Karfe A Wuta

Chapter 56 of 167

aura. Yaya hafsa sai anjima".

Ya ce "Tsaya na baki na mota" ya saka hannu a aljihunsa ya ɗebo kuɗin da bai san yawan su ba, ya miƙa mata ta girgiza kai ta ce "A'a na gode"

Hafsa ta ce "Baby kawo ka ga" ta karɓi kuɗin ta turawa jauhar a jakarta, ta ce ba a mayar da kyautar manya, ku gaida gida. Tuni Al'amin ya juya ya fice, idan ya cigaba da tsayuwa, zai iya yi wa Alhaji mu'azzam illa, da wuƙar da take cikin rigarsa a soke.

Tun da suka tafi hanya, bai ce mata uffan ba, hakan ya sanya ta cikin matsanancin tashin hankali.

Da ya ajiyeta a gidan ma, tafiyar sa yayi, bai ko shiga gidan ba.

Ta din ga addu'a Allah ya sanyaya masa zuciyarsa. Duk yadda ya so ya sarrafa kansa ya kasa, sai da yayi shaye-shaye, domin rage raɗaɗin abun da yake ji, dan zuciyarsa har wani tururi take yi.

Har sha biyun dare, idonta biyu tana zaune, tana jiran dawowarsa, ya koma mata Al'amin ɗin sa, dan ko sallama bai yi ba ya shigo, ya wuceta ya tafi ɗakinsa.

Cikin fargaba, tana addu'a, ta bi bayansa, warin wiwi duk ya cik wurin.

"Sannu da zuwa, nan zan kawo maka abincin?"

"Fita ki bani wuri, kafin na kakkaryaki na zubar. Idan ba kya son zama da ni, ba sai kin wulaƙanta ni, ta hanyar kai ni wurin tsohon saurayinki ba, shiyasa nake ta baki zaɓi tuntuni a kan zama da ni, ba dan na sarrafa zuciyata ba, sai na kashe mutumin nan har lahira yau, fita ki bani wuri, bana ƙaunar ganinki ma".

Ta marairaice ta ce "Dan girman Allah ka yi haƙuri, wallahi da na san zamu ganshi da ba mu je ba, ni saboda 'yar uwata na je".

"Saboda 'yar uwakki, ko kuma saboda ki ganshi?"

"Ya za ayi na je ganin wani, alhalin ina ɗauke da igiyar aurenka a kaina"

"Ki daina wani kwantar da murya, na riga na gane abun da ki ke nufi, da in da ki ka dosa, if you still loves him zan iya sakin ki, ki iya koma wurinsa, tun kafin na illata ki, ba zan juri wannan cin fuskar ba, nan gaba ban san me zaki aikata ba"

Cikin tsananin ɓacin rai ta ce "Idan ka sake ni, hakan baya nufin rayuwata ta zo ƙarshe, jaririn da ya zo duniya ma Allah ya na iya karɓar rayuwar mahaifiyar sa, kuma ya raya mata shi. Ka yi mini duk hukuncin da ka ga shi ya dace ni" ta fice daga ɗakin, cikin tsananin ɓacin rai da damuwa.

Ransa yayi matuƙar ɓaci, jin yadda ta gaya masa maganganu, gashi dama a cake yake, ya nemi wata ƙwaya ya haɗiya ya kwanta, dan kar ayi ɓatacciya. Da asuba ya farka, ya saba ta zo tayi ta fama ta tashe shi, amma yau taƙi zuwa.

Yayi sallar asuba, gari yayi haske ya fito, amma ba ta fito ba, ya gaji da zama ya fita.
Da azahar ma, abincinsa ta ajiye masa ta yi zamanta a ɗaki, idan yana falo tana ɗakinta, idan yana ɗaki sannan zata fito.

Ya shareta shi ma, yana jiran ta zo ta bashi haƙuri kamar yadda ta saba, amma taƙi, sai ya ji gidan yayi masa duhu babu daɗi. Kusan kwanaki uku, ba wanda yake shiga harkar wani.

Yau har ya cire kaya ya kwanta, ya tashi ya zauna yayi shiru yana tariyo maganganun da ya gaggaya mata, sai ya ji sun ɗan yi nauyi da yawa.

Ya tashi ya tafi ɗakinta, kasancewar babu wuta, ya kunna fitilar wayarsa, ya shiga.

Tana banɗaki tana wanka, ta jingina fitilarta a kan mudubi, tana haska mata cikin toilet ɗin.

Ya ƙarasa gaban mudubin, ya ɗauki wayar ya kashe fitilar.

"Waye a nan?" Tayi maganar cikin tsoro, dan ba ta san ma ya dawo ba.

"Waye?" Yayi shiru bai yi magana ba.

Da sauri ta gama kwara ruwan a jikinta, ta fito sai dai ɗakin yayi duhu, ba ta ganin komai.

"Wai waye ne?" Tayi maganar tana laluba hanya.

Direction ɗin da yake ta nufo, cikin tsoro, kawai ta ji ya zaunar da ita a kan cinyarsa. Cikin tsananin tsoro ta ware baki za ta yi ihu ya tsohe mata baki ya ce "Shhhhh, Al'min ne"

Ayshercool
08081012143

39
🔞 LITTAFIN KUƊI NE ₦500 VIA 0009450228
AISHA ADAM JAIZ BANK
SAI SHAIDAR BIYA TA 08081012143
YOUR RECEIPT VALIDATE YOUR PAYMENT.








Cikin cunkusa baki ta ce "To kuma shi ne zaka tsorata ni? Ko gama wankan ban yi ba na fito"

Ya ce "To mu je na ƙarasa miki"

Tsuke bakinta ta yi ta kasa magana, jin abun da yake yi, da ba ta yi zato ba.

Kasancewar bayanta, yana jikin ƙirjinsa, yana jin bugun zuciyarta yana fita da sauri-sauri.

"Meyasa ki ke shareni? Kwana uku kin yi mini laifi, kuma kina gaba da ni ko?"

Ba ta yi mamakin ƙarfin hali, da ƙwarewa a iya rainin hankali, irin na Al'amin ba, wato ma zaman jiran ta bashi haƙuri yake yi.

"Kin san zaki yi gaba da ni, meyasa ki ka bari muka saba? Ba ni da saurin sabo, ki ka yaudare ni ki ka sa na fara sabawa da ke, shi ne zaki wani din ga mazewa. A din ga manta abu a kwana ɗaya ya wuce kawai a cigaba da life. Ni kaina ban san dalilin da ya sanya nake matuƙar jin baƙin ciki idan na ga wani abu ya raɓe ki ba"

Da ƙarfi ta ce "Master" tayi maganar tana ƙoƙarin miƙewa.

Hankali kwance ya ce "Yes" ba tare da daina abun da yake yi ba.

Cikin rauni ta ce "Wai meye haka?"

"Aure" ya bata amsa kai tsaye.

Shiru yayi, jin yadda zuciyarta ke cigaba da bugawa da sauri, tana nema ta fara haki, saboda tsoro.

A hankali ya ce "Common, relax mana"

"Babyn roba" tayi masa shiru, "Kodayeke yanzu babyn ƙarfe ce, ki amsa mana" still ta yi masa shiru, yana jin yadda ta saka ƙarfinta ta riƙe hannunsa.

Fito yake yi mata a kunne, hakan ya sanya ba shiri, ta saki hannunsa, ta toshe kunnenta.

"Ki amsa mana, tambaya zan yi miki mai muhimmanci. Kin san bana mantuwa, kamar na'aura mai ƙwaƙwalwa nake, in dai ka ajiye zaka zo ka ɗauka. Idan ban manta ba kin ce kina so mu rayu tare. Ina ta tsoron taɓa abun da nake ganin ban dace da shi ba. Ba na son cutar da rayuwarki, in yi silar gurɓacewarta kamar yadda tawa ta gurɓata, duk da kin daɗe ki na nuna mini ina rintse ido, Al'amin ba ya abu bisa zalunci"

"Na nuna maka me?"

"In faɗa kenan, ko shekaranjiya meya kawo zancen zuriya? Ke 'yar yarinya kallonki kawai nake yi, amma kar ki damu da hakan ai lafiya ce" wato da wani ne yake ba wa jauhar labarin maganganun nan daga bakin Al'amin suke fitowa, sai ta ƙaryata, amma ƙiri-ƙiri, ya shige duhu yana sakin maganganu yadda yake so, alhalin ya ce ba ya jin komai.

Tana cikin tunanin ta ji ya ce "Kin amince mu rayu tare, a matsayin abu guda? Ba na son cutar da ke, ke ma kin shiga ƙalubale da dama, bana son ki sake shiga matsalar rayuwa, rayuwarki ta tafi a haka kawai. Idan kin amince, zan yi iya ƙoƙarina wurin zama da ke da zuciya ɗaya, amma sai kin yi wa yanayin rayuwata uzuri, duk da a yanzu ma kin taka muhimmiyar rawa a rayuwata. Be mine"

Haka kurum ta fara kuka, kukan da ba ta san na menene ba ma.

"Talk babyn roba".

"To ka ƙyale ni, gobe da asuba sai na gaya maka"

Cikin buɗɗiyar muryarsa, da take fitowa daga ƙirjinsa, ya ce "Na ƙi wayon, yanzu zamu gama maganar"

"Master"

"Mmmm"

"To zaka daina saka ni kuka?"

Ya ce "In sha Allah"

Ta ce "Zaka daina shaye-shaye?"

"In sha Allah, ina iya ƙoƙarina, ba abu ne da zan daina lokaci ɗaya ba. Mu bar wannan maganar, baki bani amsa ta ba, zaki cigaba da zama da ni, a yadda nake, ina talaka marayan da ya rasa kulawa, sai bayan shigowar ki rayuwata?"

Tana kuka ta ce "Dama ai kai ka ke cewa zaka sake ni, ka ke sakani kuka, ina son in zauna da kai"

Yayi ajiyar zuciya ya ce "Duk wani abu da ki ka yi mini na alkhairi, yana rubuce a ƙirjina, ba zai taɓa gogewa ba, ban taɓa mantawa da ko guda ɗaya ba, babu wata mace da ta taɓa playing role ɗin uwa a rayuwata sai babyn roba, bashi ne a kaina kulawar da ki ka yi mini".

"Ni saboda Allah nake kula da kai"

"Ni na isa in biya ki ne dama?"

Jauhar ido yayi tsilli-tsilli, bayan da Al'amin ya ƙaryata tunaninta na ko ba shi da lafiya ne.
Ya tabattar su a matsayin miji da mata. babu tsammani aka kawo wuta, haske ya gauraye ɗakin, Jauhar ta takure jikinta, sai rawa jikinta yake yi, yayi murmushi ya ja bargo ya rufeta.

Ya zuba wa gashin kanta ido, ba baƙi ne wuluk ba, amma mai laushi irin na fulani, ya hargitse, ta cusa kanta cikin bargo sai gashin a waje.

Ya daɗe yana kallonta, kafin ya kai hannunsa yana shafa gashin ya ce "Amm ya ma sunan angela ko?" Tayi masa shiru, ta sake dunƙulewa wuri ɗaya.

Ya cire bargon daga fuskarta, amma ta rintse idanunta.

"Kalleni mana, abu zan gaya miki fa"

Ta cunkusa baki, tana ta jan majina a hancinta, fuskarta duk ta yi ja saboda kuka.

Wani nishaɗi yake ji, ya cigaba da kallonta yana ta murmushi, kamar wanda aka yi wa Albishir da kujerar makka.

Wayarsa da ta faɗa ƙasan gado ce, ta fara vibrating, ya juya ya zura hannunsa ya ɗaukota, ya sake matsawa kusa da jauhar, ya ɗaga wayar.

"Maza" muryar liti tayi amsa kuwwa a wayar.

"Mmm"

"Kana ina ne?"

A taƙaice ya ce "Gida" yayi maganar yana cigaba da shafa gashin jauhar.

"Wai me ka ke yi ne? Ko baka da lafiya ne?"

Al'amin ya ce "Meyafaru?"

"To ai ji nayi kana amsawa kamar ana yi maka dole"

"Ina jinka ya aka yi?"

Liti ya ce "Akwai matsala ne fa"

"Ta me?"

"Yaran madaki, duk sun cire pastocin indabo, ka san ɗazu Walid da su guduma suka gama sasskawa, mu na dawowa muka tarar duk sun cire, ya tambaya aka ce masa yaran madaki ne, gashi can ya tafi, nayi-nayi ya ƙyale su, ya ɗau wuƙa ya tafi, shikaɗai kar su yi masa wani abun, ka san Walid da baƙin taurin kai, kamar jinjirin jaka, dan yafi jaki taurin kai"

Al'amin ya ja guntun tsaki ya ce "Gani nan, bari na tafi cikin garin, maza ka kira yaran nan, ka yi magana da su guduma ma, zan kira yaran unguwar mu, maza su bishi kar su yi masa wani abun, gani nan" ya yinƙura zai tashi, jauhar ta ja jikinta ta riƙe shi ta ce "Rigima zaka je ka yi ko?"

Ya girgiza mata kai ya ce "Ba rigima zan yi ba, amma idan har ba a kai masa ɗauki ba, za su iya kashe shi"

Cikin takaici ta ce "Kana ganin halin da ka sakani, a  haka zaka tafi ka bar ni, a wannan yanayin da nake ciki?"

Ya ɗagota ya ce "Ki yi haƙuri, bana son a sake asarar rai saboda ni, wallahi suka ga Walid shikaɗai, za su iya kashe shi, am sorry yanzu zan dawo, ki kwanta kar ki tashi kina buƙatar hutu" ya ƙarasa maganar yana kwantar da ita ya bar ɗakin.

Ta lumshe idonta, hawaye suka cigaba da zuba, sai da ta yi ta gaji, sannan ta saukko daga kan gadon da kyar, ta haɗa ruwa mai ɗumi sosai ta tsarkake jikinta, ta nemi wuri ta kwanta.

Da asuba da ƙyar ta tashi, ko alwala ba ta yi ba, ta tafi ɗakinsa ta duba, ko ya dawo cikin ƙoshin lafiya.

Ƙarar buta ta jiyo a banɗakinsa, alamar yana alwala, wani ɗan sanyi ta ji a ranta, yau da kansa ya tashi sallar asuba, ko yaushe ya dawo ma oho.

Ta koma ta yi salla, ta sake fitowa ta leƙa, ta ga yana salla, ga kayan shaye-shaye a kan katifarsa, ganin yana salla, ta shiga kanta tsaye, ta tattare kayan ta fice.

Bacci ya ƙara kwasheta, tana cikin baccin ta ji ta a takure, ta yi miƙa ta buɗe idonta, ta saka a nasa.

"Kalli agogo ƙarfe sha ɗaya, yunwa duk ta yi mini illa, na sayo ƙosai na kasa ci, ya ja mai, kuma farin maggi ya yi yawa a ciki sosai.

'ikon Allah, shi ko ɗan rarrashin nan ma ba zai yi bs, zancensa kawai abinci.

A ƙule ta ce "In da ka tafi ba su baka abincin ba?

"Me ki ka ce?"

Ba tare da ta kalleshi ba ta ce "Na ce in da ka tafi ba su baka abincin ba?".

Ya ce "Ba su bani ba, ke zaki tashi ki bani yanzu"

Kawai ta juya masa baya, dan daren jiya ta ƙulu yadda ya tafi ya bar ta.

Ba ɗaga ƙafa, ba komai, ya ƙara huce baƙar maganar da ta gaya masa, ya gama ya tada kai da jikinta, ya lumshe ido ya hau bacci.

Ta gama koke-kokenta, duk iya ƙoƙarin da tayi, ta ture shi ta tashi, ta kasa sai ma ji da tayi tana haki, Al'amin ya gama raina mata hankali ta ko ina.

A haka har baccin dole ya sake yin gaba da ita.

Ƙarshe har azahar ko wanke-wanke ba ta yi ba.

Ta yi wanka, ta canza kaya, ta fito ya basar da ita, kamar babu abun da ya faru, ta tarar da shi da wayarta a hannunsa, yana game, ta share shi ta wuce, sai da ta fita ya bi bayanta da kallo yana murmushi.

Ta tarar yayi wanke-wanke, ya share tsakar gidan tsaf, har markaɗen kayan miya ya kai.

Ta dawo ta koma ɗakinta, ta ɗaukko bedsheet, zata fita ya ce "Me zaki yi ne?"

"Wanki"

"Me ya same shi, zaki wanke? Ko karyawa ba ki yi ba? Ki saka shi a baho, zan wanke, ki samu ki karya"

Sai cika take tana batsewa, mazewa kawai yake yi, don dariya yake son yi, amma ya maze shi ma ya sha kunu.

Tun da ya kai markaɗen nan, ya dawo bai sake fita ba, wuni guda yana gida, duk da babu wanda yake kula wani, amma zaman kula da ita yake yi.

Har isha'i, kowa ya koma ɗakinsa, har ta kwanta, ta ji ya shigo ɗakin, kan tayi magana ya ƙaraso kan gadon ya hau.

"Malam ya ne? Menene kuma?"

"Kamar yaya?" Yayi maganar yana janyo bargonta, ya rufe ƙafarsa.

Kamar tayi ihu ta ce "Menene kuma?"

Ya ce "Da na kawo miki kajin mutum goma sha biyu, ki ka cinye ki ka yi kyautar wasu, kin tambayi ta mecece?"

Cikin rashin fahimta ta ce "Ban gane ba, ka ce a gidan oganka ka karɓo".

"To gaba sai ki dinga tambaya, kwaɗayayyiya, ki ka din ga ci kina rabarwa, ni sai dai ki sammini, yanzu kuma tambayata lafiya? Ba lafiya ba"

Cikin rauni ta ce "Master" ya ce "Yes"

"Dan Allah ka koma ɗakinka" ya kwanta ya ɗora ƙafarsa ɗaya kan ɗaya ya ce "Zuriya fa ki ke so, ki ke wani basarwa" Jauhar ta yi danasanin faɗar maganar nan.

Kawai ta zauna a zaune tana kallonsa, sai kaɗa ƙafa yake yi.

"Zo ki kwanta, na ga lokacin da baki da lafiya, har wani ƙara lafewa ki ke yi, bisimillah" yayi maganar yana nuna mata ƙirjinsa.

Pillow ta gyara ta kwanta a kai, ta ƙi kula shi, mutumin da suka wuni ba sa magana, saboda tsabar son tayar da tarzoma, ya lallaɓo yana tayar da wani tsohon zance.

Da asuba ta riga shi tashi, ta shiga ta yi wanka, tayi alwala ta zo tana tashinsa, ƙarshe sai kusan shida da rabi suka yi sallar, bayan ya saka ta canza wani wankan da alwala. A wurin da tayi salla, ta kwanta a kan sallaya ta cigaba da bacci.

Iya ƙoƙarin sa yake yi kar ya sha komai, ya kasa jurewa, kamar zai fita hayyacinsa, ya lallaɓa ya dawo ɗakinta, ya tarar tana kwance a ƙasa tana bacci, boti ma yayi lakur a kan sallayar yana bacci.

Tankaɗe boti yayi can gaba, ya kwanta a kusa da ita, ya ƙura wa fuskarta ido, ya kai bakinsa ya sumbaci goshinta.

A ranar aka saka wa jauhar fankar solar, da ƙwai, ta din ga murna tana yi masa godiya.

Sai dai Al'amin ya uzzura mata, duk dare, sai ya ce mata wai shan fanka ya zo, zafi yake ji, sai da ta gaji ta ce "Dan Allah master ka ɗauke fankar nan taka ka mayar ɗakinka , ko na huta"

Ya ce "A'a ai dama ke na sayawa, dan haka gara na din ga zuwa nan kawai ina shan isakar, idan na mayar da fankar can, bayan iska kuma takura mini za ta yi din ga yi".

Ta ce "A taƙaice dai, ni ce fankar kenan?"

Ya ce "Eh mana, ke ga taki fankar, ni kuma ga tawa" yayi maganar yana nuna ta.

***
Kwanaki suka cigaba da tafiya, sai dai tsakanin Alhaji mu'azzam da Hafsa sai dai kallo, ranar da uwargidansa ta bari ya zo ɗakin hafsa, kawai ta ga ya nemi wuri ya kwanta.
Duk da irin kunya da kawaici irin ta 'ya mace, sai da ta cire kunya ta ce "Wai ni Alhaji, menene matsayina a wurinka ne? Na kasa gane kan wannan al'amarin"

Ya kalli hafsa ya ce "Jauhar, yakam...

A fusace ta ce "Wace irin jauhar kuma? Wulaƙancin naka da rashin mutunci har ya fi da, ga mari ga tsinka jaka? Tun ranar da jauhar suka zo, ka rasa sukuni, ka ke kirana da sunanta ba na so"

Ya ce "Am sorry mistake ne, ki ƙara haƙuri ki bani lokaci, na yi wa Safiyya Alƙawarin babu abun da zai shiga tsakanina da ke, har sai lokacin da ta samu nutsuwa hankalinta ya kwanta, tana cikin damuwa sosai da sosai, kin san tana da kishi ne sosai da sosai

Download complete TXT · Novel page