SO DA BURI BOOK 2

Chapter 15 of 39

alak’a da shi ba?
Eh?
Kika barni a duhu?”

Cikin rashin fahimta tace
“Wallahi ni ban gane komai ba!
Dan Allah ka fahimci ni”.

Shiruuu, Auwal yayi yana d’an nazartarta yana kallonta..
Chaaan! Kuma yayi tsaki kafin yace “kije ki tattaro kayan ki,
ki wuce wajen Gwaggo Asabe, i’ll get back to you, idan kuma zaki zauna anan d’in ne to zan iya barinki but ki tuna abunda na fad’a miki d’azu!”.

Da sauri ta nufi d’akin ta na sama, kafin minti goma ta tattaro komai…


Auwal ji yake kamar ya shak’e ta yayi ta dukanta!
Kawai dai ya barta ne ya samu ta rabu dashi for now dan bayaso Daddy yazo kiranshi da kansa!
Amman tabbas sai ya koya mata hankali, dukda ya fahimci kamar jahilcinta da dak’ik’ancinta ne ya janyo komai..................



A gate d’in estate ta had’u da su duk sun fito har Gramma wadda ta kawo su Shuraim
don tun jiya da suka k’i bacci
da safe kuma suka dinga yiwa Abba kuka akan suna son Ummi ta dawo, ya kaisu wajenta.
Da kyar ta lallab’asu
bayan tace musu “Ummin tayi y’ar tafiya ne
amman soon za su dawo, suyi hak’uri.”

Hudan tana k’arasowa Gramma ta kamo ta, tace
“Ki kwantar da hankalinki
Ki bisu kinji, na san kina kewar Maman ki, amman na san Abba da kansa zai kaiki idan komai ya gama daidaituwa, kinji y’ar albarka?”.

Anhankali ta d’aga mata kai tanajin k’aunar matar da girman ta suna ratsa zuciyarta.
Dad shima abunda ya fad’a mata kenan sannan yace “duk abinda take buk’ata idan sunje ta rubuta ta bawa Arshaad ya kawo mishi,,already anyi mata d’an siyayyan abubuwan da zata buk’ata for now suna cikin mota.”
Da “to” da kuma godiya shima ta amsa mishi.

Auwal yana fitowa daga mik’a Jalila wajen Gwaggo Asabe suka fara shirin tafiya…
Abba ne ya bud’e mata gaban wata mota yace ta shiga, tana shirin shiga dai dai nan Gwaggo Asabe wadda ta fito yanzu ta k’araso taja Hudan tayi hugging d’inta, ji suke kamar kar su rabu dan har sun saba a cikin y’an wuni biyun da suka yi tare.

Auwal yana gefe in banda tab’e baki babu abunda yake yi, ji yake kamar yaje ya shak’e ta! Shi fa ya tsani yaga ana fifita wani, kuma ya lura kamar hakan a jinin y’an gidan yake! k’iri k’iri sun iya nuna banbanci…..gashi yanzu ma akan y’ar k’ank’anuwar Yarinya an kwashe Surukan gida kaf! An kai cell, an bar mahaukaciya!….
Ya ja tsaki yafi a k’irga k’arshema mota ya shige yana ta mita a ranshi yana cewa
“Kamar duk ba a tsatso d’aya muka fito ba!”
Mu an maida mu kamar wani bole especially ma ni….kowa idan ya tashi k’orafi sai kaji yace ‘Auwal’.”
Shi kad’ai haka yayi ta mita yana ta faman kumbure kumbure..


Su kam bama su san yana yi ba. Sallama suka yiwa juna
kafin Gramma ta ruk’o hannunta (Hudan) da kanta ta saka ta a mota ta juyo.

Daurewa kawai take yi, amman Abba yana zuwa da yayi hugging d’inta sai ta kasa ci gaba da daurewa ta fara hawaye.
Da kyar suka lallasheta sannan suka maidata gida,
suka fito, suka kama hanya ba dan ransu yanaso ba, suka
fice a estate d’in suna masu jin dumbin kewar gida cike a zuk’atansu.

Suna fita suka had’u da motar Kaka da Madu, horn suka d’anyi musu don haka suka dakata!
Dan shi Abba bai ma gane su ba.

A D’an gaba kad’an suka yi parkin, dan haka suma su Kaka suka juyo da akalar motar tasu suka isa inda suke suka yi parking….

Suna fitowa Abba ya ganesu dan haka ya k’arasa ya cewa su Aslam su zauna a motar,
shi da Dad kuma suka fita suka samesu.

Suna wucewa itama Hudan ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar amman sai ta jita a rufe!
Cikin d’an tsare gida tace “zan je wajen Kakannina!”

A k’ufule yace
“Baza ki ba!”

Wani takaicine ya rufe ta taji kamar ta rufeshi da duka, taya ga su Kaka tana kallo suna kallonta, amman ace ba zata je wajensu ba? Inaaa, ba zai yiu ba!
Dan haka ta fara k’ok’arin bud’e k’ofar ta k’arfi! Tun k’arfinta.

Ta gefen ido yake kallonta,
tanata dambe da handle d’in motar, tun k’arfin ta.

Ta fi minti biyar tana fama ganin ta kasa yasa ta juyo da d’an ladabi tace
“Ya Aslam dan Allah ka bud’e inje wajen su mana.”

Ta bashi dariya sosai amman ya danne, still amsar d’azu ya sake maimaita mata babu alamun wasa a fuskarshi
“Baza ki ba!”

Wani k’ululun takaici ne ya tokare mak’ogwaronta, dama ga haushin Arshaad da take ji tun d’azu!
(Don Abba har yana shirin shiga motar da take amman ya janyeshi yace “yazo zai tuk’a shi”)
Yanzu gashi ya had’ata da wannan boss d’in!
Shi bai bari ta tafi da Abba ba kuma shi ma ya kasa shigowa su tafi tare ko dayake ta san
saboda yana jin kunyar had’a ido da ita ne shiyasa!
Kuma ya san koda ya shigo d’in ma fita zata yi ta bar mishi motar dan haka d’in ta gama shiryawa a ranta.
Amman kuma at least ai da ya gwada
Insted
yana kallonta amman ya shige motar Abba yaja suka tafi da shi da su Shuraim..
.....Abunda Huda bata sani ba shi kuwa Arshaad fushi ya d’auka da ita bana wasa ba ata dalilin zargin da tayi mishi!.


Bata iya rashin kunya ba amman bata san lokacin data tak’ark’are ta zabgawa Aslam wata uwar harara sannan ta murguda mishi baki ba!
A tunanin ta su Abba yake kallo dan direction d’insu taga yana kalla
amma abunda bata sani ba shine duk abunda take yi yana kallonta ta gefen idonshi.
Tunda yake a rayuwarshi bai tab’a ganin harara da murgud’a bakin da yayi matuk’ar burgeshi da bashi dariya irin wannan ba, hakan ya sanya wani sassanyan murmushin da ya dad’e bai yi ba wanzuwa akan kyakkyawar fuskarshi, wanda har sai da Hudan taji sautin murmushin tayi saurin juyowa tana kallonshi amman ga mamakinta sai taga still su Abba yaketa kallo waenda suka tsaye a setin su..
Gani tayi kamar Madu yana magana da fad’a fad’a!
Cikin takaici ta juyo tana kallon Aslam a ranta tana aiyyana “wato dan yaga ana fad’a shine yake murmushi, lallema wannan mutumin!.”

A chan wajen su Madu kuwa abu bai yi dad’i ba!
Dan tun farko da Madu ya tambayi Abba “dalilin da yasa ya d’auko Hudan lokaci guda haka?”
Abba ya k’ule!
A ganinsa dan mai yasa Madu zai yi mishi tambayar ‘dalilin d’aukar y’ar sa da yayi’ bayan shekaru da dama da yayi ba tare da ita ba!.

Daga k’arshe dai, Abba tafiya yayi ya bar wajen dan bayason yayi musu rashin kunya.

Daddy ne ya tabbatar musu da “sunje har unguwar da Hudan ta taso kuma sunji irin zaman da Huda tayi a gidan Baba, wajen mutane bakwai suka tambaya amman duk maganarsu d’aya ce! Ba abunda basu saniba a halin yanzu na irin zaman da Hudan tayi na azaba a hannun mutumin nan, har k’usar da Ja’afar ya buga mata a ciki suna da labari!”

Yace musu
“Tun jiya suke ta faman lallab’a Abba, da kyar suka samu ya hak’ura amma daa cewa yayi sai ya kulle Usman kuma yayi shariah da su!”

Daga k’arshe yace musu
“Dan haka, ko kotun da Madu yake ik’irarin zai je sai dai ya kulle kanshi da kanshi dan wannan dalili kad’ai ya isa a barma Abba custody d’in Huda!.”
Yana gama fadin haka shima yayi musu sallama cikin girmamawa ya wuce ya koma mota Auwal ya ja suka yi gaba suka barsu a wajen, daman su su Abba sun dad’e da wucewa.


Tunda suka shigo gidan Huda take bin had’add’en mansion d’in mai hawa biyu da kallo!
Har Aslam ya gama parking bata sani ba, sai da yace
“Na bud’e lock d’in, ki fita sai kin fi jin dad’in kallon!”

Tukunna ta dawo hankalinta, gaba d’aya kuma sai kunya ta lullub’eta.

A hankali tasa hannu ta bud’e ta fito, still mutane waenda suka kwashe kaya daga chan gidan sunata kai kawo, da alamun basu gama jeran ba, dan gashi har sets d’in kujeru wasu ba a shishshigar ba.
K’ofar shiga gidan biyu ne manya manya!
Kamar yadda Dad ya fad’a gidan wajen zaman mutum uku ne ma amma k’ofar farko ta gefen dama yafi girma dan wajen d’akuna sha biyar ne da faluka bakwai (shine mutum biyu zasu iya using dan hatta kitchen biyu ne)
Sai d’ayar k’ofar gefen hagu ta d’an gefe kad’an na d’auke da 7 bedrooms da 4 parlourns.

Mai girman Abba ya d’auka
Daddy kuma ya nufi d’ayar k’ofar (side d’in mutum d’aya wanda bai kai na Abba ba).

Suna shiga Hudan ta kusan daskarewa…
Dukda gidan chan estate d’in shima yana da double height ceiling amman ko rabin wannan bai kai ba, ga wata mahaukaciyar chandelier da tunda take bata tab’a tunanin akwai irinta ba, wasu irin kwayayene da suke k’ok’arin makantar da ita tsabar haske a gidan!
Waiting parlour yana a ta gefe a cikin wani d’an glass door
kafin ka k’arasa shigowa makeken main parlourn k’asa wanda girman parlourn zai iya cin set d’in manya manyan kujeru 6 ko bakwai!
Gefen dining daban, sai
wata had’add’iyar matattakalar bene doguwa da zata kaika sama.
K’aramin Kitchen d’in na ata gefen waiting parlour kana iya hango cikin shi dan bangon half ne bai kai har chan sama ba
Main kitchen d’in kuma yana ta gefen dining
Amman shi rufaffiyar k’ofa babba gareshi.
Akwai wasu k’ofofin still a cikin parlourn wanda take da tabbacin d’akuna ne.


Sama suka yi gaba d’ayan su,
Parlour ne nan ma biyu
d’aya a gefen dama d’aya a hagu masu masifar kyau, dukda basu kai na k’asan girma ba saboda double height ceiling d’in da aka yanka ya cinye kusan 1/3 d’in saman amman suma sun had’u sosai ba a magana!
pop kam kamar ka kirashi ya amsa ta jikin bango ta ceiling hatta k’afar bene shima ba
a barshi ya huta ba.

Wata matattakalar suka sake bi suka hau chaan sama.
Suna hawa suka nufi side d’in su Sudais, d’akunan su da parlourn su yayi matuk’ar burgeta.
Sudais yanata murna Shuraim kuwa miskili bai ce komai ba
Sudais shi a shirmen shi ya d’auka har da Huda, dan haka ya hau tsarawa
‘Za su d’auki d’aki daya ita kuma ta d’auki d’aya, sannan ya cewa Abba “ai da anyi mata nata gadon pink ba kalar blue ba”…’

Dariya dukkansu suka yiwa shirmen shi, kafin Abba yace “a’a ita nata d’akin daban ne bara in kaita in dawo ko?”
Yana shirin fita yaji Shuraim yace
“Abba yaushe Ummin zata dawo?
Gramma tace za kaje ka d’auko ta”

A lokaci d’aya duk suka d’auke wuta..
Gaba d’aya duk sai Hudan taji ba dad’i, yadda taga Abba ya had’e rai ne yasa ta kasa cewa komai
“Bana son yawan tambaya!”
shine abunda yace daga nan ya fice daga d’akin.

Ganin haka yasa itama Hudan tayi musu sai anjima ta fice..
Tanata kallon parlourn nasu har ta fita, ta jaa musu k’ofa ta rufe.

Sai a sannan Abba yace “tazo suje ya kaita d’akinta” yana mai kama hannunta.
A gefen parlourn da suke a ciki suka shiga wani dogon corridor, k’ofar tana achan k’arshe suna isa ya sa hannu ya zura key ya murza k’ofar ta bud’u! Sanna ya jaa hannunta suka shige ciki.

Set d’in kujeru biyu ne
Peach da black, sai wani d’an k’aramin dining mai mugun kayau mai d’auke da kujeru biyu a gefe, da wata had’add’iyar tv babba mai curve.

Wucewa sukayi suka shiga bedroom a nan ta sake shiga mamaki, gadon nata pink ne mai rumfa da net a jiki (princess tent) ga wasu had’add’un resting da coffee chairs guda bibbbiyu a kusa da tvn bedroom d’in, fad’ar had’uwar d’akin kawai sai wanda ya gani! Kawai.

Still toilet d’inta ya nufa da ita don ya nuna mata…
Ta closet suka bi kafin su isa cikin toilet d’in
A nan kuwa ta saki baki, wajen wanka har uku shower da wani had’add’en jacuzzi, sai kuma wani makeken bathtub da mutum hud’u ma za su iya shiga su kwanta kamar gado
da
Showers a jikinshi ta ko ina.
Ba abunda yafi bata mamaki irin wutan pop da take gani na sama, da taga yana ratsowa ta k’asan toilet d’in toilet d’in ta ko wanne angle.

Bata gana dawowa dede ba ,
taji Abba yana cewa
“Duk abunda bai yi miki ba ki fad’a sai a chanja! Munata sauri ba a samu anyi komai a nutse ba, so if you need anything just say it sai a chanja miki ko a siyo, an d’an zab’a miki kad’an jiya
kayan suna mota mostly abaya ne da shoes da sauran y’an abubuwa, zan kawo miki tab zuwa anjima, sai kiyi shopping duk abunda kike buk’ata, in kuma a furnishing akwai abunda kikeso ki fad’a shima sai a kawo.”

Ita dai mamakine ma ya hanata yin magana, wai
A nan d’in amman still ana tambayanta ko akwai wani abun da takeso a kawo!

Girgiza kai kawai tayi, kafin tace
“Abba na gode komai yayi Allah ya k’ara Arzik’i. “

A hankali ya dafa kanta yana mai jin tsananin kaunar y’ar tashi tana ratsa ko Ina na jikinshi sannan ga tsananin tausayinta da ya hanashi sukuni!
Ji yake kamar yaje ya kama Usman yayita dukanshi har sai yaga baya numfashi tukunna ya kyaleshi!
Jiya yanda yaga rana haka yaga dare tsabar bak’in ciki…
Jin yadda zuciyarshi ta fara tafarfasa ne yasa ya kawar da tunanin yace
“Ki huta bara a kawo miki tab d’in da kayan, anyi order abinci shima na san kafin ki gama freshining up ya zama ready sai ki sauk’o muci ko?”

D’aga mishi kai kawai tayi ta kasa d’ago kanta, saboda kwallar da ta tarar mata!
Dan
tana ganin inda aka kawota a matsayin mallakinta Mama ce kawai ta fad’o mata……

A tare suka fito daga toilet d’in suka shigo d’aki.

Ganin Abba yana shirin fita yasa tunanin ta ya katse tayi saurin cewa
“Abba”

Juyowa yayi yana kallon ta.
A hankali ta k’arasa wajen da yake sanna tace
“Dan Allah Mama, mun yi waya da Sakina tace min Maman tana asibiti tun shekaran jiya”ta k’are maganan hawaye na zubowa daga idanunta.

A hankali ya kama hannunta suka k’arasa bakin gadon suka zauna sannan yace
“Zan kaiki wajenta anjima da daddare.
Ki daina kuka”
Da sauri tasa tafin hannunta tana share hawayen duka biyu.

Kallonta yayi tukunna yaci gaba
“Amman idan kinje, inaso ki yi promising d’ina zaki dawo, 30 minutes kawai za kiyi, zan
jiraki a mota!
Ku gaisa ki dubata daganan kice musu kina zuwa, in
kin fito sai mu dawo.
And karkice musu ni na kawoki”.

Da sauri ta d’ago ta kalleshi kafin tace
“To ai kamar na yaudaresu ne idan nayi hakan, kuma Mama ba zata ji dad’i ba.”

Mik’ewa yayi kafin yace
“Shine ni kuma zaki yaudareni ki tafi kik’i dawowa ko?”

Kuka ta fashe da shi….saboda daman ta san ko da ace ta yarda zata dawo d’in su Mama ba za su barta ba!.

A hankali yace “Hudan nima mahaifinkine kamar Maman ki, na san ba lalle ki fahimci komai ba, amman inaso ki san cewa ‘ban tab’a k’in ki ba’ Yadda Mahaifiyarki take sonki nima haka nake sonki, kina gani a gabanki na hukunta waenda sukayi nasarar raba ni dake!.
Ba zan tab’a yarda in barki ki koma gidan da kika taso ba, dan duk halin da kike ciki a gidan na sani.
Idan kin yarda kullum idan kina so to za kije ki dinga duba Mamaki, amman Hudan ba zan sake bari kiyi nesa dani ba..
I want to take care of you
Make it up to you
Make you forget all the sufferings that you go through.
Amman
hakan ba zai tab’a faruwa ba, sai da had’in kanki! Ba zan
b’oye miki ba har ga Allah banji dad’in yanda kike yi mini ba kwata kwata Huda, it’s like kamar ma bakya farin ciki da ganina, komai ke kawai Mamanki!
Ko maganan 10 minutes ban tab’a yi da ke ba!
Yanzu ma kalli yadda kike yi
min kukan in maidake wajen ta kamar irin na satoki d’innan?”
Ya k’arashe maganar a hankali.

Gaba d’aya Hudan sai taji jikinta yayi sanyi,
tabbas bata kyauta ba! Ya kamata ta nuna mishi shima Mahaifinta ne tunda gashi ata dalilinta har gidansu ya bari da shi da d’an uwansa don kawai ya zauna a tare da ita….
Tunaninta ne ya katse jin yana cewa
“I’m sorry Hudan dan unless you promise me ba zan tab’a barinki ki je ki ganta ba.”

Shiruu, d’akin ya d’auka kafin yaji tace
“Tam”.

Kallonta yake yi, kamar zai ce mata wani abun kuma kawai sai ya juya ya fita.

Kamar yadda ya fad’a haka aka kawo mata kayan da ya ambata..
Ita dai Hudan mamaki ta shiga yi dan bata ga kuma abun k’ari ba anan, komai akwai hatta inner wears sai dai kawai kamar ba za suyi mata ba, dan haka ta d’au tab d’in ta hau shopping…
Sai da ta hau d’in kuwa tukunna tayita gannin abubuwa dan haka ta zazzab’a, bayan ta gama ta rufe ta ajjiye.

Tana idar da sallar Magrib ta sauk’a k’asan kamar yadda Abban yace mata.

Bata samu kowa ba, amman dai ga uban abinci nan shak’e a kan dining d’in
wajen kala nawa..
Ga kuma wata maid cikin uniform sai kai komo take yi tsakanin kitchen da dining d’in tana jera su plates.
Bata yi minti uku a zaune ba, suka shigo daga masallaci…
Su Sudais ne suka fara shigowa, Sudais yana ta tsallen tsallenshi, Shuraim kuwa ya mazee, kallonsu take tana mamakin kamanninsu dan ita kam miskilancin Shuraim ne kawai yake sawa take iya gane su..
Tana murmushi tanata kallonsu tana jin tsananin k’aunarsu a ranta
su Abba ma suka shigo dukkansu, har a Auwal wanda Daddy ya matsawa akan dole sai yazo sun gaisa da cousin d’inshi! Sai kumbure kumbure yake yi, ba wanda yabi ta kanshi haka

Download complete TXT · Novel page