So da Buri 3

Chapter 9 of 36

tayi turjiya su yi mata dukan mutuwa!”

Jalila ba wani turancin kirki ta iya ba amma ta fahimci me Mom d’in tace.
Ganin sojan ya tunkarota ba alamun annuri a fuskarsa yasa ta durk’usa da sauri ta fashe da kuka, tace
“Wallahi tallahi kika saka aka fitar dani sai naje na tona muku asiri ke da d’anki a wajen Granpa.”

Dakatar da sojan Mom tayi kafin a hankali ta k’arasa inda take durk’ushe. Durk’usawa itama tayi sannan ta saka yatsa ta d’ago fuskar Jalilan..
B’ata rai tayi ta yamushe fuska kalar tausayi kamar wadda zata fashe da kuka kafin a hankali yadda ta tabbatar babu mai ji tace
“Ayyah Jalila!
Wajen Granpa zaki je?
Bismillah to ki je. Amman inaso ki san
ko da ace kin je wajensa baki da wata shedar da zaki iya nunawa against ni ko Auwal!
Mai yasa kike tunanin na barki kwana uku?”
Bata jira jin me Jalilan zata ce ta bata amsar tambayar da tayi mata da kanta tace
“To get rid of all the evidence!
Sannan ta ci gaba da cewa
“Sannan tun farkon zuwanki
ranar cewa nayi
Inna tayi min message
tace min wata zata zo ta tayani y’an aikace aikace saboda an saka ranarta so tana buk’atar kud’in kayan d’aki, kinga yanzu In aka kira Inna tunda ba ita ta turo ki ba zata ce bata sanki ba ba kuma
ta san da zancen ba!
Nima kuma daman kinga Innar nace ta had’ani da ke…
Questions d’in da zasu fad’owa y’an estate d’innan a karon farko shine
“Wacece ke?
Mai yasa kikayi outsmarting d’inmu?
Tayaya kika iya hacking wayar Innaa?
Sannan me kikeso me ya kawoki?
Waye kuma ya turoki gidan nan?.
Jalila bincike In yayi bincike believe you me har sharrin y’ar boko haram sai na d’aura miki wallahi!

Family d’innan is a well known family so dole muna da mahassada da masu son cutar da mu so kinga kema a wannan sahun za a jefaki
ta yiu ke kika zo da kan ki ko kuma wanine ya saka ki kizo
gidan nan kiyi aiki ko bincike ko wani abun wanda Allah kad’ai ya san na menene!

Granpa kuwa kinga dole ya tashi tsaye yayi bincike in ta kama a hukuntaki hukunci mai mugun tsanani
Idan anyi miki mai sauk’i shine
a kaiki cell ayi ta laftarki ace sai kin fad’i waye ya turoki...
Shawara ta gareki shine
Ki guji mutumin da kika ga Auwal yana mugun jin tsoronsa!
Ki duba kiga fa
surukan gidan nan ne mu
amman da muka yi laifi ya aka yi da mu?.

Sanann maganar ciki
Already tun a ranar na biyasu
y’an asibitin sun goge history d’inki! So kinga ko kince aje chan kina da evidence
to nan d’in ma sai dai ki sake k’ulle kanki infact duk inda kikaje ma Jalila kud’i kawai zan bayar amaida lefin kanki.
Sannan hatta chat da number Auwal duk na goge wani evidence a wayarki d’azu d’azun nan da nace miki ki ara min wayarki already kuma na san pin d’inki ba tare da kin farga ba shiyasa komai ya zo mini da sauk’i…baki da wayo Jalila sannan baki iya takun ki ba dan haka baki ta evidence ko
wani abu da zaki nuna against me…
So be a good girl!
Ki kwashe tsummokaranki
ki yi gaba tun kafin waennan k’artin su miki illar da na san ko kud’in magani ma ba lalle ki samu ba!”
Tana gama fad’in haka ta cika mata hab’arta ta mik’e ta
bar gurin tana karkad’e hannunta.


Still sojan ne ya sake nufarta yace “Stand up and leave!”

Banza tayi da shi tana wani kalar kuka mai cin rai.

K’afarsa ya d’aga yayi wani mahaukacin ball da ita
wanda sai da ta hantsila sau biyu!

Da gudu Ummi da Huda suka k’arasa wurin suka dakatar da shi dan har ya sake nufar ta.

Ummi tana duba ta taga gefen kanta ya fashe saboda yadda ta kifa a kan interlock d’in. Cikin tsananin b’acin rai ta d’ago ta cewa Mom
“Haba Adama!
Meye haka?
Kin san fa ba ita kad’ai bace ba. Yanzu na tabbatar ko mik’ewa ma bazata iya yi ba
balle ta fitar miki a gidan da kike ta faman ik’irari!”

Tab’e baki Mom tayi
sannan ta kalleshi cikin harshen turanci tace
“Jata ka fitar idan ba zata iya tashi ba.”

Ummi tana rik’e da hannunta amman mutumin nan bai damu ba haka ya kamo d’ayan hannunta ya fara janta kamar ba mutumba….
Sai da suka yi kusan rabin gidan tukunna Ummi ta hak’ura ta daina binsu rik’e da hannun Jalilan tana masa magana dan har ta fara haki.

Haka nan ya jaata ya fitar da ita kamar kayan wanki ya jefar a bakin gate!

Mai gyaran flowers kuma ya watso mata kayanta waje suka ja k’aramar k’ofar gate d’in suka rufe gidan......

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
61

Mikiya Writers Association.
Rai a b’ace Ummi ta koma inda Mom take ta rufeta da fad’a.
Ita babu abunda ya fi d’aga mata hankali irin yadda aka jaa Jalila a k’asa despite the fact that she’s pregnant, ai ko ba komai de d’an Auwal ne k’unshe a cikinta!.

Mom bata ce wa Ummi k’ala ba
har tayi ta gama ta wuce ciki.

Tana wucewa ta bi bayanta
suka bar Hudan a nan tsaye tana mamakin rashin mutunci da rashin tausayin irin na Mom
tabbas a wajenta Auwal ya kwaso duk wasu bad habits nasa daga gani kuma
ita ta b’ata shi tun farko
dan wannan uwar ba zata tab’a iya yin tarbiyyar da ta kamata a Yaro ba.
Kamar ta bi bayan Jalila
haka taji, to kuma kar Jalilan ta ganta tace zata zauna a wajenta taje sabon case ya b’ullo tsakaninta da Mom
sannan Mama ta ja mata kunne akan ta fita harkar case d’in Jalila da cikin jikinta da duk wani abun daya shafeta..
Shiyasa kawai ta share hawayenta ta wuce ciki
tausayi da k’aunar Arshaad suna sake shigar mata zuciya dan maganganun Jalila Mom da Ummi sun sake tabbatar da
ciki dai na Auwal ne.


Sai da Ummi ta kusan kaiwa d’akinta tukunna ta lura da Mom na bayanta.
Juyowa tayi tana kallonta kafin tace
“Adama baki da bakin yi min magana yanzu, ba zan
saurareki ba dan haka
kawai ki juya ki tafi.
In wulak’anci abun yi ne
ki je kiyi.
Kuma kin san Allah ki guji had’uwar ki da Auwal
saboda duk tsiya dai
cikinsa ne a jikinta kika yi mata wannan rashin mutuncin….”

Matsowa Mom tayi tana mai sauk’e ajiyar zuciya
tukunna tace
“FYI Cikin ya zube.
Ta fad’o daga bene ya zube 3 days ago”

Shiruu Ummi tayi tana kallonta
ta jima tana kallon kwayar idanun ta itama Mon d’in haka, chaan ta lumshe idanuwanta ta bud’e ta furzar da iska tana mai girgiza kai duk a lokaci d’aya kafin tace
“Adama ki ji tsoron Allah, ki bar
ganin cikin shege ne kika zubar
wallahi kina da hukuncin kisa a hannunki”

Murmushi Mom tayi kafin tace
“Gaskiya ya kamata magidanta suzo su d’auki course a wajen Abba!
Duk wadda matarsa ta botsare kawai ya mik’ata cell
zata dawo dai dai”

Cikin b’acin rai Ummi ta juya kawai da niyyar shiga d’akinta, da sauri Mom ta sha gabanta
tana cewa
“O’o’o’o’!
Tsaya mana, ai akwai abunda ya kawoni wajen ki
dear new Ummi, may be na san maganar da zan gaya miki yanzun zata dawo dake hankalinki ki koma Ummin da na sani ba wannan ba..”
..Dalla dalla! Haka Mom
ta zayyano mata duk wani abunda taji jiya Abba da Daddy suna tattaunawa
sannan ta k’ara da cewa
“Zab’i ya rage naki..
Kina gani dai abunda yake yi miki tun kafin ta dawo d’in, wallahi na tabbatar idan Maryam ta dawo gidan nan wallahi Ummi kin ji na rantse miki sai masu gadi da drebobin gidan nan sun fiki daraja a idanun Abba!
Ballantana yanzu ga y’ar ta
dan ni ban san ranar barinsu gidan nan ba tunda
kikaga sun zaunar da su anan
to ba yanzu za su sallamesu su ba! Tunda dai na san Aslam yanada gidaje balle ace wajen zama suka rasa…
Kinaji kina gani haka zaku zama y’an kallo ke da y’ay’anki
bar ganin kin haifi maza..ki dai duba ki gani yanzu haka yaya Abba yake gwada so
tsakanin Hudan da su Shuraim?”


A hankali Ummi ta runtsei danuwanta da suka kad’a suka yi jaaa! Kafin ta bud’e su ta zubasu a kan Mom.

Tausayinta ne ya shigi Mom a take dan haka ta matso kusa da ita ta dafa ta
kafin tace
“Ki yi tunani ki yi shawara da zuciyarki.
Inada plan d’in da na shirya
wannan karon kwab d’aya kawai za muyi mata.
Ummi ke y’ar uwata ce
bani da kamarki duk duniyar nan daga Inna sai ke nake
gani a matsayin nawa inji dad’i, ba zan tab’a bari a cutar da ke ba!
Ki nutsu, zuwa anjima ko gobe
ki zo ki sameni ni na san
me zamu yi mata.”

A hankali Ummi ta sauk’e ajiyar zuciya sannan tace
“Nagode Adama.
Bara in shiga in kwanta
kaina yana min ciwo”

“Okay sai anjima,
bara in wuce.”
Mom d’in tace
daga nan ta juya
direct ta sauk’a ta fice daga gidan ta nufi side d’insu
ranta fess!.


Sai yamma chan daff da Magrib Aslam ya dawo
Abba kuwa da Daddy basu dawo ba sai bayan sallar isha.
Sarai Ummi ta san inda suka je
shiyasa tunda taga Aslam ya dawo shi kad’ai hankalinta yayi mugun tashi! Ta dinga ji kamar zuciyarta zata fashe.
Da kyar! Da mugun kyar ta iya danne zuciyarta ta dinga karanto adduoi tana tasbihi
tukunna ta samu ta d’an dawo hankalinta....


EARLIER…
Da kyar Jalila ta iya taimakawa kanta ta mik’e a
hankali ta zauna

Wani sabon kuka ne ya kufce mata, tana yi ta shiga tattare kayayyakinta ta na d’urasu a cikin ghana most go d’in da Mom ta had’o da kayanta ta dinga watsowa….
Ganin bakkon duk biyun sun cika ya sanya ta ware d’ankwalinta ta d’aure ragowar kayan a ciki bayan ta nemi mayafi ta rufawa jikinta.

Cikin ikon Allah tana cikin rufa mayafinta ta hango mai napep ya taho. Goge hawayenta tayi ta samu ta mik’e tsaye da kyar Ta taka da d’an sauri
ta isa kusan titin ta tsaidashi
dan kar ya sub’uce mata.

Har bakin gate d’in gidan ya k’araso ya tayata saka kayanta a napep d’in.
Ko ciniki bata tsaya yi ba tace masa “gandun albasa!”.


A k’ofar gidan Baba ya direta ta shiga sauk’e kayanta tana jin yadda jikinta ke yi mata masifar ciwo,
kallon unguwar da layin da gidan take yi….
A hankali ta lumshe idanuwanta wasu zafafan hawaye suka shiga tsilalo mata..
Ganin kamar mutane sunata kallonta ya sanya ta jaa kayanta one by one ta kai soro
ta dawo ta sallami me napep d’in tayi cikin gida.

A nan soron ta bar kayan dan bata jin tanad da energy d’in d’aukar kaya.

Su Umma suna zaune ita da Anty Zainab
Ya Ja’afar yana gefe kamar kullum su kuma suna tattauna ta yanda za su magance matsalolin da suka sakosu gaba a yanzu Jalila ta shigo.
A mugun zabure suka mik’e tsaye duk su biyun
suna kallonta dagaje dagaje!
Kamar jira take yi a take ta fashe da kukan da take ta k’ok’arin dannewa.

A rikice suka k’arasa suka rufar mata da tambayoyi….
Bata b’oye musu komai ba ta zayyano musu abunda ya faru tsakaninta da Mom.

A zuciye Umma ta rarumi mayafinta ta rufa ta fara k’ok’arin fita tana cewa
“Wallahi yau ko ni ko wannan Adamar!
Sai dai mu tashi da juna ni da ita.”

Da sauri Anty Zainab ta sha gabanta ta tsaya ta rik’eta tace
“Sadiya nutsu!!”
Da d’an k’arfi
sannan ta d’ora da cewa
“B’ata lokacinki kawai za kiyi,
dan na tabbatar ko ganinta ba zaki samu damar yi ba.
Kinaji dai ance miki masu gadi har da sojoji ake gadin gidan
In ba so kike ta saka ayi miki shegen duka a kulleki ba to ki koma ki zauna mu nemi mafita dan fad’a da hayaniya da ita bata taso ba saboda ba iyawa za muyi ba!
Ki bari mubi ta ruwan sanyi
sai mu nemo mafita…”
Da kyar ta jaa Umma ta zaunar da ita a bakin gado tanata huci.

A hankali Jalila ta share hawayenta tace
“Bara in yi wanka da ruwan zafi tukunna. Jikina duk ciwo yake yi.”

Cike da tausayin ta Anty Zainab tace
“Maza je ki yi, akwai
ruwan da na d’aura za muyi d’an wake cike da tukunya, idan kin juye sai ki mayar da wani”

Purse d’in wayarta kawai ta ajjiye ta fice ta nufi hanyar band’akin…
Da ikon Allah kawai sai ta tsinci kanta da
shiga tsananin tashin hankali sakamokon kyankyamin bakin rijiyar ta su da k’ofar band’akin da ya shigeta lokaci d’aya!
Tabbas daman ta san ba zata iya rayuwa a gidan nan ba yanzu!
Amman ita a nata tunanin abinci ne da wajen kwana zai fi damunta.

Da kyar! Tsigar jikinta tana tashi ta samu ta d’auki bokitin da ta gani ta wuce cikin kithchen d’in
ta juye ruwan.

Hankalinta bai gama tashi ba
sai da ta shiga cikin band’akin!
Yayi mugun yin datti yayi dama dama gashi dama yana fama da nashi yanayin na tsufa da rashin had’uwa, yanzu kuma yazo ya had’a da rashin kula..
Har wani gansa kuka yake yi
ga wani ruwa bak’i k’irin a kwance mai uban yawa da wari da alamar makwarar rufewa tayi!
A ranta tace “tabbas Mama bata gidan nan.”

A hankali ta shiga ta ajjiye bokitin ta hau zame kayan jikinta…
Ta sak’ale a jikin k’aure.

Kasa wanka da soson wanka nasu tayi dan shi kanshi abun kyankyami ne!
Sabulun kawai ta iya d’auka shima saida ta wanke shi sau uku tukunna ta iya murzawa a jikinta…
Sai da tazo kwara ruwa tukunna taji inama batayi wankan ba! Dan duk zubawa idan tayi sai na k’asan nan mai uban wari wanda ta tarar ya taru ya fallatso mata jiki…
Kamar ta fashe da kuka haka take ji….a hankali ta hau zuba ruwan a hanakali..
Ta ci sa a kuwa ya daina fallatso mata d’in amman yadda ruwan kumfan jikinta yaje ya had’e da ruwan dattin nan ba k’aramin kyankyami ya k’ara mata ba!
Ganin ba zata iya jurar gani ba ya sanya ta runtse idanuwanta ta fara laluben kayanta
Cikin rashin sa’a ta bi takan d’an guntun sabulun da ya b’antare ya fad’i wanda ta gama wanka da shi yanzun!
Aikuwa santsi ya d’ebeta…
Sai da k’afafuwanta gaba d’aya suka bar k’asa tukunna ta dawo ta fad’o gaba d’ayanta a cikin ruwan da take jin kyankyamin kalla!.
Wata razananniyar k’ara ta saka!!!
Da gudu Umma da Anty Zainab waenda suka juyo ta suka fito suka nufi band’akin.

A cikin ruwan suka tarar da ita ta runtse idanuwanta da k’arfi ta k’ame waje d’aya tanata kurma uban ihu!
Su kansu sai da suka ji kyankyami da suka d’agata.
Da kyar suka iya kamata suka mik’ar tanata faman ihu mai had’e da kuka sannan tak’i ta bud’e idanunta…
Anty Zainab ce ta d’au botikin ta fice taje ta janyo ruwa a rijiya sannan ta koma ta d’auko silifas d’inta ta dawo band’akin suka shiga
shek’a mata ruwa!
Sai da suka juye mata ruwan botikin sannan suka rufa mata zani suka fito da ita tana wani irin kukan tashin hankali.

Da kyar aka samu ta bud’e idanuwanta, nan da nan zazzab’i ya rufar mata
dan haka ta k’udundune cikin bargon da shi kanshi kyamarshi take yi ta hau rawar sanyi............



NASARAWA gra.
Tunda ya dawo bai ganta a d’akin ba. Tana d’akin su Shuraim dan ita ba gwanar yin chatting ko danna waya bace ba shiyasa in dai su Shuraim d’in sunanan take zuwa wajensu..ko suyi ta hira ko kuma su yi game.

Yauma suna lunch ita da Ummi suka shigo, shiyasa suna gamawa suka d’unguma suka yi d’akinsu.


Har ya fito zai je sallar isha bai ganta ba, sai Ummi kad’ai ya gani tana shirya dining
dan haka kawai yace
“Ummi ina Huda?”
Kamar an fisgi maganar a bakinsa.

Ita kanta Ummi sai a lokacin taga rashin kyautawar ta
dan ya kamata ace ta tura ta wajensa, amman ya dawo wajen awa nawa har yanzu bai sanyata a idanunsa ba!.
Gaba d’aya abubuwa ne suka yi mata yawa shiyasa hankalinta bai je nanba.

Sai da ta d’anyi murmushi sannan tace
“Sorry Aslam.
Tana kitchen.
Wani abun ne ya shamin kai shiyasa kaga ban turo maka ita ba.”

Murmushi kawai yayi yana kallonta, kamar zai ce mata wani abun sai kuma kawai ya sa kai ya fita....


BAYAN KWANA BIYU.
Kamar kullum yau ma bayan isha suka gabatar da dinner d’insu, cikin nutsuwa da farin ciki.
Daga haka aka fara watsewa
Dining d’in ya rage daga Abba sai Huda da Ummi.
Huda tana mik’ewa shima
ya fara k’ok’arin tashi,
da sauri Ummi tace
“Am, Abba dan Allah ina son zan je wajen Mama gobe Huda ta rakani”

Bata yi tunanin zai kula ta ba,
ga mamakinta sai taji yace
“Yin me?”

A hankali tace
“Akwai wata y’ar magana da nake so mu yi.
Ni da ita”.

“Wa ta shafa?”

Kame kame ta fara chan tace
“Dan Allah Abba.
Hak’uri nake so in bata
akan abunda na yi mata”.

Tab’e baki yayi
sannan kawai yasa kai ya wuce ba tare da yace komai ba.


Huda na shiga d’aki ta tarar da shi as usual yana aiki.
Waje ta samu ta zauna a gefen gadon ta d’auko waya suka hau chatting ita da Sakina.

“Baki iya gaisuwa ba”
Taji muryarsa.

Turo baki tayi kafin tace
“Ina wuni”
Dan Sakina labari take bata za a kawo kud’in aurenta
so bataso ya katseta.

Be ce mata komai ba, ya kyaleta.
Sai da ya kai inda yake son zuwa sannan ya kashe computer yace mata
“Zo”

D’agowa tayi tana kallon shi irin ‘ni?’.

Gira d’aya ya d’aga mata alamun ‘eh’.

A hankali ta mik’e ta ajjiye wayar sannan ta k’arasa inda yake.

Gefensa ta kalla kan kujerar

Download complete TXT · Novel page