, bai san tana wurin ba.
"Eh dan Allah, duk yadda za ayi a samo mana hotunansa, ko guda ɗaya ne, nima na daɗe da wannan tunanin, ban aiwatar ba, amma a yanzu naga hakan ne kawai mafita, a samo hoton nasa, dan IG ya kira ni ɗazu, shi kansa distinguish sai da ya kira ni, ni duk na ruɗe, nayi mamakin yadda aka yi mutum ɗaya ya gagari hukuma. Duk wata hanya da na bi da zan sameshi, sai ta kuɓuce mini.
Shiru ya yi, lokacin da ya lura da ita a wurin a zaune, ya ƙarƙare wayar ya saka a aljihunsa.
"Dama har zuwa yanzu baka taɓa ganinsa ba, baka san kamaninsa ba?"
"Eh" ya bata amsa a taƙaice.
"Hmm"
"Ko zaki bani hoton nasa ne?"
"Ni a su wa?"
"Ke a 'yar kankamba mana, samunki da hotonsa ai ba abun mamaki bane ba"
Nabila ta yi murmushi, kawai ta cigaba da aikin da yake gabanta.
****
Mutumin da yake zaune a cikin ofishin sa, ya kalli P.A ɗin Indabo ya ce "Ɗan sake duba na da kyau mana malam"
P.A ya ce "Na kalleka"
"Shekaru