So da Buri 3

Chapter 31 of 36

tun jiya a wajen saloon taga kamar ma kuka take yi.
A hankali ta matso kusanta tace “Maama”
A karo na biyu.
D’agowa ta yi ta kalle ta.
A hankali ta ce
“Ki tashi ki cire lallen nan mana a yi miki black mai k’unshi ke take jira”.
Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin a hankali ta janyo abun sakace Ummu ta hau b’alle ledar…
Atake suka cire ita da Ummu ta shafa mata Mahallabiya.
Mik’ewa Ummu tayi da zummar zuwa ta kira me lallen tayi mata bakin
ta ji Mama ta rik’eta
a hankali ta ce
“Abba ya fi son jan lalle”

Murmushi Ummu tayi ta koma ta zauna ta kamo hannuwanta biyu kafin ta ce
“Kina tunawa kenan har yanzu
alamun yana nan rad’au a zuciyarki har abada amman kuma kiketa faman k’unci tun jiya Me yasa baki da walwala?
Ko kema kukan za ki yi mana kamar y’ay’anki
Huda da Sakina?”

Ajiyar zuciya Mama ta sauk’e kafin ta ce
“Bawai walwala ne bani da shi ba, dana sani nake yi.”

Da sauri Ummu ta gyara zama kafin ta ce
“Dana sani kuma?
Name?”

Wani d’an guntun murmushi Mama ta yi
kafin ta ce
“Dana sanin kuka da sab’on dana dinga yi ina cewa ‘mai yasa rayuwarmu ni da y’ata ta zo a haka?!’.
Ummu na cire rai da Abba
na cire rai da soyayya
amma gashi yanzu
Ubangijin da nake ganin ya d’aura mana kaddara mai tauri
zai sake mallakamin Abba
sannan Huda ma ta auri wanda yake tsananin k’aunarta shi da iyayensa
What more could I ever ask for?.
Godiya da tasbihi nake ga Ubangijin talikai amman gani nake yi kamar is not enough!
Bansan ta yaya zan fara yiwa Ubangijina godiya ba.
Ki duba fa kiga yadda rayuwa ta chanja mana
daga k’unci tashin hankali da bak’in ciki
zuwa
Farin ciki cikar buri
a lokaci daya!.
Ba abunda yake bani mamaki nake kuma gasgata Ubangiji mai kun fayakun ne
Irin yadda komai yake tafiya smooth..
Hatta Granpa ya sauk’o sosai
jiya fa kira na yayi a waya wai ya kira mu gaisa
sannan ya sake bani hak’uri!…
Ashe dama za mu ji dad’i ni da Huda? Ashe za mu yi farin ciki?
Ashe zan sake d’and’anar soyayya?”.

Ajiyar zuciya Ummu ta sauk’e a hankali ta matsa kusa da ita tasa hannu ta rungumeta, a
take kuka ya taho musu a tare su biyun.

Suna a haka Shuwa ta shigo.
Murmushi kawai ta yi cikin dakiya ta k’arasa inda suke ta d’an b’ata rai
kafin ta ce
“Yanzu dan Allah Maryam kema sai kin saka mu kuka?
Su Huda sunayi kema kina yi?”
Sannan cikin d’an fad’a ta cewa Ummu “tashi ki fita,
yi maza ki fita kije kin bar Zainab da had’a abinci ke kin zo nan.
Oya Maryam kema tashi ki shirya yanzunnan za ki ga an fara zuwa”.
Bata Ida rufe bakinta ba
Hudan ta shigo ita da Mommy.
Da d’an sauri ta k’arasa ta fad’a kansu Ummu
tana murna.

Jujjuya kai kawai Shuwa tayi ta ce “Nikam wannan alada taku ta turai ban santa ba!
Dan tsabar rashin man kai Huda yanzu keda za akai miki Maman naki inda kike shine kika fito? Kalleki ko nuna baki gama yi daga jinin amarcinba
amman dan fitina har kin fito?”

Murmushi Mommy ta yi suka gaisa ita da Shuwa kafin ta ce
“Hajiya ayi mana uzuri, nima
naso in hana amman ita da Mijin suka kafe!
Wai zata yi mishi kuka idan na tafi.”

Cikin d’an fad’a Shuwan ta k’arasa ta sakar mata rankwashi a kai tace “ja’ira!!
Sannnan kin zo kin wani wuce ni kin fad’a jikin iyayenki..”

Murmushi Huda ta yi ta mik’e ta yi hugging Shuwa kafin cikin dariya da zolaya ta ce
“Hajiya kawai ki fito ki ce daman kishi kike yi ban kula ki ba ba wai kiyi ta kame kame ba .”

Dariya duk akayi.

A hankali Shuwa itama tana d’an murmushi tasa hannu ta yi hugging Huda tukunna ta cika ta ta juya ta fita da sauri tana cewa “su tabbata sun sa Mama ta shirya yanzu”.

Already Maman ta yi wanka tun sassafe dan haka
kayanta kawai ta shiga bathroom ta saka
Sky blue lace
da white jaka takalmi da jewelry’s
Ummu ce tayi mata d’auri
nan take ta fito rass Amarya…
Anyi hotuna sosai
Allah sarki sakina
a video call Huda ta kirata
ta saka fuskarta akan screen din full aka d’auki hoton da ita su Ummu suna ta yiwa shirmen nasu dariya gashi Sakina ta dage sai an yi da ita.

A masallacin unguwar kusa da gidan Madu anan za a d’aura aure dan tun kafin lokaci ya cika manyan motoci suka cika layin tap! Har layin baya
saboda Abba gayya yayi kamar wannan ne na farko.

Lokaci yana cika dubban mutane suka shaida
D’aurin Auren
Yakubu Umar Farouk Mt (Abba)
Da Amaryarsa
Maryam Muhammad Madu (Mama)
Akan sadaki naira dubu d’ari uku.

Ana shirin watsewa Kaka ya cewa Limamin ya sanar za a sake wani d’aurin auren
…..……Tun lokacin da Kaka ya bada sanarwar Jalila
wani mai d’an kantin
ana ce mishi
Abdullahi
ya ce yaji ya gani!
Shi da Mahaifiyarshi basu wani dad’e sosai da tarewa a anguwar ba
kasancewar Mahaifinsa ya rasu kuma anata rigima tsakaninsu da dangi da iyayen uban a kan gado yasa suka baro Katsina suka dawo Kano da shi da Mahaifiyarshi da k’anwarsa Aminatu tsarar Jalila.

Da farko Hudan ya so
sai da mazan layin suka zaunar da shi suka yi mishi lecture
a kan ‘indai ba gudumar late comer da heartbreak yake son yasha ba tou ya hak’ura’ Tukunna ya hak’ura
ya koma kan Jalila
wadda sai da ya fara sonta ne ma ya lura yama fi k’aunarta akan Hudan, dan haka ya je ya sameta ya gaya mata..
K’iri k’iri ta fito mishi ta k’i amincewa da shi sannan ta wankeshi tass!! Ta yi gaba abunta.
Babu yanda bai yi ba amman ya kasa cire ta aranshi
har rashin lafiya yake yi saboda Jalila
tun ba ma lokacin da Auwal ya fara kwasarta ba
sai da ya yi k’aramin hauka.

Har gida Mahaifiyarsa ta je ta samu Sadiya
amman tijarar da Sadiya ta yi mata har yamafi wadda Jalilan ta yiwa Abdullahin kumafa idan ka ga Abdullahi bashi da laifi sam! Bak’in saurayi dogon gaske mai fad’in k’ashi
bashi da wani muni a fuska sam
ya kammala degree d’inshi
bai samu aiki ba
shiyasa ya bud’e shago saboda d’awainiyar Mahaifiyarsa da k’anwarsa dole shi ne zai yi.

Yana jin labari ya tafi wajen Kaka..
Ba abunda Kaka ya b’oye masa
gameda cikin da Jalila tayi amman wannan Yaro ya ce yaji ya gani.
Kaka ba k’aramin farin ciki yayi ba dan bai tab’a tunanin Jalila zata samu Miji saurayi kamar Abdullahin ba amman still sai da ya sake tura Baaba Talatu wajen Mahaifiyarsa da bayani
Itama ta amince
Dan haka aka bashi Jalila ba tare da an gayawa ita kanta Jalilan ko Sadiya ba
Baba ne kawai ya sani……


Su Sadiya suna gidan Baaba Laraba sai uban hayak’i suke yi dan Malamin nasu yace in dai sun yi wannan hayak’in a anguwar in da Maryam (Mama) take tou ba za a d’aura auren Maryam da Yakubu ba.

Suna hayakin suna ta uban tari kawunan su na ciwo suka jiyo an d’aura auren Maryam da Yakubu!……
Fatali Umma ta yi da kaskon
kafin ta fashe da wani matsanancin kuka!.

Jalila kanta sai da ta yi kwallar tashin hankali.

Ba a yi minti talatin ba suna cikin jimami da tashin hankali suka ji ana sanarwa
“An D’aura Auren Abdullahi Muhammad
Da Amaryarsa
Jalila Usman Bashir”.

BULAMA ✍️



So da Buri
Free book
73

Mikiya Writers Association.
A hankali Mama ta lumshe idanuwanta wasu hawaye suna zuba. Dai dai nan Ummu
ta shigo, ta na Isa gareta ta sa hannu ta yi hugging d’inta ta ce “congratulations”.
Ajiyar zuciya kawai Mama ta sauk’e daga nan d’akin ya fara cika da jamaa..
Banda hayaniyar mata babu abunda ke tashi.

Suna cikin hira
suka ji d’aurin auren Jalila itama, nan take kowa ta hau tofa albarkacin bakinta
wasu su ce “Allah shi k’ara” wasu kuma su ce “Ai ta ma yi sa a data auri Abdullahin,
Mutum mai kirki da hankali da zuciyar nema
wallahi ta tsinci dami a kala...”.



Kowa idan ya ga Abba a wajen d’aurin auren nan tashi d’aya zai san yau d’in fa yana cikin farin ciki. Ba shi kad’ai ba hatta su Granpa idan ka gansu fuskokinsu tap! Cike da annuri.

Ba a jima ba suka shiga parlourn Madu aka yi musu hotuna suka wuce bayan sun ce “nan da anjima in an d’an watse Abba zai dawo ya d’auki Amaryar shi da kanshi.”

Madu ya ji dad’in hakan dan dama shima ya gama deciding
akan ‘ba sai an yi wani reton kai Amarya kamar wata Yarinya ba’.

Hakan kuwa aka yi,
Hudan ta so tsayawa amman awa uku kawai Aslam ya bata daga nann ya dawo ya d’auketa a cewarshi ‘gidan yayi mishi girma ya kasa shan ko ruwa tunda ya koma’…
Tunda ta ji haka dama ta b’aro jirginsa! Dan haka ta yi murmushi kawai ta girgiza kai tana mamakinsa.

Tunda aka idar da sallar Magrib Abba ya shirya tsaf!
Ana idar da sallar isha ya kama hanyar gandun albasa bayan ya samu Dad ya cika shi dakyar dan da farko rik’esa ya yi ya ce “akwai wani important aiki da zai tayashi
dan Allah”
Kamar Abba zai yi kuka haka ya yi mishi sai kuma ya ga Dad d’in yana dariya k’asa k’asa
dan haka ya gano tsokanace!
Amman dukda haka sai da ya yi da gaske tukunna Dad d’in ya cika mishi riga ya wuce mota Dad d’in kuma ya nufi gidanshi yana dariya……….

Yana zuwa ya tadda Madu zai shiga gida ya fito kenan daga masallaci dan haka suka shiga tare har parlourn Shuwa.

Nan Madu ya d’au waya ya kira Kaka da Baaba Talatu
suka zo suka had’u suka yi musu Nasiha!
Daganan suka sanya musu albarka….

Sai da suka zo tafiya ne Mama ta ji kuka ya taho mata.

Murmushi kawai Baaba Talatu da Shuwa suka yi
daga nan Baaba Talatu ta mik’e ta k’arasa ta mik’ar da ita suka yi gaba
Abba shima ya yi musu godiya da fatan alkhairi ya bi bayansu…..

Da shi da mai aikin ne suka ja akwatunan Mama guda biyu da ta had kayanta a ciki
suka kai mota suka sanya mata a booth...

Har k’ofar mota Baaba Talatu ta raka Mama ta bud’e ta saka ta a ciiki tukunna ta ce “Allah ya miki albarka”
Tana mai rufe mata motar ta koma ciki.

Dede nan Abba ya shigo ya rufe motar ya kunna ta,
a hankali ya sauk’e ajiyar zuciya sannan ya juyo ya sa hannu ya jawota ya yi hugging d’inta wasu hawaye suna zubowa daga idanunshi..
Da sauri ta ce
“Abba mutane fa suna wucewa”
Tana mai d’an k’ok’arin janyewa.
Bai cikata ba sai da ya yi niyya tukunna ya matsa amman still yana rik’e da hannunta yana kallonta ta cikin mayafin da ta d’an ja.
Murmushi kawai ya yi yana sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya kafin ya koma ya zauna rik’e da hannunta ya tada motar suka wuce.
Sai a sannan tukunna Baba ya share hawayenshi ya juya ya nufi cikin gidan Kaka yana ganin uku uku......


Tunda suka isa bakin estate d’in ta lumshe idanuwanta.

A hankali ya yi horn aka zuge makeken gate d’in suka shige ciki.
Direct gidan Granpa Abba ya nufa da ita.
Yana kashe motar ya d’an murza hannunta wanda tun d’azun da ya rik’e bai cika ba ya ce “Maryama”
Sai a sannan ta bud’e idon ta d’an juyo ta kalleshi.
Murmushi ya yi ya ce “mu je ko?”
Jinjina kai kawai ta yi daga nan ta fara k’ok’arin fita sai kuma ta juya ta ce “hannuna”
Sai a sannan ya d’anyi murmushi ya sakin mata hannun da kyar
ta fita da k’ofar dama shima ya fito…
Suna d’an yin gaba ta ga yana shirin kama mata hannu!
Bama ta san wajen su Granpa za su je ba
amman kawai ta yi gaba da sauri!
Murmushi kawai ya yi ya girgiza kai ya bi bayanta,
daga nan suka jera suka shiga a tare.

A parlourn su Granpa na biyu
suka samesu suna jiransu gaba d’ayansu har Mommy da Dad.
Tana shiga Mommy ta mik’e ta je ta yi hugging d’inta tana farin ciki…

A gaban Granpa ta fara durk’usawa suka gaisa ya yi welcoming d’inta
sannan ta k’arasa wajen Gramma itama ta yi welcoming d’inta ta saka mata albarka
tukunna Dad shima ya yi welcoming d’inta ya sanya mata albarka.
Daganan Granpa da Gramma suka bata gifts d’insu
Granpa ya bata fili a asokoro Grandma kuma ta bata sark’ar gold babba mai kyau da bangles d’inta da zobe.

Godiya sosai su Mama da Abba suka yi daga nan Dad shima ya bata nashi gift d’in kyautar mota har da Mommy aka hau godiya..
Sannan suka sake yiwa su Gramma godiya
daga nan suka yi musu sallama da Allah ya kiyaye hanya dan sun ce jirginsu 3:00am zai tashi......



A ranar dattijawan unguwa suka zo suka zo suka bawa Madu hak’uri sannan
da maganar ‘ya koma matsayinshi na mai unguwa’!
Da kyar kuwa da mugun kyar aka samu ya yarda ya karb’a
saboda shi a ganinshi komai ya wuce sannan yanzu tsufa ya kamashi amman sam suka k’i amincewa suka ce “Ai su basu da wani mai unguwa wanda ya chanchanta sama da shi”….



Tunda Abba yake bai tab’a ganin nisan dake a tsakanin gidan Granpa da Gidan da zai zauna ba sai yau!
Allah Allah kawai yake su k’arasa.

Suna shiga Mama taga abun mamaki..har da wata k’atuwar heart a tsakiyar falon an yi decoration, ita kam abunma ma sai ya bata kunya..kar wani ya shigo ya gani..
Ruwan furniture da electronics kuwa kamar ba a san zafin kud’in ba.

A chan sama ma d’akinsu Abba ya yi decorating sosai da red hearts
Ita dai Mama in banda murmushi ba abunda take yi
dan har ga Allah abun ya burgeta.

Idanuwanta suna kaiwa kan akwatuna dozen a take ta b’ata rai!
Da sauri ya kauda kai yana d’an murmushi.

Cikin rashin jin dad’i ta ce
“Abba cewa fa na yi ka barshi.
Ka san za ka yi shine mu kuma ka hana mu yin kayan d’aki?”.

Da sauri ya sa hannu ya toshe mata baki ya ce
“Maryam wallahi bani da energy d’in arguing yanzu, ba ri mu yi sallah ko? Mu ci abinci sai mu yi magana.”

Da “to” kawai ta bishi,
tana ta faman fushi suka yi sallar suka ci abinci.
Za ta ci gaba da mitar ya ce
“Bara inyi wanka sai ayi min mitar ko?”
Ya fad’i haka yana tattare wajen ya yi waje da sauri yana mamakin Mama da mitar ta har yanzu ashe tana nan.

Itama wankan ta yi ta nad’a laffayarta bayan ta chanza kayan da ta zo da su a cikin akwatinta.
Tana cikin nad’a laffayar ya shigo, ya tsaya a bayan ta.
Ko juyowa bata yi ba
ta ce
“Yanzu inda nice na nace sai na zo da kayan d’aki nasan ba zaka ji dad’i ba amman ni kalli ka yi lefe bayan an riga an gama magana,
sai kace wata Yarinya...”

A hankali ya juyo da ita ya ce
“Wallahi bana gane abubuwan da kike fad’a!
Na gaya miki bani da energy d’in arguing................”



EARLIER..
Wata razananniyar k’ara Umma ta saka mai had’e da ashar kamar wata mahaukaciya!

Jalila kuwa
gefe guda kawai ta koma ta zauna dab’ass!! Ta k’ame a waje guda sai kuma hawaye suka hau zirya wani na korar wani ba k’akk’autawa…..
Tabbas ko jiya sai da Abdullahi ya kirata, da ta k’i d’auka ya yi mata message yana cewa
“Gobe in shaa Allah zai yi mata kyauta surprise
na ban mamaki.”
Tsananin tashin hankali da bak’in ciki suka sanya kawai ta tafi ta sulale ta sume a wajen.

Da gudu Umma ta k’arasa kanta ta hau jijjigata
amman sam bata motsa ba!
Sai da Hansai ta d’ebo ruwa aka shek’a mata
tukunna ta farfad’o,
suna had’a ido da Umma ta fashe da kuka:

Kasa cigaba da kallon idon nata Umma ta yi, ta mik’e kawai ta ja hannun Hansai suka shige chan k’uryar d’aki.
Jakarta kawai ta d’auka ta cewa Hansai “yi mini kwatancen Dajinma!”.
A zabure Hansai ta ce
“Ke!!! Sadiya? Dajinma??
Gaskiya ni kam ba da ni ba!
Har me ya yi zafi haka?”.

Cikin katseta da sauri Umma ta ce “komai ma ya yi zafi!!!
Haba Hansai!
Sai kace ba kya gani?
Ki duba kiga Maryam da Huda sun fini ta ko wacce hanya
sannan tsabar Bashir d’an kutumar bura uba ne
Kalli a yadda ya aurar da Jalila
kuma auren ma da talakan tukuf!!
Dan nasan had’in sa ne wanan, shegen tsoho ya tsaneni ya tsane y’aata!
Tun da ya kafa mata k’ahon zuk’a sai da ya yi mata auren dolen tukunna hankalinsa ya kwanta!
Ai kuwa wallahi ba zata sab’u ba! Ko sadakin ba za mu karb’a ba wallahi sai ya sakar mini y’ata, ban haifeta dan ta je ta auri talaka ba wallahi..
Ki yi min kwatance ko kuma In tafi in nema. In ba haka ba mutuwa zan yi
kin san Allah takaice da bak’in ciki sai sun kasheni!!!!…..”

Cikin son fahimtar da ita Hansai ta ce
“Sadiya wajen nan ban da mayu da aljanu ba abunda suka cikashi!
Kumafa sai kin yi tsirara tukunna zasu saurareki!
Ke kad’ai a tsakiyar daji.”

Da sauri Umma ta ce “zan iya!!
Kwatance kawai nake buk’ata
ki yi mini
idan na je
ko me akace min inyi zan iya
muddin zan ga Maryam da Huda a k’ark’ashina
sannan basu fini da komai ba!
Haba mana!
sun fi kowa ne?
Kalli mazajen fa da suka aura
Hansai zuciyata zata buga ki yi min kwatance in wuce da wuri tun kafin Maryam ta tare a lalata auren sannan a sauwwak’ewa y’ata wannan auren talakan tukuf d’in

Download complete TXT · Novel page