Ajiya A Duhu Book 2
Chapter 24 of 24
abokan tafiyarsu suke ba. Dabarar kiran wayar hotel ɗin ce tazo mata, duk da bata jin yarensu sai tai tunanin yin turanci. Haka kuwa akayi, ta sanar musu tana buƙatar wani a ɗakin da suke ta faɗi number ɗakin, bata jira amsa ba ta yanke wayar saboda yanda taga AA na yamutsa fuska da sake dunƙule jikinsa. ALLAH ko ya taimaketa sai gashi anzo anyi knocking ƙofar, babu shiri ta miƙe tana gyara veil ɗinta taje ta buɗe. Ma'aikacinsu ne namiji, bayan sun gaisa ta sanar masa mijinta ne baida lafiya ko suna da doctor dazai duba shi?. Da sauri ya ƙarasa shigowa ɗakin ganin yanda take magana a ruɗe, yana ganin a yanayin da AA ɗin yake ciki bai wani sake tambayarta ba'asi ba ya zaro waya a jikinsa yay kira. A mamakinta ko minti biyar ba'a cika ba wasu suka shigo sanye da kayan asibiti da ɗan abun ɗaukar mara lafiya. Gaba ɗaya suka ɗaga AA zuwa kan abun, shi kuma ma'aikacin yace ta ɗakko jacket ta taho dan akwai sanyi yauvkaɗan gashi safiya ce. Tashi ta jiya kawai ta yayuma ta biyo su, a tare suka shiga elevator, minti ɗaya da sakanni ta kawosu ƙasa harabar hotel ɗin, amamakinta ambulance ma na jiransu. Ciki aka saka AA itama akace ta shiga, sai ma'aikatan asibitin. Shi kuma ma'aikacin hotel ɗin da driver na gaba. Cikin sharara gudu na masifa suka iso wani ƙaton gini, da yarensu akai rubutu dan haka Maanal bata fahimci komai ba, amma dai ta tabbatar asibiti ne dan ga ambulance nan da yawa tako ina. Bata da lokacin tunani dan fitowa sukai aka shiga da AA ciki. Sai faman share hawaye take, ma'aikacin hotel ɗin nan na lallashinta da turancinsa mai fita da harshen Chaines.
Sunyi zama yakai na mintuna talatin kafin cikin ma'aikatan asibitin wani ya fito. Da Chaines yayma ma'aikacin hotel ɗin magana, sai shi kuma ya juya yana kallon Maanal da turanci yace ga matarsa nan. Kallon Maanal ma'aikacin yayi, shima da turancin ya bata takardar hannunsa yace tai signing. Bata san mi aka rubuta ba tunda Chaines ne a jiki, dan haka tai tambayar ta miye? Dan bata iya yaren ba. Su duka biyun sun fahimci tasan abinda take yi, dan haka ma'aikacin hotel ɗin ya amsa ya ciro wayarsa yayma takardar hoto, miƙa mata wayar yayi ya nuna mata inda zatai translate ya koma mata da duk yaren da take so. Godiya tai masa tayi duk yanda ya nuna mata, sai ko gashi ya koma mata da turanci. Sai da ta kammala karantawa ta fahimci komai sannan ta amsa pen tai signing ɗin ma'aikacin ya koma ciki. Bayan kamar mintina ashirin ya sake fitowa yace zata iya shiga wajensa.
Wata nannauyan ajiyar zuciya ta sauke tare da masa godiya. Ma'aikacin hotel ɗin yace mata zai koma bakin aikinsa shima. Idan suna buƙatarsa tai magana ga ma'aikatan asibitin zasu kira hotel ɗinsu zai zo. Godiya tai masa sosai shima sannan ta nufi ciki shi kuma ya juya ya tafi.....
___________★
Siyayya ce sosai yayo ta azumi, sai dai samun gidan shiru ya fahimtar da shi matar gidan barci take yi. Bai tasheta ba dan yasan wahalar data sha a hannunsa daren jiya. Sai kawai ya shigar da komai kitchen ya juya ya fita, dan yana son zuwa ya amso nama da kifi na gidansu da ya sayama iyayensa na azumi kamar yanda yay musu siyayya da kuma nasu na nan gidan. Kusan awa ɗaya da rabi ya sake ɗauka sannan ya dawo. Mamaki ya kamashi ganin har yanzu bata tashin ba kuwa. Ledojin hannunsa ya kai kitchen, sai kuma ya nufi ɗakin barcinsu. Barcin kuwa take a ƙasan tils, yay ɗin jim yana kallonta, kafin ya matsa ya ɗan taɓata yana kiran sunanta.
“Huznah! K Huznah!!”.
Motsawa tai, tare da buɗe ido sai kuma tai miƙa tana kallonsa. Zaram ta miƙe kamar wadda ta tsorata da ganinsa, sarai ya fahimceta amma sai ya fuske. Cike da kulawa yace, “Wannan wane irin barci ne? Da alama ma ko girki baki yi ba ko?”.
Fuska ta ɗan yamutsa sai kuma ta jinjina kai alamar eh.
“Okay, ki tashi kiyi salla ga nama can na kawo da kayayyaki ki adana su. Ni naje massallaci zan taho mana da abinda zamuci”.
Bai jira amsarta ba ya fice. Da kallo ta bisa, sai kuma hawaye sharrr suka shiga rige-rigen sakko mata. Wlhy bata son mutumin nan, ko kallon fuskarsa bata sanyi. Tasan in har AA na wannan duniyar bazata taɓa son kowa ba. Ita kaɗai tasan a irin ƙuncin zuciyar da take kwana, ga Sageer ya maidata kamar jaka. Sam baya raga mata, safe da dare wani lokacin har da rana idan ya dawo gidan sai ya nemeta. In ma ta masa gardama ya murɗeta yay abinda zai yi ya ƙara gaba. Ya kwace mata waya ta rasa ta ina zataji Umminta, ta ina zataji labarin AA a bakin Sille. Ji take kamar ta kashe Sageer ta hutama ranta. Sanin halinsa na tasan inya dawo baiga ta yi abinda yace ba yasa ta miƙe. Sam bata jin daɗi, kwanciyar ƙasan tils ɗin nan ce kawai ke mata daɗi, kuma babu inda ke mata ciwo a jikinta. Wanka ta farayi tai salla. Sannan ta nufi kitchen ɗin, ta jima tana kallon kayan daya jibge mata kafin ta fara ɗaukewa cikin ɓacin rai zuwa store ɗinsu. Sannan tazo ta buɗe ledar naman. Rasama yaya zatai da shi tayi, dan aikin nan dai ba sabawa tai da yi ba a gida sai masu aiki, a yanzu ma sakata gaban da Sageer ɗin yayi ne aka ɗan samu canji. Ledan kifin itama ta buɗe, ai kamar jira ƙarnin na bugar hancinta ta wani rikice, a guje ta buɗe ƙofar baya ta fita ta fara sharara amai a ciki filawoyin wajen. Sageer dake shigowa ciki kakarin aman nata ya sashi nufo bayan cike da mamaki. Shi sai ma ya tsaya kawai yana kallonta. Sai da ta gama tai lagab a ƙasa sannan ya ƙaraso wajen, da yake akwai rijiya ata bayan ruwa ya jawo ya zuba a boket dake ajiye ya kawo mata yana mata sannu. Kanta ta jinjina masa ta ɗauka ruwan ta wanke bakinta da fiskarta, ta zuba akan filawoyin data ɓata sannan ta miƙe da ƙyar. Taimaka mata yay suka shiga, suna shiga kitchen ɗin tasa hannu ta toshe hancinta. Kitchen ɗin yabi da kallo, sai kuma baice komai ba ya shige da ita cikin falo. A kujera ta zaunar da ita, sai dai bata iya zama ba ta zamo ƙasa ta kwanta. Muryarta har rawa yake tace, “Bana son ƙarnin kifin can, dan ALLAH ka fita da shi”.
Sosai yake kallonta da mamaki, dan shi dai yasan a zuwanta gidan nan yasha sayo kifi ya kawo suci har ɗanye suyi abinci balle yace bata ci tun fil azal. “Yau kuma kifin ne zaki ce baƙya so Huznah?”.
Hawaye ya cika mata ido ta ce, “Wlhy bana so, dan ALLAH ka taimakeni ka fita da shi. In ba haka ba zan sake yin amai”.
Shike nan ba damuwa zan fita da shi tashi kici abinci”. Yay maganar yana ajiye mata ledar takeaway daya yi musu. Shi kuma ya nufi kitchen ɗin ya shiga gyara kifin da naman dan a tunaninsa sabon iskanci ne dan kar ta gyara, tunda sarai yasan halinta dan ma baya mata da wasa ne. Tsaf ya gyara komai ya zuba su a freezer ɗinsu sannan ya koma falon shima.......✍️
Hajiya Huznaty😂🤣🤣bara dai nayi shiru.
*_AJIYA A DUHU na kuɗi ne, 500 ne kacal, ƴar uwa bazaki ragu da komai ba dan kinzo kin sauke hakkin wahalata ta rubutu. Dan ALLAH magana ta WhatsApp kawai 😀🙏_*
*09032345899*
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*