Karfe A Wuta
Chapter 57 of 167
".
Kamar ta ɗura masa ashar ta ce "Au har gaya mata ka ke ba abun da ya shiga tsakanina da kai, har sai ta yadda? Ita take aurena kenan? Bakomai na gode, ta ci lokacinta when it comes to my turn, zata gane shayi ruwa ne" ya girgiza kai ya ce "Kin ga ba na son rigima, ba zaki zo ki sameni, ina zaune lafiya da iyalina ki ɗaga mini hankali ba Please, ina respecting farincikin matata sosai da sosai "
Hafsa ta ja tsaki, ta fice ta bar masa ɗakin.
Al'amin na zaune a falon Indabo, ana ta tattauna yadda al'amura za su tafi kafin lokacin zaɓe, dan wata ɗaya kawai ya rage babban zaɓe, wanda yake dai-dai da lokacin sallar layya.
Ya rage daga Al'amin sai P.A da Indabo yana ta sake jaddadawa Al'amin, idan aka ci kujerar nan za su ji daɗi, dan tun yanzu an ce masa idan ya samu senator ɗin nan, akwai vacancyn mutum uku za a bashi a NNPC.
Al'amin ya ce "A cikin yarana, ko Nura guduma ne, ina son a samo masa aiki ko direban manyan motoci ne, yana can na saka ana koya masa jan manyan motoci"
Indabo ya ce "Ba ka da matsala, kawai ku yi aikinku, duk akwatin da ku ka ga zata bayar da matsala, ku tayar da tarzoma. Maganar da nake yi maka, a yarjejeniyar da muka yi da uwar jami'iyya ta ƙasa, kan na dawo cikinta, nan da wasu shekaru, za a tsayar da Abdul takarar mataimakin gwamna"
Al'amin ya ce "Har masu shaye-shaye ake tsayarwa su yi jagorancin al'umma kenan?"
"Shaye-shaye kuma, yaron da yake karatu a waje, in sha Allah shi zai zama mutum mai ƙarancin shekaru da zai zama gwamna"
"Menene sadakin aikina?"
Indabo ya ce "Me ka ke so ayi?"
Hajiya Bilki ce matar indabo ta shigo da laces, da atamfofi da lesuna sun kai talatin a hannunta, ta shigo ta zube a gaban Indabo.
Ya kalleta ya ce "Madam ya dai?"
Ta ce "Kala goma zan zaɓa ka saya"
"Ke dai kullum cikin ɗinka tsumma, ko gajiya ba kya yi"
"Kana shirin zama distinguish, ba dole na ɗinka sutura ina shiga ina fita, ina barazana ba".
Indabo ya ce "To ki ɗauka, ina ta jiran Kwamishinan ayyuka ne, rage kuɗin wata kwangila, mu ƙara rage na campaign, ya haɗa kayansa yana kan katanga, jami'iyyar da tayi nasara zai koma da an yi zaɓe.
Ala'amin ya tashi ya tafi gaban kayan, ya zaɓo zuƙa-zuƙan lesuna, guda uku, da atamfa uku.
Indabo ya ce "Yaya saya zaka yi?"
"Kai dai zaka saya, daga cikin sadakin aikina".
Hajiya Bilki ta ce "Kai, lesunna hannunk fa dubu tamanin guda biyu, ɗaya dubu hamsin da takwas, atamfofin nan dubu arba'in da biyar, har nawa zai baka? Kuɗin da yawa ai"
Ya kalleta ya ce "Ke zaki biya? Kuɗin kwangilar mutane za a sata a biya miki ai, wannan ma ya biya, ai ba kyauta zai bani ba, jinina da rayuwata zan saka a hatsari dan samun nasararsa. Ya miƙe da kayan a hannunsa, ya kalli Indabo ya ce "Sauran kuɗina za su zama ajalan a kanka, komai daren daɗewa zan waiwaye su, yadda ku ke ƙwamusar kuɗin mutane ta gajimare dole a din ga kasawa da mu, idan ana son a ga dai-dai, tun da damu ake wahalar waccan 'yar yarinyar ta gidana, itama yakamata a din ga damawa da ita. Kuma rabon tallafin karatu ma, a saka mini ita a ciki"
Indabo ya ce "Aminu kenan, shikenan jeka Allah ya taimaka"
Ya haɗa hannayensa biyu ya ce "Sa'a dai" ya fice daga falon.
Hajiya Bilki ta ce "Gaskiya honorable, yaron nan yana wuce gona da iri, kamar tsoronsa ka ke ji"
Ya ce "Ba tsoronsa nake ji ba, aikin da yake yi mini yana da yawa, kasada duk girmanta yana ɗauka. Akwai lokacin da tilas na yakice shi ai".
Al'amin bai shiga da kayan gida ba, sai cefane da yayi na abincin dare.
Ya tarar ta yi dambu tayi wa dambun miyar jajjage, da salad da awara.
"Ke dai Allah ya yi miki iyayi, dambun da ake sakawa mai, ki ke yi wa miya, har da wata munafukar awara".
Jauhar ta ce "Idan munafuka ce, bamu mu raba da ni da boti, shikenan ba canji, kullum sai dai dambu da mai? Ai gara a din ga upgrading"
"Sai dai ya mutu da yunwa kuwa, to ai awarar ce, 'yar kaɗan"
"Wai master ba ka iya abun 'yan gayu ba? Babu naman da zan saka a cikin miyar, sai na haɗa da awara, bai bada ma'ana ba? Ko sai an cika kwanon da awarar passion ce a kai"
Ya taɓr baki ya ce "Eh to, gashi nan dai, zoɓon ma kamar yayi tsami, amma kwantai ne na jiya ne ko?"
"Mmmm, na waccan shekarar ne" ta bashi amsa tana cigaba da aikin gabanta, na shirya stone.
Tsoknarta yake yi, ya matsata tayi tsiwa, ita kuma taƙi.
"Yaushe WAEC ɗin ku za ta fito ne?"
Jiki a sanyaye ta ce "Ta kusa, har ba na son tunawa da ita"
"Saboda ba ki yi abun arziki ba ko?"
"A'a lokacin kana tsare, bana iya karatun"
Ya ɗan rausayar da kai ya ce "Eyya, abun tausayi, Yallaɓai dan Allah ku sake shi, ba shi da laifi, laifina ne, wallahi ba shi da lafiya ma, master dan Allah ka gaya musu ba ka da laifi" yayi maganar cikin sigar kwaikwayon yadda ta yi waccan ranar.
Murmushi ta yi ta ce "Kada Allah ya kawo abun da ba zai wuce ba, a lokacin nan ji nake a duniya kamar nikaɗai aka tsana wallahi. Da aka ce mini an kai ka prison, kawai na saddaƙar ciwon zuciya ya kama ni, kuma wai ka ce kar a kaini na ganka, ai na ji haushi, a duniya ba zan manta da su yaya walid ba, duk da suna taimakawa wurin ƙara ingizaka a shaye-shaye, amma sun tsaya tare da ni a lokacin da kow yake ganin idan ya taimaka mini zai kwana a ciki"
Ya ce "Allah sarki 'yar madara, ba na son in ga kina kukan nan ne, ko kina yi wa 'yan sanda magana, suna wani yanƙwana mini ke, raina ɓaci yake yi shiyasa na ce kar a sake kawo ki".
Ta ce "Gashi ya wuce, duk da lokacin gani nake kamar ba zai wuce ɗin ba"
Ta tashi ta shiga ɗaki, ta dawo ta tarar da robar alawar madarar da take sayarwa, a gefensa bakinsa kuma yana ta tauna, ta ɗaga robar ta ce "Alawata ka ke sha ko?"
"Eh, ta guda uku na sha sittin, a rage mini naira goma hamsin kenan"
Sororo take kallonsa, "To ai ba a jikina ake tatso madarar ba, da zan sayar da ita ashirin ashirin, naira hamsin ce fa duk ɗaya "
Ya waro ido ya ce "Ki ji tsoron Allah, har na sha ta ɗari da hamsin, gaskiya saba'in zan bayar".
Abun da yake so ya gani ɗin ta fara, shagwaɓa tana cewa sai ya biya ta.
"Gaskiya bani da kuɗi yanzu, zo ki shanye abarki" ya fito mata da harshen sa.
Ta harare shi ta ce "Bana so, kuma idan na zo yi maka wanki na tsinci kuɗi, sun zama nawa"
"Eh ai dama kin saba kwashe mini 'yan canjina, da kayan cajina shiyasa ki ke yi mini wanki ba dan Allah ki ke yi ba" ya tashi kamar zai tafi, amma ya riƙeta, yayi kissing ɗin ta, ya ce "To kin ga tare muka shanye, yanzu talatin ma zan baki" ya saka hannu a aljihunsa ya ciro dubu biyu ya ɗora mata a wuyanta ya ce "Gashi nan, uwar son kuɗi"
"Ai talatin ka ce zaka bani, saura dubu ɗaya, dubu uku yakamata ka bani"
Ya ce "Biyoni ɗaki ki karɓa"
Ta ce "A'a na yafe maka sauran, amma kar ka sake"
Sosai wani bond mai ƙarfin gaske ya shiga tsakaninta da shi, har mamakinsa take yi, duk da mai hali baya fasawa, idan miskilancinsa ya motsa, ko kuma ya cake, ba ya sarrafuwa ta daɗi, amma haka take jurewa. Ga babban abun da yake ci mata tuwo a ƙwarya yanzu, wasu lokutan idan ya dawo daga shaye-shayen sa, da ƙaurinsa da komai yake zuwar mata, gashi ba abu ne mai sauƙi ba, ta nuna masa hakan ba, dole sai ta cikin hikima da dabara.
Haka zata zauna, komai daren da zai yi sai ta jira dawowarsa, ta saka shi yayi wanka, ya canza kaya.
Yau bayan ya bar ɗakinta, bayan ta idar da salla ta je ta same shi, a zaune a kan katifa.
Ta ɗauki kwalin sigarin gabansa, ta ciro guda uku ta bashi ta ce "Wannan ta isa, kar a sha sama da haka dan Allah"
"Bani in je ƙofar gida in sha"
Ta ce "A'a ai shan nake so ka rage sosai da sosai, wannan ta isa"
Ya juya mata baya ya shanye, tana zaune tana jiransa, ta bubbuɗe window, saboda hayaƙin ya fita.
Jira yake ta fita ya kuma kunna wata, amma ta cire masa shirt ɗin jikinsa, ta ce ya kwanta, ya kwanta yana jiran ta fita, amma ta kwanta a jikinsa, a hankali ta din ga karanto azkar ɗin safiya.
Babbar salla na ta ƙaratowa, jauhar hada-hadar neman kuɗi, ta cigaba da kankama, Al'amin bai taɓa saka ido a kan abun da take samu ba, dan yanzu iya ƙoƙarin sa yake yi, ya yi cefanensa, duk da kuɗin da take ɗan samu, in dai ya ji kuɗi a jikinsa, a kaso ɗari tamanin, ita zai kashewa, bai fi ya ƙarar da kaso ashirin ba, goma ya rabar goma ya yi shaye-shaye.
Idan ta fuskanci da kuɗi a hannunsa, ta din ga lallaɓa shi kenan, ayi wani abu mai muhimmanci, idan ba haka ba, ba zai sai abubuwan da suka fi buƙata ba.
Kuma babbar hanyar samun kuɗinsa, wurin Indabo, ya din ga tatsarsa kamar mai, duk da yana samun hanyoyin samun kuɗi yanzu, tun da kakar siyasa ce.
Ana jibi salla, ya ba wa jauhar kuɗi, wai tayi kitson salla ita ma, ta je ayi mata zane a hannunta.
Ta dawo ta tarar da kaya a kan gadonta, ta zazzage taga kaya na alfarma duk an ɗinka su, har da takalmi da turare.
Mamaki ya cikata, yana dawowa ta fito falo ta ce "Master kayan waye a kan gadona?"
"Na kishiyarki ne"
"Wace kishiyata?"
"Ban sani ba, ko ina da wata matar ne bayan ke"
Gaba ɗaya ta rikice ta ce "Master wai nawa ne Gaba ɗaya?"
Ya ce "Naki ne babyn roba"
Har ƙasa jauhar ta durƙusa tana yi masa godiya, ta rasa ma wace kalar godiya za ta yi masa, har da matse ƙwalla.
"Ni ba irin wannan godiyar nake so ba, a sheƙa mini girki, a yi wa fankata caji, in sha iska sosai" sunkuyar da kai ta yi, cikin matsananciyar jin kunya.
"Allah ya ƙarawa fankata gudu, tana ba da iska sassanya, ƙarfin gudunta, bai sanya tana bada iska mai cutarwa ba"
"Amm bari na je na yi jajjage" ta juya ta nufi ɗaki.
"Dama a ɗaki a jajjagen" ko waiwayowa ba ta yi ba, ta shige.
Ranar idin babbar salla ma, tare suka tafi sallar idi.
Ta sha kwalliya, tayi kyau sosai da sosai, a abun da bai fi wata guda ba, ta yi ƙiba fatarta ta ƙara fresh.
Ta sha ɗaurin ɗan kwali, hannunta yayi kyau da zanen lalle ja da baƙi. Su liti suka din ga kiransa a waya, suna jiransa, yaƙi fita, sai da suka zo har gida sannan suka fita da shi, bayan sun kwashi wainar masa da sinasir da miyar agushi.
Bayan la'asar sosai, ya dawo gida da nama kaya guda, har da karfatar sa, ga kayan ciki da uban nama.
Kamar tayi kuka ta ce "Master, aiki daf da magariba ya zan yi?"
"Ke da aiki ba ya yi miki wahala, ɗan wannan aikin zaki yi raki?".
"To aikuwa sai ka tayani, kuma ba ka sayo itace ba"
Ya kalleta ya ce "Ba a yi a gas, an hanaki shiga hayaƙi".
"Gas ɗin dubu nawa za a zuba? Dole sai a itace"
Ya kalli naman, ya ce "Ki shiga ciki, bari na aika nura ya sayo itacen, su walid suna waje, sai su shigo mu yayyanka"
Ƙarshe dai hayaƙin da ba ya so, sai da ta shiga, har sha biyun dare suna aiki ita da shi.
Duk da haka aikin bai ƙare ba, sai washegari, ta ce masa tana son zuwa gida, ya ce sai ta gama yi masa kwalliyar salla kan ta fita.
Ya samu dambun nama da cin-cin, ya din ga tumurmusa, jauhar ta ce "Ni ban gane wannan lamarin ba, gaskiya rabawa za ayi. Kana ta ci idan cikinka ya ɓaci babu ruwana".
"Ke ki ke da ruwa kuwa".
Sai huɗu ga salla, sannan ya bari ta je gida, ya kaita da kansa.
Aka yi sa'a Hafsa ma ta je gidan, tun da ta jauhar ta je, suke kallonta da kayan jikinta.
Sai da mama ta magantu ta ce "Jauhar wannan leshin fa?"
"Mama kayan salla ne"
"Kin san kuɗin leshin nan kuwa?"
Ta girgiza kai ta ce "A'a shi ne ya kawo mini"
Ta kalleta ta ce "Wai sana'ar me yake yi haka ne?"
Tayi murmushi ta ce "Yana sana'oin sa, kuma kin san yana tare da 'yan siyasa".
Hafsa ta din ga kallon jauhar, yadda take komai nata cikin walwala, kamar ba ta da wata damuwa, duk da tana auren ɗan daba.
Bayan jauhar ta ba su nama, dambun nma da cincin, aka din ga gaya wa jauhar, ai mijin hafsa rago ya kawo.
Ta ce "Masha Allah, Allah ya saka da alkhairi" Duk yadda Hafsa ta so mazewa, sai da yanayin ta ya nuna akwai damuwa.
Sai yamma Al'amin ya dawo, ya ce ta fito su tafi, babu yadda ba ta yi da shi ba, amma ya ce ba zai shiga ba.
Gidansu ma da ya kaita, a waje ya tsaya, a gurguje jauhar ta shiga ta gaisa da Rahila, ta bata naman sallar sai dai ita ma, kayan jauhar kawai take kallo.
Ana gama bikin salla, aka shiga hada-hadar zaɓe.
Hankalin jauhar ya kasa kwanciya, saboda yawan shige da ficen da yake yi yawa.
Yau ake zaɓen sanatoci, dan haka tun kan ta tashi daga bacci ya fice.
Har yamma shiru bai dawo ba, kuma wayarsa ba ta shiga.
Gaba ɗaya jikinta a sanyaye yake, jikinta ya din ga bata akwai matsala, har bayan magariba bai dawo ba.
Jin ana knocking ɗin gate, gabanta ya faɗi, ta saka hijjabi ta fito, ta ga Nura guduma a tsaye ta ce "Yaya wannan karon me kuma yayi?"
Ya ce "Ki sako hijjabinki mu tafi"
"Mu tafi ina?"
"Asibiti!"
"Innalillahi wa Innalillahi raji'un!"
Ayshercool
08081012143.
40
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa
Arewabooks ayshercool7724
Muryarta na rawa ta ce "Meyafaru? Wani abun ne ya same shi, ko ya yi wa wani?"
Ya ce "Ni ma ban sani ba, oga walid ne ya ce "In zo mu tafi tare "
Jikinta a sanyaye, ta kulle gidan, ta bi Nura guduma suka tafi, suna tafe tana ta addu'a a ranta.
Wani private clinic suka je, emergency suka nufa, ana ta kai komo da matasa, da aka ji wa raunuka daga wurare daban-daban na harkar zaɓe, kasancewar an yi tarzoma sosai da sosai a wasu wuraren, kuma nan asibitin ne mafi kusa.
Da ƙyar take iya ɗaga ƙafarta, wani irin yammmm haka jikinta yake yi mata, saboda tsoro da tashin hankali.
A ƙofar wani ɗaki, ta tarar da Walid hankalinsa a tashe, yana kaiwa yana komowa.
"Yaya walid, meyasame shi? Ko mutuwa yayi?"
Walid ya ce "Ki nutsu ba mutuwa yayi ba, yana ta kiran sunanki ne kafin mu zo nan".
"To meya same shi, yana ina?"
Ganin likita ya fito daga ɗakin da yake facing ɗin su, ya sanya ta saka kai ta shiga ita ma.
Gigicewa ta yi, ganin Wuƙa a kwiɓin Al'amin a tsaye tsororo, jini baya zuba, amma tana jikinsa, ga gefen kansa, an naɗe shi da bandeji. An saka masa oxygen, gefe ga oxymetre na reading vitals ɗin sa.
Cikin kuka ta ce" Innalillahi wa Innalillahi raji'un, meya same shi haka? Waye yayi masa haka, Master dan Allah ka tashi, kar ku ce mini mutuwa yayi" tayi maganar tana rirriƙe hannunsa cikin tsananin tashin hankali.
Kukan jauhar ya janyo hankalin likitoci, da m'aikatan jinya, suka ce meyasa aka bari ta shiga?
Da ƙyar aka fito da jauhar ana rarrashinta, aka tabattar mata da yana da rai, tiyata za a shiga da shi a cire masa wuƙar, sai a duba kansa.
Cikin tashin hankali ta ce "Dan Allah likita zai rayu?"
"In sha Allah, da kun biya kuɗin za a shiga da shi"
Ta kalli Walid ta ce "Yaya Walid, nawa ne kuɗin?"
Walid ya ce "Kuɗin da yawa, P.A ɗin Indabo muke kira, su biya kuɗin, hannunmu kuɗin ba za su kai ba ayi masa aikin"
"Ka gani ko? Sun ma ƙi ɗaga wayar, su suna can hankalinsu a kwance, suna jiran sakamakon zaɓe, ni kuma an kassara shi, wannan tashinsa ai sai Allah"
Liti ya ce "Ki yi haƙuri, in sha Allah zai tashi"
"Nawa ne kuɗin?"
"Da ɗan yawa, ki bari kawai"
Ta girgiza kai ta ce "Ni ku gaya mini dan Allah, a nema tun da wuri, wuƙa ce fa a cikinsa" tayi maganar tana wata irin ajiyar zuciya mai ban tsoro.
Suka din ga rarrashinta, amma taƙi saurarsu, Liti ya ce "Bari na yi gaggawa na je na samu wannan banzan mutumin P.A, ko dai a san yadda za ayi a biya, wallahi ko mu jiƙa musu aiki"
Jauhar kamar za ta yi hauka, ƙarfin Addu'a ne kawai ya saka mata nutsuwa, ta din ga kaiwa tana komowa, gashi an ce ba zata sake shiga ta ganshi ba.
Jauhar ba ta san yadda aka yi ba, liti da Nura guduma suka dawo da kuɗi, suka biya.
Ake ce ana buƙatar jini, dan da yiwuwar ana