So da Buri 3

Chapter 30 of 36

sai ta ga an kaisu hotel!
So take tayi tambayar ‘Ina Auwal d’in’ dan in akwai wanda tafi buk’atar gani ta ga lafiyar shi a halin yanzu tou Auwal ne..so take ta yi magana amman kuma kunyar su sai ta hanata dan haka kawai ta bi bayan Mom wadda take ta wani lallab’ata har suka isa k’ofar wani d’aki.

Wanda ya d’aukar mata akwati yana ajjiyewa
Mom ta bud’e d’akin ta ja suka shige bayan ta mik’awa Daddy makulli.

Suna shiga Mom ta rufe k’ofar kafin ta kamo hannun Sakina duk biyun ta rik’e, a hankali ta ce “Dota ki huta ki ci abinci
daga nan sai ki je asibiti wajen Auwal ko?”
Sai kuma ta d’an yi shiru
chan ta ce
“Ki yi hak’uri akan abunda na yi miki ranar birthday d’in su Shuraim, ki yafe min”.

A hankali Sakina ta ce
“Ba komai Mom ya wuce,
ki daina bani hak’uri dan
Allah”

A hankali Mom ta saka hannu ta yi hugging d’inta.
Sun d’an jima a haka kafin ta cikata ta juya ta fita tana cewa
“Yanzu za a kawo miki abinci,
ki ci ki yi wanka
sai mu zo mu wuce gaba d’ayanmu.”

Da “to” kawai ta iya binta dan ita har ga Allah so take kawai ta ji ance ta zo su wuce wajensa.


Ba yadda ta iya haka ta daddannna abincin ta yi wanka duk ranta a jagule.
Allah yaso su Mom basu wani d’auki time ba ta ji ana knocking..
Ta san sune
dan ta gansu ta jikin d’an TVn dake jone da cctv camera d’in gaban k’ofar, dan haka gudun ma kar a sake yin wani jinkirin
ta d’auko har handbag d’inta ta sak’ala akan bak’ar abayar da ta chanja dama ta yi rolling
ta nufi k’ofar ta bud’e ta fita.
Suna ganin ta a shirye chap suka ce “su wuce kawai”
Mom na y’ar dariya k’asa k’asa
tana yaba tsantsar k’aunar da Sakina take yiwa d’anta
tana jin k’aunarta na shiga zuciyarta. Tun d’azu ta lura da yadda Sakinar take ta rawar k’afar son zuwa ta ga Auwal d’in……
Da wannan tunanin
suka k’arasa mota
Drivern jiya shi ya ja su ya kaisu har cikin tafkeken asibitin.

Tunda suka fara takawa cikin asibitin gabanta yake mugun fad’uwa! Had’e da wani sanyin farin ciki da ya lullub’eta.

Suna shiga dakin ta fashe da kuka, duk da kuwa Aaima dama ta gaya mata halin da yake ciki amman bata yi tunannin samun shi da oxygen har yanzu ba.

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin ya k’arasa wajen ya tsaya a dede kanshi yana kallon shi..
Ya rame ba kad’an ba
ya yi haske sosai.

A hankali ya shafa kanshi ya ce “Son”

Tun lokacin da suka shigo yake d’an jinsu sama sama. So yake ya bud’e idanuwan nashi amman ya kasa
dan haka kurum suna shigowa gabansa ya yanke ya fad’i.

A hankali ya samu ya bud’e idanuwan nashi
da suka k’ank’ance..
Suna had’a idanu da Daddy ya sakar masa d’an murmushi.

Murmushi Daddyn shima ya yi masa kafin ya ce
“I’ve a surprise for you”
Ya yi maganan yana mai juyawa ya yafito Sakina.

A hankali ta k’arasa inda suke.
Tunda ta taho jikinshi ya bashi,
yana cikin tunani
kawai ya ganta a tsaye a kanshi!

Mutumin da ko iya motsin kirki baya yi kawai su Daddy suka ga ya yunk’ura da sauri
zai tashi sai kuma ya ce “auch!!”
Yana dogarar da guiwar hannunsa a kan gadon for sopport
dan da mugun ciwo
k’irjinsa wuyansa kafad’unsa da kansa suka sara!
Sai kuma ya fara juwwa.

Da sauri Daddy ya tareshi yana mai zama a bakin gadon ya maida shi kwance
ya ce
“careful mana”
Sai kuma yasa dariya ya ce
“har ka warke kenan?”

Sai a lokacin kunya ta rufe Auwal….A hankali ya d’auke idanuwansa a kan fuskar Sakina ya mayar ya lumshe…..
Tsananin farin ciki ya ji da ya ganta by surprise
dan ji yayi kamar an tsundumashi a aljannah!
Sai kuma a take batun
Aurenta da Ashraff ya fad’o masa dan haka take lokaci guda ya ji wani tsananin tashin hankali
sanann k’irjinsa ya hau zafi.
Muryar Daddy ce ta katseshi jin yana cewa
“Auwal ba komai mutum yake sa rai kuma ya samu ba!
Kar ka ga ka mallaki Sakina ka yi tunanin duk wani abu idan ka sa rai nan gaba zaka samu.
Ubangiji shi ya baka ita ba wai saboda nacin ka da rashin lafiyarkaba.
An d’aura muku aure jiya kai da ita sakamokon matsalar da ta b’ullo a alamarin
Aurenta da Ashraff.
Amana ce Yarinyar nan
Mahaifinta yayi mana kawaici da mutunci
Dan Allah kar ka bamu kunya.”

Tunda ya fara magana Auwal ya k’ame! Ya kasa motsi sam!
Ji yake yi ma kamar iskar oxygen d’in bata isarsa………

A hankali Daddy ya yi wani sassanyan murmushi ya ce
“Dota idan kuna buk’atar wani abun ga waya chan….idan Likita kuke so za ki ga digits d’in a gefe
idan kuma abinci ne
shima digits d’in suna gefe.
Mu bara mu wuce ko?
Yana da number mu
duk abunda kuke buk’ata ku kira.
Allah ya yi muku albarka.”

A hankali Sakina ta ce “ameen” tana mai sunkuyar da kai.

Da kyar ya iya bud’e idanuwanshi ya ce
“Thankyou Daddy”
A hankali dan shi kad’ai ya san luguden da zuciyarsa take yi masa.

Murmushi ya yi daga haka suka juya shi da Mom suka fice
tare da alk’awarin ‘zuwa anjima za su dawo’
Bayan Itama Mom d’in ta yi musu addua sun amsa......


A hankali ta ga ya mik’o mata hannunsa yana kallonta.

Cikin nutsuwa ta k’arasa ta sa hannunta a cikin nashi.

Still yana kallon fuskarta ya zaunar da ita a gefenshi.

Da kulawa ta ce
“Ina wuni”
Tana kallon bakinshi ya amsa da “Alhamdulillah”
a hankali.
Daga nan ya ja hannun nata ya d’aura a gefen fuskarsa saman kumatunshi ya had’a da nashi hannun ya runtse
kafin ya maida idanunsa ya rufe…
Ko minti uku ba a yi ba ta ji
yanayin rik’o da ya yiwa hannun nata ya sauya
alamun ya yi bacci, bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba..
Kallon shi kawai take yi tana sakewa..ya d’an tara k’asumba har da gemu, tabbas ta so
ta tarwatsa rayuwarta da hannunta dan bata jin akwai wanda zata iya so ta zauna ta rayu ta yi farinciki da shi idan ba Ya Auwal ba. Bata tashi sanin zazzafar soyayyar da take yi mishi ba sai da ya kwanta ciwo….

Sun fi 40 minutes a haka
gaba d’aya hannunta ya k’age amman bata so ta motsa gudun kar ya farka dan
ta lura baccin nashi mai dad’i ne yake yi cikin nutsuwa da kwanciyar hankali
kamar ma murmushi taga yana yi.

Sai da ya yi 1 hour yana baccin tukunna ya farka. Yana bud’e ido da fuskarta ya fara tozali
Itanma shi take kallo dan haka ya sakar mata wani tsadadden murmushi. Sai kuma ya d’an gyara ganin kamar a takure take kafin ya ce mata “call the Doctor” a hankali.

Ta fahimci me ya ce
shiyasa ta mik’e ta je ta danna kiran Doctor d’in. Bayan sun gama magana ta koma ta zauna.
Tana zama ya sake kamo hannunta yana kallonta sam murmushi ya ki barin fuskarsa.

Ba ta jima da zama ba Likitan ta shigo.

Yanayin yadda ta ganshi kwance yana kallon kowa tar hakan ba k’aramin dad’i ya yi mata ba. Jininsa ta fara aunawa cike da mamaki ta shiga dudduba shi…
Ganin no nid of oxygen d’in ne
ya sa ta cire ta yi mishi y’an allurai
daga nan ta cewa Sakina “ta k’ok’arta a samu ya ci abinci
jikinshi is weak kuma ta cire mishi drip d’in da yake d’an rik’e shi
tunda ba abincin yake iya ci ba.....”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fita tana murmushi…Irin wannan soyayyar haka
tabbas saboda wannan Yarinyar ne zuciyarshi ta d’an tab’u dan gashi daga zuwanta
komai ya fara yin normal a hankali..Ashe dama Nigerians ma suna irin wannan zazzafar soyayya haka?
Dukda ba bak’ak’en fata bane amman ta fahimci Hausa suke yi..........

Sakina na shirin mik’ewa
ya sa dukkannin d’an ragowar k’arfinsa ya jawota, bata ankara ba shiyasa yayi nasarar janyotan, ta tafi ta fad’a jikinshi.
A zabure ta yunk’ura zata tashi ya ce
“Don’t move please”
A hankali dede kunnenta.
Shiruu ta yi kawai
tana jin yanda bugun zuciyarshi yake yi da k’arfin gaske....

Ganin lamarin na shirin sauya masa ya sanya ya d’an cikata.
Da sauri ta tashi ta koma gefe ta zauna dan tabbas ba zata iya had’a ido da shiba kuma.

Ya fahimci ta gano shi
shiyasa kawai ya yi murmushi ya girgiza kai
kafin cikin kasala da rashin k’arfin jiki ya ce
“D’an duba chan locker
ki fitar min brush da maclean da body lotion
sai jallabiya da k’aramin wando. Please.”
Ya fad’i hakan a hankali.

Jinjina kai kawai ta yi ta mik’e ta isa inda locker take, ta
d’auko duk abubuwan da ya lissaafa mata ta dawo
ta ajjiye a gefen gadon kafin ta ce
“Gashi”
tana kauda kanta
sannan ta d’an turo baki..kallon nashi ya fara isarta
kwatakwata ko kifta idon ma fa baya son yi!
Aranta ta ce
“Har sai ya hango muni na”

“Um”
Ta ji ya ce
wanda hakan yasa ta juya ta kalleshi.

Gani tayi ya d’an d’aga hannuwanshi biyu irin yanda Yara suke yi idan suna so a d’auke su.

Bata san lokacin da dariya ta sub’uce mata ba, da sauri ta sa hannu ta toshe bakinta sannan cikin dariyar k’asa k’asa ta ce
“In d’auke ka?”
Ta yi maganar tana nuna kanta.
D’aga mata kai yayi kawai
Idanuwanshi a kanta
kafin a hankali ya ce
“Allah na kasa tashi!
Jikina ba kwari ko mostin kirki fa ba iyawa nake yi ba
so kike in mik’e in zube?”

Cikin yin kalar tausayi ta ce
“Ya Auwal dan Allah ta yaya zan iya d’aukar ka?”
Tana maganar tana kawar da kai dan bataso su had’a ido.

Murmushi ya yi yad’an ciji lower lip d’inshi kafin ya ce
“To shikenan naji ba zaki iyaba
Zo to ki taimaka min In tashi.”

Da sauri cikin tarar numfashinsa
ta ce
“A’a gaskiya”

This time around sai da ya d’anyi dariya wadda ta taho mishi da d’an tari, sai da
tarin ya tsagaita tukunna ya ce
“Mai yasa ba za ki rik’e ni in tashi ba?
Ko bakya so in sake.....”

Da mugun sauri ta k’arasa ta sa hannunta ta toshe mishi baki, cikin muryar kamar wadda zata fashe da kuka ta ce “Wallahi idan ka k’arasa sai na tafi yanzunnan zan koma wajen su Mom”

Da kyar dan jikinshi sam ba k’arfi ya iya zare hannun nata ya ce
“Ni kuma wallahi idan baki taimakamin na tashi ba
sai na k’arasa kuma In rufe k’ofar in hanaki fita sannan In yi ta maimaitawa.”

Kamar zata yi kuka haka ta sunkuya kansa yadda za ta iya taimaka masa.

Sai da ya gama d’aga mata gira yana kashe mata ido tukunna ya sak’ala hunnunshi a kafad’arta
yana dariyar yadda ta chuno baki ta kauda kai gefe.
Sai da ta yi bismillah tukunna ta d’an motsa da niyyar taimaka mishi, d’an yunk’urawa shi kuma ya yi hakan ya bashi damar mik’ewa
ya zauna, da taimkon Ubangiji da na Sakina da kyar ya samu ya mik’e! K’afafuwansa har d’an karkarwa suke yi……
Ita ta d’an fara motsawa yana rik’e da ita ya ce “ta d’auka kayan da ta d’auko mishi”
Hannu kawai tasa ta d’auka
daga nan suka d’an fara takawa……..

Har Cikin bathroom d’in ta kaishi.
A bakin tangamemen bathtub d’in ya zauna, sai da
jirin yad’an sakeshi tukunna ya cikata ta had’a mishi ruwan wankan tab bathtub d’in
sanann ta matsa mishi Maclean ta mik’a masa..
Sai da ta taimaka masa ya isa wajen sink d’in yayi tukunna
ta fara k’ok’arin fita domin ya samu ya yi wanka.

Cikin ruk’o hannunta ya ce
“Saurin me kike yi?
Jikina fa babu kwari!
Idan kika fita na fad’i baya fa za ki dawo damu.”

A hankali ta d’an matso suka nufi bathtub d’in tare……….
Sanabe! Kala Kala
awajen Auwal dan
hatta shirt d’in ma ita ta b’alle mishi mab’allin ta cire, da kyar ya yarda ya sa hannu ya cire singlet d’in!
Tun daga nan ta sunkuyar da kanta sosai ta fara k’ok’arin tafiya amman ya rik’e mata hannu….
Drama sosai suka yi
dan ya kafe akan wandon ma ita zata cire masa gashi ya tare hanya ya rik’eta for support ya hanata tafiya.
Ganin da ya yi ta tubure sannan tama k’i kallonshi tana shirin fashewa da kuka yasa kawai ya kama wandon ya fara ja yana dariya k’asa k’asa
a hankali ta ji ya ce
“FYI! Babu boxers a ciki.”
Ta mugun k’arfi ta saka kuka ta durk’usa a wajen dede nan kuwa ta ga ya saki wando ya fad’o k’asa dan
haka ta ci gaba da kuka ta k’i dagowa sam! Ta runtse idonta.

Kukan da take yi ne yasa ya cika mata hannu, ai kuwa
bata yarda ta kalli direction d’insa ba ta juya
ta mik’e ta fice da mugun gudu.

Banda dariya ba abunda yake yi…
A hankali ya zare boxers d’in jikinsa ya shiga cikin ruwan da kyar. Ya kwanta a ciki ya lumshe idanuwanshi yana jero wa Ubangiji kirari da godiya….
Ya dad’e a haka tukun ya ja sponge da soap ya fara wankan....

Banda dukan uku uku ba abunda k’irjinta yake yi!
Da kyar ta samu ta tsaida kukan nata…
Kana ganinta ka san a mugun tsorace take
ba abunda yafi d’aga mata hankali irin kar ya zo fitowa ya fito mata a haka! Tunda ta lura sam babu d’igon kunya a tattare da shi…..
Da wannan tunanin ta juya gaba d’ayanta tana me kallon bango. Ta jima a haka ta ji k’arar bud’e k’ofar, sake
matsawa jikin bangon ta yi
wanda hakan ba k’aramin dariya ya bashi ba.

Tana jinshi yana yi mata dariya ta yi banza da shi.
A hankali ta ji ya ce
“Relax! Har da jallabiyata da towel a kaina na fito,
Okay?!”

Bata yarda ba sai da ya matso kusa da ita ya kamo hannunta ya d’aura akan jallabiyar jikinshi tukunna
t sauk’e ajiyar zuciya ta juyo
amman still dukda haka bata kallonsa.
A gefen ta ya zauna da kyar yana jin tsananin jiri da rashin kuzari ya ce
“Anya ba a sauya mini ke ba kuwa? Ina tawan ta tafi ne?”

B’ata rai ta yi ta turo baki.

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya ya d’an matsa ya yi peckn kumatunta ya ce
“Matata!”
Yana kallonta yana murmushi.

Bata san lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba
Itama.

A hanakali ta mik’e ta yo musu order abinci sannann ta dawo ta zauna a kusa da shi.


Yana nan rik’e da hannunta tana bashi labarin Ashraff aka kawo abincin....


Auwal,
ya ma manta rabon da ya ci abinci irin wannan sai dai drip most a times, da kanta take bashi!
Wani nishad’i farinciki da jin dad’i yake ji wanda ba zai misaltu ba.
Haka nan ta ciyar da shi suka yi baccin su tare suka farka
suka yi sallah tare!
Kafin washe gari kam Auwal ya warke ba laifi
sai dai yawan baccin da yake yi da kuma rashin k’arfin jiki da y’an abubuwan da ba za a rasa ba..
Dan ko da Daddy ma ya je da daddare yana bacci.
Ba k’aramin dad’i Daddy ya ji ba da ganin shi har yayi wanka kuma babu oxygen.
Bai wani jima ba gudun kar motsin shi ya tada shi yasa ya yiwa Sakina sallama bayan ya bata abubuwan da ya tsaya ya siya musu.
.....……………..
Suna gama video call d’in Daddy ya mik’e idanunshi sharkaf da hawaye zai wuce!
Da sauri Mom ta ruk’o hannunsa ta durk’usa a gabansa.
Ta lura tun d’azu da ta fara bada labarin ta’asarsu ita da Mammy Daddyn yak’i kallon direction d’inta,
yanzu ma haka.
Tana kuka ta ce
“Dan Allah Daddy kar ka yi min wannan shirun naka……Ka hukuntani! Ka yi min duk hukuncin da kaga ya dace dani amman dan Allah kar ka rik’eni a zuciya ka banxatar da ni.”

A hankali cikin share hawaye Daddy ya ce
“Adama I love you
morethan you can ever imagine! Amman ba zan iya zama ince wai na yafe miki duk abubuwan da kikayi min lokaci guda kuma naci gaba da sonki ba!
Tbh, wallahi k’aunarki da k’imarki tayi mugun raguwa a zuciyata…
How could you?!
Haba Adama!
Saboda son zuciya?
Adama Mommy fa kusan a kwance ta yi rayuwarta
kin sani kin san matsalar
amman kika yi shiru!.
Sannan kika taimakawa Mammy dan ku kwantar da Aslam yayi jinya shima?
Doguwar jinya!!!
saboda kawai kwad’ayin MT??”.

Cikin kuka ta ce
“I was wrong!
I have been wrong for so long Daddy dan Allah ka yafe min.
Ban san ta Ina zan fara baka hak’uri ba, ka yi hak’uri tabbas na yi kuskure kuma kuskuren ya dawo mini
tunda gashi na rasa y’ar uwa ta d’aya tilo a duniya.”

Numfashi Daddy ya furzar kafin ya ce
“Duk son da nake yi miki
dole ne in kin tab’a min family zan ji haushi Adama!
Ba zan iya kallon ki ban tuna abubuwan da kika yi ba.
Ki je wajen Inna!
Ni ban ce na sakeki ba
amman kawai ki tafi wajenta
zan nemeki
idan na huce.”
A hankali ya zaro atm ya bata ya ce
“Akwai driver da Aslam ya turo ya taho
wai Auwal ya ce a kawo mishi wasu abubuwa..
Idan ya zo zan turo miki shi ku je ke da shi ku yi visa da komai
Direct ki wuce wajen Innaa.
Dan Allah ko kira na kar ki yi.
Idan na neme ki to..Idan kuma ban neme ki ba shikenan,
zan aika miki da takardarki!
Allah ya raya mana Auwal.....”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita da sauri.

A wajen ta durk’ushe tana wani irin mugun kuka.......


..BAYAN KWANA BIYU..
Haka kurum tunda Mama ta tashi yau jikinta a mace
Ummu na lura da ita dan

Download complete TXT · Novel page