So Da Buri Book 1
Chapter 19 of 43
da d’an kud’i a hannunshi, amman dai sai da ya sake neman shawarar Maryam wadda itama tunaninta ya zo daidai da nashin. Dan haka a mintunan da basu gaza 20 ba sukayi parking komai nasu suka fito.
Managern yana ganinsu da kaya ya fahimci decision d’in Abba na barin wajen nasu ne kenan, dan haka ya kuma b’ata rai ko godiyar da Abba yake yi mishi bai amsaba. Shi dai Abba bai damu ba yayi mishi sallama suka nufi cikin kitchen d’in dan ko ba komai ba zai manta da manager ba, kuma idan an d’an kwana biyu in sha Allah zai d’an dinga lek’owa suna gaisawa.
A kitchen d’in daman sun tab’a hirar apartments masu sauk’i da cook d’in da suje shiri dan haka ya tambayeshi “inane yake ganin zai fi dacewa ya zauna?”
Cike da farin ciki cook d’in yace “apartment d’in da yake zaune akwai security a estate d’in!
Ya bashi 3 minutes ya chanja kayanshi ya zo suje sai ya rakashi har gidan mai estate d’in, daman Neighbour d’inshi bai dad’e da tashi ba sai ya karb’i gurin.”
Cook d’in yanata murna da taya Abba murnar samun sabon aiki, a haka suka d’unguma, saida suka biya apartment d’in cook d’in, 2 bedroom da parlour da kitchen, anan suka ajjiye kayansu, sannan shi da Abba suka tafi gidan mutumin, aka bar Maryam da matarshi mai mutunci tanata janta a jiki Yaransu uku.
Kamar yadda cook d’in yaso kuwa, apartment d’in gefen su aka bawa Abba, bayan ya biya kud’i ya cike duk wani abun buk’ata.
Sai wajen 1 suka gama settling…har moping sai da mutumin nan da family d’inshi suka tayasu sannan suka yi musu sallama suka tafi nasu gidan.
Washegari da safe Abba ya nufi wajen aiki.
Da kyar Abba ya yarda Maryam ta fara aikin kitchen, shima sai da ta saka mishi kuka, saboda ba fita take yi ba sannan ba aikin da take yi, shiyasa gaba d’aya kafafunta har wani kumbura suka yi.
Sai da yaga dai rashin exercise d’in ka iya yi mata illa tukunna ya yarda, amman dai shara wannaan aikinsa ne idan ya dawo, wankin toilet kuma kafin ya tafi office da safe tare sukeyi idan sun shiga wanka,
wanki kuwa yanzu sunada washing machine abunsu............
Kano, Nigeria.
5months ago…
Da mugun gudu Sadiya ta shiga cikin gidansu Maryam bayan taga tashin motar Abba, tana shiga takaici ya rufeta ganin babu kowa. Gidansu ta koma ta sanarwa Baaba Laraba halin da ake ciki dan ta d’an jiyo maganar Maryam d’in da Abba sama sama…Baaba Laraba kuwa sarkin y’an tsurku nan ta zari mayafi tayi waje…Gidan aminiyarta dillaliya ta fara lek’awa ta fesa mata.
…Wannan gayawa wannan, kafin awa d’aya labari ya baza unguwa ‘Maryam ta gudu da saurayinta wanda aka kamasu a makaranta suna lalata!’.
Har majalisar maza zancen da akeyi kenan, magana har ta kai kunnen tsofaffin unguwa ana ta cewa “Y’ar gidan mai unguwa kuma Limami ta gudu ta bi saurayinta!’.
Ana cikin haka Madu da su Shuwa suka dawo, har da Ya Usman wanda jikinshi ya d’anyi sauk’i dan a asibitin a gabanshi aka yanke shawarar aura mishi Maryam da zarar an dawo gida!.
Duk da sun san ba a neman aure cikin aure amman zasu je su yiwa Yayan Abba bayani su nemi alfarma a wajensu.
Baaba Talatu ma da farin cikin ta ta dawo.
Tun kafin su shigar da mota gida K’asimu ya tsayar da motar da yaga Madu da Bashir a ciki, parking Madu yayi a gefe dan ya bawa motar da Ya Jamilu yake tuk’awa damar wucewa, bayan sun fito, ko gaisawa K’asimu bai bari sun yi ba ga y’an unguwa da ganinsu yasa suka k’araso suma domin suji k’arin bayani….ba tare da tauna zance ko lafazi mai kwantar da hankali ba K’asimu ya shiga koro musu bayani kamar a gabanshi aka yi, har da cewa “sai da Maryam da Abban suka gama rungume rungume ma tun kafin su shiga motar su gudu.”
Ba tare da Madu ya kula kowa ba ya kamo hannun Baba Bashir suka nufi cikin gidan Baba Bashir d’in, tun kafin su k’arasa shiga ya fara jiyo kukan Shuwa, suna shiga tsakar gidan ciki suka tarar da Baabaa laraba da dillaliya suna ta kora mata
bayani tana kuka!.
Ya Jamilu ne yace “dan Allah ya isa haka!!”
Sannan ya cewa su Sadiya “an gode, ku je, za muji da lamarin!.”
Suna fita kamar jira Shuwa take yi ta mik’e ta fara yiwa Madu bala’i kamar ba Mijinta ba, gaba d’aya laifin ta d’aurashi a kansa, a cewarta “Ai shi ya shagwab’a Maryam d’in ,ba dan shi ba da duk haka bata faru ba!
Sannan saboda rashin lissafi yaje ya bawa Yaron da bai gama sani ba Y’arsu, gashi yanzu ya gudu da ita!! Wannan wanne irin abin kunya ne, da wanne ido zata kalli jama’a??? Mai zata ce wa mutane?.
A yanzu haka Innaa tana kasuwa taje siyowa Maryam kayan d’aki! Shin ta Ina zata fara yi mata bayani idan ta dawo? Mai zata ce mata???”
kuka take kamar ranta zai fita tana cewa “Madu ya cuceta duk shi ya jawo mata.”
Baba Bashir ne yace “suje gida su duba koina, a dudduba sosai.” Dan shi bai gama yarda da maganar su Sadiya ba.........
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
18
Babu inda ba a duba ba, amman babu Maryam babu alamar ta, gaba d’aya hankalin kowa a tashe yake, tunba ma da Innaa ta dawo daga kasuwa nik’i nik’i da kayan d’aki ba!.
Babu kalar zagin da bata yiwa Madu ba, Mallan shima yana k’arasowa ya iske mummunan labari.
Har dare basu zauna ba domin shi Madu ya dage akan ‘bai yarda Maryam guduwa tayi ba!’. Sune har police station
da daddare bayan sallar Isha……..da kyar suka iya cin abinci tun safe…..
Suna zaune a gidan Madun, Inna tana ta yada magana tana cewa “Madu ya janyo musu abun kunya! Itakam Allah ma yaso ta tunda idan aka bi tsattso ba a jikinta ya fito ba!! Kuma kowa ya san Shuwanta bata da laifi…”waye waye….
Har sai da taga ran mallan ya b’aci ya fara yi mata bala’i shima, tukunna tayi shiru.
Sallamar da aka yi da Madu ce ta katse mata guna gunin da take yi akan ‘itafa shiyasa tun farko bata so auren Shuwa da Madun ba’…..
Cikin mutuwar jiki Madu ya mik’e Baba Bashir yana binshi suka fita tare domin amsa kiran da ake yi mishi a waje!.
Suna fita suka tarar da dattawan unguwar, da sauri Madu ya k’arasa ya shiga basu hannu yana tambayar su “ko lafiya??” Dan shi a tunanin sa anga Maryam ne. Amma sab’anin hakan sai yaji wai ‘su meeting d’in gaggawa suka zo ayi saboda guduwar da y’arsa tayi, domin kuwa y’an unguwa sunce ya kamata a chanza sabon Limami.!’
Da mamaki yake kallon su, shi yana ta neman y’arsa, su kuma suna ta muk’ami! shiyasa ba tare da b’ata lokaci ba ya sanar musu da ‘ya sauk’a!’.
Amman hakan bai sanya sun barshi ba saida suka jashi akaje wajen meeting d’in.
Suna zuwa yaga dubban mutane, su kawai ake jira.!
Sai a wannan lokacin Madu ya san ba K’asimu kad’ai ba ne mak’iyinsa a layin!! Harda waenda yake ganinsu Abokanan sa duk cikinsu babu ya bi bayanshi..
Mutum uku ne kawai suka bi bayan Baba Bashir wanda Allah sarki dudda halin da Usman yake ciki bai sa ya juyawa Madun baya ba.
A lokacin mutanen gurin rabuwa sukayi kashi uku
Kashi na farko ‘sune su Baba Bashir su hud’u!’
Kashi na biyu ‘sun ce, y’ar Madu tayi laifi kuma shi ya janyo tunda shine ya shagwab’ata kuma baya son laifinta, amman bai kamata ace laifinta ya hau kanshiba, har a kai ga sauk’e shi ba’.
Kashi na uku kuwa (su K’asimu) sunce ‘ai laifinshi ne y’arsa ta gudu yawon karuwanci, tun farko shine ya yi mata lagalaga ya shagwab’ata, baya tsawatar mata duk abinda takeso baya hanata! Haka k’iri k’iri aka koreta a makaranta saboda abunda take yi amman ya rufe yak’i gayawa kowa idan an tambayeshi sai dai yace chanza mata makarantar yake son yi! Ai y’an unguwar da aka taso sama da shekaru ashirin da biyar tare ya kamata ace yanzu an zama d’aya dan haka su ba zasu dinga bin mutumin da yake ha’intarsu! Sallah ba. Su idan matsala ta taso a nasu gidajen tuni sunzo sun saki baki dan neman shawara da yarda da juna, amman shi y’arsa daya kamata ace tun kafin abun ya kai haka a taka burki yak’i yarda ya bada k’ofar yin hakan kuma shima ta bangarenshi bai yi ba, gashi yanzu ta tafi tabi saurayi.
Saboda haka..
Su baza su bi uban karuwa ba a masallaci har ma da unguwa.’
Harda cewa ‘ci yake yi da addini.’
Nan suka fara jidar kaya za suyi zanga zanga!
Dattawan unguwa na ganin haka suka hau basu hak’uri, sannan a take aka sake sauk’e Madu daga matsayinshi na mai unguwa ma gaba d’aya!
Dan a samu a zauna lafiya.
Babu kalmar da ta fi b’atawa Madu rai irin na kiran ‘Maryam karuwa da aka yi’
Shiyasa tun baya mayar musu har ya zo yafara mayar musu da martani, da kyar Baba Bashir ya janye sa suka bar wajen sukayi gida.
Dishi dishi kawai Madu yake gani, bai san ta Ina zai fara ba,
Da kyar ya iya kai kanshi gida.
Yana shiga Inna ta tisa shi a gaba da tata mitar, harda d’akko mayafinta tace ‘sai ya kaita gidan Yayan Abba! Ai sunce sun yi bincike dan haka ya kaita ko wajen wani nashi ne…’
Madu kuwa tun rana, suke ziryar zuwa ganin Alhaji Yahaya amman mai gadi yace musu wai yace ‘kar a barsu su shiga!!’. Shiyasa ma abun ya kuma dagule musu, amman dai basu fad’awa kowa ba suna so suyi settling ne a tsakaninsu,
shiyasa yanzu furucin Inna ya sake rikitashi!.
Ba yadda ya iya hakanan kawai ya sanya Jamilu ya jasu a mota suka nufi gidan, dan bashi da wani sauran energy.
Har da Inna da Mallan aka tafi,
suna zuwa, daidai motar Alhaji Yahaya tana k’arasowa.
Da sauri Madu ya fita ya isa gaban motar tashi ya tsaya!.
Alhaji Yahaya ganin an ritsa shi yasa kawai ya fito dan babu yadda zaiyi, a hankali ya k’arasa inda Madun yake wanda isar tashi tayi daidai da k’arasowar su Inna wajen.
Duk da rikicin da Madu yake a ciki hakan bai hanashi tsayawa suka gaisa da Alhaji Yahaya wanda ya kasa had’a ido dashi ba.
Inna ce ta matso sannan tace “Kai Yaro!! Ina kuka saka mjni jikata?? fito min da ita dan tun yanzu anan zan fara cin uwar ta kafin mu k’arasa gida.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya juyo ya fuskanci Madu ya fara kwararo masa bayanin duk abinda ya faru tun daga safiyar yau har kawo yanzu, hatta furucin da granpa ya yiwa Maryam akanshi da Shuwa da Bilkisu duk bai b’oye ba. Sannan ya k’ara da cewa
“Shima dalilin da yasa, yaketa dudging karsu had’u shine ‘mahaifinsu yace indai ya yarda ya sauraresu to ranshi sai yayi mugun b’aci, kuma sai ya kulle zuri’ar su Madu gaba d’ayansu!’.”
Yace “Mahaifin nasu yace ‘babu su babu duk wani abunda ya shafi Maryam da Abba’.”
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan yace “A tunanina zamu iya shawo kanshi, amman ranar da nazo gidan ka bayan mun koma naje na sameshi, b’acin ran dana gani a fuskar shi tabbas yayi matuk’ar tsoratani, shiyasa na cewa Abba ya hak’ura! Amman Yaran zamani kaga abunda suka je sukayi…
Ni ban san ta Ina zan fara baka hak’uri ba, amman yanzu dai Ina rok’on ka da kuyi saurin barin nan, mahaifin mu yana da c i ds da yawa especially ma yanzu da case d’innan yake going! Idan yaji labarin na ganku akwai babbar matsala.”
Yana gama fad’in haka yayi saurin komawa cikin motarshi ya danna horn mai gadi ya bud’e mishi ya shige ciki da gudu.
Da kyar Baba Bashir da Ya Jamilu suka ja Madu suka saka shi a mota, dan daskare musu yayi a wajen kwata kwata yak’i motsi.
Duk tsauri da k’ok’arin Madu sai da hawaye ya zubo ta idonsa…..
Yanzu wannan itace kalar rayuwar da Maryam d’insa zata yi? Da irin wannan mutumin a matsayin suriki?? Wanda d’an cikinsa ma daya
haifa bai sarara wa ba ballantana ita karan kad’a miya!! Gashi k’iri k’iri ya nuna ya tsane ta!
Tabbas Maryam guduwa tayi amman aure tayi! Abu d’aya daya sani shine idan zai had’iyi AlQurani yana rantsuwa yana fad’awa mutane Maryam aure tayi babu wanda zai yarda.
He is very disappointed in Maryam! Sam bai tab’a tunanin zata iya aikata haka ba!
Bai ankaraba yaji fuskarshi ta jik’e sharkaf da hawaye!!! Baba Bashir ma tausayinshi ne yasa ya share tashi kwallar da yake ta k’ok’arin b’oyewa saboda yanaso nunawa Madun kwarin gwiwa.
Inna ma duk surutunta tayi shiruuuu! Kamar ruwa ya cinyeta, tabbas ta san Maryam bata kyauta ba, amman ko da irin wannan surikin aka barta hukuncinta yama yi yawa.
Haka Mallan shima da Ya Jamilu suma duk sun yi shiru….motar shiru baka jin sautin komai sai na sauk’ar ajiyar zuciyar Madu.
A haka suka k’araso, suna
shiga suka tarar dasu Baaba Talatu sunyi cirko cirko, nan suka hau tambayarsu, Innaa ce ta fara labarta musu……
Salatin da Shuwa tasa tare da kuka a lokaci daya ne ya juyo da hankalinsu kanta, aikuwa da gudu suka k’araso , sakamokon ganin Madu a k’asa wanwar kamar babu rai a tare da shi…
A take su Ya Jamilu suka kinkimeshi aka saka a mota
suka nufi asibiti dukkan su. Sai da Likitoci sukayi da gaske tukunna suka samu numfashin sa ya daidaita…
Bai farka ba sai bayan kwana hud’u amma ya samu stroke mai k’arfi dan hatta bakinshi da hancinshi sun koma b’angare daya a fuskarshi.
Idan ka ganshi abun tausayi dole kayi kuka, Likitocin ne suka yi ta basu kwarin guiwa akan zai dawo daidai da yardar Allah da taimokon therapy da excercise d’in da za’a d’aurashi akai.
A hankali ahankali zai dinga samun sauk’i in sha Allah.
Hakan kuwa akayi dan jikin nashi da kad’an kad’an ya fara gyaruwa…
Ya Usman kuwa shaye shaye ya fara gadan gadan babu kama hannun Yaro, cikin wata uku ya lalace gaba d’aya, tun iyayen basu fahimta ba har suka gane, Ya Usman wanda a daa yake fari tass yanzu kam sai ka k’ura ido tukunna zaka iya tantance hasken fatar tashi, dan sai dai a kirashi da chocolate colour, duk ya yamushe ya fige ya rame over!!! Da aka yi k’ok’arin hanashi sai ya nemi haukacewa, dan basu saniba ashe abun ya shiga jikinshi sosai, idan yazo sha ashe shi over dose ma yake yi!
Shiyasa yanzu abun yake neman tab’a kwakwalwasa, ko zuwa kayi kusa dashi idan bakayi masa ba sai dai kaji duka!! Wannan dalili ya sanya kowa yake tsoron rab’arsa, Sadiya! Kad’ai ce take iya zuwa inda yake, duk da kuwa itama d’in idan taje sai ya mareta ko yayi mata duka amman bata gajiya….ita zata je ta kai mishi abinci ta share mishi d’aki ta wanke mishi band’aki!. Tun Laraba da K’asimu suna hanata suna zaginta har suka daina badan suna so ba sai dan rashin kunyar da take zuba musu a duk lokacin da suka so hanatan kuma ba yadda za suyi da ita.
Watan Madu hud’u yana fama, da ikon Allah a wata na biyar ya warke dama anata samun cigaba a hankali a hankali. Bayan ya dawo gida hankalinshi yayi matuk’ar tashi da halin da yaga Usman shiyasa ya duk’ufa ya dinga yi mishi addu’o’i ta tofi, a hankali a hankali kafin wata d’aya shima Allah ya bashi lafiya amman dai kana ganinshi ka san yana cikin damuwa saboda lokuta da dama ma idan ka shiga sai dai ka tarar dashi yana kuka…
D’agawa K’asimu hankali da Sadiya tayi ne yasa ya taso ya zo wajen su Madu akan maganar ta da Usman d’in.
Da ‘to’ kawai suka bishi amman ko suna hauka baza su
bari su had’a Jini da K’asimu ba….dan a lokacin da Al’Amarin Maryam ya faru shi yafi kowa zak’ewa, kusan shi ya yayata maganar ma har kowa yaji, kuma ya tsaya tsayin daka saida aka hukunta Madu
(Da kyar ma aka barshi ya cigaba da sama a unguwar dan da cewa sukayi Madu sai ya bar unguwar).
Sannan sam K’asimu bashi da hali mai kyau!
Shima Usman duk da alkhairin da Sadiya tayi mishi hakan bai sa ya amince da auren ba, dan shi yanzu sana’a ma zai yi ya tara kud’i ya tafi Madina neman Maryam! Sai ya dawo da ita ko da bala’i ne.
Shiyasa ranar da Sadiya tazo mishi gyara, yaji tausayinta dan sai nan nan take yi dashi, dan haka ya yanke shawarar ‘gara ya fad’a mata gaskiya’ saboda a yanzu yana ganin mutunci ta ko ba komai ita ta kula dashi a lokacin da kowa ya k’i shi.
Zaunar da ita yayi ya fad’a mata cewa “shifa babu maganar aure a tsakaninsu, akwai abinda yasa a gabanshi, in ma saboda haka ne taketa kula dashi gara ma ta daina ta nemi wani suarayin tayi aurenta!. Amman yana mai tabbatar mata da bazai tab’a mantawa da irin alkhairin da tayi mishi ba, har abada!! Ya gode ya gode sosai.”
Kuka kawai yaga ta fashe mishi dashi, da kyar ya samu ya lallasheta, ta tashi ta tafi gida.
Tana zuwa gida ta tarar da Baba Laraba da dillaliya suna hira a tsakar gida da gudu ta fad’a kan Baba Laraba tana rusa kuka, nan ta koro mata abunda Ya Usman d’in yace..
Baba Laraba ce ta hauta da fada tana cewa “idan ita ba mayya baceba to ta hak’ura da Usman.”
Dillaliya ce ta katse su ta cewa Sadiyan “ta tashi ta tafi ta daina kuka” sannan ta matso kusa da Baaba Laraban ta rad’a mata wasu maganganu….
Bayan kwana uku da safe, sai ga Baaba Talatu tazo gidansu Sadiya, da yamma Baba Bashir da Ya Jamilu, duk akan neman auren Sadiya….har wani b’oyewa