Karfe A Wuta
Chapter 78 of 167
da tunanin lamarin.
***
Abdul yana sauka a Abuja, sai da ya kira Ramma, ya ce mata ya sauka, sai dai ba ta amsa masa ba sai cewa tayi "Yaya ka baro mini mama? Tana nan lafiya? Ta tambaye ka yaya nake?"
"Ni ba zaki tambayi ya na sauka ba, sai mama kawai?"
"Dan Allah ka gaya mini, ko na ji daɗi"
Abdul ya ce "Zan gaya miki da daddare idan na huta" ya katse wayar yana fargabar ranar da ramma ta san halin da ake ciki, bai san ya zai yi ba. Ya san duk laifin shi zata ɗorawa.
***
Katafaren falo ne, ya sha ado da kayan alatu na zamani, manyan mutane ne su uku, zaune a falon wanda kaf ɗin su sanannun fuskoki ne da su a ƙasa.
Kayan shaye-shaye ne a gaban su, suna sha suna hira, gefe ga kayan marmari.
"Distinguish ma'aruf Indabo, ya ake ciki ne gaba ɗaya baka walwala?"
"Komai ma ya dame ni ne, Abdul sai so yake yi sai ya watsa mini lissafi, da ƙyar na yaƙo shi, ya tafi Abuja, zaman taron nan, nima gobe in Allah ya kaimu zan tafi birnin tarayyar"
"Ya salam, wai meyasa Abdul yake haka ne? Ya san wahalar da muka yi kuwa kafin mu zo nan, shi me yake damunsa ne?"
Indabo ya kora ruwan lemon da yake cikin kofin hannunsa, ya ce "Oho masa, gaba ɗaya na kasa gane kansa, ina tsoron Allah ina tsoron ya aikata wani abun da zai yi dalilin takarar nan, amma ina nan na kafa na tsre ina monitoring activities ɗin sa".
"Ohh Allah ya kyauta, ya batun wannan yaron ne da ake nema?"
Indabo ya girgiza kai ya ce "Hmm honorable kenan, wallahi kullum da shi nake kwana nake tashi, kamar wani iblishi, ya gagara kamuwa, na rasa uban da yake tsaya masa, sai dai na samo wata yarinya da nake son ayi masa tarko da ita, to ita kanta yarinyar ba ta da cikakken saiti, wata barrister ce, 'yar wani tsohon soja, idan na matsa zata iya tona mana asiri, na saka ana yi mini monitoring ɗin ta, ta hanyar ƙawarta. Saboda wani furuci da tayi. Duk dai na ga hanyoyin ba sa yi mini sauri, na san dole yaron nan bakam yayi mini, at any cost sai na canza dabara, wadda za ta ɓulle mini da wuri, na kashe Aminu na huta"
Haka suka cigaba da jimantawa, tare da tattaunawa da neman mafita, suna yi suna shaye-shaye.
Ramma tana duƙunƙune a cikin bargo, karnukan estate ɗin, da na gidan sai haushi suke yi.
Video call suke yi da Abdul, ta ce "Ba ka ce mini komai a kan mama ba"
"Mama tana lafiya, ta ce a gaishe ki"
Ta ce "Hmm, to ya take, tana cikin damuwa ko? Tayi kuka?"
Ya ce "A'a, na bata tabbacin kina nan lafiya, har hotonki na nuna mata"
Ramma ta ce "A'a hankalinta ba zai taɓa kwanciya ba, ka manta rashin ɗa'ar da ka yi mata, ranar da ka je ka tabattar mata da kai ka keta mini haddi, kuma ka tafi da ni, ai a yanzu idan akwai wanda ta tsana bai wuce ka ba, kodayeke akwai wanda suka yi mata wasu laifuffukan"
Yayi shiru jiki a sanyaye ya ce "Laifin da suka yi mata irin nawa ne? Ai na nemi afuwarta"
"Ta ina ka nemi afuwarta? Hmm ta ce ta yafe maka ne? Kai baka ganin girman laifin da ka aikata fa saboda mu talakawa ne kana da kuɗi.
Mama ta sha wahala sosai, gashi duk mun ɗaiɗaice, kaga ƙanina sani daka je?"
Ya girgiza mata kai ya ce "Ina ga yana makaranta"
"Shikenan, sai da safe, bari na rintse idona ko zan yi bacci, haushin karnukan nan ya isheni"
Ya ce "Ni kuma sanyi ne nan ya dame ni, da muna tare da kin bani ɗumin jikinki"
Cikin tsiwa ta ce "Saboda gani heater ko?"
Ya ce "No, jikinki akwai ɗumi sosai, da duk ba zan ji wannan sanyin ba"
"Sai da safe"
"Dan Allah ki tsaya ban gama ganinki ba"
ta ce "Sai kuma ka yi ai"
"Miƙo bakinki na yi miki kiss"
"Ba na so" tayi maganar bacci yana kwasarta, tana lumshe ido.
Ya ce "Rahama"
"Na'am" ta amsa tana buɗe ido da kyar. Sai kuma yayi shiru yana cigaba da kallon fuskarta, har bacci ya kwasheta, yana kallonta, tausayinta ya din ga ratsa zuciyarsa.
***
Yau weekends, Nabila tana gida, tana kai komonta, ta bayar da wankinta ayi mata, ta fito harabar gidan tana zagawa, Nasir ya fito da shirin fita.
"DSP sai ina? Ko zance za a tafi rana tsaka"
"Wurinki zan zo zancen" tayi dariya ta ƙarasa gabansa ta ce "Ina zuwa yanzu?, La'asar ta kusa?"
Ya kalli agogon hannunsa ya ce "A kan Viper ne"
Cikinta yayi ƙuuu, amma ta maze ta ce "Ya ake ciki?"
Ya ce "Eh to, na canza dabara ne, a yanayin neman nasa, mun riga duk mun yi connecting da mutanen unguwar su, an ce yana zuwa gidansa da ya zauna, to kwana biyu bai je ba. Abokin faɗansa da na kama kwanaki madaki, an ce ya dawo yana cikin gari, akwai ƙishin-ƙishin na zai iya zuwa unguwar, neman rigima da shi madakin, duk mun baza komar mu, akwai wurin shayin yaransa, an ce ma wurin nasa ne, zuwana biyu wurin cikin fararen kaya, an kwatanta mini wani yaronsa Walid, na haɗu da shi a wurin, amma ko kaɗan ba sa zancensa a wurin. Da na so na zunguro zancen daba ma, na kama sunansa, cewa suka yi na tashi na fita. Ina kyautata zaton wannan Walid ɗin ya san in da yake, motsinsa zan sakawa ido sosai, ana ta yi mini binciken ina yake da zama, da a unguwar suke zaune, amma tun da Viper ya bar prison, sun daina kwana a unguwar sai idan za su yi aikin rabawa ƙanan dealolinsu wiwi. Ba zan motsa da wuri na kama shi Walid ɗin ba ba, kar shi ma ya zille mini, kuma an tabattar mini da ɗan amanrsa ne, ina dai ta bibiyar su ta hanyar mai unguwa, da wasu daga mutanen unguwa. Wanda nake baki labarin nan ma ɗan mama, ya daina zuwa arear da aka gaya mini kai kayan shaye-shayen na su, abun ne dai duk sai a hankali".
Tayi ajiyar zuciya ta ce "Wani aiki sai mai shi, Allah dai ya ba da sa'a, sannu da ƙoƙari DSP"
"Yauwwa arfan Abba, bari na tafi"
"To yanzu can ɗin zaka tafi?"
"Eh, zan je in sake zaɓar yarana su shiga unguwar su madakin a farin kaya"
Ta ce "Shikenan, a sauka lafiya, Allah ya tsare" ya amsa da Amin, ya nufi motarsa.
Cikin sassarfa, ta nufi ɗakinta, Wayar Viper taƙi shiga, ta din ga kira amma a kashe.
Hankalinta ya ƙara mummunan tashi, har la'asar wayar viper ba ta shiga.
Shiryawa tayi ta saka niƙab, ta lallaɓa ta fice, ba tare da yi wa kowa sallama ba.
Sauri take yi tamkar za ta tashi sama haka take fafaka sauri.
A hanya aka fara kiraye-kirayen sallar la'asar, har ta ƙarasa kiran lambarsa take yi, amma shiru bai ɗaga ba.
Ɗan mama ta tarar a tsakar gida, shikaɗai, yana ta shafawa wuƙaƙe wani abu, da ba ta san ko mene ne b. Ya miƙe yana kallonta ya ce "Dan Allah suna ina?"
"Su wa?"
"Su viper, da sauran".
Ɗan mama ya ce "Oga Viper ya fita, ya tafi cikin gari wurin madaki, da shi da Oga liti, Oga walid sun yi faɗa ya fita"
Jikinta na rawa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, shi Walid ɗin ina ya tafi? Wai ma meyasa Vipern ne yake da taurin kan tsiya, akwai hatsari a hakan fa "
"Ke, Oga Vipern ki ke faɗar baƙar magana a kan shi?"
Ta juya zata fita ya ce "Ina zaki?"
"Bin sa zan yi"
Ya waro ido ya ce "Ina?"
Ta tsaya ta kalleshi ta ce "Dabar madakin, ai na san wurin" zai yi magana, ta fita da sauri sosai.
Shida saura na yamma, ta isa unguwar su madaki, saboda azalzalar da ta din ga yi wa mai adaidaita sahun da ta hau.
Ta cikin niƙabinta, take kallon unguwar, ba zata taɓa manta, yadda aka sakar mata karnuka ba, suka kusa cinyeta.
Ta nufi cikin unguwar, sai dai kamar babu mutane, sai ɗaiɗaikun mutane da suke guje-guje.
Ta tsaya tana neman wand zata tambaya meyake faruwa, amma kusan kowa ta kansa yake yi.
"Kai ku tafi gida, wannan ɗan tijarar ne ya shigo neman masifa, mai zamani ne da yaransa, suke faɗa da yaran madaki" taji muryar wani matashi, yana yi wa wasu yara magana" maimakon ta tsorata sai ta kutsa kai ta cigaba da tafiya tana fatan Ubangiji Allah ya sa kar wani abu ya same shi, Allah ya sa ta ganshi.
Tana saka kai wani layi, ta ga an yanki wani a cinyarsa, jini ya yi tsartuwa, ta gigice cikin tashin hankali ta fara ihu, ji tayi an ja hannunta da ƙarfi, an shiga da ita wani layi daban.
Ayshercool
0808012143
54
Cikin matsanancin tsoro, ta rintse idanunta, zuciyarta na bugawa da sauri sosai.
Da kyar ta iya buɗe ido ta ga wanda ya ja ta, kallo ɗaya ta yi wa idanunsa ta cire nata, saboda mugun kallon da yake yi mata.
"Uban me ya kawo ki nan?" Mamaki take yi, yaya aka yi ya ganeta da niƙab.
"Ba magana nake yi miki ba?"
Ta ɗaga kai ta kalleshi ta ce "Haka muka yi da kai? Meyasa zaka fito, kana da tabbacin idan suka kamaka a wannan karon zasu barka da rai ne, ba fa za su yadda su sake wannan kuskuren ba, dan Allah kar ka ɓata mini aiki, dan Allah ka daina fitowa" mayafin da ya rufe fuskarsa da shi, ya sake gyarawa, ya sake damƙar hannunta, ya din ga ratsa hanya da ita, kowa ya gudu gida ya ɓuya.
A haka suka ƙaraso titi ya ɗaga wa wani mai baburin adaidaita sahu hannu, ya yi mata nuni ta shiga, shi ma ya shiga.
Ta kalli yadda duhun magariba yayi, sai a lokacin hankalinta ya kai kan me za ta ce a gida.
Ya ciro wayarsa, ya danna wata lamba, ya saka a kunnensa, a hankali yake magana ba ta iya jin me yake cewa a wayar, ya zirawa mai napep ɗin dubu ɗaya ya kama ƙarfen adaidaita sahun, ya dire ba tare da mai napep ɗin ya tsaya ba.
Cikin sauri ta leƙa, ta ga wani ya tsaya a babur sanye da face mask, Viper ya hau suka yi wani wurin.
Tana jin yadda wayarta take ta ringing, amma taƙi ko ɗaukkota, balle ta ga waye.
Ta gaya wa mai napep in da zai kaita, tuni aka fara kiraye-kirayen sallar isha'ai, motar Abba ta tarar da ta Nasir, alamar duk suna gida, gabanta ya faɗi.
Sannu a hankali ta ƙarasa falon, ta tarar da Abba a tsaye, hannunsa riƙe da waya, take wayarta ta hau vibrating alamar ita yake kira a waya.
Yayi mta wani irin kallo, da sai da hantar cikinta ta kaɗa.
"Daga ina ki ke?"
Tayi tsuru-tsuru da ido, tana kallonsa.
Nasir ya ce "Magana fa ake yi miki"
"Amm, Abba dama wallahi wata shaida nake so na haɗu da ita, wani case ne a hannuna shiyasa na fita".
Abba ya ce "Wa ki ka gaya wa zaki fita?"
Mama ta ce "Yaushe za ta gaya mana, tun da bamu isa ba"
"Wato arfa kullum rashin jinki ƙara gaba yake yi ko? Idan baki yi wasa ba, hatta aikin sai na hana ki zuwa, an ce tun safe ba kya gidan nan, wace irin shaida ce haka?"
Nasir ya ce "A'a har azahar tana nan ina ga da la'asar ta fita"
"Koma menene yanzu yakamata ta shigo gida, ƙarfe takwas da wani abu tun la'asar?"
Ta sunkuyar da kai ta ce "Dan Allah Abba ka yi haƙuri, in sha Allah ba zan sake ba"
"Daga yau, ki ka sake fita babu wanda ya sani, zamu gauraya da ke" ta jinjina masa kai, ta wuce tana yi wa Allah godiya, da bai yi mata faɗa sosai ba.
Addu'a ta din ga yi, Allah ya sa kar Viper ya aikata wani abu da za a kama shi, ko kuma ya yi wa kansa illa.
Gashi ba ta samu sun yi magana a kan abun da ya kaita ba, na shirin da Nasir yake yi na son kama shi ta hanyar Walid ba.
Madaki ne a tsaye yana kallon Al'amin da yake tsaye a gabansa, duk da duhun dare ne, amma manyan fitilun solar sun haske ko ina da ina.
Idon Al'amin kamar ana hura wuta, Madaki yayi dariya ya ce "Mahadi mai dogon zamani, ka ci na wasu gaka kana cin naka. Viper ka ke maciji mai hatsarin gaske, dodon cinnaku masu ƙaryar kaki.
Barka da sake haɗuwa da kai a dai-dai wannan lokaci, bayan dogon lokaci bamu yi ido da ido.
Tabbas labarin Mai zamani ba zai taɓa cika ba, sai an ambaci madaki.
Maza gumbar dutse ya ake ciki ne?"
Yana rufe bakinsa, Al'amin ya soka masa russia a cinyarsa, a take jini ya fara kwarara a jikin madaki. Madaki ya kalli cinyarsa, ya kalli Al'amin.
Al'amin ya kalli madaki ya ce "Na san zaka yi mamakin, yaushe na samu makarin tsafinka, amma na ƙyaleka a raye kana cin karenka babu babbaka.
Yadda daba ta bar mini mugun tabo a zuciyata, ka rubuta ka ajiye, kamar yadda ka ce labarin Viper ba zai cika ba, sai an ambaci sunanka. Ina mai tabbatar maka Viper zai yi maka saran da bai taɓa yi wa wani irinsa ba.
Kamar yadda ka canje ni, ka ke yi wa Indabo aiki, a madadina, ina da saƙon da zan baka ka bashi. Ka gaya masa ya toshe dukkanin ramukan da ke gidansa, ofishin sa da duk wani wuri da yake zuwa, saboda maciji ba ya raina ƙofa komai ƙanƙantarta, kuma ya tsammace ni, ta in da bai taɓa zata ba, kuma lokacin da bai taɓa zato ba.
Al'amin na rufe bakinsa, madaki ya saka masa ƙarfe a damtsensa, a take kokawa ta kaure a tsakanin su, sai dai madaki ya kasa sarrafa ƙafar da Viper ya soka masa wuƙa, rabon da a zubar masa da jini har ya manta, saboda laƙanin taurin da yake amfani da shi, fitar masa da jinin da Al'amin yayi, yana nufin laƙanin ya karye, kuma a kowane lokaci, ana iya yi masa rauni da ƙarfe koma a kashe shi.
Sosai suka din ga yi wa junansu illa da makami, sai dai Madaki ya fara galabaita, dan haka ya fara ƙoƙarin guduwa, dan ba ya son wasu su farga cewar ƙarfe ya fara tasiri a jikinsa.
Amma Viper ya hana shi yin hakan, zuciyarsa ta din ga wata irin tafasa, ya din ga saran madaki, madaki ya saka hannu ya shaƙe Viper, take Viper ya ji abun da ya taɓa ji idan madaki ya shaƙe shi, tamkar an yi masa sarƙa da dutse, ya kasa motsi.
Viper ya ji an saka masa wani abu a gefen wuyansa, a take ya silale ya ya faɗi ƙasa.
Madaki ya ja da baya yana kallon yadd mutumin ya saita shi da bingida, dan bai ga ta in da ya ɓullo ba.
"Zaka iya tafiya" mutumin yayi magana yana nuna masa hanya.
Madaki ya ja jiki da kyar, yana ɗingisa ƙafa ya bar wurin.
Wasu mutane manya manya majiya ƙarfi suka ɓullo wurin
"Yaya kun tarwatsa yaran?"
"Eh sir, amma fa har an sanar da 'yan sanda zancen rikicin sun taho"
"Maza maza ku ɗauke shi ku tafi da shi, ayi masa treatment, ayi sedating ɗin sa, har a gama yi masa komai, kar ku mayar da shi maɓoyarsa yanzu, a bari zuwa da safe, idan yaransa sun fita nemansa sai ku mayar da shi. Su kuma su musa su tabattar sun goge duk wani trace da zai sanya a gane yazo unguwar nan"
"Ok sir"
Suka cicciɓi Al'amin, suka saka shi a mota, suka ɗauki wuƙarsa da wayarsa, suka tafi.
Har wajen goma na dare, Nabila tana kiran wayar Viper, amma ba ya ɗagawa, hankalinta ya fara tashi, ko wani abu ne ya same shi, amma sai ta tuna, kaɗan da aikinsa ya ƙi ɗagawa mussaman ma da tayi masa laifi yau.
Liti kuwa bayan ƙura ta lafa, ya koma gida, sai dai bai tarar da Viper ba, sai Walid.
"Wai Viper bai dawo ba?" Yayi maganar yana kallon Walid.
Walid yayi masa banza.
"Malam magana nake yi maka fa"
"Ban sani ba, da ni kuka fita?"
Liti yayi tsaki ya ce "Bari na san yana hanya shi da ɗan mama"
Walid ya ce "Ina fatan kun kashe madaki, kun wuce kun kashe Indabo"
"Ban sani ba"
Walid ya girgiza kai, ya cigaba da abun da yake yi.
Ɗan mama ya shigo shi ma, jikinsa duk jini da alama yayi ɓarna sosai, ya ce "Oga liti ina Vipern, ina fatan yana lafiya, ni fa tun da muka afkawa su lakwari, ban sake ganinsa ba"
Liti ya tashi tsaye ya ce "Kamar yaya? Ya haɗu da madakin ne?"
"Ai ban sani ba, da muka rabu da ku, wani wurin yayi ai"
"Bari mu jira nan da awa ɗaya mu gani"
Walid ya ce "Hmm"
"To yana nan lafiya, ai ba wani abun ne ya same shi ba"
Walid ya ce "Na yi maka magana ne?"
"To kama yi mana"
Walid ya ce "Wallahi wani abun ya same shi, sai ranka ya ɓaci liti, daga kai har ɗan mama muguwar kasada cw da ganganci abun da ku ka biye masa ku ka yi. Kuma tun da ya kai i yanzu, akwai abun da yake faruwa gara kawai" yayi maganar yana miƙewa tsaye, ya ɗauki wuƙa ya soke a jikinsa, ya fice.
"Ɗan mama, Walid fa gaskiya ya faɗa anya ba wani abun ne ya faru ba?"
"Tashi mu koma, akwai matsala mun yi wauta da muka bar shi ya yi mana wayo, da ƙyar idan bai haɗu da madaki ba" haka suma suka tashi, suka fita.
DSP Nasir