SO DA BURI BOOK 2

Chapter 13 of 39

farko yana shigowa zata fara kuka!! Sai kuma ta dawo ihu!!! Daga k’arshe dai ko asibitin in Aslam ya shigo tun kafin ya k’araso inda take zata hau kururuwa tana kuka
kowa ta nan ne yake gane Aslam ya iso!
Wani abun mamaki shine ta warke garau ta fara magana ta gane kowa amman fa ko a labari idan aka sako Aslam tou yanzu hankalin kowa zai tashi!!

Ba k’aramin kid’ima Likitocin suka yi ba dan su kansu sun zama confuse..A iyaka sanin su masu irin wannan matsalar basa haka amman duba da suka yi da shi ta fara ganewa a lokacin data farfad’o ya sanya suka yi y’an bincikensu, iya abunda tunanin su ya basu ne ya sanya su dangantata da psychiatric.

Allah sarki Aslam, a lokacin
sai da ta kai ga shima aka bashi gado a asibitin tsabar tashin hankalin daya shiga.
Yaro ne shi a lokacin amman kasancewarshi mai kaifin basira yasa ya fahimci komai.
Dan zan iya ce miki har yau ban tab’a ganin Yaro mai wayo tarin ilimi da kaifin basira irin Aslam ba, har gobe in da wani d’an ajinsu da suka yi makaranta zai zo gidannan to ba zaki tab’a ji ya kirashi da aslam ba , sai dai suce mishi ‘gifted’
Dan wani abun time d’in a makaranta ba sai an koya mishi bama yake iyawa, in kuma ya iya to ya zauna kenan!
Ga wayo kamar wani d’an shekaru dayawa.”

Ajiyar zuciya Gwaggo Asabe ta sauk’e sannan ta ci gaba
“A lokacin hankalin kowa a tashe yake, ni kaina da nake nan da ban ganta ido da ido tana haukan ba sai da naji a jikina, abu yak’i ci yak’i cinyewa har aka shafe wata biyu a haka, ga Aslam a kwance…
Tausayin shi da ya lullub’e Granpa gashi yana ganin yana neman mutuwa
ne
yasashi fara nemawa Aisha magani gadan gadan ba kama hannun Yaro, duk inda yaji labarin Likitan kwakwalwa nan zai tarkata su su nufi k’asar! Cikin shekara biyu zan iya ce miki sun kusa zagaye duniya dan ba k’asar da ba a je ba, in dai kinajin ta kuma sananniyace.
Amman dukda haka Allah bai kawo sauk’in ba, saboda lokacin samun sauk’in bai yi ba.
Daga karshe dai hak’ura suka yi suka dawo gida Nigeria.

Ai ana dawowa abun yafi na daa, ba k’aramin tsorata muka yi ba dan nima nazo a lokacin…Idan Aslam baya gidan nan to k’alau amman ko bakin MT yazo yanzu zata birkice, abun tausayi In kana nan dole kayi kuka, don Aisha mahaukaciya tuburan ta koma.

Shawara d’aya Granpa ya yanke shine na ‘kai Aslam boarding school’
don samun sauk’in kowa and ya kamata yaci gaba da karatu kuma ya maida hankali saboda an barshi a baya sosai…
A lokacin shekarunshi sun haura 14.

Da kyar Aslam d’in ya yarda, ya tafi bayan Granpa yayi mishi alkawarin ‘duk inda magani yake a duniyar nan in dai akwaishi to zai nemawa Mommy d’insa, ko nawa ne kud’in ba zai gaji da biya ba, koda kuwa zai k’arar da duk abunda ya tara ne!!!’.

Haka nan aka tarkata Aslam aka kaishi boarding cikin tsananin k’unci, yana kuka
muna kuka ba dan munso ba.

Wani abun takaicin ko hutu Aslam bai isa ya zo ba, sai dai In kana buk’atar ganinshi kai kaje ka ganshi a inda yake, k’iri k’iri zaman estate d’innan ya gagareshi…
Ganin abun na Aisha bana k’are bane yasa suka kira wani babban Likita daga k’asar waje har gida Nigeria ya dinga kula da ita, shi ne ya bada shawarar a kulle su ita da Aslam a d’aki d’aya su kad’ai, for 24 hours, to kuma abun bai yi dad’iba don shi yayi sanadiyyar da Aslam ya bar k’asar nan wanda sai yanzu ne Allah ya dawo mana da shi!

Da farko an tsara akan zai d’an dinga lek’owa Hutu sai yake sauk’a gidan Abba, yadda ba zasu had’u da ita ba, har zuwa lokacin da Allah zai kawo sauk’i
Amman abunda ya faru a wannan rana ya sanya Aslam yin yaji mai mugun tsayi ya tarkata komai nashi ya tafi
sai dai waya, shima wani lokacin sai yake gudun d’auka!.

Arshaad da su Abba suna yawan zuwa duboshi, Auwal ne ma yaje sau d’aya, amman Arshaad a shekara ma yakan je sau biyu shi da Abba..saboda shi Aslam
ko hutu idan anyi na makaranta baya iya dawowa sai dai yayi achan Oxford Uni inda yayi karatunshi.

Aslam a Oxford yayi karatu,
Arshaad kuma Dubai aka kaishi Auwal kuma Cairo.
Da yake Granpa ne duk ya kaisu..duk da halin da Aslam yake ciki sai da aka fara k’ananan maganganu, Adama da Ummi, wai ‘har yanzu Granpa bai daina nuna bambanci ba’
Sosai Granpa da maganar ta koma mishi yayi musu tataas!!!Kuma ya taso da maganar mallakawa Aslam MT gaba d’aya inyaso sai yaga me za suyi!.

Da kyar da sid’in goshi Gramma ta tausheshi, sannan ta lallabashi, sannan tai k’ok’arin fahimtar dashi abubuwan da hakan ka iya janyowa….
Awannan lokacin kuwa anci sa’a ya fahimceta sosai, don da kanshi kuma ya dawo yace ‘a tsakanin Auwal Arshaad da Aslam, duk wanda yaga he’s capable to shi zai mallakawa MT’.
Dad yayi mugun mugun yin farin ciki daga jin wannan decision na Granpa, bawai yana zargin wani ba, kawai dai yaji releaf, kuma shima baya son bambancin da Granpa d’in ya dad’e yana nunawa especially tsakanin Arshaad da Aslam, don duk abun nan da ake yi ko sau d’aya Arshaad bai tab’a nuna b’acin ranshi ba, dukda kuwa uba d’aya ne ya haifesu shi da Aslam d’in,
Idan akwai fitinanne tou Auwal ne!
Amman Arshaad shi ba ruwanshi yana da kauda kai
kunyarshi ce ma ta sanya Dad yake yiwa Mahaifiyarshi wani abun dan kar yaga ga kamar bai damu da ita sosai ba.
Kowa idan zaki tambaya a estate d’innan ya baki sheda akan Arshaad to zai ce miki ‘yanada hak’uri da kauda kai da kuma saurin yafiya’.


Aslam yana kammala degree na farko aka d’aura shi a matsayin MD na MT branch d’in dake achan k’asar da yake, wanda ada Abba ne a wajen.

Ayyuka Aslam yake yi bashi da lokacin kanshima,
kuma daman hakan yake so dan hakan ya tsarawa kanshi tun farkon komawarshi UK d’in,
yana k’ok’arin kullum yaga ya zama busy dan kar ma ya bawa kanshi daman yin tunani..
Aikin kuwa ya taimakeshi ta b’angarori da dama
dan
Yana da nashi campny d’in a chan, na sarrafa takalma wanda k’wazonshi guminshi da kuma taimakon Granpa wanda yake aika mishi kud’i kamar hauka suka taimaka
masa ya had’a ya bud’e
wanda yanzu naji suna cewa yanaso ya bud’e wani branch d’in anan ko kuma ya dawo nan ma, gaba d’aya. Kuma akwai wani daban da zasu bud’e na zanen gidaje shi da Abba!
Ga mt ga kuma karatu wanda a yanzu ya kammala PHD d’inshi…
A b’angaren nasarori Aslam ya samu kam ba a magana sai dai kuma shi duk basa gabanshi, inda za ace ya tatttara ya bada abashi lafiyan Mahaifiyarshi na tabbatar kafin k’iftawar ido zai iya sallama komai!
Ba shi kad’ai ba hatta mu duk tsawon wannan lokacin buri daya muke da shi shine ‘Aisha ta warke hankalin kowa ya kwanta’
Dan shi kanshi Aslam d’in abun a jiye mishi ne, saboda gaba d’aya rayuwarshi ya yita ne cikin fargaba, k’unci da damuwa. Yanzu haka ko Abokanai baya iya tarawa shi kad’ai d’insa yake komai
sai dai a d’an dinga zumunci sama sama, Abokin shi na k’ut da k’ut guda d’aya tak a duniya wato Arshaad, da Arshaad ne kawai za kiji suna waya suna d’an raha amma ko mu y’an gida wani lokacin idan ka kirashi sai yak’i d’auka.
Tsoronma shiga mutane yake yi balle yayi huld’a dasu..
Naji su Abba suna cewa
‘Kana ganinshi in dai ka fahimci yanayin shi tou tashi d’aya zaka fahimci he’s depressed! Kuma hakan ba a so a mutum especially mai k’arancin shekaru kamar nashi, zai hanashi yin farin ciki a rayuwa ne kwata kwata, har abada!.”

Ahankali tace
“To amman ya za ayi? Magani in dai sunanshi magani tou ba kalar wanda ba ayi ba amman har yanzu shiru............”
Ta k’arshe maganar tana share d’an hawayen daya biyo idanunta a karo na ba adadi.

Hudan, itama hawayenta ta goge, a ranta tace “Allah sarki bawan Allah, ashe shiyasa kullum yake cikin fushi, da har nake jin haushinshi..
In shaa Allah daga yau na daina jin haushinshi, Allah ya bawa Mahaifiyarta lafiya.”
Maganar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa
“Kema dan Allah idan kin yi sallah ki dinga sakamu a addua Allah ya kawo k’arshen wannan abu.”

A hankali Hudan ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“In shaa Allah”
Sai kuma ta gyara zamanta ta ci gaba “Amman Gwaggo a duk cikin bayaninki banji inda aka yi mata Sauk’ar Alqur’ani ba!”
Cikin katseta Gwaggo Asabe tace “anyi sauk’a Huda, Granpa da Dad da kansu suka je suka raba kud’i lokacin da suka dawo farko farko a islamiyoyi da tsangayar almajurai aka yi ta sauk’a!.”

Murmushi Hudan tayi sannan tace “Gwaggo Asabe, idan zan bada shawara a d’auka inaga daa mu da kanmu ya kamata muyi mata sauk’ar bayan an raba a islamiyoyin, kuma in na fahimceki kamar sau d’aya aka tab’a yin sauk’ar ko?”
Bata jira jin mai Gwaggo Asaben zata ce ba ta ci gaba
“Ni a lokutan baya, idan bamu da lafiya ko wani alamari mara dad’i ya afku
Tou bayan Mama ta bamu magani sai ta kammala mana sauk’a, ko lokacin da nake k’arama akwai Yayanmu da yake shaye shaye sai da Mama tayi mishi sauk’ar AlQur’ani sau bakwai!!
Ta fara tayi sau hud’u ya warke ya daina amman dake tayi niyyar bakwai d’in zata yi sai da ta k’arasa.
Da kuma muka yi wayo haka zata rarraba mana muna tayata da ni dasu Ya Jalila koda izu d’ai d’ai ne mu kan taimaka.
Ko yanzu haka In wani abun ya faru rabawa muke yi ni da ita da Sakina wani lokacin da Sumayya, bama wata d’aya muke k’arasawa, in kuma mun kwallafa to a sati muke idawa.
Balle nan gidan munada d’an yawa..
Yanzu for example ace mutum shidda kowa ya d’auki izu goma, duk bayan sallar Farilla kayi izu d’aya a kwana biyu fa za mu dinga kammalawa, In kuma izu biyu za ana yi a cikin kwana 1 mun kammala, inda hali kowa in ya kammala sai yayi mata addua dafatan waraka bayan an tofa aruwa a bata tana sha,
Daganan ayita yi, kuma akai akai.
In Allah ya yarda sai kiga an dace.
Dan dai gaskiya kamar yadda kika fad’a abun sam kamar bana asibiti bane ba!
Koda ace ma na asibitin ne Sauk’ar Alqur’ani fa shine k’arshen waraka
Especially idan mune muka yi da kanmu, saboda waennan na islamiyya ba mu da tabbas, yanzu duniya ta chanja ba lalle In sun karb’i kud’in suna sakawa anayi ba…..”
Maganarta ce ta katse jin mutum a tsaye a bayanta ya dafa kanta, tana juyowa sukai ido hud’u da Dad
da Abba a bayanshi suna murmushi, waenda shigowarsu kenan suna d’an tatauna wata magani suka ji bayanin Hudan.

Dad ne yace “y’ar albarka, naji dad’in wannan shawarar taki sosai.
Kuma daga yanzu in shaa Allah zata fara aiki.
Kafin masu kwashe kaya su gama na san mun kammala in shaa Allah, na yau.”
Yana gama fad’in haka ya d’au waya ya kira Arshaad da Aslam yace “su sameshi.”

Sai da ya gama wayar, Hudan ta d’an zame daga kan kujera inda take ta shiga gaida Abba. Shima Dad d’in ta sake gaidashi.
Cikin kulawa suka amsa mata sannan suka cigaba ta tattaunawarsu da alamun magana mai muhummanci suke yi.

Hudan sai d’ar d’ar takeyi a tunaninta kar Abba yai mata fad’an abunda tayi mishi jiya, shima ya lura da yanayin ta shiyasama ya fasa zuwa inda take, amman da yayi niyyar jin yadda ta kwana da kuma jin ko akwai abunda takeso dan harga Allah shikam yana so ya zama tare da y’arsa ya jaa ta a jiki ko sa samu su saba da juna sosai.

Arshaad ne ya fara shigowa…
Tsayawa Hudan tayi tana kallonshi dan ta manta rabon da ta ganshi da k’ananan kaya, yafi ta’ammali da shaddodi da yadi, sab’anin yau da yake sanye da wata shirt army green dark an rubuta ‘KING’ a jikin gaban rigar da zanen crown d’in king d’in ata k’asa.
Rigar irin mai d’an kama jiki ce, hakan ya taimaka wajen fito da ainahin surar jikinshi dan kana iya hango packs d’inshi na sama sama ta cikin rigar da yadda dantsen hannunshi yake a mummurd’e!
Wandon nashi shima ba jeans bane yana yin rigar ne black in colour bai kamashi ba kwata kwata ta sama amman roba ne, kasancewar ya d’an matse daga guiwar wandon zuwa k’asa yasa ya zama kamar pencil trouser ta k’asan…
Kayan yayi matuk’ar fito da asalin surarshi ta giant!
Ga wani fitinannen k’amshi mai tsayawa a rai da yake zubawa
dan tunda ya shigo parlourn ya karad’e da k’amshin shi, tun bai iso inda suke ba….
Hudan bata gama k’are mishi kallo ba suka had’a ido da shi,
gira d’aya ya d’aga mata yana d’an murmushin gefen baki, da sauri ta sunkuyar da kanta k’asa kunya duk ta lullub’eta ganin ya kamata tana kallonshi .
Ganin yadda tayi ne ya sanyashi sakin wani lallausan murmushi, kafin ya k’arasa inda su Dad suke ya shiga gaidasu cikin girmamawa. Ya so ya k’arasa wajen Hudan dan shima ba k’aramin kyau tayi mishi cikin rigar abaya blueblack mai stones, d’aurin da ta yiwa kanta da d’ankwalin abayan ya yi matuk’ar burgeshi!
Amman sai Dad ya tsareshi ta hanyar fara yi mishi bayani abunda za suyi ba tare da b’ata lokaci ba, 100%ya amince da kuma jinjina ga wanda ya kawo shawarar dan abunda ya kamata ayi kenan, cikin jin dad’i Dad yace “ai Hudan ce”
da d’an murmushi ya juyo yana kallonta, yanzun ma sauri tayi tai k’asa da kanta, don still satar kallonshi take yi, harga Allah Ya Arshaad yayi kyau yau sosai……

Tana wannan tunanin hancinta ya fara jiyo mata wani k’amshi na daban, wanda a take ya cika mata hanci, kuma ta fahimci wanene
Kasancewar a kan kujerar dake gaban side d’inshi take ne yasanya ta fara jin k’amshin kafin kowa, bata san daliliba ba kuma tasan mai ya faru ba, amman ko lokacin idan anyi laifi a islamiyyarsu za a dakesu tabbas zuciyarta bata yin kalar bugun da take yi a yanzu….
A hankali ta runtse idanunta ta sake yin k’asa da kanta jin takunshi a daf bayanta!Sannan bugun zuciya da k’amshin da yake shak’a na k’ara yawa….
Kamar yadda Arshaad yayi shima hakan ya gaida su Dad waenda suke ata gefe kad’an kusan hanyar shigowa sai dai shi bai k’arasa inda suke ba, hasalima zagayowa yayi ya zo kan kujerar da Gwaggo Asabe take ya zauna..
Kasancewar Gwaggo Asabe a 3 seater take zaune Hudan kuma a 1, sai ya zamana kamar suna facing juna shi da Hudan!
A hankali ya d’ago idanuwanshi ya sauk’e su a kanta, da tayi k’asa da kai wanda ita kanta ta kasa tantance dalilinta na yin hakan

Magana Gwaggo Asabe take yi mishi amman kamar ma baya jin ta, ganin hakan yasa ta d’an tab’a shi kad’an..
Lumshe idanunsa kawai yayi kafin ya bud’e su ya sauk’e a kan Gwaggo Asabe, d’an murmushi kad’an yayi mata kafin yace “barka da gida”.
Cike da tausayawa Gwaggo Asaben take kallonshi, ko ba a fad’a mata ba ta san tun d’azu da ya fito daga d’akin Mommy yake cikin tashin hankali!! Dan gashi idanuwanshi sunyi jaaa sosai bakinshi yayi pink shima hatta kan hancinshi yayi jaaa
Amman kuma ko ba a fad’a mata ba ta san ba kuka yayi ba
wanda wani lokacin har addua take yi Allah ya bawa hawaye ikon fitowa daga idanun Aslam ko ya samu ya rage rad’ad’in da zuciyarshi take ciki.

Hannunta ta d’aura akan lallausan gashin kanshi ta d’an shafa…
Hakan ya sanya shi sake maida hankalinshi a kanta!
Tana shirin yin magana
Dad ya fara yiwa Aslam bayanin abunda ya tarasu anan bayan ya zagayo ya zauna,
Abba ma ya zauna.
Ajiyar zuciya Aslam ya sauk’e bayan ya gama sauraron Dad wanda ya k’arashe maganar shi da cewa
“Zamu fara yanzu saboda mu samu mu gama akan lokaci kafin a gama Parking su Abba su tafi”
A hankali ya juya ya kalli Abba kafin yace
“Abba ka bari I’ll speak with Granpa, dan Allah don’t leave.”
Murmushi Abba yayi ya mik’e daga kan kujerar da ya zauna ya k’araso inda yake kafin ya dafa kanshi tukun yace
“Karka damu Aslam, ai bamu da nisa anytime kakeso zaka iya visiting, ni kaina i need some time with my daughter, wanda in muna nan na san Granpa ba zai barni ba, and ya dinga k’untata mata kenan, ni kuma from this time forward inaso In bata cikakken kulawa da happiness d’in da ban bata ba a baya, so we need some space from him, Daddy kuma he wants to leave ne saboda yaci ace Granpa ya fara rage abubuwan da yake yi.
In bamu tashi mun tsaya munyi mishi haka ba, al amarin family d’innan ba zai tab’a daidaituwa ba!
I hope u understand”
Yayi maganan yana shafa kanshi, a hankali Aslam ya sauk’e ajiyar zuciya a karo na ba adadi sannan ya d’auke idanuwanshi daga kan Abba wanda tunda ya fara magana ya kafe shi dasu, a hankali
yace “shikenan” sannan ya mik’e ya wuce zuwa inda ya fito yana cewa “zan fara daga Fatiha zuwa Nisa’i ayat 147!
Someone should continue from were i stop.”
Yana gama fad’in haka ya shige ya jawo k’ofar shi ya zuge.

Dad ne yace “Abba ko zaku tafi tare, kasan yadda kuka saba da shi, and ga incidence d’in daya faru d’azu kar abun yai mishi yawa”

“Ba zai yarda ba but let me try”
Inji Abba, ya mik’e yana k’ok’arin shiga side d’in Aslam d’in.

Dad ne yace mishi ya tsaya tukunna…
Sai da suka tsara yadda za

Download complete TXT · Novel page