Abban Sojoji Book 3 (Takun Karshe)
Chapter 78 of 104
juna,tunkan su ƙaraso Sehrish ta hango Sgr dake gefen Kanal Yusuf ya lumshe idanuwanshi,kamar mai jin bacci,da alama Jiyan nan baiyi bacci ba,ko bai samu isasshen bacci ba,
Ƙarasawa Cikin palourn su kayi,A nan saman Carpet gefen Jahad suka zauna suma tare da lankwashe ƙafafuwansu,
Ɗagowa Ya Mu'allim yayi tare da binsu da kallo,kafin yace"Akwai saura ko su kenan"?
"na kira Aunty Azmee,Yanzu zata zo itama,"Fawan ne ya bashi amsa,Duk sun ƙagara suji abunda Ya Mu'allim ke son sanar dasu,
Saukowa Azmee tayi daga 3 steps na fitowa daga Corridor ɗin ɗakunansu,bata nufi falon kaitsaye ba,kitchen ta nufa,after few minutes ta fito hannunta ruƙe da faffaɗan tray saman shi glass cups ne,Wanda ta shirya masu abunsha ciki,
Jin takun takalmanta ne Ya jawo hankalinsu,tana ƙarasowa wurin sofas ɗin da suke zaune,Kamar ance ta ɗago karaf Suka haɗa ido da Ya Mu'allim,A gigice Azmee ta saki tray ɗin hannunta Wani irin sauti suka bada ji kake fass fass tatass Glass Cups ɗin suka faffashe,ganin haka yasa kowa Ya shiga tambayarta Lafiya,kasa buɗe baki tayi don tayi magana,gaba ɗaya duk tabi ta firgice ta rasa natsuwarta,Da gudu ta juya zata bar wurin Ya Mu'allim Ya daka mata tsawa"Karki kuskura kice zaki bar wurin nan,idan har kika ƙara ɗaga ƙafarki a wurin nan,Saina sa6a maki,"Cak ta tsaya lokaci guda wata irin Zufa ta shiga wanke mata fuskarta,
Abun ya ɗaure masu kai,har suna haɗa baki wurin tambayarshi A ina yasan Azmee?,
Miƙewa tsaye Ya mu'allim yayi tare da nuna ta da yatsan hannunshi"Wannan itace Silar duk wani hali da kuka shiga acikin gidan nan!"
Saboda tsabar firgitar da su kayi gaba ɗaya suka miƙe suna kallonshi,
"Anya kasan me kake faɗa kuwa?Wannan fa Azmee ce,me aikin gidanmu,kusan Shekara Ashirin tana Yi mana aiki,"kanal Yusuf ne yayi maganar,
"Kodai tayi maka kama da wadda ka sani ne"?acewar Irfan,
A tsanake Ya mu'allim ya soma magana"Niko nasan Azmee farin sani!Ku ne baku santa ba,Wannan matar da kuke Gani,Mushirika ce ƴar qungiyar asiri",
Hankali A matuƙar tashe Suke kallonshi,Duk basu kaiga yarda da maganarshi ba,
Azmee kuwa tuni ta ɗaura hannu asaman kanta,Tunda Ya Mu'allim Ya fallasa cewa ƴar gungiyar asiri ce ita,tasan cewa Alƙadarinta ya karye!A ƙa'idar ƙungiyarsu daga inda wani Yasan sirrinka shikenan ƙarfin sihirinka zai naƙasa............"
"Kinji haushin rayuwarki!Muguwa azzaluma,dama Alƙawarine na ɗaukarwa kaina saina Tona maki asiri,koda kuwa zakiyi silar mutuwata ne,balle kuma ke baki isa ki kawar dani ba,"
Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu,Kowa yasha jinin Jikinshi,
Hankali atashe Mommy tace"Don Allah ka fahimtar damu,"
Cigaba da magana yayi"nasan ba lalle ne wasun ku su gane ni ba,Amma mahaifinku zai iya tuna fuskata,Ni ina ɗaya daga cikin malaman da aka ɗauko don su koyama Junaid karatu lokacin yana yaro,A lokacin Mahaifinku Ya faɗamun cewa duk malamin daya ɗauko don ya koya mashi karatu,tun arana ta farko idan Yazo bai ƙara dawowa,Abun Ya ɗaure mun kai,farkon haɗuwata dashi A masallaci ne,Ta dalilin yabona da mutane keyi ne ya jawo hankalinshi akaina,harya jani gefe yake sanar dani game da ɗanshi da yake son indinga zuwa ina koya mashi karatu,
A ranar dana fara zuwa gidan nan koya ma junaid karatu,A garden muka zauna dashi in ban manta ba,Saman darduma ne muke zaune dashi,Idan inayi mashi karatu sai ya ƙura mun ido yana kallon bakina kamar yana fahimtar abunda nake cewa,Ashe kwata kwata bai ganewa ne,Abun ba ƙaramin ƙona mashi rai yake yi ba,a ƙarshe sai ya fashe mun da kuka yana cewa shi baiso ana zuwa yi mashi karatu tunda ba ganewa yake yi ba,Wahalar dashi muke Yi,naji tausayinshi sosai a wannan lokacin,Na kuma Yi mamakin yarda bai gane karatun al'qur'ani,sanin cewa Ƙaramin yaro yafi ɗaukar karatu a lokacin ƙuruciyarshi,Amma shi ko Bismillah wuyar faɗi take yi mashi,Idan na matsa mashi akan yayi karatu da zarar ya buɗe baki zai amsa karatun da nake biya mashi,kwatsam sai inga ya sanya hannu ya toshe kunnuwanshi,La66anshi na kerma,wani lokacin kuma sai inga yana ruƙe maƙoshinshi,tundaga nan na sanya ayar tambaya akanshi,bayan na koma gida,Yini nayi da tunanin Junaid,Saboda Yaron akwai shiga rai,Ya kwantamin araina sosai,a daren ranar,wuraren ƙarfe 1 na dare aka kira wayata Ana yi mun barazana akan karna kuskura na ƙara zuwa koya ma junaid karatu idan ba haka ba zan rasa raina ne,duk da haka ban daddara ba,A washe garin ranar na kuma dawowa koya mashi karatu hada ruwan Zam Zam na addu'a nazo mashi dashi don yasha,ruwan Addu'ar yana karya sihiri duk mun ƙarfinshi in akayi ma mutun in ba wani iko na Allah ba,Aranar nayi ƙoƙarin na bashi yasha ruwan addu'ar nan amma wani abun mamaki daga nayi yunƙurin kafa mashi ruwan a bakinshi don yasha Sai kawai inji an buge mun hannuna,tun daga nan na ƙara yarda cewa akwai sihirin ajikinshi,Sae na fara tunanin yin bincike akan Wanda ke sarrafa kwakwalwarshi,domin in taimakeshi,Akwai wata rana Da Azmee ta kawoshi da hannunta,A ranar na gane cewa itace ke sarrafa shi,Allah yayi mun baiwar gane mutun mai sihiri da zarar mun hada ido,ta kalle ni na kalleta,Bayan tafiyarta nake tambayarshi Wacece ita,ko mahaifiyarshi ce?Sai ce mun yayi Eh,Mamansu ce,banyarda da maganarshi ba a lokacin saboda sam babu kamanceceniya a tsakaninsu,Hasken yaron ba irin nata bane,ko irin kama ta jini babu atsakaninsu,da na tsare shi da tambaya sai yake cemun mamanshi bata nan,kuma bata sonshi ta tafi tabarshi,Sai tausayinshi ya kamani,Bayan na koma gida na shiga zurfin tunani akanshi,Abunda ya tsayamun araina shine meyasa mahaifiyarshi ta tafi tabarshi?Wacece wannan matar dake sarrafa kwakwalwarshi,Meyasa take son juye mashi tunani don karya gane karatu,Na nace akan son sanin dalilinta na yin hakan,Gashi bansan wa zan tambaya ya bani amsa ba,matasan gidan kuma ba gwanayen son magana bane,Gasu sojoji in nace zan tambayesu ba dole su fahimce ni ba,Zasu yi mun wata mummunar fahimtar ne,akwai wata rana da muka haɗu da mahaifinku a lokacin na kammala Koya mashi karatun ranar,Shi kuma ya dawo daga wurin aiki,Na ƙarasa muka shiga gaisawa dashi har yake ce mun in shigo daga cikin gidan muci abinci atare,Dayake mutun ne shi mai son jama'a,baida girman kai ko kaɗan,Yana da kyakkyawar zuciya,Banyi niyyar shiga cikin gidan cin abinci ba,Amma tunawa da binciken da nakeso nayi saina Yanke shawarar binshi,
Lafiyayyen Abinci Azmee ta shirya mana tare dashi,a lokacin in ban manta ba,Hada waɗannan tagwayen guda biyu,ko gaishe ni basuyi ba lokacin,Dama tunda na kallesu nagane cewa suna da girman kai,wani kallon ƙaskanci suke yi mun,Amma wani abu dana hasko shine,Hasken fatarsu irin na Junaid ne,Sai na fara tunanin kodai cikin Iyayensu akwai jinsin turawa ne?Saboda ƙwayar idon ɗaya daga cikinsu,muna cikin cin abincin Sai naji ɗaya na tambayar Abbansu,na kasa kunne ina sauraronshi,
"Abba,har yanzu Mommy bazata dawo ba"?Sai Abbanku Yace"bana tunanin zata dawo da zama Nigeria,
Sai naji yaja dogon tsoki yana cewa"Gaskiya batayi mana adalci ba,kodan saboda Junaid yakamata ta dawo taci gaba da kula dashi,Ni bana so Azmee taci gaba da rainonshi....."bai kai ƙarshen maganarshi ba sai Abbanku yayi mashi tsawa,nan take yaja bakinshi yayi shiru,bayan mun kammala cin abincin,Na shirya tafiya mahaifinku yayi mun jagora a lokacin ko abun hawan kaina ban mallaka ba,A ƙafafuna nake yawo,ko in hau abun hawa,to a lokacin shima yana da wani uziri a waje,Sae yace mun in shiga motarshi su rage mun hanya,
Muka shiga motar atare,Driver ɗinshi Yaja motar muka fita,A cikin motar ne,na soma ƙoƙarin bugun cikinshi,
"Na lura kamar akwai damuwa akan fuskarka,"sai yayi ƙoƙarin 6oye damuwarshi yace mun bakomai,
Sai na canza maganar nace"Maganar Junaid Alhaji,Yau mahaifiyarshi data kawo mun shi daƙyar ya tsaya,Yana ta kuka sai ya bita,"Nayi mashi zancen junaid ne don na lura ba ƙaramin son Yaron yake yi ba,indai kanason kaga fara'arshi toh kayi mashi maganar Junaid,
Nan yake ce mun ae ba mahaifiyarshi bace,Mommynshi bata a ƙasar tun lokacin da ta haifeshi tabar ƙasar,Wannan matar dana gani mai aikin gidan ce,Itace ta shayar dashi,sun shaƙu sosai,Ya saba da ita baison rabuwa da ita,iya haka ya tsaya mun da bayani,Bai faɗamun dalilin dayasa Mahaifiyarshi tabar ƙasar nan ba,batare data ƙarasa shayar dashi ba,Ni kuma a wannan lokacin na samu abunda nakeso,bayan sun sauke ni a gida,Yinin ranar da tunanin maganganun mahaifinku na kwana,Saboda yarda nasa ma raina junaid har mafarkinshi nake yi,Dana zauna nayi nazari sosai,Sai na hasasho wani abu game da Azmee,tabbas akwai wata mummunar manufa dayasa take zaune a gidan,In ba haka ba meyasa zata Juye mashi kwakwalwarshi?Saboda yaron yana da kaifin basira!he's genius,irin yaron nan ne masu wayon tsiya,Gifted Ne shi,ita kuma Azmee ita ke rainonshi dole zai iya kasancewa A ɗakinta yake kwana,koda yaushe yana manne da ita,duk wani surkulle da zatayi agabanshi take yi,Tanajin tsoron kada Ya tona mata asiri,that's the reason Why Ta toshe mashi kwakwalwarshi Ta yarda bazai Iya gane komai ba.........."
Gaba ɗaya hankalinsu Ya tashi haikam,Musamman Sgr da Mommyn Junaid,Jikinsu har tsuma Yake yi,Su kanal Yusuf kuwa sun shiga ruɗani sosai,Abun yafi ƙarfin tunaninsu,Har yanzu basu samu ƙwaƙƙwarar hujjar da suke son samu ba,Farat ɗaya bazasu fara Accusing ɗinta ba,
Azmee kuwa tuni ido ya raina fata,Jikinta sae kerma yake yi,Ta gaza buɗe baki tayi magana,binsu kawai takeyi da ido,
Cigaba da magana Ya mu'allim yayi"A lokacin sai tafiya ta kamani zuwa ƙasar Egypt,scholarship na samu don ƙaro ilimin addini acan,ba don naso ba haka na kwasa nabar ƙasar nan,cike da tunanin Junaid,Tsorona kada kafin in dawo Nigeria,Azmee tayi silar mutuwarshi,tunda ta fara zautar dashi,
bayan tafiyata ƙasar egypt,duk da bana a nigeria,ina samun Labarin halin da Junaid ke ciki,Duk in mukayi waya da mahaifinku yana sanar dani,Har na samu labarin ciwon Shi daya tashi har akayi mashi aiki a ƙirjinshi,Lokacin nashiga damuwa sosai,Saboda ni nasan cewa Junaid baida ciwon asthma,Lafiyayyen mutunne shi,Wannan ciwon asthma ɗin duk aikin Azmee ne,itace ta sanya mashi ita,duk don saboda kada yayi Lafiya,domin kuwa lafiyarshi zai iya jaza mata matsala,ta ko'ina ta hanashi sakat,ta mayar dashi tamkar soko,Yanayin wasu abubuwan irin na mata bayan shi namiji ne,kuma tundaga kan Iyayenshi da yayyenshi babu wani rago acikinsu balle ace ya ɗauko wani daga cikinsu ne,kuskuren da kukayi shine,Yarda da Azmee ta shayar dashi,Tabbas kun tafka babban kuskure na Yarda da ƴar aiki ta shayar maku da ƙaninku,Sauke ajiyar Zuciya Ya Mu'allim Yayi kafin ya ɗaura da cewa"Bayan wasu shekaru Allah yayi na dawo Nigeria,A lokacin bansan wani hali ahalinku suke ciki ba,Domin kuwa nadaina samun mahaifinku a waya sakamakon Rasa wayata da nayi wadda nake da saving ɗin Layinshi aciki,lokacin dana dawo mahaifinku Ya samu karin girma a wurin aiki,Na chief of army staffs,Hakan yasa gidanku Ya ƙara tsaro sosai kuma mahaifinku yayi wuyar gani,Har zuwa saida nayi amma Sojojin dake gadin gidan suka hanani shiga ciki,saboda banda shaidar da zasu Iya barina na wuce,kusan sau biyar ina zuwa amma bansamu shiga ciki ba,A ƙarshe na haƙura da zuwa gidan,
Ana haka,Na samu koyarwa,A makarantarsu wannan Yarinyar,Yayi maganar yana nuna Sehrish dake atsaye,
Kullum naje koya masu karatu sai inga yarinyar nan tana ta sharar bacci abunta,Sae kace ba karatu tazo ɗauka ba,Abun saiya ɗaure mun kaina har rannan na tanka sai yan ajin suka sanar dani haka take,duk in ana karatu sai tai ta bacci,jin haka yasa naje har seat ɗin da take zaune na tasheta daga bacci ta miƙe tana mutsuttsuka idanuwanta,Kallo guda nayi mata na gane cewar akwai matsala atattare da ita,Nace mata ta ɗago ta kalleni,Taƙi yarda mu haɗa ido,Ni kuma a lokacin inaso in gani idan akwai Jinnu ajikinta,Don naji ajikina cewa ba ita kaɗai bace,Dana tambayeta a wani gida take ne,Sae take sanar dani cewa ita Ƴar family ɗin SALAHUDDEEN HOSSEIN ce,Inajin hakan sai na gane cewa Ƴar uwar Junaid ce ita,tunda sunan mahaifinshi ne,kuma naga kamanninshi a fuskarta,
Tunda naji hakan sai na gane cewa Har lokacin Azmee na acikin Family ɗinku,Kuma ina tunanin itace ta shiga jikin Yarinyar tayi mata sihiri,ban tabbatar da zargina ba,Kawai na yanke shawarar in bata wannan ruwan addu'ar na zam zam,Ta hanyar ƙawarta Amrish gata nan a gefenta,Ita naba ruwan zam zam ɗin acikin robar ruwan donta ba Sehrish tasha,Har nace ta sanar da ita cewa idan bata sha ruwan ba,ƙusumbi zai fito mata abayanta ne,Nace haka ne don ta tsorata tasha ruwan,in ba haka ba nasan daƙyar ne tasha ruwan,To ni bansan tasha ruwan Addu'ar ba,ko bata sha ba......"ya dakata da maganar yana kallon Sehrish,hankali Ya koma kanta,.
Daƙyar ta iya buɗe baki tace"A'a bansha ba,Nazo dashi gida,Amma na neme shi na rasa,A lokacin nayi tunanin ko Junaid ne Ya ɗaukeshi saboda shikaɗai ne ke zuwa ɗakina,daga baya ban ƙara tada maganar ba,
Tunda ta soma magana Ayaan da Jahan ke kallon Juna,saboda sun gane cewa Wannan ruwan da suka sha ne,Har suka samu warakar Cutar dake damunsu,Na neman juna da suke yi,
Da sauri Ayaan yace"Ni na ɗauki Robar ruwan acikin fridge,bansan waya kaita ba,Amma nida Jahan ne muka sha ruwan.......'anan Ayaan ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar dasu,Bai 6oye masu komai ba game da homo sex ɗin da suke yi shi da Jahan,Saboda ƙwarin guiwar da suka samu ayanzu,
"Yanzu haka robar ruwan,Tana a hannun Jahan,Shiya 6oyeta saboda muyi bincike akan wanda ya kawota cikin gidanmu,Ashe Sehrish ce ta shigo da ita,"
Kallon Jahan Sgr yayi"inason ganin robar ruwan da kuka sha,"da sauri Jahan Ya nufi part ɗinsu,
Tashin hankalin da ba'a sama shi date,Gaba Ɗaya idanuwan ko wannansu na akan Azmee,Duk tasha Jinin jikinta,After some minutes Saiga Jahan ya dawo hannunshi ruƙe da bottle water ɗin,mai rubutun Larabci ajikinta,
Miƙa ma Sgr yayi,Bayan ya kar6i robar ya kalli Ya Mu'allim"Itace wannan"?
Jinjina kai Ya mu'allim yayi,"ƙwarai kuwa itace wannan,idan kana jin harshen larabci ka karanta rubutun dake ajikinta,Zakaga Bayanin da take ɗauke dashi na karya sihiri,"
A fili Sgr ya karanto musu Larabcin dake rubuce a jikin robar,kafin Yayi masu translation ɗinshi,kowa Yaji a kunnanshi,
"Tun daga ranar da muka sha ruwan nida Jahan bamu ƙara neman junanmu ba,mun samu sauƙi,dama kullum cikin fargaba muke,Allah shikaɗai yasan irin raɗaɗin da muke ji acikin zuciyoyinmu,Saboda munsan cewa aikata homo babban zunubi ne wanda ubangijinmu Allah Ya haramta yinshi,Ga kuma tsoron hukuncin da za'a yanke mana idan aka kamamu muna yinshi,"idanuwanshi cike tab da kwalla Yayi maganar,
Tuni guiwowinsu sun sage,Zuciyoyinsu sun karaya sosai,
Cikin sanyin murya Kanal Yusuf Ya soma Yi mata magana"Aunty Azmee dagaske ne duk wannan Abun da malamin nan Ya faɗa akanki?Amsarki kawai muke son ji,"
"Amma in har dagaske ne,Azmee kin gama da mu,Kin cuce mu,kin zalunce mu,Laifin me muka aikata Maki?da har kika shigo cikin rayuwarmu,Tsawon Shekara ashirin kina yi mana aiki,"Acewar Jabeer,
Ganin taƙi basu Amsa yasa Sgr Ya daka mata tsawa har saida ta firgita,
"Zaki buɗe baki kiyi magana!ko kuwa saina sa kinyi"?
Maimakon ta bashi amsa,Saita rufe idanuwanta ta soma karanto wasu zantuttuka cikin wani harshe mara daɗin ji,Zuba mata ido sukayi suna kallonta,Watsa hannuwanta tayi saman iska tana kaɗasu,
Murmushin takaici Ya Mu'allim Ya saki tare da cewa"Kada ki wahalar da kanki AZMEE,Domin kuwa Allah Ya rigada ya kamaki,Sihirinki bazaiyi aiki ba A yanzu,"
Buɗe idanuwanta tayi akan fuskarsu,Duk a tunaninta tayi masu layar zana,Basu ganinta hakan yasa ta saki murmushi tare da juyawa zata kama hanyar fita daga falon,Wani irin kukan Kura Alexandra tayi tabi bayanta da gudu ta damƙo wuyan Jallabiyar jikinta da ƙarfin gaske ta wurgota,A sukwane goshinta Ya daki ƙasan tiles,bugu ta shiga kai mata,shaƙo wuyan rigarta tayi"Bazaki buɗe baki kiyi magana ba,"rai a matuƙar 6ace Alex ke magana,
"Dama ni ban ta6a yarda dake ba AZMEE,I have been accusing you for a very long time,Nayi shiru ne saboda banda hujjar da zan kamaki,"
Daƙyar Abusufyan yashawo kan Mommy ta rabu da ita,
"Kodai kiyi mana jawabi da bakin ki ko kuma musa kiyi,"
Motsi ta soma yi da la66anta,Yayin da idanuwanta ke kallon fuskokin kowannansu,lokacin da suka haɗa ido da Sehrish saita fashe da kuka,ita kanta sehrish ɗin hawaye ne sharkaf akan fuskarta,
Hannu tasa tana goge jinin da Mommy ta fitar mata agefen bakinta,
Lokaci guda idanuwanta suka canza sosai,Suka yi jawur tamkar garwashin wuta,
Duk wannan abun dake faruwa akan idanuwan Abbansu,Wanda ya jima da fitowa,Bawan Allah ya girgiza da jin abunda suke tattaunawa,ƙarasowa Yayi wurinsu daƙyar yake jan jikinshi saboda rashin ƙarfin jikin da babu,
"Na kasa yarda da abunda kunnuwana suke jiye mun,Azmee dagaske kece kike son ɗaukar fansa akan ahalina?Laifin me suka yi maki?Me Junaid Yayi maki da kikeson kashe mun shi,Idan ma fansar ce zaki ɗauka meyasa ni baki kashe ni ba,Sai Ƴa'ƴana kawai"?fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yayi maganar,
Girgiza kai Azmee ta shiga yi kafin ta soma magana,
"Da ace inason kashe ɗaya daga cikin ƴa'ƴanka,Wlh da yanzu na jima da shafe Babinku a doron duniyar nan!Dama nawa na samu?Meyasa ban sanya guba acikin abincin gidan nan kowa yaci mutu ba?Tabbas Dama nasan wannan ranar zata zo,Nikaina na jima ina jiranta,Banzo gidan nan don inyi maku aiki ba,Nazo ne don in ɗauki fansar kashe mun Iyayena da kukayi da kuma Mijina,Kun jima kuna cin zalin danginmu amma bamu ta6a ɗaukar mataki ba,Kun tarwatsa mana farin cikin Zuri'armu Yayin da ku Kuma kuke rayuwarku cikin Farin ciki....,
Wacece Azmee?
Azmee cikakkiyar bafullatana Ce ƴar jihar Gombe state,asali garinsu daga ruga ya fara kafin a hankali ya zama gari,A tsakanin family ɗinsu da family ɗin Salahuddeen basu Shiri,faɗansu tun kaka da kakanni ne,Dama tsakanin family ɗin soja da family ɗin Masu tada ƙayar baya a kasa basa jituwa,faɗan nasu ya fara tun daga kan kakanninsu,Kaka wanda sunan kakansu ne kuma dashi ake yi masu inkiya amatsayin sunan family ɗinsu,Kaka Mugun mutunne wanda ya gagari kowa hakan yasa al'ummar dake kewaye dashi Ke tsananin tsoronshi,Matsafin gaskene a wurinshi duk suka gado wani tsaface tsafacen da suke Yi,Sun kasance wasu irin mutane marasa buri a rayuwarsu,Mugunta kawai sukasa a gaba,Kuma abunda zai baka mamaki Suna da ilumin addinin musulunci,Da yawansu Mahaddatan Alqur'ani ne,Suna Yin iliminne ba don komai ba,Sai don su kawar da idanun mutane daga kansu,Don Tafiyar da rayuwarsu batare da jama'a sun zargesu ba,Kuma suna yin amfani dashi wurin Gudanar da sihirinsu,Dama ance in mutun ya 6ace ya 6ace kenan,Sae wani iko na Ubangiji,Sun tsunduma tsulundum wurin aikata shirka,Zubda jinin al'umma da kuma Yin amfani da Mutane wurin yin tsaface tsafacensu,A zamanin kaka,Salahudeen shi ne Ya kawo ƙarshen tawagarsu