Karfe A Wuta

Chapter 158 of 167

ka tsaya ka ɗauki fansa, ka jira kaga yadda Allah zai yi da shi kuma".

Viper ya sunkuyar da kai yayi shiru, sai huci da yake yi.

Nabila ta dafa kafaɗarsa ta ce "Vi, ka yi haƙuri dan Allah, kar ka sanya damuwa da yawa a ranka, kamar yadda wasu daga cikin mutane ba sa girbar tarin alkhairin da suka shuka, suke komawa ga Allah, su tarar da sakamakon su a can, haka wasu daga cikin waɗanda suke aikata ɓarna, ba sa girbar abin da suka shuka, sai a gaban Allah. Wata shari'ar sai a lahira ai"

Viper ya jinjina kai ya ce "Haka ne"

Alhaji mu'azzam ya ce "Haka ne zancenki, ni kaina nayi iya ƙoƙarina, na ga Indabo an hukunta shi, amma abu ya gagara, shiyasa na haƙura na zuba wa sarautar Allah ido, ka yi haƙuri Viper, mun san an cutar da kai, amma ci gaba da jayayya da dagewa lallai sai ka ga bayan indabo, zai ƙara complicating abubuwa ne kawai, lokaci ya yi da yakamata ka yi relaxing, ka huta ka nutsu ka yi enjoying life ɗin ka. Indabo kuma ka zuba ido, hakkin abubuwan da ya aikata, ba zai taɓa barinsa ya rayu cikin aminci da kwanciyar hankali ba, ko a yanzu ka kafa tarihi, kuma rayuwar gidan indabo ta watse, dan haka ka yi haƙuri"

Viper ya jinjina kai, "Yauwwa, Ubangiji Allah ya yi maka jagora, ya kawo maka ci gaba na ban mamaki"

Suka amsa da Amin.

Viper ya kalli Alhaji mu'azzam ya ce "Na gode sosai da sosai, Allah ya saka da alkhairi"

"Bakomai kar ka damu"

Ya sake kallon Alhaji mu'azzam ya ce "Ka tafi da ita wurin hafsa dan Allah, ta huta ta kwana a can idan ban takura maka ba"

Alhaji mu'azzam ya ce "Wane irin takura kuma, ba takura ai dama yakamata ta kawo mana ziyara"

Nabila kuwa ta ce "Yaya za ayi na tafi na bar ka, wa zai yi jinyarka?"

Viper ya ce "Kar ki damu, babu abin da zan nema na rasa in sha Allah, ana kula da ni"

"Ni gaskiya ko na tafi ba zan iya nutsuwa ba, hankalina ba zai kwanta ba, ka bari idan ka samu lafiya na je gidan nata"

Ya tsuke fuska ya ce "Zaki fara ko? Ba zan ce ayi abu ba ki yi, sai kin yi gardama ko?"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah vi, wallahi hankalina.... Kallon da ya yi mata ne ya sanya ta yin shiru, idonta na cika da hawaye.

Haka tana ji tana gani, ta tafi ta bar shi.

Gidan hafsa gida ne haɗaɗɗe mai matuƙar kyawun gaske, Hafsa na ganin Nabila ta rungumeta tana murna.

Ta kalli Kankarofi ta ce "Yallaɓai, ina ka tsinto mini ita, ko ta biyo maigidan ne ban sani ba, ba ta gaya mini ba?"

Ya ce "Ina fa, wani case ɗin ya kuma tasowa" nan ya gaya mata abin da ya faru.

Jiki a sanyaye hafsa ta ce "Kai, Allah ya isa tsakaninmu da wannan azzalumin mutumin, Allah ya shiga tsakaninmu da shi, amma ya jikin Yaya Al'amin ɗin?"

Alhaji mu'azzam ya ce "Jikinsa da sauƙi, duk da yana da ƙarfin hali, amma an harbe shi a kafaɗa"

Cikin tausayawa ta kalli Nabila ta ce "Ki yi haƙuri kin ji ƙanwata, in sha Allah zai samu lafiya" Nabila kuwa ɗan kukan da take maƙalewa ya ƙwace mata, Hafsa ta din ga rarrashinta, ta kaita ɗaki ta yi wanka ta bata kaya ta saka.

Ta ci gaba da rarrashinta, daga nan kuma suka shiga hira, a lokacin Nabila take bata labarin wasu abubuwan, tun daga haɗuwarta da Viper.

"Ya sha wahala sosai da sosai, ina matuƙar jin tausayinsa, daga wannan sai wannan"

Hafsa ta ce "Kin san da haka amma ki ka din ga bori wai ba kya son aurenku"

"Ina da dalilina mai ƙarfi na yin haka, amma koma dai menene ya riga ya wuce, Ubangiji Allah ya sassauta masa"

Hafsa ta amsa da Amin tare da ci gaba da rarrashinta.

A ranar aka fitar da sanarwar cewa, Viper ba ɗan ta'adda bane ba, domin yana aiki ne da rundunar tsaro ta ƙasa, kuma harbi ya yi shi ne a kan ƙa'ida, babu daɗewa za su fitar da rahoton ainihin abin da ya faru.

Walid ya dawo daga kasuwa, bai samu dawowa gida da wuri ba, saboda ayyuka da suka yi yawa, kuma sai da ya biya wurin liti suka ɗan yi hira, suka zauna a joint tare, daga nan ya taho gida.

Ya sha shagwaɓa da tuhumar dalilin daɗewarsa daga wurin amarya Shahida, kafin daga bisani ta gabatar masa da abincin sa na dare.

Wayar Viper ya kira, bayan ya gama, ya ɗaga amma bai ce komai ba.

"Mai zamani, wai ina ka shiga ne kwana biyu bana samun wayarka, hankalina ya tashi sosai, liti ma ya ce mini ba ya samunka"

Ya sauke numfashi ya ce "Ina lafiya"

"Mai zamani"

"Mai laya"

Walid ya ce "Akwai matsala, menene yake faruwa?"

Viper ya ce "Nothing much, kar ka damu ya ƙanwata"

"Da akwai matsala, kuma ba ƙarama ba ce ba, kamar yadda ka ke faɗa, meyake faruwa?"

"Koma da akwai matsala, ba gashi kana ji na ba, babu wata matsala ba abin damuwa ba ne ba"

"Ka san ba abu ne mai wahala na yi sammako na taho Abujan nan ba, ka gaya mini menene?" Walid ya yi maganar a hasale.

"Easy maza, harbina aka yi, amma ina samun sauƙi, kar ka ɗaga hankalinka"

Walid ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, kuma ka kasa gaya mini, ka ke cewa ba abun damuwa bane ba"

"Eh, bana son ɗaga muku hankali ne, dan Allah kar ka gaya wa kowa, kuma kar ka ce zaka zo, ba ni tabbacin hanya tana da kyau"

"Anya zan iya haƙuri ban zo ba, Viper kar ka ɓoye mini wani abu"

"Kai dalla ware ina gaya maka magana kana ja, zan saka maka ƙarfe ka kuma ƙoƙarin ƙaryatani, ja jiki dalla, mai laya" Walid bai san lokacin da dariya ta suɓuce masa ba ya ce "Na kiyayi mai zamani, tuba nake ka san ɗaukar ƙarfenka ba duk kai ba, na sallama tuba nake, Allah ya ƙara lafiya, ya ja zamaninka mai dogon zamani"

Viper ma yayi murmushi ya ce "Sai da kai na wajena, ka gaida mini ƙanwata"

"Zata ji in sha Allah" suka yi sallama ya ajiye wayar yana murmushi.

Ba a awa uku, sai Nabila ta kira Viper, ta tambaye shi yaya jikinsa.

Har ga Allah ta so ta kwana tare da shi, amma ya koreta ya saka aka tafi da ita.

Da kyar ta iya cin abincin dare, Walid ya kirata, yana yi mata mitar, meyasa ba ta gaya masa abin da ya samu Viper ba, ta gaya masa ba ta sani ba sai daren jiya, ita ma yau ta zo ta ganshi, amma ta tabattar masa da jikinsa da sauƙi.

Ƙarfe uku da rabi, alarm ɗinta ya buga, ta tashi zaune, haka kurum sai ta kira lambar Viper, gani take yi kamar wani abu zai same shi, ga mamakinta kawai ta ji ya ɗaga.

"Vi"

"Mmm"

"Baka yi bacci ba idonka biyu?"

Ya ce "Mmm"

"To meyasa?"

"Ciwo" ya bata amsa muryarsa ƙasa-ƙasa.

Ta miƙe tsaye ta ce "Ka gani ko, da ka bari na kwana tare da kai, atleast ina kusa da kai, na taimaka maka da wani abun, wurin harbin ne yake yi maka ciwo?"

"Mmm"

"Sannu Vi, Allah ya baka lafiya ya sanya kaffara ne" tayi maganar tana kuka.

"Abla, stop crying, babu zafi sosai kawai na kasa bacci ne"

"A'a da zafi mana, ina jin zafin a zuciyata"

Shiru ya yi yana tuna lokacin da jauhar take yi masa magiyar, ya daina zuwa in da za a cutar da shi, saboda ita take jin zafin a zuciyarta.

"Ki na ji na?"

"Eh"

"Ki kwantar da hankalinki, ki daina kuka Please, idan ba haka ba, zan ba da umarni a hana ki ganina, har sai na warke"

"Yi haƙuri na daina"

"To shikenan, ki yi bacci mai daɗi"ya katse wayar.

*****
Bunkure ta din ga zuba ido, ta ga ta ina za ayi belinta, domin kuwa ba wuri ɗaya aka kaita da su Indabo ba, ita Kano aka yo da ita, domin ta fara Fuskantar tuhuma ta farko, da ake yi mata a kano, amma shiru babu alamar za ayi belinta, jami'an tsaro suka tabbatar mata da cewa a gaban kotu za a gurfanar da ita.

Abokan aikinta da suka kai mata ziyara, suka tabattar mata da cewa an bayar da belin indabo, daga majiya mai ƙarfi, kuma ba a sanar da cewa an kama shi ba, ita ce kaɗai labarin kamata ya cika media.

Abin ya ɗaure mata kai sosai da sosai, sai dai ta yi masa uzuri, ta ƙara masa kwanaki, ko zai waiwayota ya sanya a bayar da belinta.

Washegari da sassafe Nabila da Hafsa tare da Alhaji Mu'azzam, suka tafi wurin Viper.

Ko da su ka je, Nabila da Hafsa ne suka shiga, shi kuma Alhaji mu'azzam ya tsaya a wani office.

Suka tarar an buɗe wurin raunin Viper ana dressing.

Da sauri Nabila ta ƙarasa, ta zauna ta gefen sa tana yi masa sannu, cikin kulawa da tausayawa.

Ya langaɓo kansa jikinta ya ce "Washh da zafi" sai ta sake rikicewa cikin tausayawa ta ce "Sannu Vi, dan Allah doctor ka yi masa a hankali"

Likitan ya ce "Ba wani zafi, tun ɗazu nake durje ciwon, bai ce da zafi ba sai da ki ka zo"

Viper ya ce "Abla zafi, da zafi yake yi mini"

Hafsa kuwa riƙe baki tayi, tana kallon ikon Allah, da wani ne ya gaya mata zata ce an zabga mata ƙarya ne, kodayeke ba abin mamaki bane, ko a baya Jauhar yana sakin jiki da ita. Nabila kuwa ta sake rikicewa ta ce "Dan Allah ciwon nan ya wanku haka a ƙyale shi"

Likitan kasancewar sa, bahaushe ne ya ce "Sai dai ya yi kukan jini, sai na cuɗe shi sosai"

Marairaicewa Nabila ta yi kawai ta saka kuka, domin ramin da taga wurin harbin yayi, kuma a haka likitan yana cewa wai bashi da ƙan jiki, wurin ya ciko.

"Ke da wasa nake yi fa, ba wani zafi kawai ina son in ga kina kula da ni ne"

"You are just pretending, amma na san da zafi"

Yayi murmushi ya ce "Idan muka koma gida, ke zaki ci gaba da yi mini dressing ɗin fa"

Ta girgiza kai ta ce "Ba zan iya ba, kuka zan ta yi" Viper yana kallo Hafsa ta silale ta bar ɗakin, bayan ta ajiye kayan abincin hannunta.

"Zafin shigar bullet ɗin, bai kai zafin ƙiyayyar da ki ka nuna mini ba, ya taɓa zuciyata sosai"

Ta marairaice ta ce "Am sorry Vi, dan Allah ka daina tunawa mana" dai-dai lokacin likitan ya kammala nananɗe masa hannun ya ce "Gashi nan maza ki haɗiye shi madam" Nabila ta yi murmushi, sai a lokacin ta farga Hafsa ba ta nan, ta ce "Kai, tare fa muka shigo da hafsa, tana ina?"

"Ta fita tun ɗazu, taga abin naki ba na ƙare bane ba" yayi maganar yana janyota jikinsa.

Ta tura baki ta ce "Ni da suka din ga soyayya a gabana ya na yi, ko kunyata ba sa ji"

"Mhmm su su na can su na soyayya, ke ki na takaicin an yi miki auren dole"

Tashi ta yi daga jikinsa, saboda da lafiyayyen hannun, yake ƙoƙarin fara lalubeta, ta ce "Bari na baka abinci ka karya, yaya ka kwana da jikin?"

"Jikina Alhamdilillah, yau zan fita ma na zagaya, na ji sauƙi sosai da sosai"

Tana cikin haɗa masa breakfast, Alhaji mu'azzam ya shigo tare da Hafsa.

Suka duba jikin Viper, Alhaji mu'azzam ya ce "Minista zai zo dubaka anjima in sha Allah"

Viper ya ce "Ni ɗin?"

"Eh kai fa" ya kalli Nabila ta kalle shi.

Ta ce "Yallaɓai, Viper ministan tsaro zai zo ya duba?"

Alhaji mu'azzam ya ce "Ni ma ba ƙaramin ministan bane, ai komai sila ne Nabila, kuma idan Allah ya yi niyyar yi maka wani abu, ko da sai ka sha baƙar wahala, kan ka same shi, sai ya baka abin nan.
Da gudunmawarsa ɗari bisa ɗari na din ga gudanar da wasu abubuwan, na taimaka wa rayuwarka.
In sha Allah kukan da ki ke yi na sha wahala, zai zame masa alkhairi, dan na yi masa bayaninsa sosai da sosai, kuma mussaman saboda kai ya kira ya ce lallai ayi bincike a wanke ka, dan haka ka kwantar da hankalinka in sha Allah babu abin da zai faru da kai sai alkhairi, wahalar da ka sha, ba zata taɓa tafiya a banza ba in sha Allah"

Shi dai Viper jin abin yake kamar ba gaske ba, bayan sun gama, Alhaji mu'azzam suka tafi, suka bar Nabila, da zummar da yamma za a zo a ɗauke ta.

Viper zuciyarsa ya din ga kaiwa nesa, kasancewar sa da daga shi Nabila, saiti yana neman ya ƙwace masa, duk da a da yana iya sarrafa kansa yadda yakamata.

Ya ja ta suka fita yawo, idan suka haɗu da na ƙasa da shi, su sara masa, idan na sama da shi ne, ya sara musu.

Duk da gargaɗin da Viper ya yi wa Walid, amma sai da ya gaya wa Liti, abin da yake faruwa, ƙarshe sai da suka yi video call da shi, sannan hankalinsu ya kwanta.

Sai da aka kwana huɗu, sannan Alhaji mu'azzam ya zo tare da ministan tsaro, kamar yadda ya sanar da Viper zai zo duba shi, ba kuma shikaɗai ba, har da babban hafsin soja na ƙasa, da wasu daga manyan shugabannin rukunin sojoji masu irin aiki irin na Viper.

Yana zaune a kan gadonsa, Nabila na kan kujera, suka shigo, ta tashi tsaye tana kallon su, sai da ta gansu tare da Alhaji mu'zzam, sannan ta ɗan nutsu.

Yana zuwa ya miƙa wa Viper hannu, sai da ya ɗan yi jimm, sannan ya miƙa masa suka gaisa.

"Finally, yau gani ga Viper, ya ci sunansa Viper, yayi kalar mazaje" yayi maganar yana murmushi.

Ɗaya daga sojojin ya ce "He's very intelligent, and hardworking man, da taimakon team ɗin sa, mun daƙila hare-hare masu yawa, yana taimakawa rundunar tsaro sosai da sosai"

Ya jinjina kai ya ce "Na ji daɗi sosai da sosai, duk da ta wani fannin mun aikata laifi, na cireka daga prison, aka yi maka horo na musamman, amma da wata ɓarnar gara wata, na ji labarin duk abin da ya sameka, hakan ya sanya na ƙara samun ƙwarin gwiwar saka hannu a taimaki rayuwar ka, duk da ka bamu wahala da farko, dan sai da na ce, idan zaka bayar da matsala gara a kasheka, amma Kankarofi ya dage, ya ce a bika a hankali.
Ina jimanta abin da ya same ka, Allah ya baka lafiya, sannan zan san abin da zamu yi maka, mu ƙara ɗaga darajarka a gidan soja, you are brave man Al'amin, the entire nation is proud of you. Ka yi abin da ya dace, sauran kuma ko su hukunta masu laifin, ko su bar su, wannan kuma su da Allah ne, get well soon my man" yayi maganar yana dukan kafaɗar Viper.

Alhaji mu'azzam ya ce "Ga kuma madam ɗin sa fa, his lioness wife, barrister Nabila, yarinyar da nake baka labari, mutuniyar Naja'atu Bunkure"

"Kai, to ai na ganta yarinya ƙarama"

"Eh yarinya mai kasada ba, su suka assasa lallai ayi wa Indabo kiranye, amma aka daƙile su, ai nan Abuja zata dawo, ku nema mata gurbi gaskiya, a din ga matsawa matasanmu, suna gwada mana tasu baiwar, hatta cheif judge ya san da ita, amma ita ba ta sani ba"

Shugaban hafsin Sojojin ya ce "Tabbas ƙasarmu Nigeria tana da nagarttun matasa, wanda za a basu dama, zasu kawo gayar a abubuwa da yawa. Kamar history ɗin Viper da na duba, da tun tasowarsa, ya samu abin da ya dace, to da tabbas a irin ƙwaƙwalwarsa, da wataƙila shi ne a kujerata, ya zama matashi mafi ƙarancin shekaru da ya riƙe rundunar tsaro ta Nigeria, na yaba da basirarsa nesa ba kusa ba"

Nabila ta ji daɗin yabon da Viper ya samu, bakinta har kunne, bayan fitarsu ba ta san lokacin da ta rungume shi ba, tana ta yi wa Allah godiya.

Ta ce "Ka ga abin da na gaya maka ko? Dama lokuta da dama, Allah yana jarraba bawansa, kafin ya yi masa wata baiwa, Alhamdilillah ala kulli halin, Allah ya ƙara ɗaukaka Vi"

Murmushi kawai ya yi mata, shi dai baya fatan ace za ayi masa wani babban matsayi, saboda yana da 'yan adawa a cikin jami'an tsaron, gani suke kamar akwai wani fifiko na musamman da ake ba shi.

Bayan tafiyar baƙin, shugaban sojojin yake cewa kankarofi, yana yi wa Nabila kallon sani, tana kama da wani tsohon ubnagidansa a sojoji, major Yusuf maitama.

Kankarofi ya ce "Ai 'yar sa ce"

Ya ce "In dai jarumta ce da taurin zuciya, ba ta yar a ƙasa ba"

Minista ya ce yana son a saka sunan Viper, cikin sabbin naɗe-naɗen da za ayi na sojoji, a yi wa manyan ritire.

Shugaban ɓangaren su Viper ya ce "Amma sir, lokaci bai yi ba ayi masa wannan muƙamin fa"

"Eh a banza ma, ana saka waɗanda ba su cancanta ba, dan haka a saka mini sunansa, dan ya cancanta" ya ja bakinsa ya tsuke, domin kuwa kujerar da za a ɗora Viper, daga ita sai tasa.

A daddafe Viper yayi kwana tara, ranar na goma ya ce a gidansa zai kwana, ya din ga zuwa dressing ɗin, ya gaji da zaman Asibiti.

Nabila ma ta ji daɗin hakan, dan kuwa ta gaji da sintirin nan, babu wanda suka gayawa halin da ake ciki, a 'yan uwa, duk Major ya samu labari, ya kira Viper ya din ga faɗa a kan meyasa ba su faɗa ba, Nabila ta kaee shi, ta ce masa basa son tayar wa mutane hankali ne.

Allah ya taimake su, an daƙile yaɗuwar labarin ƙaryar cewar Viper ɗan ta'adda ne.

Nabila tana ta yi wa Viper

Download complete TXT · Novel page