Karfe A Wuta

Chapter 105 of 167

huɗu rak idan Allah ya bani aron rai, suka rage mini nayi retire, a tarihin aikina, ban taɓa karɓar cin hanci na aikata son zuciya ba, ban ƙi ba wasu lokutan ina karɓa in yi abun da ya dace, duk da hakan ma saɓa doka ne. Ba za a haɗa kai da ni ayi rashin albarka ba, a tozarta harkar shari'a ba, idan na ci amana na tsayawa ƙarya a duniya, wa zai tsaya ni a kotun Allah idan zai yi mini hisabi, a cikin kai da uban gidanka, waye zai ƙwace ni? Tambayarka nake yi, na ce waye zai ƙwace ni? Kotun Allah saɓanin tunanin ɗan Adam ce, kuma wallahi dukkanin mu, sai mun tsaya a wannan kotun, kotun da bata buƙatar lauya, ɗan sanda balle ka yi tunanin bayar da cin hanci.
Duk da na san badaƙalar da ake tafkawa a cikin harkar shari'a, na yi mamakin wasu abubuwan da yarinyar nan ta din ga faɗa, yar cikina ce amma ina sauraron programs ɗin ta, kuma ko kaɗan ban ji haushin yadda take tsigalewa aikinmu ba, yadda ake amfani da mu, ake aikata abun da ake so. Babu wani rashawa da zaku bani na karɓa, zan yi abun da ya dace ne kawai, idan kuma aka sake zan yi abun da rai zai ɓaci. Kai in taƙaice maka doguwar magana zuwa gajera, daga sama aka yi mini magana a kan lallai nayi abun da ya dace a kan shari'ar nan, ba a buƙatar kuskure a ciki, kuma ko ba haka ba, ni sonake na gama aiki na ajiye shi lafiya"

P.A ya jinjina kai ya miƙe tsaye, ya ce "Hakan ma babu laifi, muna godiya sosai" ya juya ya fita daga office ɗin.

***
Missed call kusan uku Nabila ta yi wa Viper, amma bai ɗaga ba, sai da ranta ya sosu, ta rasa irin wannan murɗaɗɗen hali nasa, gashi ko zata yi fushi da shi, na ɗan lokaci ne, ana jimawa ta manta.

Viper kuma fitowar sa kenan daga wanka, ya kalli wayarsa ya ga missed calls ɗin ta, har guda uku.

Bai kula ba, ya fara ƙoƙarin neman kayan da zai saka, wayar Walid ta far ringing.

Walid ya ɗaga yayi sallama, ta amsa ta ce "Oga walid barka da wannan lokaci"

"Yauwwa barkanmu barrister, ya aiki ya jama'a"

"Alhamdilillah, ina ta kiran Viper ya ƙi ɗagawa, wai ni ko wani laifin nayi masa ya tsane har haka ne?" Walid  ya kalli Viper, sannan ya ce "Wanka yake yi yanzu ya fito"

Ta ce "Ai dama kai kare shi zaka yi, baka taɓa yadda yayi laifi, ko yayi laifin sai ka kare shi, dama magana nake son mu yi da shi, kuma na ma fasa barshi kawai, sai anjima"

Da sauri Walid ya ce "A'a ba za a bari ba, ko na haɗa ki da shi?"

"Ba zai kulani ba ai na sani, shiru zai yi mini kamar kurma, in dai yana lafiya shikenan sai anjima"

"Kin ga Nabila, tsaya ki ji mana, gaba ɗaya ke ce baki fahimci Al'amin ba, ba wulaƙanta ki yake yi ba"

"Ba wulaƙanta ni yake yi ba kace? Idan ba wulaƙanci ba, mai zai sanya ya ce baya so na, wallahi ban taɓa cewa ina son wani ba, ina zaman zamana, ƙaddara da rashin ya ja ni ya kai ni har in da yake, yayi ta wulaƙanta ni bai damu da rayuwata ba, amma ko haushi bana ji naƙi zuciya, ko kwana biyu nayi ban ji ɗuriyarsa ba sai na damu" ta ƙarasa maganar cikin damuwa, da alama abun ya na damunta sosai da sosai.

"No, Viper mutumin kirki ne, kuma abun so, in dai ka zauna da shi zaka so shi, saboda yana da halaye masu kyau sosai da sosai, kina kallon muma da muke tare da shi, wasu lokutan haka yake yi mana, amma muna duba halaccinsa a garemu ne, kema baki fahimce shi bane"

"Ba wani ban fahimce shi ba, kalli yadda na shiga siraɗin gobarar nan, na zo nayi hatsari, amma sannu kawai ba wani abu ba, ya kasa ce mini"

Walid ya ce "Ki yi haƙuri, halinsa ne a haka, amma zan iya ce miki, bayan iyayenki, akwai wanda ya kai shi shiga damuwar abun da ya faru da ke"

"A hakan? In kusa rasa raina har karo biyu?" Babu tsammani Viper ya fizge wayar hannun Walid, ya kashe ya dire masa ita, ya fice. Walid ya bishi da kallo yana kallon ikon Allah, shi bai rarrasheta ba, kuma ya hana a rarrasheta.

Ko da ya fice daga gidan, wayarsa yake kallo, yana jin tamkar ya kirata, har ya ɗaga ya kalli lambarta, sai kuma ya tsaya ya cigaba da kallon lambar, fasawa yai kawai ya mayar da wayar aljihunsa ya yi gaba.

***
"Arfa, wai meyake damunki ne duk kin wani rame kin tsotse" Sumayya ta yi maganar tana ƙare mata kallo.

Baba magajiya ta ce "Gara dai ki yi mata, ko ta ji, taƙi gaya mini meyake damunta, sun samu saɓani da babanta, kuma sun shirya, amma kwanan nan sai ƙarewa take yi kamar kuɗin guzuri, ko abincin kirki ba ta ci, duk ta zube sai uban nono da take kayansa kamar ya rinjayeta" Sumayya ta ƙyalƙyale da dariya ta ce "Wallahi kuwa baba magajiya, da 'yar ƙibarta tafi kyau, haba jarumar mu, idan ki ka saka damuwa a ranki, mu wa zai bamu ƙwarin gwiwar? Muje mu zanta na ji menene ya faru".

Suka tafi ɗakin Nabila, Nabila ta zauna a gefen gado, sumayya ma ta zauna ta ce "Gaya mini menene? Naji baba magajiya ta ce kun yi faɗa da Abba, me ki ka yi?"

Ta kalli sumayya ta ce "Sumayya haka soyayya take dama?"

"Soyayya kuma, ita ta hana ki cin abincin ki ke ramewa?"

Ta girgiza kai ta ce "Ba ita ta hana ni cin abinci ba, damuwoyi ne kashi-kashi suka sha mini kai sumayya.
Da fari nifa zuciyata na azalzalata a kan son ganin mahaifina, ina son sanin waye shi, ko yaya yake a bani dama na san shi, ni zan fara bincike ta ƙarƙashin ƙasa da kaina"

"A'a Nabila, kar Abba ya sani ransa ya ɓaci"

"Sumayya ya zan yi, ni ba na son na mutu ban san babana ba, idan a gidan babana nake, wani abun ba za ayi mini shi ba"

"Naji, zamu dawo kan wannan batun, naji kina maganar soyayya"

Ta numfasa ta ce "Ƙaddara ta kaini ta baro sumayya"

Sumayya ta waro ido ta ce "Kamar yaya?"

"Son abun da ba zan samu ba nake yi"

"A'a kar ki ce haka, amma wa ki ke so ɗin tukuna ma dai"

Nabila ta tashi, ta saka key, ta buɗe wardrobe ɗin ta, ta ɗaukko file ta zo ta ajiye a gaban Sumayya.

Sumayya ta ɗauka ta fara bubbuɗewa, ta tsaya ta gama dubawa sannan ta kalli Nabila cikin matsananciyar kiɗima da tashin hankali ta ce "Ban gane me ki ke nufi ba haryanzu Nabila"

Nabila ta goge hawayen da ya gangaro mata, ta sunkuyar da kanta ƙasa.

Ta daki kafaɗar Nabila ta ce "Kin san in da mutumin nan yake, da gaske haɗuwa ku ka cigaba da yi da shi, har ki fara son ɗan daba?"

"Ɗaga murya zaki yi, ki tona mini asiri Sumayya"

"Nabila wannan hauka ne, ga yaya Nasir a cikin gida, yana ta haƙilo yana fama, ko ɗazu an kawo mana sanarwa, yan sanda na cigaba da nemansa ruwa a jallo, duk wanda ya nuna in da yake, ko in da za a same shi, akwai kyauta, kawai ki ke zuwa in da yake, idan aka kama da ke fa? Menene sunanki bayan mun gama fitowa duniya muna ɓaɓatu da nuna mu masu goyon bayan gaskiya ne?"

"Ban damu da abun da duniya za ta ce ba, ko yadda za a kalleni ba, zan tsaya a bayan gaskiya ne duk rintsi duk wahala. Sumayya zan tsayawa Aminu Viper, kuma kamar yadda ki ka faɗa tabbas ina haɗuwa da Viper, kuma na san in da yake, amma ba zan taɓa bari hukuma ta kama shi ba"

Sumayya ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace lalacewar ce ta same ki har haka Nabila? Kina ya mace, ki ke zuwa wurin ɗan daba mashayi, dan ta'adda?"

Ta girgiza kai ta ce "Sumayya ƙaddara ce, kamar yadda na gaya miki da farko, idan zaki rufa mini asiri ne shikenan, idan kuma tona mini asiri zaki yi, kina da zaɓin yin wanda ya dace". Ta tashi ta nufi wardrobe ɗin ta, ta mayar da file ɗin.

"Kai!! Nabila ki canza tunani, ni ba zan bari ki cutar da kanki, ina kallonki ba"

"Ai ba gaya miki na yi, dan ki bani shawara ba, na riga na yanke abun da nake ganin shi ne dai-dai"

Sumayya ta ɗauki jakarta ta fice, tana zare idanunta, dan tabattar da ba mafarki take yi ba, dan bata taɓa tsammanin wauta da haukan Nabila ya kai wannan limit ɗin ba.

Bayan tafiyarta, Nabila ta duba wayarta, ta ga announcement ɗin jami'an tsaro, ta ɗauki, jakarta ta saka kayanta, ta faki ido ta fice daga gidan.

Sumayya kamar za ta yi kuka, ta marairaice a waya ta ce "Sir dan Allah ka yi wani abu a kai, rayuwarta zata shiga cikin hatsari da matsala, za ayi mata kallon mutuniyar banza, ɗan ta'adda take shirin kasadar karewa"

Yayi murmushi ya ce "Sumayya ƙawarki ba ta ji, bar ta ai ɗaukaka take nema, mu yi mata fatan nasara"

"A'a sir, dan Allah ba zata iya ba"

Kankarofi ya ce "Haka ta ce miki? She can do it, ni na bayar da file ɗin sa aka kai mata, ki ja da baya ki tayata da addu'a, in da ki ka ga ana buƙatar taimakona kuma, ki yi mini magana kar ki yi ƙoƙarin dakatar da ita, wannan gargaɗi nake yi miki" ya kashe wayar.

Sumayya ta ce 'Naga ta ta kaina ni sumayya"

***
Suna zazzaune a ɗakin, suna ta shan sigari, ya ɗaga kai kawai ya ganta a tsaye a ƙofar ɗakin, tana kallonsu, ko sallamarta bai ji ba.

Ta rame sosai da sosai, duk da fuskarta kawai ake iya gani, saboda facemask.

Ganin ya tsareta da nasa idanun, ya sanya ta sunkuyar da kai, waiwayawa su Walid suka yi, su ga me yake kallo, suka ga Nabila a tsaye.

Liti ya ce "Su 'yar anace ce da yamaccin nan ashe"

Walid ya ce "Afuwan barrister, kin zo mun cika wurin da hayaƙi, gashi ke ba kya son hayaƙi"

Viper ya yinƙura ya tashi, ya ce "Ki tsaya karki shigo, ki zo kina sumewa mutane sai an ta jagwalgwala ki" yayi maganar yana nufota, sai da ya tunkarota sosai, sannan ta lura rigar jikinsa sunansa ne a jiki, an rubuta Viper, da zanen kan macijiya a  jiki ta fito da harshenta.

Ya fito ya tsaya, yayi crossing lega ɗin sa, irin ina saurarenki.

Banza tayi masa ita ma, suka cigaba da tsayuwa, sai dai tsayuwar bata damunsa, ita kuwa ta fara gajiya, yana zuƙar sigarinsa, yana fesarwa a gefe.

Hannunsa ta kalla ta zare sauran sigarin ta yar a ƙasa, ya kalleta amma ta haɗe rai.

"Ina jinki ya aka yi?"

"Alhaji mu'azzam da ku ka haɗu, dama ka san shi ne?"

"Haka ya ce miki?"

"A'a, tambayarka kawai nake"

"Ki bar maganar sa kawai"

"Saboda me?"

Ya ce "Saboda haka na ce"

"Nifa ina tsoron sai na je gaban kotu, in tarar da wasu abubuwa da ban san da su ba, na rasa yadda zan ɓullowa lamarin, ka gaya mini shi menene alaƙarka da shi?".

A hasale ya ce "Na ce ki bar maganarsa ko? Na san shi, amma sanin waye shi ɗin ba shi da wani amfani".

"Shhhh ka daina yi mini shouting, ka yi shiru ka saurare ni, aikina nake yi malam" tayi maganar tana kallon ƙwayar idon Viper.

Ayshercool
08081012143

72
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724



*Ina ma'abota bibiyar litattafan bright pens, ƙarƙashin mikiya writers association, marubutan da suka kawo muku CUTARWA, MUNAFUKIN MIJI, YI WA KAI, A first batch ga second batch, ƘARFE A WUTA, MUTALLAB ya fara zuwar muku da na sa saloz sai kuma ZAYTOON DA HADARIN GABAS NA NAN TAFE SUMA A CIKIN WANNAN WATAN, KAR KU BARI A BAKU LABARI.




Waro ido suka yi waje, jin abun da Nabila ta yi wa Viper, liti ya doko tsalle yana faɗin "Ke! Saken da ki ka samu har ya kai haka, mai zamanin ki ke yi wa tsawa?"

"Nayi ɗin, kai kuma a suwa?" Tayi maganar cike da son huce takaicinta a kan liti.

Walid ya yinƙuro ya fito, amma Viper tuni ya danƙi ƙeyar Nabila, Walid ya yinƙuro, amma Viper ya ɗaga masa hannu, ya yi waje da Nabila.

Sai da ya yi nisa da ita, sannan ya saki ƙeyarta, ta ja da baya, tana ƙifta idanu.

Ya taka a hankali ya ƙarasa gabanta, ya tsaya ya kalleta ya ce "Ni ki ke wa tsawa a gaban jama'a ko?"

Ta sunkuyar da kai, tana yamutsa fuska tare da tura baki.

"Karki yi ƙoƙarin tsallake iyaka, ki kaini bango, idan na yi magana bana son jayayya, ki ƙyale wannan maganar, ki tafi da id card ɗinki zan tura miki adress ɗin da zaki je, a asibiti ne kiga shaidan da nake da shi, wato madaki.

Ta ɗago ta kalleshi ta ce "Kai ba zaka je ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Tsoro nake ji, na samu labarin yayanki ya ƙara tsananta nemana kar ya kamani"

Nabila ta ce "Hotonka yake nema, ya ce a samo masa hotunanka, ina tunanin hotunanka za ayi sharing ace ana nemanka"

Ya ce "Duk neman da yake yi mini ma bai sanni ba, a confused blind man" yayi maganar tare da yin murmushi. Sai da ta kuma kallonsa, ganin yana murmushi, murmushin ma a nutse yake yi.

Kallonta da ya yi, ya sanya ta daina kallonsa, ya ce "Amm kwanaki, kamar akwai maganar da ki ke son ki yi mini, something like wani abu yana damunki"

"Baka tambaye ni a lokacin ba sai yanzu, ka manta ba wani abu bane, ya wuce" tayi maganar cikin tsiwa, tana kawar da kanta gefe.

Kallonta yayi, bai ce uffan ba, ya zira hannu a aljihunsa, ya ciro wayarsa, ya danna ya saka a kunnensa, ya ce "Kawo mini abun nan, na ƙasan katifata, ina wajen bishiyar kalgon nan"

Shiru ya wanzu a tsakaninsu, sai ga ɗan mama ya ƙaraso, ya miƙawa Viper envelope, ya saka hannu ya karɓa ya ce "Zaka iya tafiya"

Ya kalli Nabila ya ce "Gashi, wani abu ne daga aikinki ne na fara biyanki wani abu, idan komai ya kammala, in sha Allah zan yi miki kyakykyawan biya"

Ta karɓi envelope ɗin ta jujjuyata, ta saƙala masa a hannunsa ta ce "Da dan kuɗi zan yi maka aikin nan, da ba zan yi shi ba, bana buƙatar kuɗinka, a wurin Allah nake neman ladan abun da zan yi maka, ba wai dan halinka ba"

Shi ma ya jujjuya envelope ɗin, ya ce "Rashin sani, ya fi dare duhu, abun da yake ciki yafi kuɗi muhimmanci a wurinki, zaki dawo ki nema da kanki, shikenan a sauka lafiya"

Ta shagwaɓe fuska tana kallonsa, shi ma ita yake kallo, ji yake kamar ya tambayeta me yake damunta, ta rame, amma ya kasa.

"Kayi haƙuri"

"Da me?"

"Kayi haƙuri ka bani"

Ya zira aljihunsa ya ce "Ai kuma kin yi wa kanki, maganin mara kunya, wuce ki tafi gida, kan a fara nemanki"

Ta sake marairaicewa ta ce "Dan Allah"

Viper ya ce "Kar ki ɓata mini rai, wuce ki tafi"

"Korata ka ke yi ko? Dan Allah meyasa ka tsane ni ne? Me nayi maka?, Kalli duk rashin lafiyar nan da nayi, ko sannu fa Viper, sannu kawai baka iya yi mini ba, abun yayi mini zafi fa"

"Really?"

Ta haɗiye wani abu mai ɗaci, ta gyaɗa kai ta ce "Shikenan, bari na tafi, in sha Allah zan yi duk abun da ya dace" ta juya zata tafi ya ce "Amm meye ma sunan naki? Abla ko?" Ta waiwayo ta kalleshi, ta fara tunanin a ina ma aka taɓa kiranta da wannan sunan?.

Ta girgiza kai ta ce "A'a Nabila"

"Ohh, sunan yayi mini tsayi, just accept it Abla"

Kamar ba yanzu ya gama yi mata wulaƙanci ba, ta ce "Nice one, na gode sosai" tayi maganar tana ɗaga masa hannu.

***
"Hello, Salim kana ina ne?"

"Bokan turai, ya aka yi ne?"

"Dan Allah gida nake son ka samo mini"

Salim ya ce "Gida kuma?"

"Eh salim, amma ba na son kowa ya sani, a wajen gari kuma, saboda na san daddy zai saka a fara bibiyata, sun dage lallai sai sun gano in da rahama take".

"To kai yanzu hakan da ka ke yi kana ganin shi ne dai-dai?"

Abdul ya ce "Shi ne, dole zan danƙata a wurin iyayenta, na kai ta makaranta kafin su san in da take"

"Abdul, ina tsoron abun da zai biyo bayan abun da kake yi ne?"

"Salim, rayuwar rahama nake ƙoƙarin karewa da ingantanwa, dan Allah ka taimaka mini, kar a kuma cutar da yarinyar nan a wannan karon"

"Shikenan, babu damuwa za a duba in sha Allah"

"And sirri ne Please, ko saif ba na son ya sani"

"Haba mutumina, ba sai ka jaddada mini ba, you are safe"

"Thank you"

***
Kankarofi yana zaune a kan gadonsa, yana daddana wayarsa, ya ci karo da lambar Hafsat. Ya yi shiru yana kallon lambar ta ta, ya shafi saman lambar yana tuno ta, yarinyar ta nuna masa so, kuma shi kansa ya san ba dan yana son ta ya aureta ba, amma beside his wealth, ta so shi, ta yi iya ƙoƙarin ta a kansa, amma ya kasa sakewa da ita, yayi mata adalci, har auren ya mutu.
Amma ita jidda bai ji haka a kanta ba, hasali ma sosai suke gogawa ita da Safiyya, duk da dama Jidda tsohuwar budurwarsa ce, lokacin tun suna jam'iyya ɗaya

Download complete TXT · Novel page