Karfe A Wuta

Chapter 77 of 167

an ajiye duk abun da ki ke buƙata, sai dai ko haraba ba zaki fita ba. Zan ajiye miki waya duk abun da ake ciki, ki kirani ko idan kina buƙatar wani abu, wayar lambata kawai zaki iya kira".

"Wai dan Allah nikaɗai zaka bari a gidan nan, ni tsoro nake ji wallahi"

"Ki yi haƙuri mana, ba zan daɗe ba, na ɗan lokaci ne, zaki yi missing ɗi na ko?" Yayi maganar yana kissing ɗin goshinta. Kuka take yi sosai, ya rungumeta yana rarrashin ta.

***
Yau ma kaca-kaca Walid ya yi da su Viper, Liti yana supporting ɗin Viper a kan iya wuya, kawai su afka su ɗauki fansa.

Duk yadda walid ya so fahimtar da su, suka ƙi fahimta.

Nabila ta fara gane kan hanyar zuwa gidan su Viper, kanta baya kullewa kamar da.

Babu tsammani ta yi karo da Walid, ta ja ta tsaya, ta zata zai yi mata masifa, ta ce "Ina wuni?"

"Lafiya ƙalau"

"Amm yana ina?"

Ya nuna mata dutsen da yake can gaba, ya ce "Yana can, amma ki daina wahalar da kanki, taurin Al'amin yayi yawa, an ɗaukko masa wuƙarsa, zai je ya yi gaba da gaba da madaki yau, ki ƙyale shi kawai"

Ta girgiza kai ta ce "A'a, zan jarraba sa'ata" tayi gaba ta nufi in da dutsen yake, ba ta ƙarasa ba ta hango shi, a zaune a gefen bishiya, cikin inuwa yana ɗan kaɗa ƙafa, ya na shan sigari.

Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi ta ce "Barka da rana" bai amsa ba, ta saka hannunta, ta zare sauran karan tabar hannunsa ta ce "Ayi mini uzuri, ba na son hayaƙi, mara zuciya na sake dawowa. Dan Allah kar ka shaƙe ni, magana zamu yi ta fahimtar juna"

Ya ɗaga kai ya kalleta, ya yinƙura ya miƙe, ita ma ta tashi ta tsaya a gaban sa, ka saurare ni ko sau ɗaya ne, zafin zuciya da gaggawa shi ya sanya ka rasa da yawan mutane masu muhimmanci a rayuwarka".

Sweazland ya saka mata a wuyanta, ya ce "Gargaɗi na ƙarshe, ki rabu da ni, ki fita daga rayuwata".

Ta kalli yadda wuƙar ke ƙyalli a saitin wuyanta ta ce "Sai na ji ƙarshen labarinka, na ji wa ka kashe? Kuma ina jauhar da abun da yake cikinta?"

Ya kalleta ita ma cikin ƙwarin gwiwa ta cigaba da kallonsa, duk da ƙasan zuciyarta a tsorace take.

"Ki daina kallona a haka, meyasa ki ke son ki zama raunina ne?" yayi maganar muryarsa na rawa.

Ayshercool
08081012143

53
🔞₦500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank sai shaidar biya ta 08081012143
Wanda za su jira document 1K ne.

90009343
'Yan Nijar ku turo katin airtel na 300fcfa

Arewabooks ayshercool7724


"Meyasa zan zama rauninka ne? Wallahi ba cutar da kai zan yi ba, ba na nufin yin hakan. Idan niyyata kenan a baya yanzu na canza tunani, dan Allah ka fahimce ni".

Ya sauke numfashi ya ce "Me ki ke buƙata?"

Ta ce "To dan girman Allah mu zauna, sai mu yi magana, ba dan ni ba"

Ya koma ya nemi wuri ya zauna, ta yi ajiyar zuciya, tare da ƙara jinjinawa Jauhar.

Ita ma ta zauna, ya ce "Ina jinki"

"Kamar yadda na gaya maka da farko, na yi nadamar abun da nayi, wallahi ba ni da niyyar cutar da kai ko kaɗan.
Dan Allah ka yi haƙuri, a shirye nake na taimaka maka, na ƙwato maka hakkinka, da na matarka kai har ma da na yaronka Nura, ko hakan zai sanya na baya su kuɓuta daga irin abun da ya faru da ku, amma hakan ba zai yiwu ba, sai ka ƙarasa mini labarin abun da ya faru"

"Bana buƙatar taimakonki, zan yi abun da nake ganin ya dace"

Ta girgiza kai ta ce "Bari, ɗan hakin da ka raina, shi ka iya tsole maka ido, ni ko ba dan kowa ba, dan 'yar uwa jauhar, wallahi labarinta kawai da na ji ta tsaye mini a rai, ina sonta saboda girman Allah, rayuwarta abun tausayi ce kuma abar koyi, har cikin zuciyata nake jin raɗaɗin abun da ya faru, ban rayu da ita ba, amma halayenta sun yi mini, sun burgeni kuma duk in da na zauna, zan buga misali da su. Dan Allah ka yarda da ni, ka bani haɗin kai"

Kallon hawayen da take yi yayi, ya ji ina ma shi ne ya samu wannan damar, yake zubar da hawaye ya ji sanyi a ransa. Duk da yadda take ƙular da shi, amma hawayenta ya sanya zuciyarsa motsawa, da jin kamar ya amince mata, ko da cutar da shi za ta yi, tun da ta nuna tausayi da ƙauna ga matarsa, haƙiƙa ta samu wani mutunci a idonsa.

Ta share hawayenta ta ce "Na bibiyi file ɗinka na shari'a, an rubuta kisan kai ake tuhumar ka da shi, wa ka kashe? Garin yaya ka yi kisan kai? An kama ka an sake ka, kuma an dawo ana nemanka".

Ya kaɗa kai ya ce "An bar jaki ana dukan taiki ba, sun fuskanci ƙarfen cikin wuta ne ni, na fi ƙarfin hannu. Shekara ɗaya, biyu, uku, huɗu, biyar, Naja'atu Bunkure" yayi maganar yana kallon yatsunsa.

Cikin zaƙuwa ta ce "Me ta yi maka?
nima da ka ji ina waya, na yi zancenta, wata yarinya aka yi wa fyaɗe ta shiga case ɗin ta karɓa, kuma an yi wa wani dattijo sharri wai shi yayi mata, alhalin ainihin case ɗin wani ɗan babba ne yayi, wallahi abun da ya sanya na ambaceta kenan a maganata, ba wai aiki nake yi musu ba. Ka yi mini magana dan Allah. Bana fatan ka ɗauki fansa ta hanyar da ba ta dace ba, ba zaka taɓa hucewa ba, ka bari rayuwarsu ta tagyayara tukuna.
One of the biggest fear na masu mulki, shi ne rasa ƙwarin gwiwar su daga mutane, yayin da asirinsu ya bankaɗu mutane suka daina yarda da su. Indabo yayi ƙarfin da ka tunkare shi kai tsaye, ba zai yiwu ba.
Kisan mummuƙe yakamata ka yi masa, dan Allah ka gaya mini me Bunkure tayi maka, hakan zai taimaka mini a wurin Shari'a".

Viper ya ce "Ba na buƙatar wata shari'a, ko wani ya ƙwato mini hakkina, shari'a ita ta fara cin zarafina, babu komai a harkar nan ta ku, sai zalunci da son zuciya, taimakon wanda ku ke so, da tozarta wanda ya gaza baku kuɗi duk gaskiyar sa".

Taji daɗin yadda yake yi mata magana, dan bata taɓa zaton yana magana haka ba.

"A'a kar ka ce haka dan Allah, Dan Allah da gaske kisan kai kayi?"

Ya ce kalleta ido cikin ido ya ce "Eh, kisan kai nayi, Naja'atu Bunkure made me confess it"

Ta haɗiye wani abu, ta girgiza kai ta ce "Ba zan taɓa yadda da hakan ba, labarin Viper da na ji, bai taɓa kisan kai ba, wa ka kashe?"

Tashi yayi, ya ɗauki wuƙarsa yayi gaba, kamar mayya ta tashi ta bishi cikin sauri, amma saurinsa ya ninka nata, dan haka ya rigata isa cikin gidan, kafin ta ƙarasa har ya shiga ɗaki ya rufe kansa.

Ta taga ta tsaya tana leƙawa "Dan Allah ka daina bani bayani guntu-guntu ka ƙarasa mini, hakan zai taimaka mini wurin sanin ina zan kama, wa ka kashe dan Allah?"

Ya tsaya ƙyam ya juya mata baya, ya dafa jikin bango, zuciyarsa tamkar ruwa na tafasa a ƙasan gagarumar wuta, haka wani Irin zafi ya din ga taso masa daga ƙirjinsa zuwa ƙwaƙwalwarsa.

Nabila ta din ga bubbuga ƙofar, tana yi masa magiya ya buɗe, amma yaƙi, ta koma ta window, ta ga tuni ya fara ɗurawa kansa allura.

"Dan girman Allah ka bari, lafiyarka da ta ƙwaƙwalwarka, wannan ba mafita ba ce ba, dan Allah kar ka illata kanka".

Liti ya ce "Zo ki fita, koma uban menene ba ke ce sila ba, uban waye ya ce ki zo, yau ya tashi da 'yar walwala kawai kin zo kin kuma tunzura shi".

Cike da tsananin damuwa, da tashin hankali ta baro gidan, tana tunanin to ita menene laifinta, da suke cewa ita ce sila idan ya ganta yake burkicewa.

***
Ramma ta zubawa Abdul ido, ya haɗa akwatin sa tsaf, ya kalleta ya ce "Ƙarfe huɗu jirgina zai tashi, dole na shirya da wuri, akwai in da nake son zuwa kafin na tafi"

Ta turɓune fuska, tayi masa shiru.

Ya zauna kusa da ita, ya ɗago haɓarta yana kallon fuskarta ya ce "Ya dai?"

"Ni dai kar ka tafi dan Allah, tsoro nake ji wallahi, nikaɗai zan zauna a nan dan Allah"

Ya kwantar da murya ya ce "You start missing me?" Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Your excellency, ba iya tsoro ne a idonki ba, missing ɗina zaki yi"

Ta ture hannunsa ta ce "Allah ya kiyaye, ni gaskiya tsoro nake ji"

Abdul ya ce "Tafiyar nan dole ce, sannan ina son na je garinku yau, zan ce wa mamanki kina gaisheta"

Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka mayar da ni mana"

Ya girgiza kai ya ce "Ba yanzu ba"

"Nan gaba zaka mayar da ni?"

"Eh to, sai ƙura ta lafa" tayi shiru tana wasa da yatsunta.

"Ki yi haƙuri, zan dinga kiranki kullum muna magana, idan da wani abun ma sai ki gaya mini, na ajiye miki komai na amfani a kitchen, ai kin iya girki ko?" Ta jinjina masa kai alamar eh.

Ya ce "Yauwwa your excellency" ya tashi ya shiga wanka, yana ta shiri, ya zauna a gefen gado yana shafa mai, ta riƙe shirt ɗin sa tana kuka.

Nan ya lalace a wurin rarrashin ramma, "Wai wannan kukan duk dan kar na tafi ne?"

"Ni ina ruwana da tafiyarka, tsoro nake ji ne"

"Ƙarya ki ke yi rahama, faɗi gaskiya dai"

"Ni ba na ƙarya" tayi maganar tana murguɗa masa baki sannan ta ce "Kuma wallahi ka bi mata Allah ya isa" bai san lokacin da ya ƙyaƙyace da dariya ba, har sai da ya bata haushi.

Har ƙofar falon ta rako shi, tana kallonsa, ya kasa gane kallon me take yi masa har haka, yayi mata sallama, ya sanya mukulli ya kulleta, ya ja akwatinsa.

***
Kan Nabila tamkar zai yi bindiga, ta rasa abun da yake yi mata daɗi, haka ta koma jiki babu daɗi, kanta fal tunani daban daban.

Har ta shirya, zata ci abinci, kawai ta tuna kwana biyu ba ta haɗu da Nasir ba, kuma ba ya shiga sabgarta, gashi tana son sanin a ina ya tsaya a binciken Viper, saboda duk yadda za ayi ba ta son ya gano Viper ba ta gama na ta binciken ba, idan ya so ko kotu za a shiga, ta shiga da ƙwarin gwiwar ta.

Gaba ɗaya mayar da hankali a kan aikinta ya sanya, ba ta shiga sabgar yan gidan, hakan ya rage yawan faɗace-faɗace da suke yi da 'yan gidan.

Ta fito falo, dan ta gaji da zaman ɗaki, abubuwa duk sun dameta, sai ga Nasir yayi sallama a falo, ta amsa sallamar tana kallon sa, amma ya basar da ita ya nemi wuri ya zauna.

Ta ƙarasa ta zauna a kusa da shi ta ce "Sannu da zuwa"

"Yauwwa" ya amsa mata a ciki.

"Wai me na yi maka ne ka ke wani share ni?" Tayi maganar a shagwaɓe.

Rasa me zai ce mata yayi, yai shiru, ya kawar da kansa gefe.

Ta zagaya in da ya kawar da kan ta ce "Me na yi ne?"

"Bakomai". "To ka kula ni mana".

Nasir ya ce "Na gaji, kar ki dame ni dan Allah"

"Sai na gaya wa Abba kana hantarata"

Ya ce "Sai kin dawo" ta rausayar da kai ta ce "To ni dai ka yi haƙuri, dan Allah" ya kalleta ya ce "Ya wuce"

"Yauwwa DSP, to ya ake ciki ya aikin?" Ya gyara zamansa ya ce "Alhamdilillah, mu na ta fama ya naki?"

Ta kwaɓe baki ta ce "Babu daɗi, duk na gaji, da fa ajiye aikin zan yi, aka bani haƙuri" Nan ta bashi labarin abun da barrister Kabir yayi mata.

Nasir ya ce "Ke baki da haƙuri ne, shiyasa wasu lokutan ba kya cin ribar abubuwa, ki daina gaggawa"

"Ai abun ne ya bani mamaki, daga zuwana wurinta, har an kira barrister Kabir an gaya masa, baka ga abun da ya yi mini ba, da cewa na yi sai na gaya wa Abba ma".

Nasir ya ce "No, ba za ayi haka ba, duk abun alkhairin da yake yi miki, sai a kan laifi ɗaya ki yi fushi"

"To meyasa zai yi mini tijara a kan wata Naja".

Ya ce "Hakan yana alamta miki cewa, kin ɗaukko gagarumin abin da sai kin yi kyakywan shiri na gaske".

Tayi ajiyar zuciya ta ce "Haka ne, ya ake ciki da naka aikin, yaya batun case ɗin Viper, akwai cigaba kuwa?"

"Wallahi ba wani cigaban kirki, ina da ta fafutuka, gashi sai hura mini wuta ake yi"

"Kai abun babu daɗi, but you can do it, na yarda da kai ai".

Mama ce ta fito fuska a haɗe ta ce "Nasir menene haka?"

Ya ce "Mama a ina?"

"Ban sani ba, uban me ka ke zaune a nan ka ke yi? Ka dawo gida tun ɗazu, amma ka gagara shiga inda nake?"

Nasir ya ce "Wallahi nayi tunanin bacci ki ke yi, shiyasa na yada zango a nan muke magana da Arfa, yi haƙuri"

Nabila ko a jikinta, ta sake gyara zamanta ta kwanta sosai a kan kujerar tana danna waya.

Mama tayi mata wani mugun kallo, ko a jikinta, sai ma wani irin murmushi da tayi.

Messages aka din ga turowa Viper, da private numbrn nan, da ake kiransa da ita.

"Muddin ka cigaba da biyewa yarinyar nan, asirinka zai tonu, kuma zata iya rasa rayuwarta a dalilinka, ba ka da sa'a wasu lokutan, kar ka bari ta zama raunin da maƙiyanka za su yi amfani da ita, wurin cimmaka har maɓoyarka" Ya din ga jujjuya wayar, yana sake tunanin waye wannan, kowaye ya sanshi, ya kuma san in da yake, kuma yana ankare da duk abun da yake yi, amma meyasa yaƙi bayyana kansa?.

Kiran Nabila ne ya shigo wayarsa,
tana zaune hannunta riƙe da waya a kunnenta tana kiran lambarsa, babu tsammani ta ji ya ɗaga.

Ta kalli agogon ɗakinta, ƙarfe goma daidai na dare.

"Barka da dare, duk da ba amsawa zaka yi wa ba. Amma ina fatan kana lafiya?
Na kasa jurewa ba zan ɓoye maka ba, ban ji daɗin yadda na baro ka ba, muna cikin magana ka tashi ka tafi, kuma ka je ka na yi wa kanka allura, gaba ɗaya ban ji daɗi ba, dan girman Allah ka rufa mini asiri kar ka yi wa kanka illa, ka bari mu yi nasara mu kamo bakin zaren. Na san maybe ka raina gogewa ta, kuma kamar ba zan iya ƙwato maka hakkinka ba, amma na san Allah yana tare da mu, dan Allah ka daina shan abun da zai yi maka illa, ba na jin daɗi, na san yayata ma 'yar madara ba zata ji daɗin hakan ba, dan gaskiya sai ta matsa mini na shigo, daga ni sai a rufe. Saboda son da nake yi mata make son mu kasance tare, idan na shiga gidanta, kaga gani ga ta, in ƙara koyon halayenta, in ƙara sonta, amma gaskiya ayi mana adalci, saboda kishi ne da ni sosai da sosai fa, kuma alamu sun nuna mini kana sonta da yawa"
Kamar mai sauraren karatu, haka ya nutsu yana jin ta, ɗan mama da yake kusa da shi, har kuma leƙa idonsa yake yi, ya ga reaction ɗin da zai yi, tare da jinjina rawar kan Nabila, a gaban Viper ko ƙwaƙwaran motsi ba ta iya yi, amma ta sameshi a waya, sai karairaya take yi tana shagwaɓa.

Ta sauke numfashi ta ce "Bari na ƙyaleka, amma yakamata na san ƙarshen labarin nan, saboda na san yanayin shirin da zan yi, kuma kar sai na gama zaƙewa 'yar madara duk kirkinta ta ce ba zan shigo mata gida ba, dan ni gaskiya idan ba gidanta ba sai rijiya. Sai da safe take care" tayi maganar tana ajiye wayar, cikinta na kaɗawa saboda ita kanta ta san ba ƙaramar kasada take yi ba, abun da take yi. Amma hanyar da matarsa ta bi ta iya samun kansa da farko, dole ita ma ta bi, domin cimma nasara, saboda gaba ɗayansa hukuma ne, sai da rarrashi.

***
Sanye yake da face mask, yana tuƙi a hankali, saboda yadda hanyar ta ƙara lalacewa, a ƙofar gidan su ramma yayi parking, ya fito ya tsaya a waje yayi sallama, amma shiru, ya shiga cikin gidan sai dai tsakar gidan babu kowa, ƙofofin ɗakin duk a buɗe.

Ya ɗan jira ko za a shigo, ko fita tayi, amma shiru, ba ta dawo ba.

Ya fita ya tambayi maƙwabta, suka sanar masa kwanaki huɗu kenan, su ma ba su san in da ta tafi ba, ba ta yi wa kowa sallama ba.

Yanayin gidan ya tabattar masa da ba fitar nutsuwa tayi ba, ya lissafa shi yanzu kwanaki uku kenan, da mahaifinsa ya kira shi yai masa magana a kan batun ramma balle ya ce ko mahaifinsa ne.

Yayi shiru yana tunanin to garin yaya haka, ya za ayi ta fita ta bar gida a buɗe haka babu kowa, tsawon kwanaki huɗu, ba ta yi wa kowa sallama ba, lallai akwai wani abu a ƙasa, yanzu me zai cewa ramma? Ya tambayi kansa.

Lallai akwai wani abu a ƙasa, gashi lokaci na nema ya ƙure masa, ƙarfe huɗu zai tafi.

Saif ya kira a waya, ya sanar masa halin da ake ciki, saif ya ce "Kuma baka tunanin ko guduwa tayi, ko kuma daddy ne yayi mata wani abun?"

Abdul ya ce "Bana tunanin haka, shekaranjiya yayi mini zancenta, da shi ya saka aka ɗauke ta zai gaya mini, na rasa wani lissafin ma yakamata na yi"

Saifu ya ce "Ka tafi kawai, zan tsaya na sake bincikawa, in Allah ya yadda ba wani abu".

Ya ce "To shikenan, ina saurarenka dan Allah" ya ajiye wayar yana cigaba

Download complete TXT · Novel page