So da Buri 3
Chapter 10 of 36
sai kuma ta kalla k’asa kan kafet d’in gaban kujerar ta fara k’ok’arin zama..
Ji tayi kawai ya kamo hannunta ya jaata ya ajjiye ta a gefen sa..
B’ata rai tayi sosai..ita kam wallahi zata maka masa warning! Dan me yasa ba zai mata ta zauna a gefenshi ba instead zai wani janyota?
Hala bakinsa yana ciwo ne..
Muryarshice ta katseta
jin yana cewa
“D’azu Ummi tace za ki rakata wajen Mama”
Da sauri ta d’ago ta kalle shi
sai kuma ta fara murmushi…bata san zancen ba amman kawai sai ta hau d’aga masa kai.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya juyo ya bata dukkannin attention d’insa sannan yace
“Ina jinki”
Cikin rashin fahimta tace mishi
“Me?”
“Okay, baki san me ya kamata ki yi ba?”
Yayi mata tambayar still yana kafeta da idanuwanshi.
Shiruuu tayi ita harga Allah bata san me yake so ta yin ba!
A hankali tace
“Me zan yi ni?”
Kallonta yayi na some seconds sannan yace
“Tashi ki je,
goben kawai kya bata sak’on gaisuwa ta kaiwa Maman
besides saboda Ummi ne ma shiyasa zan barki daman kije
dan ai bai kamata ace kinje gida tun yanzu ba.”
Sarai zuwa yanzu ta gano so yake yi ta tambayesa, a ranta tace
“Wannan wanne irin mutum ne mai son jan magana?
Ba Ummi ta tambayar min ba!”
Ganin da tayi tambayr da yake son tayi shine mafi sauk’inta
ya sanya kawai ta kauda kai tace
“Ya Aslam zan raka Ummi wajen Mama gobe”
Kafin ta rufe bakinta taji yace
“Order kike bani?
Ko kuma gaya min kike yi?
Ko kuma tambayata da neman izinina kike yi?”
Ya mata tambayar a hankali cikin class da nutsuwarshi.
B’ata rai tayi sosai kamar zata fashe da kuka.
A ranta ta aiyyana
‘Ga zuwa wajen Mama ga kuma wasu shegun renin hankali da Aslam yake yi mata, wanne zata d’auka?’
A ranta tace
‘Ya na iya?
Haka zan hak’ura in yi tolerating d’insa.”
Muryarsa taji yana cewa “had’o min coffee.
Shikenan tunda ba kya son zuwa”
Yana fad’in haka shima ya juya yana kallon wani wajen kamar yadda tayi mishi.
A hankali yaji tace
“Ya Aslam nafa tambayeka.
Me zan ce?”
Juyowa yayi yana kallonta
itan ma shi take kallo
Sai dai suna had’a ido tayi saurin d’auke kai.
A hankali ya lumshe idanuwansa kamar mai yin bacci…..
Sun fi minti biyar kafin yaji tace
“Dan Allah Ya Aslam zan raka Ummi wajen Mama gobe”
Wayarsa kawai taga ya mik’o mata yace “ki hau ki yi searching ya ake tambayar Miji fita!
Ko kuma ki d’auko wayarki and ask Sakina, na san maybe ita zata iya sanin me ya kamata ki ce”.
Wani takaici ne yazo mata bata san lokacin da ta fara hawaye ba. Karb’ar wayar kuwa tayi ta hau google ta typer, wasu abubuwa daban aka sako mata…
Shiruu, tayi tana share hawayen da suka k’i tsayamata, a ranta tace
“Wanne irin mutum ne wannan wai shi?
Kalla yadda kanshi tsaye yake wani cewa Mijinta!”.
Sun d’an jima a haka
chan! Kamar wadda ta tuna wani abun yaji tace
“Dan Allah Ya Aslam Ina neman izinin ka zan raka Ummi wajen Mama”
Wani sassanyan murmushi yayi kafin a hankali ya fara bud’e idanuwanshi yace
“That’s more like it ....”
Muryarshi ce ta sark’e sakamokon ganin fuskarta dagaje dagaje da hawaye.
A hankali ya matso kusa da ita
yace
“Mai ya faru?”
Kamar jira take yi kuwa
ta saki kukan nata
dan ji tayi ya taho mata da mugun k’arfi….
Kuka take yi tun k’arfin ta tak’i ma ta saurareshi, sai faman tambayarta yake yi amman tayi mishi banza!
Bata yi auni ba taji ya janyota jikinsa bai yi wata wata ba ya rungume ta gabad’ayanta!
Ba ita kad’ai ba hatta shi sai da ya tsorata da yadda zuciyarshi take bugawa!
A lokaci guda kuma wata nutsuwa ta lullub’esa…jin shi kawai yake yi a saman gajimare.
A b’angaren Huda itama kusan hakan ne dan d’iff haka kukan nata ya d’auke lokaci guda
in banda ajiyar zuciya babu abunda take ta faman sauk’ewa….
Ita dai ba zata ce ga yanayin da take ciki ba
saboda lokaci guda
firgici mamaki nutsawa da fargaba suka rufar mata.
Da kyar ya iya d’aga hannunsa ya d’aura a kan gadon bayanta ya fara shafawa a hankali, dede setin kunnenta yace
“Shii, yi hak’uri. Wasa nake miki fa. Naga d’akin kullum boring ne shiyasa nake d’an jan magana da ke amma
sorry tunda bakya so
ba zan k’ara ba.”
Zuwa yanzu
ita kam ba ma jin sa take yi sosai ba!
Mamakin kanta kawai take yi
yadda ta kasa turesa daga jikinta Infact ita ji tayi ma bataso ya barta!
Abu d’aya ne bataso shine
bugun zuciyarta da yake yi da k’arfi! Amma apart from that
bata k’aunar duk wani abunda zai rabata da duk wani part of yanayin da taje ciki a yanzu.
A hankali take shak’ar k’amshin jikinsa da na turarensa tana jin wata nutsuwa da nishad’i suna sauk’ar mata…
Bata san lokacin da ta fara lumshe ido tana bud’ewa ba.
Wata kasala ce ta rufar mata dan haka ta d’an fara sakin jikinta tana lumshe ido tana sauraron bugun zuciyarshi da yake yi da k’arfi da sauri har ma yafi nata....
A hankali yake jin nauyin jikinta yana k’aruwa a nashi…
Sun fi 10 minutes a haka, chaan! Ya ji ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya
sai kuma ya fara jin sauk’ar numfashinta a kan k’irjinsa a hankali a hankali…
Ajiyar zuciyar shima ya sauk’e
kafin yace
“Huda”
a hankali.
Shirun da yaji tayi ne yasa ya fahimci ta yi barci.
A hankali kamar wanda rayuwarshi yayi depending akan barcin nata ya janyo trow pillow ya fara k’ok’arin kwanciya da ita a jikinshi.
Mik’ewa yayi sosai akan kujerar kwanciyar rigingine.
Kusan dukkan nin sangalalin k’afafuwansa sun kere kujerar gashi kuma akan d’an tudun edge d’in kujerar ya d’aura su,
tabbas ya san k’afar zata yi mishi tsami amman
he can’t even think of ruining wannan best moment d’in, ba.
A hankali ya kwantar da ita akan hak’ark’arinsa..
Daga shi d’in har ita ba wani k’iba garesu ba
shiyasa faffad’ar kujerar ta ishesu ciff ciff.
Mayafin kanta yayi dabara ya ware ya lullab’a mata…
Yau ma yana jin sanyin
amman yana gudun kar ya motsa ta farka
dan haka kawai sai ya hak’ura ya bar bargon…
Bai yi cikakken minti biyar ba wani bacci mai mugun dad’in da ya manta rabon da yayi kwatan kwacin irinsa, ya kwashesa...
Yau ma, kamar yadda ta farka jiya haka ta rigashi tashi.
K’amshin turarensa ta shak’a!
A hankali ta fara k’ok’arin motsawa amman sai ta jita ta kasa. Addua tayi ta bud’e idanunta sosai tana kallon d’akin……
A chaan ta hango gadon a gefe ba kowa a kai!
A d’an zabure ta sake yunk’urin tashi had’e da kallon kusa da ita….
Tsayawa tayi kawai tana kallonshi yana baccinsa peacefull, sannan ya zura hannunsa d’aya ta k’asan ta gefen cikinta, ya kuma d’aura d’ayan a gefen cikinta ta sama
ya had’a hannayen nasa guri guda.
Gabantane taji ya yanke ya fad’i! Sai kuma ta tuna yadda suka yi jiya!
‘Kenan bacci tayi ta kwana a jikinshi?’
Ta aiyyana tambayar a cikin ranta.
Wani takaici da haushin kanta ne suka rufeta a take.
Hannunta ta saka ta fara k’ok’arin raba hannayen nasa da suka kanainayeta.
Sai a lokacin ya bud’e idanunsa ya zuba mata.
Itan ma shi take kallo dan haka idanuwansu suka sark’e ana juna……
Tun tana k’ok’arin kwance hannuwan nasa a jikinta da sauri har tazo ta fara yi a hankali daga baya ma sai ya zamana hannuwantane kawai akan nasa ko motsasu bata yi…..
A hankali take jin fad’uwar gaba da kuma wani sanyi da nutsuwa a yayin da take kallon cikin idanunsa…ta fad’a a yau kuma ta sake tabbatar wa
‘babu wanda ta tab’a gani mai kyawun idanuwa kwatan kwacin na Ya Aslam’
A ranta tace
“tubarkallah ma sha Allah”
Cikin muryar bacci taji yace
“Good morning wifey!”
A hankali ta lumshe idanuwanta a ranta take tunanin
‘Anya wannan ba aljani bane ba kuwa?
Kallafa yanzunnan ya tashi a barci amman idanuwansa basu yi ja ba
sai ma wani kyalli da taga sunayi sannan bakinsa kamar
ma sweet ya sha dan in dai
taji da kyau tou k’amshin mint taji……….’
D’umin numfashinsa ne taji yana k’ara bak’untar fuskarta!
A hankali take sauk’e ajiyar zuciya tana sake rik’e hannunwansa…..
Chan! Kamar wadda ta tuna wani abun, tayi saurin bud’e idanuwanta tarr!! A d’an zabure….dai dai shi kuma ya samu nasarar d’aura lips d’insa a kan nata........
A mugun firgice ta sanya dukkannin k’arfinta ta turesa
amman ko gezau! Bai yi ba.
Wani rikitaccen kuka ta saka masa!
Dan haka yayi saurin sakinta ya d’an jaa baya yana kallonta.
Tana jin ya saketa, ya bata iska ta bi ta kansa da wani irin sauri ta sauk’a daga kan kujerar!
Mayafinta da yake lullub’e a jikinta wanda ya fad’i yanzun kawai ta samu damar d’auka
daga nan ta nufi k’ofa………
Tana jinsa yana kiran sunanta
amman tayi banza da shi ta fice da mugun sauri....
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
62
Mikiya Writers Association.
Chan sama ta nufa.
tana tafe tana adduar
‘Allah yasa side d’inta a bud’e yake’.
Tana isa ta tura, cikin sa a ta tarar a bud’e dan haka ta shige ta saka key!
Tana zuwa ta zauna a kan kujerar parlourn tana haki kamar wadda tayi gudun famfalak’i…
Ta dad’e a nan zaune, jin
an shiga masallaci ya sanya ta mik’e tana tunanin komawa d’akin dan ta samu ta d’au hijabi ta yi sallah.
Kamar aslam d’in ya biyota
haka ta d’an bud’e k’ofar kad’an ta lek’a!
Ganin babu kowa a dogon corridorn ya sanya ta sauk’e ajiyar zuciya ta fito tana sand’a…..
Sai da ta kai tsakiyar parlourn taji muryar Ummi a bayanta
“Hudan”
Runtse idanunta tayi a hankali kafin ta bud’e sannan ta juyo, ta shiga k’ok’arin k’ak’alo murmushi…
Kallonta Ummin tayi from head to toe sannan ta nufota, tana zuwa “me ya kawoki nan?”
Kame kame ta fara…chan! Da kyar tace
“Daman zuwa nayi In karb’i Qur’ani a wajen Shuraim
kuma d’akin nasu ma a kulle ne “
Had’e fuska Ummi tayi kafin tace
“Yaushe kika koyi k’arya?
Ina d’aki fa Ina karatu naji an hawo
Ina lek’owa naga wucewarki d’akinki tun d’azu!
Mai ya faru??”
Tayi maganar tana tsareta da idanuwa.
A hankali ta sunkuyar da kanta
batai auni ba kawai taji hawaye sun zubo mata.
Sarai daman Ummi ta so ta fahimci wani abun…murmushi
kawai tayi a ranta
tana mamakin Aslam!
Kafin ta jawo Hudan zuwa jikinta cin son sake fahimtar lamarin tace
“Yi shiru, shikenan.
Bara in d’auko miki Qur’anin a d’akina sai ki wuce kije ko?
Kar Aslam d’in yaga kin dad’e, yau ma na san da wurwuri za su fita.
Kiyi sauri kije ki tayashi shiryawa, ko?”
Kuka kawai taji Hudan ta kece dashi kamar wadda akace za a yankata! Cikin kukan tace
“Ummi dan Allah karki bari in koma, Allah ba zan iya had’a ido da shi ba, baki san meh....”
Kamar kuma wadda aka datse harshenta sai ta
tsaya da maganar chak! Tana mai ci gaba da kukanta.
Murmushi Ummin tayi
ranta fess. Tace mata “to shikenan
jeki ki yi alwala ki yi sallah
ki daina kuka haka.
Anjima sai muyi magana ko?
Muje d’akina.
Tayi maganar tana jan hannunta.....
Bayan, Ummi ta gabatar da sallar Asubah, ta yi azkar,
ta zauna ta hau nazari…
Wani sanyi da dad’i take ji a ranta..ta san Huda Arshaad take so amman tabbas kamar yanda su Dad sukace
‘Ko bayan auren Mammy bazata barta ta zauna lafiya ba’
Aslam shine wanda take gani zai bata cikakkaiyar kula da soyayyar da take buk’ata,
bayan haka
sun yi mugun dacewa
sannan ita daman ta d’an fahimci kamar Aslam d’in yanas son Huda!
In dai kuwa hakanne
Allah Ubangiji ya barsu tare ya k’ara musu k’aunar juna
ya sanyasu farin cikin da basu yi tun tasowarsu ba……
A zaune taga Huda ta fara gyangyad’i dan haka tace mata “ta tashi ta kwanta a kan gado”
Da sauri kuwa Hudan ta mik’e
saboda daman addua take tayi kar Ummi tace mata taje ta had’awa Aslam breakfast.
Tana kwanciya bata dad’e ba bacci ya kwasheta
Ummi kuma ta mik’e ta fita dan had’a musu breakfast d’in..
Tana cikin bacci taji muryar Abba yana kiran sunanta,
a hankali ta bud’e idanuwanta.
Zaune ta ganshi a gefenta yana mata murmushi
dan haka itama ta d’anyi murmushin sannnan ta mik’e ta zauna tace
“Abba Ina kwana”
“Lafiya, Alhamdulillah.
Kin tashi lafiya?”
“Alhamdulillah”
Tace
Mik’ewa taga yayi tsaye kafin yace
“Zamu wuce UK ni da Daddy.
Urgent tafiya ya taso,
akwai abunda kike buk’ata?”
Murmushi kawai tayi tace
“Ba komai.
Allah ya kiyaye ya tsare hanya ya dawo daku lafiya”
A hankali ya d’an matso ya shafa kanta yace
“Ameen princess,
take care.
Sai mun dawo ko”
Yana gama fad’in haka ya juya ya nufi hanyar fita, har ya kama handle d’in sai kuma yaga rashin kyautawarshi
dan haka ya juyo ya kalli Ummi dake gefe a tsaye yace
“Na tafi.
Zan saka miki kud’i ta account ko akwai abun buk’ata.
In akwai wani abun you can call me”
Wani kalan murmushin farin ciki ne ya baiyyana a kan fuskarta, tana murmushin tace
“Nagode.
Sai kun dawo”
Murmushin daya mayar mata ne ya bata kwarin guiwar binsa a baya domin tayi mishi rakiya.
Hudan ma taso ta rakasa
amman ganin sun fita da Ummin ya sanya ta bari kawai,
dan ta barsu su samu alone time su biyu.
Kallon agogo tayi taga har 10 ya d’an gota. Ta san by now Aslam ya fita dan haka ta sauk’e ajiyar zuciya ta zuro k’afafunta k’asa tana
tunani da mamakin guts! Kalar na Ya Aslam….mai yasa yayi mata hakan? Ya san ba sonta yake yi ba mai yasa zai dinga yi mata wasu abubuwan kamar waenda sukayi auren soyayya!?
She definitely has to stay very far away from him
har sai ta gano inda relationship d’insu ya dosa da ita kanta dan
gaba d’aya Aslam ya juya mata lissafi kwana biyun nan kanta duk ya d’aure
It’s like bama ta san me take so ba! Tabbas ta san tana son Ya Arshaad sannan tana son rabuwa da Ya Aslam
Amman kuma when ever she’s with him
she feels complete and safe!
Da farko bata fahimci hakan ba sai a jiya da yayi hugging d’inta ta kasa kwace kanta daga k’arshema bacci ya kwasheta………..’
Ajiyar zuciya ta sauk’e, a chan k’asan ranta tace
“A complicated marriage is enough!
I can’t deal with complicated and confused relationship.”
Tun d’azu idan ta tuna da moments d’insu na tsakanin jiya da yau da safe sai taji tana feeling somehow…bata k’aunar wannan feeling d’in at all
bata son abunda zai na janta garesa shiyasa gara tun
kafin ta gama zama confuse tabbas ya kamata ta d’au mataki….
A haka Ummi ta shigo ta sameta.
“Tunanin me kike yi?”
Taji muryar Ummin.
A hankali ta d’ago ta kalleta
sai kuma ta maida kanta k’asa tace
“Ina kwana”
Murmushi kawai Ummin tayi tace
“Lafiya” sannan tace
“Oya tashi ki shirya mu yi sauri mu tafi ko?”
Ai tun kafin Ummi ta ida rufe bakinta Hudan ta sauk’a ta fita daga d’akin cike da d’oki.
Murmushi kawai Ummin tayi itama ta hau nata shirin…
Sai pass 11 sannan suka shirya suka fito
Hudan bata wani yi kwalliya sosai ba, Abaya ce a jikinta nude colour mai kyau sosai, tayi rolling ta d’an saka lipstick, sai zobe da bracelet a hannunta.
Ummi kuma lace ne mai kyau da tsada a jikinta peach da farin mayafi da jaka da takalmi.
Suna baya suna d’an tab’a hira driver yana jansu, haka suka kama hanya…
A wani babban mall Ummi ta cewa drivern “yad’an tsaya”
Dai da suka fita tukunna ta bawa Hudan kud’i, tace
“D’azu Aslam yace abata ta yi siyayyan tsaraba ta kai gida”
“Angode” kawai ta iya cewa
daga nan suka shiga sukayi y’ar siyayayr tsarabar suka fito
Ummi tana lura da yadda mood d’in Hudan ya chanza tun daga lokacin data ambato sunan ‘Aslam’
So take ta fassara yanayin nata amman ta kasa
a haka driver yayi parking a kofar gidan Madu....
Fita suka yi,
Driver ya tayasu kai kayan har bakin k’ofar parlour
daga nan suka sallameshi
bayan sun yi da shi akan 3:00pm zai dawo ya d’auke su.
A parlourn k’asa suka tarar da Mama tana zaune tana kallo.
Sallamar su ce ta sanya ta maida hankalinta bakin k’ofar, kamar a mafarkin haka taji
nan take wani farin ciki ya lullub’eta.
Cikin farin ciki Huda ta ajjiye ledojin hannunta a farkon parlourn ta k’arasa da gudu ta fad’a jikinta ta yi hugging d’inta.
Tabbas Mama tayi farin cikin ganin d’iyar tata
amman sai ta maze ta zarota daga jikinta ta fara yi mata fad’an ‘mai yasa ta fito?
Dududu yaushe ma aka kaita?”
Ummi ce ta k’araso inda suke tace “Ayi hak’uri Mama ni nace sai ta rakoni”
Murmushi Maman tayi
dan ita ta ma manta Hudan tare take da bak’uwa hakan
yasa ta d’anji kunyar barinta da sukayi a tsaye ita kad’ai.
Cikin fara a tace
“Bismillah ki zauna.
Yi hak’uri wannan ta gudo ta barki bama ta tsaya kun k’araso tare ba”
Murmushi Ummi tayi
sanann ta k’arasa ta ajjiye ledar hannunta a gefe tukun ta zauna a kan d’aya daga cikin setin kujerun da Maman tayi mata nuni da.
Tana zama Mama tayi kitchen..
Sai da ta cika mata gabanta da kayan kwalama da su lemuka tukunna ta nemi waje ta zauna tana raba d’ayan biyu
‘Ko dai babar Auwal ko kuma matar Abba!
Amman anya kuwa matar Abba zata yarda tazo kuma tana mata fara’a haka sosai?’
“Ina su Hajiya? Na ji gidan shiru”
Muryar Huda ta katse mata tunani.
Sai da ta d’anyi jimm!
Tukunna tace
“Tana gidan Baaba Talatu,
Baba ne aka dawo da shi
wai bashi da lafiya sosai”
“Allah ya bashi lafiya”
Shine abunda Huda tace kawai
dan jiya ma sai da suka