So da Buri 3

Chapter 16 of 36

ga wani abu a hannunta tana sha suna d’an hira..........

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
64


Mikiya Writers Association.
Da d’an saurinta ta fita ta nufi gate saboda ta ji Sakina tace mata ‘ta yi sauri’ Kuma ta ji muryarta dishi dishi
sannan kamar maa fa ba muryar Sakinar ta ji ba!

Gidan ba kowa shiruu, bak’in duk an watse kasancewar kowa da motarsa yazo wasu kuma drivers ne suka kawosu suka tsaya suka jira su
shiyasa ana gamawa kowa ya kama gabanshi.

Sai da ta kusan kaiwa gate tukunna ta danna kiran Sakina.
Bugu uku ana hud’un ta d’auka, tana d’auka Hudan tace
“In fito ko za ki shigo?”

Da mamaki Sakina ta zare wayar daga kunnenta ta kalli sunan sanann ta mayar tace
“Ki fito Ina?
Ina zan shigo?”

Turuss!
Haka Hudan taja ta tsaya
itama ta zaro wayar ta kalli sunan kafin ta mayar tace
“Sak’on fa da kika ce za ki bani?”

Cikin rashin fahimta Sakina tace
“Wanne sak’o?”

Ahankali Hudan ta sauk’e ajiyara zuciya tace
“Dan Allah Sakina bar wasa, yanzun nan ki ka kirani kika ce in fito kin manta sak’o in zo in karb’a da sauri…”

Cikin katseta a d’an firgice Sakina tace
“Hudan yi sauri ki koma gida
maza maza yanzun nan!
Inaga kidnappers ne suka yi hacking wayata
sun ga yau kuna taro.
Yi maza ki koma ciki da sauri
kar ki sake fitowa.”

Da sauri kuwa Hudan ta juya k’irjinta yana dukan uku uku!
Har da d’an gudu ta shiga had’awa da shi.

Parlourn ba kowa shiruu, nan ma duk an watse….
Haka nan ta wuce kitchen d’in jikinta yana karkarwa tana salati.

Tana shiga taga kamar an fita ta k’ofar baya!
Dan haka tsoronta ya sake nunkuwa.

A hankali ta shiga takawa tana kallon k’ofar da aka bi aka fitan dan gani take yi kamar har yanzu ana tsaye jikin k’ofar ba a matsa ba!

“Huda”
Ummi wadda ta shigo yanzu taga tana sand’a ta kira sunanta.
A mugun tsorace tace “wayyo Allah!!” Sai kuma ta juyo jikinta yana karkarwa.

Dariya Ummi tayi kafin tace
“Matsoraciya!!!
Ai kuwa gara tun wuri ki yakice wannan tsoron saboda gidan da za ku zauna a UK inaga ya kusa rabin wannan…
D’azun Dad yake gaya mana
Granpa although yana fushi da Aslam akan ki
amman ya kasa jurar fushin da yaji labarin zaku koma UK
ya bashi kyautar gida da mota a chan.

A hankali ta kalleta kamar za tayi magani sai kuma ta sunkuyar da kai kawai
kafin ta juya ta nufi inda ta ajjiye had’in coffee d’in Aslam.

Murmushi Ummi tayi,
ganin kamar Hudan bata son maganar yasa itama ta kawar da zancen ta hanyar cewa
“Yauwa coffe d’innan na biyo!
Gaba d’aya drinks d’in nasu na yau zak’iii sosai kaina har sarawa yake yi idan nayi sipping.
Allah yasa baki saka sugar da yawa a wannan ba, bana
son sake saka wani abu mai sugar sosai a baki na.”

A hankali Hudan wadda duk jikinta yayi sanyi daga fitarta zuwa yanzu tace
“Eh.
Naga kamar shima baya so sosai shiyasa dama zan
ajjiye mishi a gefen tray d’in in yana so sai ya k’ara.

Murmushi Ummi tayi sannan tace
“To za a zuba min inshaa ne
ko sai na jira an fara kai mishi ya d’iba?”
Ta k’arashe tambayar cikin sigar tsokana.

Murmushi mai had’e da y’ar dariya Hudan tayi
kafin tace
“Haba Ummi”
Tana mai juyawa ta d’auko cup mai d’an girma, ta dawo ta hau tsiyaya mata.
Sai da ta kusan cika kofin tukunna Ummin tace
“Okay tam ya isa haka na gode dota, Amaryar Aslam.”

Sunkuyar da kai Hudan tayi…Ta lura Ummi so take sai taga ta saka ta tayi walwala
shiyasa kawai ta d’an sake
suka hau hirar yadda birthday d’in ya kasance, suna hirar tana juye coffe d’in a cikin flask……..


Ummin kuwa daman hakan take so dan ita kunyar Hudan ma take ji akan abunda aka yiwa Sakina yau gashi saboda su Shuraim takanas ta zo
shiyasa ta dinga janta da wasa har sai da taga ta d’an sake
tukunna ta shirya bata hak’uri akan abunda ya farun!
A lokacin Huda har ta juye
ta had’a tray ta d’aura cup da spoon da sugar tana shirin d’auka Ummi tace
“Amm Huda
iwant to apol....”
Kamar an mak’ale ta haka maganar tata ta tsaya cak!

Da sauri Hudan ta ajjiye tray d’in ta nufeta saboda yadda tana juyawa taga Ummin ta damk’i wuyanta kamar zata shak’e kanta sannan ta runtse idanuwanta.

Da kyar Ummi ta iya cewa “ya subahanallah!”
Sai kuma ta zube a wajen ta fara tari…..


“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Hudan ta ambata a firgice da k’arfi!
Sakamokon ganin jini yana fitowa daga bakin Ummi wadda take nan k’asan tiles d’in kitchen d’in kwance tanata tari.

Da sauri ta durk’usa ta hau jijjigata tana “Ummi! Ummi!! Ummiii!!!
Abbaaa! ya Aslam!
Ya Arshaad!
Ummi ki tashi..”


Kuka take tana ihu tun k’arfin ta dan tun lokacin da ta durk’usa akan Ummin ta ga ta daina motsi sannan jikinta ya sake.

Da gudu ta mik’e ta nufi k’ofa da niyyar fita ta kira jama’a azo a kai Ummi asibiti…
Tana gudu tana juyowa tana kallon Ummi
bata yi auni ba taji ta fad’a jikin mutum!
Da sauri ta d’ago tana kallon Arshaad wanda shima ita d’in yake kallo bakinsa yana d’an rawa da alamun magana yake son yi amman ya kasa.

Cikin kuka ta hau juyawa tana nuna mishi Ummi wadda ke nan kwance a k’asa kan tiles!
Sannan ta juya da gudu ta nufi Ummin tana cewa
“Harda jini! Tama daina motsi”
tana mugun kuka.

Da kyar Arshaad wanda gaba d’aya ilahirin jikinsa ya d’au karkarwa tun lokacin da ya ga Ummin nan kwance, ya taka ya k’arasa inda Hudan da Ummin suke.

Da sauri ya durk’usa a wajen a mugun rikice yace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Kawai kuma sai hawaye ya biyo ta idanunsa.

Da sauri Hudan tace
“Ya Arshaad dan Allah kar ka ce ta mutu!
Wallahi bata mutu ba!
Bata mutu ba!!
Ka kaita asibiti zata farfad’o.
Dan Allah ka kaita asibiti..
Ummi ki tashi!
Abbbbbaaaa!!!”
Ta sake kwala kiran Abba dan taga Arshaad d’in yak’i motsi kwata kwata so ba lalle ya iya tab’uka komai ba,
da alamun ya yi mugun firgita da ganin Ummin.

A rikice Aslam ya afko cikin kitchen d’in sanye da bathrobe a jikinsa da alamun ma bai gama wankan ba dan har da y’ar kumfa a gefen kumatunsa.

Ganin Ummi yasa shima ya k’araso ciki da mugun gudu ya durk’usa a inda suke
dai dai nan su Shuraim suma suka k’araso cikin kitchen d’in.

Sai ga Mom itama ta shigo tana cewa
“Ife ifen me nake ta ji ne wai hak……?”
Muryarta ce ta katse sakamokon kitchen d’in da taga cike da jama a a nata ihu ana kuka!
Dan su Shuraim suma suna shiga suka yi kanta sukai joining Hudan a kukan.
Da sauri ta k’arasa tana cewa “waye ba lafiya ne mai ya far..”
Maganarta ce ta katse sakamokon had’a ido da tayi da Aslam! Sanye cikin bathrobe…
Da mamaki take kallonsa har da y’ar kunfar sa a gefen fuska, har zata yi masa maganar fitowar dayayi half naked dan bathrobe d’in bata da wani tsayi sosai sai kuma kawai ta shareshi dan jin dalilin kukan da take ji ne priority yanzun.
D’auke kanta tayi ta maida inda su Hudan suke durk’ushe….

Dishi dishi ta fara gani
sakamokon Ummi da ta gani kwance bakinta duk jini!
A hankali jikinta na mugun karkarwa tace
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Sai kuma ta tafi luuuuuuu ta sume a wajen…


Sudais da Shuraim ne suka fara k’ok’arin ciccib’ar Ummi
dan haka Hudan ma ta sa hannu suka d’auketa.
Aslam yana ganin haka ya bisu a baya duk ya rikice…
Da gudu ya wuce su ya shiga d’aki ya d’auko mukullin
motarsa ya mik’awa Huda yace “su jira sa”
Sannan ya koma ya zura jallabiya mai kauri daman already ya saka boxes a k’asan bathrobe d’in! Ya
fito ya bi bayansu.

Yana zuwa ya kunna motar already sun gama shiga
suka yi gaba kowa hankalinsa a tashe sai kuka su Hudan suke yi.

Da kyar Arshaad ya iya mik’ewa ya d’auko ruwa a fridge ya shiga yayyafawa Mom……
Har ya d’an fara tsorata dan da farko k’in farkawa ta yi, kafin
daga baya kuma ta farka a firgice tana salati sai kuma ta tashi ta zauna ta fashe da kuka!
Kallon inda taga Ummi d’azun tayi ganin ba kowa sai d’an ragowar jini jinin da aya zuba a k’asa ne yasa a rikice ta juyo tana kallon Arshaad
kafin tace
“Tana Ina?”

Bai ce mata k’ala ba!
Dan kanshi a mugun d’aure yake ‘jini, Ummi, how?’
Sune abubuwan da suka taru suka hautsina mishi kwakwalwa.

Mik’ewa kawai yayi ya wuce d’akinsa ya d’auko key ya cire rigar suite d’in jikinsa ya rage daga long sleeve sai dogon wando da belt, ya fito ko cover shoe d’in k’afarsa bai tsaya chanjawa ba.

A parlourn ya tarar da Mom tanata faman safa da marwa
Yanzun ma bai kulata ba ya wuce ita kuma ta bi bayanshi da sauri suka fice.

Sai da suka shiga motar ya kunna tukunna ya kira Aslam.
Shuraim ne ya d’auka, nan yake tambayarsu “suna Ina?”
Cikin kuka yace
“Basu riga sun k’arasa asibiti ba amman duk wanda suka samu mai kyau nearby nan za su je”

Ajiyar zuciya Arshaad ya sauk’e daga nan ya katse kiran ya tada motar ya fice daga gidan.

Driving kawai ya hau yi towards asibitin da ya san yana a kusa dasu mai kyau….
Kamar had’in baki kuwa
yana shiga ya hango motar Aslam nurses suna d’aura Ummi a akan gado.
Yana k’arasawa yayi parking suma suka fito suka
d’unguma gaba d’ayansu suka rufa musu baya.

Da kyar aka iya tsayar da su Shuraim da Hudan daga shiga investigation room d’in…haka nan suka dawo in banda
kuka ba abunda suke yi.

Da sauri Mom ta k’arasa ta jawo Sudais da Shuraim ta rungumesu itama tana kuka.

A hankali Aslam ya k’arasa inda Hudan take tsaye tana kuka, ya juyo da ita ya rungumeta a hankali ya shiga bubbuga bayanta.

Da sauri Arshaad ya tashi ya fita a wajen waya kare a kunnensa. Dad, yana amsa wayar ya fad’a masa halin da ake ciki daga nan
ya nemi waje ya zauna a harabar asibitin..


BAYAN MINTUNA TALATIN.
Cirko cirko haka kowa yake tsaye sun cika wajen
Dad Daddy Aslam Abba Mom Mammy Gramma Mommy Arshaad Sudais Shuraim da Hudan!
Kowa ka ganshi ka san hankalinsa a tashe yake dan
ko zama ba wanda ya iya yi.


K’arar bud’e k’ofar inda aka shiga da ita suka ji, dan
haka duk suka juya suka zubawa Likitan da ya fito ido.

Yana kallonsu ya yi saurin sunkuyar da kanshi
kafin ya zare glasses d’insa yad’an murza idanunsa sannan ya mayar ya d’ago ya kalli Aslam yace masa “follow me”

A hankali ya zame hannunsa a cikin na Hudan ya bi bayan Likitan..


BAYAN MINTUNA BIYAR.
A hankali Aslam ya bud’e k’ofar office d’in ya fito, kamar
wanda aka zarewa laakka a jiki haka yake taku, sai da ya kusan k’arasawa corner da in ya shiga zai gansu tukunna ya zaro wayarsa ya danna kiran Granpa!

Yana karyo kwana suka yo kanshi gaba d’ayansu suka hau tambayarsa….

Kallonsu kawai yake yi da waya kare a kunnensa, sai ya
bud’e baki kamar zai yi magana sai kuma ya kasa.
Jijiyoyin kansa sun yi rud’u rud’u! Gashi idanuwansa sun kad’a sun yi jaaa!
Wanda hakan ba k’aramin sake gigita ahalin yayi ba.

Sai da wayar ta kusan katsewa tukunna Granpa ya d’auka!
Jin shiru yasa yace
“Talk to me Aslam”

A hankali bakinsa na rawa yace “Granpa, its Ummi!
Incase you have something to say to her…
Likita yace she has less than 1 hour.”

“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Shine abunda kowa ya hau maimaiitawa a zuciyarsa dan
k’amewa k’am! Gaba d’ayansu suka yi kamar an d’auke musu numfashi haka wajen yayi tsit!.

A hankali kukan Gramma ya fara tashi followed by na Mom da Mommy sai su Sudais da Huda…
Tashi d’aya kuma sai wajen ya hautsine! Masu hawaye nayi masu kururuwar kuka ma suna yi.

Da kyar Abba ya iya k’arasawa ya dafa Aslam yace
“What happened to her?”
Jikinsa yana mugun karkarwa.

A hankali da kyar ya iya cewa “poision ta sha!
Ya tsinkamata gaba d’aya hanjinta
The Soctors where even shocked! Ta yadda take numfashi har yanzu.”

A rikice Abba yace
“Poison kuma?
How? A ina?
Wa ya bata poision?”

D’agowa yayi ya na kallon Hudan yana son tambayar ta ‘ya aka yi?’
Ganin yadda gaba d’aya hankalin jama’ar wajen ya koma kanta ne
ya sa kawai ya d’auke kai.
A hankali yace
“Ihun Hudan kawai na ji, ina
zuwa na ganta tana tarin jini.
Ba mu san a ina ta sha ba.”

Da sauri Mammy ta matso tana matsar hawaye tace
“Ta ya zaka ce baka san a ina ta sha ba!?
Ga wadda za ku tambaya nan?”
Tayi maganar tana nuna Hudan.

Cikin karkarwar jiki Hudan tace
“Ban san a ina ta sha ba”

Dasauri cikin katseta tace
“Ai tare kuke! Dan haka dole
kinga ta sha wani abun.”

Cikin rashin fahimta Hudan tace
“Ina cikin had’awa Ya Aslam coffe ta zo tace zata sha, sai
na zuba mata a cup
That was the only thing da naga ta sha daganan ta fara tar..........”
Shiruuu, tayi ta kasa k’arasawa sai kuma a rikice ta d’ago tana kallon Mammy wadda ita ma itan take kallo kafin ta matso kusa da ita tace
“Hudan we all know
ba kya k’aunar Aslam!!!
Da kika zo kashe shi kika san kin yi poisioning coffe d’insa! Me ye laifin Ummi da zaki had’a har da ita ki bari ta sha?”

Cikin tsananin tashin hankali Hudan take kallonta zata yi magana Mammyn ta katse ta ta hanyar sake cewa
“Ko jifan tsuntsu biyu kike son yi da dutse d’aya?
Because it’s obvious yanzu babu abunda zai sake shiga tsakanin Maryam da Abba!”

Wani kalar kuka da Hudan take yi sai da ta kusan shid’ewa!

Zata yi magana Mammy ta sake cewa
“Wachche irin zuciya ce da ke Hudan? Na tabbatar idan kika rok’i Aslam kika ce ya sakeki tsaf z........”

Da mugun k’arfi Aslam wanda ya zo iya wuya yace
“Mammy!!!”
Wanda gaba d’ayansu sai da suka razana! Kowa ya d’auke wuta……..

A hankali Abba wanda tun lokacin da Mammy ta fara magana ya runtse idanuwan ya bud’e ya kamo hannun Aslam yace
“Za a iya ganinta ko?”

Sai da ya d’an dedeta kansa tukunna yace
“Eh” ba tare da ya kalleshi ba
dan wani kalar kallon kallo suke yiwa juna shi da Mammy wanda da ace Mammyn ta san kallon da Aslam d’in yake yi mata to daa ba zata yarda ta bar kwayar idanunta a cikin nasa ba.

D’akin da aka shiga da ita sanda aka kawota nan Abba ya shiga dan basu ga lokacin da aka fito da ita ba.

Sai a sannan Mommy ta matso ta jaa hannun Aslam suka fice daga wajen gaba d’aya.

Suna fita Mammy ta sake juyowa kan Hudan a karo na biyu tace
“Yau wallahi mai kwatar ki a hannuna sai Allah,
kin san ya Ummi take a wajena kuwa......”

Banda kallon Mammy ba abunda Mom take yi tana wani irin kuka, so take tayi magana amman ta ma kasa.

Cikin fushi Mammy ta yi kan Huda kamar zata shak’ota.

Damk’ar hannunta d’in da Dad yayi ne ya sa ta juyo tana kallonsa!
Ba tare da ya kalleta ba
ya jaa hannunta da mugun k’arfi ya fita da ita……
Sai da ya sakata a mota ya cewa driver ya maida ta gida tukunna ya juya ya koma ciki ba tare da ya bi takan bak’ak’en maganganun da take jefa mishi ba.

Mammy kamar zata mutu haka ta ji, wato bashi da time d’in da zai yi mata magana sai in zai wulak’antata sannan a gaban mutane ko kuma in ba su kad’ai bane to ya kan kulata.
Gashi yanzu Arshaad shima ya fara, tsabar wulak’anci ga ta ga shi amman iya gaisuwace kawai take shiga tsakaninsu, d’azu taje d’akinsa har sau biyu baya nan
a na ukun kuwa da tayi sa a yana nan tana shiga ya mik’e ya fita ya barta kamar ba uwar da ta tsugunna ta haifesa ba,
bama fa ta san ya dawo ba sai a gidan kawai ta ganshi!
Takaici da b’acin rai kamar ta d’aura hannu aka tayi ta kurma ihu........


A kwance ya ganta da oxygen da wasu na’urori tana janyo numfashi da kyar!
A hankali ya k’arasa wajen ya tsaya a dede kanta yace
“Ummi”
Sai kuma wasu zafafan hawaye suka shiga sintiri a kan kyakkyawar fuskarshi.

A hankali ta shiga bud’e idanunta…
Tun tana ganinsa dishi dishi har ta d’an fara ganinsa sosai
dan haka ta fara k’ok’arin mik’ewa.
Da sauri yace
“Nooo..
Stay still”
Sai kuma ya juya ya janyo wani stool ya zauna a kai ya kama hannunta ya rik’e.

A hankali ta d’an jaa oxygen d’in k’asa, tace
“Naji Likitan yana cewa poision na sha ko?
Wai hanjina sun tsitstsinke.”

A hankali Abba ya kawar da kansa yayi amfani da free hand d’insa ya share hawayen fuskarsa kafin ya juyo yace
“You are going to be okay”

Murmushi ta yi a hankali tace
“K’arya fa ba halin ka bane
Abba”

This time around kuka ne ya kufce masa…
A hankali ya kamo hannunta ya d’ago ya kai setin bakinsa yayi kissing hannun
cikin kuka yace
“Ki yi hak’uri Ummi.
Dan Allah ki yi hak’uri.
Na nuna miki k’iyayya,
ni kaina naji ina jin haushin kaina ballantana ke.”

Murmushi tayi
a hankali tace
“Ko sau d’aya ban tab’a jin haushin abunda kake min ba Abba
remember
tun muna Yara
na sha gaya maka
‘ko menene idan kayi burgeni yake yi’
dan haka kar kayi tunanin na rik’e ka a zuciyata!
Zuciyata iya kar k’aunarka da tsananin son ka ta sani
bata san wani abu akasa sin haka ba”

Download complete TXT · Novel page