Abban Sojoji Book 3 (Takun Karshe)

Chapter 79 of 104

ta matsafa,Sunyi nasara akansu wurin ruguza ƙungiyarsu,Tundaga wannan lokacin Suka zama abokanan gaba,Salahuddeen Ya kafa dokar duk inda akaga ɗaya daga cikinsu yana yawo nan take A yanke mashi hukuncin kisa,Suma haka su kaka suka sanarwa jama'arsu da zarar sunga Jinin Salahudeen Su kashe shi,Kisan wulakanci,ya kasance suna farautar junansu,A lokacin da su salahudeen sukayi nasara akansu,Saida suka ƙarar da rabi da kwata na jama'arsu,Kuma a wannan lokacin suka kashe Kaka har lahira,sunyi tunanin sun gama dasu ashe akwai sauran runa akaba,Kaka ya mutu yabar ƴa'ƴanshi,Wanda bayan mutuwarshi,su kuma suka tada ƙungiyar,suka cigaba da aikata munanan laifuka acikin ƙasa,Nan fa su salahudeen suka bazama neman inda suke shirya maƙarƙashiyarsu,Babban danshi ne ya amshi mukamin mahaifinsu kaka,Sunanshi Ubaid Hatsabibine harya fi Ubanshi kaka,Su biyu kaka Ya haifa dashi da ƙaninshi Wanda suke Kira Uba,Dukkansu Mugayene Basu da Imani ko misƙala zarratin,Shan jini ya zama ruwan dare a wannan lokacin,cire sassan jikin ƴa'ƴan mutane abun ba'a magana,Sai dai kawai a tsinci gangar jikin mutun an cire wasu Organs na jikinshi,Abun Ya tashi hankalin Al'umma,Zama baiga su salahudeen ba,Nan fa suka Bazama neman waɗannan hatsabiban guda biyu,Ubaid da Uba,Yadda kasan aljanu haka suke,Baka ta6a ganinsu cikin jama'a,Sai Lokacin Sallah,Ubaid ma Shike jan Sallah a babban masallacin Yankinsu,Babban limaminsu ne,kuma babban Malamin addini ne,Baka ta6a gane halinshi inba gani kayi ya aikata agabanka ba,Fuska biyu ne shi,A fuska musa azuci fir'auna,a yadda mutane suka sanshi,Mutumin kirki ne,Mai tausayi ga son jama'a,Yafi kowa Iya kiran sunan Allah,Idan Ya hau mumbari zaiyi wa'azi sai ka sha mamakin yarda yake kuka Yana kira ga mutane su Koma ga Allah,shu'umin mutunne mai wuyar sha'ani,Ƴa'ƴanshi Biyu Gali shi ne babban ɗanshi,Sai mai bi mashi mace ce Wadda suke kira da Saratu,Ƙanin mahaifinsu Uba shima Ƴa'ƴanshi Biyu,Babbar ƴarshi itace Azmee,Mai bi mata kuma Namiji ne,Wanda suke kira da Sayyad wato Ya sayyadi,

tundaga kan Iyayensu maza har matan Mugayen mutanene,Mushirikai,Tun daga kan kakanninsu ne abun Ya fara,Sai wanda Allah yaso acikin zuri'arsu yake zama na gari,kamar Azmee duk acikin ƴa'ƴansu itace bata ɗauko mugun hali ba irin na sauran,Hasalima batasan me iyayensu ke aikatawa ba,Mace ce mai tsananin son addini,Kamilar gaske,Tun tana da shekara goma sha Biyar a duniya ta haddace alqur'ani mai girma,Saratu kuwa ƴar wurin wan mahaifinsu jakkace,bata gane komai sai Iya mugunta,

Ana haka Azmee ta fara soyayya da wani bawan Allah,Wanda Ya ta6a taimakonta,akan hanyar dawowarta daga islamiyyar dare,Wasu ƴan iska suka biyota suna ƙoƙarin yi mata fyaɗe,A wannan lokacin wani matashin saurayi ƙakƙarfan gaske ya riƙesu sun kewayeta,Haɗa kawunansu yayi ya dinga bugu sai da yayi haɗa masu jini da majina,Sannan Yace ta sanya hijabinta suje ya rakata gidansu,A ƙopar gidansu yayi sallama da ita,Tunda ta koma gida ta kasa runtsawa saboda tunanin bawan Allahn nan daya taimaketa,tun adaren ranar ta kamu da tsananin sonshi,so bana wasa ba,

Saboda shi kullum sai taje islamiyar dare,tunda ta gane cewa hanyar dawowarshi ce,duk in suka haɗu saiya rakata har gidansu sai ya tsaya yaga shigarta kafin shima ya wuce gidansu,Soyayya mai ƙarfi ce ta shiga tsakaninsu,sam batasan asalinshi ba,Abu ɗaya kawai tasani akanshi yana da kyakkyawar Zuciya,

Tun tana 6oye ma Iyayenta soyayyarta dashi har suka fara lura da yadda Azmee ke yawan ambaton sunanshi Jabeer,ko bacci take yi sai ta dinga sambatu tana ambaton sunanshi,Sa6anin da in tana bacci karatun haddar da aka basu ne zaka ji tana biyawa a bakinta,

Da iyayensu maza suka gane cewa tana son wani bare ba danginsu ba,Sai suka gargaɗeta akan ta rabu dashi,In ba haka ba zata ja mashi ne,su sunfi son suyi mata auran zumunci dama kuma Family ɗin kaka basu auren bare,Yasu yasu ne,ita kuma ta tsani Wanda suke son su haɗa ta dashi,Ɗan wurin Ubaid ne yayan mahaifinta,Wato Ghali mugun mutunne kuma Arne ne shi,Sunan yana musulmi ne ko sallah baya yi,a lokacin taƙi jin maganarsu ta kangare,Aikuwa mahaifinta Uba yasa aka ɗauko mashi Jabeer,A wani kogon dutsi suka Rufe shi,Anan suke gana mashi azaba,duk don su raba ta dashi,kwana biyu da azmee bata sanya shi a idanuwanta,Ko abinci tadaina ci a ƙarshe ciwon zuciya yakusa kamata,ganin dagaske takeson Jabeer kuma zata Iya Kashe kanta akanshi gashi kuma Uba yafi Sonta cikin ƴa'ƴanshi,Sae ya yanke shawarar zai aura mata jabeer,ashe da wata mummunan manufa Ya amince zai aura mata shi,Saboda yayi bincike akanshi ya gano cewa Jinin Maƙiyansu ne,mutanan da suke hari,shi kanshi Jabeer ɗin baisan wanene shi ba,Yawo kawai yake yi acikin garinsu tun yana ƙarami ba'asan danginshi ba,Amma su dayake Shu'umaine da suka bi diddigi saida suka gano ainihin wanene shi............

Cikin lokaci ƙanƙani aka ɗaura auren Azmee da Jabeer,Aranar Hamma Gali kamar Ya haɗiyi zuciya Ya mutu,Ya tsaneshi kamar mutuwarshi,Saboda Shi ke son Azmee,duk da ba son Allah da Annabi yake yi mata ba,Yasha yin kokarin Keta haddinta amma Allah bai bashi iko ba,

Bayan sun ɗaura auren Azmee da jabeer,Mahaifinta da kanshi Ya basu kyautar gidan da zasu zauna,Saboda Jabeer baida komai,Talaka ne shi gaba da baya,

A ranar da aka kai Azmee gidan Jabeer wani mummunan abu ya faru,lokacin da kowa yabar gidan Amarya Ya kasance su biyu ne acikin gidan,Bayan sunyi al'wala sun gabatar da sallah,jabeer ya ɗauketa zuwa saman gadonsu,sai da yafara karanta addu'ar saduwa da iyali kafin suka soma biyan buƙatar junansu,Ita dai a wannan lokacin tasan da jabeer suka kwanta,Amma a washe garin Ranar da ta farka cikin mawuyacin hali,Hamma gali ta gani kwance saman gadonta babu kaya ajikinshi,ta fasa wata irin gigitacciyar kara ta soma ƙoƙarin mayar da kayan jikinta,Da gudu ta shige bandaki tana kuka,Bata fito daga toilet ɗin ba har saida taji Muryar Jabeer yana ambaton sunanta,
Sannan ta fito tana kuka,A gefen gadonsu ta same shi zaune,Hawaye wasu na bin wasu akan fuskarshi,Jikinshi sai kerma yake yi,Zuƙunnawa tayi agabanshi tana kuka,
Cikin shessheƙar kuka take tambayar meya faru dasu a daren jiya?ina ya tafi yabarta har Hamma Gali ya shigo cikin ɗakinsu,ta rikice ta rasa gane waye ya kusanceta a cikinsu,A lokacin Jabeer Ya amsa mata da cewa shine ya kusance ta,Bata yarda da kalamanshi ba,Hakan yasa ta soma tambayarshi Idan har dagaske shi ya kusanceta meyasa da ta farka da safe bata ganshi ba,Sai dai Hamma Gali ta gani kwance Saman gadonsu,Sannan meyasa yake kuka?"ganin halin da ta shiga ne yasa bai sanar da ita ainihin abunda ya faru ba,Shi dai A iya saninshi a daren jiya bashi kaɗai ya kusanceta ba,An gusar mashi da hankalinshi,Ya mike a wani irin yanayi yabar ɗakin bai ƙara sanin inda kanshi yake ba,A wannan lokacinne Gali ya shiga ya ƙarasa aikin,shi kanshi kokwanto Yake yi Anya Shine ya kawar da budurcinta ko kuwa Gali ne?kamar yarda tace Gali ta gani kwance saman gadonsu,Allah kaɗai yasan Ƙuncin da jabeer yaji acikin Zuciyarshi,Iya cuta dai an cutar dasu,Hakanan ya daure Ya rungumi matarshi suka ci gaba da rayuwa da ita,

Ana haka,Azmee ta fara ganin sauyi atattare da jabeer,Ya canza mata sosai,kwata kwata babu kwanciyar hankali atare dashi,Ko magana baisan yi,abinci ma baya ci,idan dare Yayi baya bacci sai dai ta farka ta same shi saman darduma Yana sallah yana kuka,Duk in ta tambayeshi meke damunshi sai yace mata,tayi ma mahaifinta magana,Yadaina yi mashi abunda baiso,Ta rasa gane me jabeer ke nufi,ita dai a iya saninta Mahaifinta mutumin kirki ne,babban malamine shi,ko maiyasa jabeer ke ƙorafi akanshi,duk yarda taso ya sanar da ita,ainihin abunda Iyayenta keyi mashi amma Yaƙi sanar da ita,tun tana tambayarshi har ta gaji ta ƙyaleshi,

Wata ɗaya da yin auransu,Azmee ta fara laulayin samun ciki,A lokacinne suka shiga ruɗani ita da jabeer,Ga ciki Ya bayyana ajikinta,Amma basu da tabbacin Cikin Shi ne kona Hamma Gali,A wannan time ɗin Jabeer Ya bata kyakkyawar kulawa,ya rage nuna damuwarshi,don kawai farin cikinta,

Ranar da Azmee bazata ta6a mantawa ba,Shine ranar da cikinta Ya shiga wata Tara ta fara nakuda,Dayake ƙa'idar family ɗin kaka in mace zata haihu,a gida suke kar6ar haihuwarta,


Cikin ɗakin mahaifiyarsu Dije aka shigar da ita saman gadon karfe,Su biyu ne akanta zasu kar6i haihuwarta,Hada matar wan mahaifinsu Ubaid,mahaifiyarsu Gali,Inno bata da mutunci matar nan,Halinta sak ƴa'ƴanta suka biyo,Duk acikin gidan suke,Dayake babban gidane na iyali,zumuɗinta akan jaririn da za'a haifa ne saboda gali ya sanar da ita cewa ɗanshi ne,


Azmee bata haihu ba Sae daren Ranar Allah yayi zata haifi santalelen ɗanta Namiji,Ko wanke jikin jaririn ba'a kaiga Yi ba,Kwatsam Ba zato ba tsammani Sojoji Su kayi masu dirar Mikiya,A fusace sojojin nan suka shigo,Kuma sunci sa'a Gaba ɗaya family ɗin sun taru a gidan suna jiran Haihuwar Azmee,Bisa umarnin Salahuddeen A lokacin shine shugaban sojoji na Nigeria,Umarni aka basu kai tsaye su kashe duk wanda suka Gani acikin Family house ɗinsu,amma banda mata da ƙananun Yara,Nan fa sojojin nan suka buɗe masu wuta,ta ko'ina sautin bindigu kake ji,Sunga tashin hankalin da basu ta6a gani ba,Anan Suka kashe ubaid da kuma Uba,Daga ciki hada iyayensu mata,domin sunyi ƙoƙarin Ɗauko makamai a cikin ɗakunansu da niyyar su taimaki Mazajensu,wannan ya tabbatar masu da cewa suma matan suna da sa hannu a aikata ta'addanci tunda har sunsan suyi harbi da bindiga,aikuwa suka kashesu gaba ɗayansu,A ranar an zubda jini kamar kamar mi,Daga cikin waɗanda tsautsayi Ya ritsa dasu,Hada Jabeer bawan Allah baiji ba bai gani ba,Suka kashe shi,A lokacin yazo duba jikin Azmee yaga in ta sauka lafiya,Shigowarshi keda Wuya,Sojojin suka harbeshi saitin zuciyarshi,Anan Ya yanke jiki ya faɗi matacce,


A ƙarshe mutun uku suka tsira,Azmee data 6oye a ƙarkashin gadon mahaifiyarsu,hannunta ruke da jaririnta, itama Saratu Ta tsira a wannan Lokacin,Sae kuma Gali tare da Ya sayyadi da basa acikin gidan abun Ya faru,

Azmee bata tashi sanin Jabeer ya rasu ba,Sae a washe garin ranar,ta fito daga ƙarkashin gadon hannunta ruƙe da jaririnta,jini duk ajikinshi domin ba'ayi mashi wanka ba,haka ta fito dashi rungume a hannunta,ta tsorata da ganin yadda sojoji suka wanke gidan da jinin Iyayenta,Tasha kuka kamar ranta zai fita,A lokacin Allah ne kawai Yayi zata rayu,A nan tsakar gidan taga gawar Jabeer yashe a ƙasa,ga gawawwakin Sauran Ƴan uwanta,nan take ta yanke jiki ta faɗi kasa a sume,jaririn hannunta ma Ya faɗi wanwar yana ta tsala kuka,

Bayan wasu kwanaki da yin wannan Tashin tashinar,Azmee ta farka a gadon asibiti,bayan ta shafe sati biyu kwance bata acikin hayyacinta,

Tasha kuka kamar ranta zai fita,ita sam bata damu da iyayenta da aka kashe mata ba,Mijinta tafi ji,shi da baisan komai ba,Bai aikata laifin komai ba,Amma an haɗa dashi an kashe,

Hamma Ghali ne Ya kawo ta asibitin,Lokacin data farka tare da sayyadi da saratu tagani tsaye akanta,sune ke jinyarta tun daga wannan lokacin rayuwarsu ta tagayyara,mutane suka ƙyamace su,kowa gudunsu yake yi,saboda sanin Abunda iyayensu suka aikata,Idan suka biyo hanya har jifarsu akeyi da duwatsu ma,Dole suka daina shiga cikin jama'a,

Tundaga wannan Lokacinne,Hamma ghali Ya tunzurasu akan su ɗauki fansar kisan wulakancin da Family ɗin SALAHUDEEEN HOSSEIN suka Yi masu,Kunji silar shigar Azmee ƙungiyarsu,Wadda bayan Su salahuddeen sun ruguzata a karo na biyu,Ghali kuma Ya tada ƙungiyar ta hanyar wasu abokanan Iyayensu da suka rage ba'a kamasu ba,A lokacin ne kuma Salahuddeen yabar duniya,Saboda ɗaukar fansa Azmee ta jefa kanta cikin halaka,duk don saboda Mijinta da aka kashe,ko lokacin bataso shiga ƙungiyar ba,Hamma ghali ne Ya tunzurata sosai har saida ta amince Ta tsunduma tsulundum,Da ita da Ya Sayyadi da saratun dukkansu,Jinjirin da Azmee ta haifa ba kowa bane,Face Haroon shine ɗanta da take dashi ɗaya tilo,

Shiri na musamman sukayi domin ganin sun tarwatsa Family ɗin salahuddeen,Wannan yasa suka raba kansu,Ya sayyadi yabi Ta 6angaren Abusufyan dake zaune a kano,Da biyu ya shiga rayuwar abu saboda kawai Ya cimma burinshi na Ƙuntata rayuwar Abusufyan,Azmee kuma ta hanyar hajjaju ta biyo masu,Sai da tayi bincike sosai ta gano cewa hajjaju tana da kusanci sosai da mutanan gidan kuma itace ke kai masu ƴan aiki duk in suka buƙata,Wannan dalilin ne yasa taje har gidan hajjaju ta nemi da ta taimaka mata ta samo mata aiki a gidan Abban sojoji,
Ganin yarda take roƙonta,Ga ƙaramin yaro yasa hajjaju ta tausaya mata,har dai ta amince zata sama mata aiki a gidan,kuma cikin sa'a Batare da ta sha wahala ba,ta samu aiki agidan duk da dama sai da tayi ma hakan shiri........"

  *Masu cewa Basu son littafin abban sojoji na kuɗi bane,Littafina na kuɗi ne,Book one ne kawai nayi shi kyauta,Amma 2 da 3 Na kuɗi ne,Dukansu 300 ne duk maiso yayi mun magana kaitsaye Amma message ta whatsapp 08103884440*
 
 



  *Masu cewa Basu son littafin abban sojoji na kuɗi bane,Littafina na kuɗi ne,Book one ne kawai nayi shi kyauta,Amma 2 da 3 Na kuɗi ne,Dukansu 300 ne duk maiso yayi mun magana kaitsaye Amma message ta whatsapp 08103884440*
 
 
[3/19, 2:57 PM] +234 810 388 4440: 💋𝔹𝕠𝕤𝕤 𝔹𝕒𝕥𝕦𝕣𝕖💋





𝑗𝑜𝑖𝑛 𝑡𝒉𝑖𝑠 𝑙𝑖𝑛𝑘 𝑡𝑜 𝑓𝑜𝑙𝑙𝑜𝑤 𝑚𝑦 𝑇𝑖𝑘𝑡𝑜𝑘 𝐴𝑐𝑐𝑜𝑢𝑛𝑡👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت❤🤍❤
𝐹𝑎𝑡𝒉𝑒𝑟 𝑂𝑓 𝑆𝑜𝑙𝑑𝑖𝑎𝑟𝑠

*🔥𝕋𝕒𝕜𝕦𝕟 𝕂𝕒𝕣𝕤𝕙𝕖🔥*



_Ga masu karanbanin haɗa mun document,koda gigin wasa kada wanda ya kuskura Ya ƙara haɗamun document,kuma bazaku ta6a samun Complete document na takun ƙarshe ba,saboda ba yanzu zan haɗa shi ba koda na kammala littafin,Dole sai a wurina za'a same shi from page one to the end,if not babu wanda zai baku shi cikakken shi,Sannan Zan canza Lokacin posting_





Lokacin dana fara aiki acikin gidan nan,mahaifinku ya mayar dani tamkar ba ƴar aiki ba don alokacin ya tambayeni game da mahaifin yarona,na sanar dashi cewa ya rasu dalilin hadarin mota,daga haka kuma na kulle bakinshi don kar ya nemi jin wani bayani agame da dangina,Ya ɗauki Haroon ɗansa,Kuma Ya nuna yana so inbar mashi haroon ya kasance acikinku,baya son Ya taso a matsayin bare,Ba ƙaramin daɗi naji ba,Duk da mummunan ƙudirin da nake dashi,

Tsawon Lokaci da fara aikina cikin gidan nan,na fara shirya maku maƙarƙashiya,da niyyar tarwatsa farin cikin gidan nan,Amma silar kyautatawar da mahaifinku keyi mun da kuma wasu daga cikinku yasa na ɗan dakata,Akwai wani hadithi da manzon Allah (SAW) yake cewa"Jubilatul ƙulubu ala hubbi man ahsana ilaiha,Wabugudi man Asa'a ilaiha,(An halicci zuciya da Son mai kyautata mata da kuma ƙin mai munana mata),Wannan kyautatawar da kuke Yi mun ita ta Jani har izuwa tsawon lokacin nan Batare dana Aiwatar da abunda ya kawoni cikinku ba,a lokacin banyi tsammanin zan faɗa tarkon son wani acikinku ba,Sai gashi na kamu da tsananin Son mahaifinku,Saboda yafi kowa kyautatamun,Ya yarda dani sosai Kuma ya damu dani akan kowa na cikin gidannan,Da yake ita zuciya ba ƙashi ne da ita ba,bansan lokacin dana afkawa Sonshi ba,sai kuma na fara kishi da Alexandra,don nasan cewa muddin tana acikin gidan bazan ta6a samun soyayyar mahaifinku ba,Wannan dalilinne Yasa nayi Amfani da sihirina wurin Ƙuntata mata,ta fara jin ƙunci acikin ranta,Zaman Nigeria ya gagareta,babu arziƙi ta tattara tabar ƙasar nan,batare da ta ƙarasa shayar da Junaid ba,ta barshi cikin tsummanshi yana ɗan jinjirinshi.......... "

Bata ƙarasa maganar ba,Sakamakon wani irin kukan Kura Da Mommy tayi takai mata damƙa a wuyanta,Muryarta adisashe take magana hawaye na zuba"Amma kin cutar dani Azmee,Kin cuci rayuwata,Da kuma rayuwar Junaid,Ashe kece silar dana tafi nabar mijina da ƴa'ƴana,I will neva forgive you....."kasa ƙarasa maganar tayi,nan take ta fashe da kuka,Daƙyar Abba ya samu ta saki wuyan Azmee,har tangal tangal tayi zata faɗi da sauri Jahan ya ruƙota,Ya taimaka mata ta zauna saman hannun kujera tana kuka"matar nan tajima tana cutar da rayuwarmu,Dama ance makashinka Yana tare dakai"Sosai take kuka,Ita kanta Azmeen kukan takeyi,Su Sehrish da Jahad dukkansu kuka sukeyi,Oummansu ma idanuwanta cike tab da kwalla,
Bayan ta tsagaita da yin kukan taci gaba da cewa"A lokacin mahaifinku Ya ɗauki Junaid ya bani shi don inci gaba da shayar dashi,babu yarda Hajiya azeema batayi ba akan Ya bata Junaid ta shayar dashi,Amma ya nuna cewa yafison na shayar dashi,Ba don komai ba Sae don baison Junaid Yayi nisa dashi,tunda ita a lagos take zaune,bayan ya damƙamun Amanar Junaid,naci gaba da shayar dashi,Allah shine shaidata,Inason Junaid sosai,Fiye da son da nake yi ma haroon,Sai na dinga ji kamar ni na haifeshi,har banso su Fawan suzo ɗaukarshi,gashi lokacin haushina suke Ji saboda ina ƴar aiki ƙasƙantacciya an bani Ƙaninsu ina shayarwa,ni kuwa daɗi na dinga Ji,Saboda ina tunanin ta hanyar Junaid zan samu soyayyar mahaifinku don tsakani da Allah nike sonshi hakan yasa banyi mashi wani sihiri ba wai don ya so ni,babu wanda yasan Inasonshi,Sae Laila matar Ishaq da yake ƙawatace duk da ba wani shiri nake da ita ba,Amma ina neman shawara awurinta,haka Hajjaju ma muna mutunci da ita,Dukkansu babu wanda yasan Ainihin wacece Ni,Duk irin son da nake yi ma Abbanku bai ta6a lura ba,Naso na sanar dashi amma ina tsoron Yace baiso na,bansan wani hali zanshiga ba,Lokacin da Junaid Ya fara tasawa,abunda Ya bani tsoro dashi irin wayon dake gare shi,Kullum agabanshi nake yin waya cikin harshen fulatanci,kwatsam wata rana,bayan na kammala waya,sai yake ce mun ae Yaji duk abunda nace,A lokacin na ɗauka da wasa yake yi don nasan baijin fulatanci,Sai cewa nayi toh ya faɗamun me nake cewa acikin wayar,ba zato ba tsammani Yaron nan Ya fassara mun maganganun da nayi acikin wayar,hankalina yayi mugun tashi,Ko makaranta ba'a sanyashi ba,na ruƙe shi ina tambayarshi a ina ya koyi harshen fulatanci,Sae ce mun yayi a wurina yaji ina yi,duk in zanyi waya,tunda naji haka saina tsorata dashi,tabbas wata rana zai iya tona mun asiri,tunda har ya iya yaren da nake yi wanda a waya kawai nake magana da harshen,Kawai na yanke shawarar In juye mashi tunaninshi ta yadda bazai ta6a fahimtar komai ba,Tun daga wannan lokacin Junaid Ya zama soko,Bai ɗaukar karatu ko mis'ƙala zarratin,Nasan na cuci Junaid,Da ace Yayi ilimi da ina da tabbacin cewa zai kasance ɗaya daga cikin ƴaran da duniya zatayi alfahari dasu saboda baiwarsu,A kwana a tashi,Rana ta farko dana fara Yin tozali da Rafayet,Bazan ta6a mantawa da wannan Lokacin ba,dawowarshi kenan daga U.S,Ya soma tambayar ina Babyn da Mommynsu ta bari,Su fawan ke sanar dashi cewa Yana a wurin mai aikinsu har suke bashi labarin cewa ni na shayar dashi,Ranshi yayi mugun 6aci Yasa su kirani,Na fito ɗauke da Junaid a hannuna,ya rufesu da faɗa don me za'a ba mai aiki ta shayar da ƙaninsu,sun tabbatar da tsaftar jikina ne,A karshe ya kar6e Junaid daga hannuna,Ya wuce dashi dakinshi,

Tunda na koma ɗaki,na kasa runtsawa saboda tunanin Rafayet,Kyawun fuskarshi dana surarshi suka ɗebeni

Download complete TXT · Novel page