So da Buri 3

Chapter 17 of 36

Ta k’arashe maganar tana d’an murmushi.

Kuka ne sosai ya kufcewa Abba.

A hankali take d’an matsar hannunsa wanda yake rik’e da nata tace
“Good bye Abba,
ka kulamin da su Shuraim dan Allah, har da Hudata itama
ka cigaba da kula min da y’ay’ana.”

Cikin tsananin kuka yace
“Ummi ki yi shiru..
Fad’ar Likita ba fad’ar Ubangiji bace ba. Ki yi shiru da waennan maganganun dan Allah.”

A hankali tace
“Lokacina yayi!
Tun ba yau ba na fara jin hakan a jikina.”
Shiruu ta d’anyi kafin ta lumshe idanunta ta bud’e a hankali tana ganin dishi dishi tace
“Ina takaicin
Ba zaka dinga tunani a matsayin masoyiyarka ba
bayan raina! Sai dai
a matsayin wadda ta sanya rayuwarka a k’unci
ta saka ka tunani da bak’in ciki. Da ace za a bani chance d’in da zan iya komawa farko
to da na fita a rayuwarka kayi farin ciki daga farkonta har k’arshe.”

Cikin katseta yace
“Ummi mun wuce wannan wajen, na fad’a miki
na riga na yafe miki na manta da komai.
Ba zan tab’a tunoki a matsayin wadda ta sanya rayuwata k’unci ba sai a matsayin ki na matata!
Amaryata!
Uwar y’ay’ana!
K’anwata
sannan
masoyiyata
wadda take tsananin so na.”
A hankali ya matso da bakinsa ya d’aura a kan goshinta
yayi kissing yana kuka
ya d’an d’ago yana kallon idonta yace
“I love you, Zainab”

Wasu zafafan hawayene suka shiga zubo mata,
a hankali tace
“Now I’ll have a nice nap!
In sha Allah.
Thank you.”

Kasa ci gaba da zaman yayi dan haka ya mik’e da sauri ya fita a d’akin yana kuka sosai.


Yana fita Hudan Shuraim da Sudais suka shigo.
Tana jin kukan su ta fahimci sune suka shigo
dan zuwa yanzu ba
sosai take gani ba.
A hankali ta bud’e musu hannuwanta alamun su je gareta. Da sauri kuwa suka nufeta suna zuwa tayi hugging d’insu gaba d’aya….

A hankali suka cikata suka matsa gefe suna kuka.
Cikin kuka Huda tace “Ummi wallahi ban san poison bane ba”
A hankali Ummin ta katseta ta hanyar cewa
“Shhh”.

Sai da ta ga ta d’anyi shiru
sannan tace
“Magana d’aya zuwa biyu nake so in gaya muku…
Ku had’a kanku ku so junanku ku rik’e zumunci a duk inda kuke ku rik’e amana
dan Allah
sannan kar ku cuci wani..”

A hankali Granpa ya turo k’ofar ya shigo
Idanuwanshi sun yi jajawur!
Tun lokacin da Gramma ta fad’a mishi ta fito sam sai ya gagara sukuni
shiyasa shima kawai ya yanke shawarar zuwa asibitin. Yana hanya ma lokacin da Aslam ya kira shi ya fad’a mishi abunda Likita yace.

Da kyar ya taka da y’ar sandarshi ya k’arasa bakin gadon.
Inda Abba ya tashi nan ya zauna tukun
a hankali yace
“Ummi”

Juyowa ta yi sanann ta d’an d’ago hannunta tana k’ok’arin kama nasa.
A hankali ya kamo hannun nata da nashi hannayen duka biyu ya rik’e.

Inda su Shuraim suke a tsaye yanzu tun shigowar Granpa ta d’an kalla kafin tace “ku bamu guri”.

Har sun juya za su fita suka ji tace “Allah yayi muku albarka”
Sai da suka juyo gaba d’ayansu tukunna suka ce “Ameen Ummi”
Sannan suka juya suka fita suna wani irin kuka.

A hankali ta maida idonta inda take Jin Granpa tace
“Daddie, dama inada niyyar bada sak’o a baka koda ace baka zo ba.
Na gode kuma naji dad’in zuwanka.

Maganata ta farko
Itace
Godiya!
Kasancewar ka Uncle kuma Uba a gareni
Is one of the luckiest thing da kuma nake alfahari da a rayuwata.
Tun tasowata har kawo yanzu bana jin akwai abunda na tab’a nema na rasa shi, baka
rage ni da komai ba
akoda yaushe k’ok’ari kawai kake yi kaga nayi dariya na samu abunda nake so!
Na gode kwarai Daddie
bana jin aduniyar nan a kwai d’iyar da tayi sa’ar samun uba mai tsananin kaunarta kamar ni.”

Runtse hannunta da yake a cikin nashi hannayen yayi
hawaye ya fara sintiri akan tsohuwar fuskarshi.

A hankali dan muryarta tayi low zuwa yanzu
ta ci gaba da magana
“Sai magana ta biyu
Shawara ce zan baka!
Iyaye da manya suna ganin kamr duk abunda babba yayi shine dai dai
alhalin wasu lokutan wani babban yana yin abunda ko d’an shekara tara ba zai aikata ba saboda ya san ba dede bane ba
amman tsoro da fargabar gayawa wannan babban gaskiya sai a sanya ido ayi shiru a nad’e hannu a koma gefe a taru ayita tafka b’arna!”
Shiruu, ta d’anyi tana k’ok’arin jawo numfashi kafin tace
“Same thing da yake going a estate d’inmu kenan…
Ka yi hak’uri da abunda zan fad’a yanzu
Kai da kanka da hannunka ka hargitsa estate d’innan wanda yanzu abunda ya faru yau yasa na tabbatar da hakan kuma inajin takaicin rashin sanin k’arshen wannan bala’i da musiba da ta shigo mana ko kuma ince muke ciki tsundum ba tare da mun sani ba.
Granpa dan Allah dan Annabi
the first thing da zan rok’eka shine
ka daina nuna bambanci!
Yanzu ni
ba a maganata
amman in baka tashi ka tsaya ka gyara tsagwaran bambancin da kake nunawa a tsakanin Aslam Auwal da Arshaad ba to
akwai matsala babba!.
Bani da tantama bani da shakku akan Aslam akaso ayi poisioning yau ni kuma na sha ba tare da na sani ba!
Ban ce Arshaad ko Auwal bane ba amman dai na san dole a cikin estate d’in mu ne
wanda na tabbatar ata dalilin kyautar gidan da kayi mishi ne
da kuma ragowar abubuwan da kake tayi tun haihuwarshi har kawo yanzu,
sannan ina so ka san
wallahi tallahi ba Huda bace ba”.
Numfashinta da ya fara sark’e wa ne yasa ta yi shiru ta hau kokawar janyowa….

Da sauri Granpa ya mik’e ya fara kiran
“Doctor!!”

Ruk’o hannunshi tayi tace
“One last thing
abunda nake so
abunda idan kayi min zan ji dad’i shine
Granpa dan girman Allah
da manzonsa
ka yi hak’uri ka daure
ka yarda sannan ka taimaka wa Abba ya maida Maryam!
Ka yi accepting d’inta ita da Huda
Dan Allah Granpa
sannan ka tayani neman yafiyar mutum uku
Maryam Aisha da Huda!
Although na san su Maryam sun yafe min
amman Ina buk’atar ka sake nema min yafiyarsu”
Tana gama fad’in haka numfashinta ya fara sama
maganar ma da take son sake yi ta sark’e harshenta ya fara fidda maganar da ba ita ba!
Da sauri Granpa ya sake cewa
“Doctor!!”
Da k’arfi yana zubarda hawaye da k’ok’arin barin wajen amman sai yaji still ta sake rik’e hannunshi tak’i saki.
Juyowa yayi suka had’a ido yaga yadda idanuwanta suke shirin k’afewa tana ta
faman kokawa da numfashinta!
Da sauri ya k’arasa yayi cupping fuskarta
yana kallon idonta yace
“Ashhadu allailaha illallah”

A hankali tace
“Ashhadu allailaha illallah”

Wani kuka ne ya taho mishi yanayi yace
“Wa ashhadu anna muhammadrasulullah”

Cikin jan numfashi da kyar tace
“Wa ashhadu anna muhammadrasulullah”

Dai dai nan Doctor nurse da ragowar ahalin MT gaba d’aya suka shigo d’akin ata dalilin kiran Doctor d’in da Granpa yayi….

Cikin tsananin kuka dan har idanuwanta sun k’afe
yace
“Salllallahu alaihi wa sallam”

A hankali yaji ta maimaita
daga nan dip! Komai nata ya tsaya ta chak! Ta daina k’ok’arin janyo numfashin da take ta faman yi yana wahalar da ita
K’arar naurar da aka jojjona mata shima ya chanja…….

Kifawa Granpa yayi abkanta yana tsananin kukan da rabonshi da yi tun ranar da Yaya da Doctor suka rasu..........


A hankali Likitan ya k’araso ya hau dudduba ta, chaan! Ya
d’ago agogon hannunsa ya duba kafin ya juya ya kalla nurse d’in da suka shigo tare yace mata
“Time of death!
1:30am”.

Kuka gaba d’ayansu suka saka lokaci guda, babu mai lallashin wani.

A hankali nurse d’in tace “su d’an bata guri zata gyarata ta saka mata auduga kar iska ya shiga kafin zuwa gobe tunda ta san dole zatayi kwanan keso”
……………..
A waje suka samu Arshaad da Aslam suna zaune kowa yayi jugum.
Daman tunda suka ji Granpa ya kwala kiran Doctor sun san menene
shiyasa ma suka k’i shiga
yanzu kuma fitowar su kowa yana kuka ya sake tabbatar musu.

Da sauri Aslam ya mik’e ya fice a wajen haka shima Arshaad d’in dan basu san wa za su fara lallashi ba! Kowa ka ganshi kuka yake yi masu hawaye nayi
hatta Granpa ya kasa tsaida hawayensa.


Cikin mintuna 15 nurse d’in ta fito ta mik’a musu kayanta da ta saka a box tace
“An gama.
Saura rufe bill, daga nan
su wuce da ita”
A take Dad ya bita ya gama komai har file
sanann ya dawo suka turata kanainaye cikin farin bedsheet har mota shi da Daddy, su Mommy da Mom suka shigar da ita suna kuka.

Mom ce ta zauna a baya ta d’aura kan ta a kan cinyarta tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.

Mommy kuma a gaba Dad yana tuk’i, a haa suka kama hanyar MT..

Aslam shi ya ja su Huda da Shuraim da Abba
Arshaad kuma suka tafi tare da Daddy
Granpa kuma driver d’in da ya kawoshi ya maida shi tare da Gramma.

A hanya Granpa bai bari sun k’arasa ba ya kira Abba yace mishi “dan Allah a wuce da ita estate idan ba damuwa”

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
65

Mikiya Writers Association.
Direct side d’in Granpa aka nufa da gawar Ummi.

Kafin zuwa asuba Mommy da Gramma suka yi mata wanka suka shiryata.
Haka nan suka sakata a gaba suka dinga yi mata karatu da tofi tun jiyan dama suke yi
su biyar har Huda Shuraim da Sudais, suna yi suna kuka.

Ana idar da sallah
aka sanar jana’iza k’arfe 9:00am a masallacin estate, daga nan gaba d’ayan su kowa ya nufi side d’in Granpa.

Shiruu! Haka b’angaren ya kasance amman kowa da Al’quraninsa, masu hawaye suna yi suna karatun…..
Har zuwa lokacin da gari ya waye jama’a suka fara taruwa,
mak’ofta da suka ji ana ta lek’awa estate d’in ana gaisuwa, sai k’awayensu da family friends da suka ji ta wayoyi…..

K’arfe tara tana yi mazan suka shigo domin fita da gawar
sai a sannan abun ya dawo sabo! Abun tausayi
especially yadda Huda Shuraim da Sudais suka k’amk’ame gawar suna kuka kamar ransu zai fita!
Da kyar Arshaad ya janye Sudais
Auwal kuma wanda Daddy yaje ya d’auko ba da jimawa ba ya janye Shuraim
Aslam kuma yaja Huda!
Tukunna su Daddy suka saka gawar a makara aka fita da ita waje domin a sallaceta……

K’arfe tara aka gabatar da jana’iza aka mik’a Ummi gidanta na gaskiya.

Ta samu halarta d’umbin jama’a maza da mata
dan kamar yadda mak’abarta ta cika haka ma cikin estate d’in.

Suna dawowa Granpa ya cewa Abba “Su zauna anan (estate d’in) ayi zaman makoki
ba sai sun koma chan gidansu ba......


Washegari,
Sumayya Ummu da Baban su Sakina suka zo suka yi ma Huda da Abba gaisuwa.

Ranar sadakar uku,
Huda tana d’akin Gramma dan a nan take ita da su Shuraim
ta ji wayarta tana k’ara!
Tana d’auka Auwal yace
“Ta yi bak’o yana waje a bakin estate, wai ya zo mata gaisuwa, yace ‘sunan shi
Junaidu’ Ta sanshi
a barshi ya shigo?”.

Bata san lokacin da ta diro daga kan gadon ba
tace
“Eh Ya Auwal na sanshi sosai yayana ne!
A barshi ya shigo.”
Daga nan ta zari hijabinta
ta yi waje tana adduar Allah yasa Ya Junaidun ne da gaske.

Bata samesu a compound d’in Granpa ba daman bata yi expecting hakan ba!
Dan haka ta fice daga gidan
ta nufi tsakiyar main compound na estate d’in.

A inda ake parking motoci ta hango Auwal sanye cikin bak’ar jallabiya fuskarsa tayi fayau! Idanuwansa da suka ci kuka sun yi jaa sun k’ank’ance
yayi tsananin rama sannan kana ganinshi ka san bashi da lafiya….
A tsaye tare da wani ya juya baya sanye cikin shadda fara d’inkin boda da bak’ar hula
ya jingina a jikin booth d’in wata bak’ar mota Jeep!
Yanayin takalmi da shadda da kuma hular kansa kad’ai sun isa su sa ka san cewa kud’i sun zauna…

Da Auwal suka fara had’a ido
yana shirin yin magana
a hankali yaji tace
“Ya Junaidu”

Shiruu yayi da maganar da yake yi kafin ya gyara tsayuwarshi daga nan kuma ya juyo gaba d’ayanshi yana murmushi…..

Kusan daskarewa Huda tayi,
a hankali hawaye na gangarowa akan kumatunta ta ce
“Ya junaidu”

Murmushi yayi yace
“Na’am Huda”

Cikin share hawayenta tace
“Where have you been? Yaushe ka dawo?
Me ya faru?
How have you been..”

Murmushi ya saki mai d’an had’a da dariya kafin ya shafa k’asumbar da ya tara tayi mishi tsananin kyau yace
“Ya muka ji da hak’uri?”

A hankali ta sunkuyar da kanta tace “Alhamdulillah”
Cikin sanyin murya.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“Allah ya ji k’anta yasa chan tafi nan”

A hankali ita da Auwal suka ce “Ameen”

Kafin Auwal d’in ya juya ya yi mishi sallama ya wuce.

Gyara tsayuwarshi yayi yana kallonta kafin yace
“How are you?.”
Congratulations
you have finally found your Dad”

Jijjiga kai tayi sanann tace “Thank you”
Tana mai d’ago da kanta sannan ta sake jeho mishi tambayar
“Where have you been?”

Dede nan Arshaad wanda dawowar sa kenan daga airport d’auko Aaima suka k’araso wajen shi da Aaima.

Murmushi Junaidu yayi kafin yace “Arshaad!”

Da sauri Huda ta juya dan ita bama taga tahowarsu ba.

A hankali ta k’arasa inda Aaima take ta rik’e mata hannu tana kallonta kafin ta yi hugging d’inta.
Bata iya ce mata komaiba
Har ta cika ta ta d’ago.

Ahankali Aaima da muryarta ta d’an dishe tsabar kuka tace
“Ya hak’urin mu?”

“Alhamdulillah” Huda tace
Daga nan Aaima ta d’an d’ago ta kalli Junaidu wanda
ya kafe Arshaad da ido
tace
“Ina wuni”

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya juyo ya kalleta a hankali yace “Alhamdulillah.
Ya hak’uri?”

“Alhamdulillah” tace, daga nan tace “Ya arshaad bara in wuce ciki, thank you.”
Tana gama fad’in haka
ta juya ta wuce ciki.

A hankali Huda ta d’an juya ta maida hankalinta akan Arshaad kafin tace
“Ina wuni”

Ba tare da ya kalletaba ya ce “lafiya”

Junaidu Hudan ta kalla
wanda tun wucewar Aaima ya maida idanuwanshi a kan Arshaad tace
“Ya Junaidu baka bani amsa ba”

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace
“Actually..
Ni kaina ba zan iya ce miki ga a inda nake ba.
Forget all that bana so ma In dinga tunowa…”
Sai kuma yayi murmushi yace
“Congratulations
Na ji kin yi aure!”
Ya fad’i hakan yana kallon Arshaad kafin ya ce
“And kamar ba Arshaad kika aura ba ko?
Mai yasa?”

Da sauri Huda ta d’ago ta kalleshi, ganin ba ita yake kallo ba gaba d’aya hankalinshi yana akan Arshaad d’inne yasa tace
“Ya Junaidu”

Juyowa yayi ya kalleta,
a hankali ta jujjuya mishi kai
alamun ya bar maganar.

Murmushi kawai yayi yana maida idanunsa akan Arshaad still kafin yace
“No i was just curious ne
He has done so much
and a lot
for and because of you!
I wonder why bai samu aurenki at the end of the day ba…”

A hankali Arshaad ya d’ago jajayen idanuwanshi wanda har sai da suka so firgita Huda ya watsa su akan Junaidu
kafin yace
“Did you come here to mock me?”

Da sauri Huda ganin Junaidun yana sake shiri yin magana tace
“Ya junaidu ka daina mana.
Gaisuwa ka zo ko?
To kayi iya gaisuwar please.”

Shiruu yayi
ya d’an sunkuyawar da kanshi yana kallon k’asa
kafin ya d’ago yace
“Forgive my manners”
Yana kallon Arshaad
sannan ya juya ya kalli Huda yace “Allah ya ji k’an Ummi.
Bara in wuce, su
Umma ma basu ganni ba
dan ban je ko gida ba
I came here straight.”

Hudan gaba d’aya lamarin Junaidu ya d’aure mata kai!
Bai je gida ba?
Tou a Ina ya san Ummi ta rasu?
Sannan waya gaya mishi ta yi aure?….

“Sai anjima”
Ya ce yana d’an murmushi yana kallonta.

A hankali tace
“Na gode ka gaida su Umma”
daga nan ta juya ta wuce.

Wani abun mamamkin..
har ta kai gate
Arshaad da Junaidu suna tsaye suna magana
kuma da ga yanayin yadda suke demonstrating har da hannayensu zai sa ka fahimci serious magana suke yi.

Har ta hau sama d’akin Gramma ta lek’o ta window sai da ta gansu kafin chaan Junaidu ya bud’e motarsa ya shige ransa a mugun b’ace ya ja yayi gaba ya bar Arshaad nan tsaye a wajen….
Tana shirin juyawa sakamokon
k’amshin da k’ofofin hancinta suka jiyo mata, ta ji anyi huggin d’inta ta baya.
Runtse idanunta tayi da k’arfi!
A hankali dede setin kunnenta ta ji ya ce
“Haramun kike kalla fa”
Muryarshi na d’an rawa.

Da sauri ta d’an ture shi
kafin ta juyo tana kallonsa
sai kuma tayi saurin yin k’asa da kanta dan gaba d’aya
sa taji ba dad’i
especially ma yadda taga kamar ranshi bai so ba!
Sannan ba lalle ya fahimci kallon me take yi wa Arshaad d’in ba.

Tana shirin yin magana ya katseta ta hanyar cewa
“Who is the other guy?”

A hankali ta d’an sunkuyar da kanta kafin tace
“Ya Junaidu. Tare muka taso.”

Ajiyar zuciya ya sauk’e
kafin ya matso kusa da ita sosai kamar zai shige jikinta
yayi cupping fuskarta
a hankali ya d’ago da fuskarta yadda za su kalli juna sosai yana kallon cikin idonta yace
“Kar ki sake abunda kika yi yanzu, please.”

Yadda yayi mata magana
da yadda taga idanuwanshi sun yi da yanayin voice d’inshi
ya sanya ta kasa cewa komai
ta lumshe idonta kawai
tana jin yadda
jikinshi yake karkarwa a hankali…

Ya dad’e yana kallon fuskarta kafin ya cikata a hankali ya juya ya fita.

Tana jin fitarshi ta bud’e idanuwanta tana sauk’e ajiyar zuciya a jejjere….
Bayan rasuwar Ummi
Idan akwai abunda yafi damunta ya fi rikitata
tou Ya Aslam ne!
Kwata kwata ta kasa gane gabanshi ta kasa gane bayanshi ta rasa me yake nufi da ita, sannan ita kanta yanzu ba zata ce ga tak’ameme abunda take ji a kansa ba!
Adduar ta d’aya ‘Allah yasa ba ta

Download complete TXT · Novel page