Showing 300001 words to 303000 words out of 452169 words

Chapter 101 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

ta shigo gaidaka sai ta zauna a tsanake ta gaisheka cikin ladabi da biyayya har ma ta tambayi ko da abinda zata maka amma yanzu sam ba haka bane, ai dai kinga figil figil daga gaisuwa ta mike ta fice kamar ana mintsilinta, to shi dama Guban haka yake in an ci sa" Aunty Mariya dai tayi murmushi tace "Daga tafiya fa suke Mama Ladi, kuma kin ga ai da gajiya" Mama Ladi ta kara kyabe baki tace "Aa gaskiya Meran da na sani ba haka take ba da, yarinya ce nutsattsiya ga sanyin hali" can kuma ta kalli Ammi da ta fasa gayan abinda ke ranta game da bayyanar iyayen Mayraah da Allah yayi cikin ruwan sanyi, taji gwara kawai ta ja Aunty Mariya ta gaya mata, Mama Ladi tace "Nasan sai da Yahanasu tayi da ni a kadunan nan ko? Shegiya rubabbiyar mata gidanta yanda kika san gidan almajiran kana rad, ko ni da nake karaye sai a siya gidana sau dubu ita ba a taya nata ba" Ammi ta hade rai tace "Haba Mama...." Mama Ladi ta dakatar da ita da sauri tace "Kin fi ni sanin halinta ne ko er uwar ki ce? Matar dake bakin ciki da ni tun muna yara, yanzu haka don Mamuda na shiri da ni har mu zauna mu yi shawara gashi kome nace masa yayi yi yake kansa tsaye yana mutunta ni yana girmama ni wallahi haushin hakan Yahanasu take, to ni nace a tara mata jikoki a gaba su hanata rawan gaban hantsi ta kasa zuwa ko ina? Ba don tulin jikokin gabanta ba wllhi wataran sai Mamuda ya rufe ido ya koreta tsabar yanda zata mayar masa gida kasuwar kurmi don zarya, kullum tana hanyar gidansa kinsan ba kai gareta ba, amma ni ai kinga sai da dalili nake zuwa ba haka kawai ba, banda wannan mata da ta ci Guba na taho ba sai ayi shekara biyu ma ba a ji ni ba, gashi in mutum yaje kaduna tace lallai sai ya sauka a kuturun gidanta kuna shakar numfashin juna to a ina aka taɓa haka fisabilillahi, ke ba tsaftace gida kike ba ba komai ba kice sai an sauka gidanki" Mikewa Ammi tayi ta nufi kofa ta fita daga dakin, Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta bi bayanta, Mama Ladi ta kara kyaba baki tana yagar bredin gabanta tace "Ba dai kwa son gaskiya" A hankali Mayraah ta bude ido jin ana tapping pillow din da take kwance kai, ta daga kai tana kallonsa with sleepy eyes, yace "Baki ci abincin ba Mimi" Ta rufe ido ta maida kanta daya side din tace "Later" ya sauke idonsa yace "Are you not hungry?" Tayi shiru kuma bata bude ido ba, ya duka kusa da gadon yace "Mimi" Juyowa tayi ta ɓata fuska tace "Yaya bacci fa nake ji, ai nace ma Ammi ba yanzu zan ci ba" A hankali yace "Ohk" Daga haka ya mike ya juya zai fita ta bi sa kallo sai kuma tace "Za ka ci ne?" Juyawa yayi ya kalleta yace "Noo, naga it's almost 3pm baki ci abincin ba, kuma Mama Ladi na ta shiga kitchen din tana fitowa tana tambayar na waye, kar taje ta cinye maki...." Mayraah ta lumshe ido tace "Idan ta ci you can buy me another one" Ya ɗan yi murmushi yace "Ohk then" Ya juya ya nufi kofa sai kuma tace "Ko kuma ka ɗan kawo min nan pls" Ya kalleta bai dai ce komai ba ya fita daga dakin ya kullo mata kofar. Ammi na zaune tare da Aunty Mariya bayan ta sanar mata duk abinda ya faru daga shekaranjiya zuwa yau, sosai Aunty Mariya tayi farin ciki, don har sai da tayi hawaye, she was soo happy for Mayraah but deep down ta fi tausayin er uwarta sanin yanda ta kwallafa rai kan Mayraah, iyakacin son da zata ma er cikinta shi tayi ma Mayraah babu algus, gashi kuma yanzu ba ita kadai ke da ita ba ya kuma kamata ta fara koya ma kanta amincewa da hakan a zuciyarta, she have to start adapting to that gradually, bayan wani ɗan lokaci tana kallon Ammi a hankali tace "Yanzu zata je can wajen mamarta ne tayi kwana biyu?" Ammi ta daga kai tana kallonta babu ko kiftawa, Aunty Mariya ta kwantar da murya tace "Ya kamata ne Ammi, tun da kin ce ga halin da uwar ma ke ciki tun bayan rabata da er ta da aka yi, it's high time ki san Mayraah is not ours alone anymore Ammi, iyayenta suna nan da ran su har ma an maida auren su yanzu haka, ko yaya ne za su bukaci er su ta kusantosu don kaddara ce tayi parting dinsu tun asali, kakanninta ma duk suna nan za su so suma su saba da ita ta saki jiki da su, Ammi baza mu hana Mayraah creating bond da iyayenta da relatives dinta ba" Hawaye ta gani idon Ammi, Aunty Mariya da jikinta yayi sanyi don tasan idan ba ita din ba babu wanda zai ganar da Ammi wannan lamari, ta girgiza kai tace "Kiyi hakuri Ammi, amma ina son ki sani Mayraah ba yarinya bace, she knows her left from right, nasan kuma tasan matsayinki a wajenta tasan wacece ke, don haka kar ki wani sa damuwa a ranki, abu daya ne zai kara nisanta ki da Mayraah, nisa kuma na har abada...." Ammi ta daga kai tana kallonta har sannan hawaye na zuba idonta, Aunty Mariya ta dauko mata tissue ta bata, cikin sanyin murya Aunty Mariya tace "Yau ace Mayraah ta auri wannan saurayin nata ni kai na nasan zata mana nisa, and that is just the fact, don kuwa zata koma cikin dangin ubanta ne Automatically and we have nothing to do about it, kuma sai sanda Mijinta ya bata izini zata zo wajenki, may be ma ba gari daya ba, he can decide su zauna kaduna, gata ga kakanninta, ga kuma iyayenta, in kika ga hakan bai faru ba to sai in dai a gidan nan Mayraah zata yi aure" Ammi ta sunkuyar da kanta tana goge hawayen da yaki tsaya mata, bayan few seconds ta girgiza kai cikin rawan murya tace "Mayraah tana son Musharraf, shi ma kuma i believe yana sonta sosai, bazan iya hanata amincewa da aurensa ba saboda nawa interest din, bazan tauyeta ba, after all her happiness is all what i am after, her happiness is my first priority, bayan duk abubuwan nan da ta fuskanta a baya yanzu she deserves to be more than happy, even though i have other plans for her a baya, yanzu kam plan din isn't going to work, my plans are of no use duba da yanda abubuwa suka kasance a kwana biyun nan, i believe Allah ne ya bani Mayraah a sanda ya so sannan zai kuma rabani da ita a yanzu da ya so for other people to play their roles in her life...." Tana kai wa nan ta mike ta nufi kofa Aunty Mariya ta bi ta da kallo cike da tausayinta, Ammi na kokarin bude kofar dakin Usman ya rigata budewa, ta bi gefensa ta fita daga dakin ya bi ta da kallon mamaki ganin kuka take, sai kuma ya kalli Aunty Mariya, karasawa yayi cikin dakin da sauri ya zauna yana facing dinta cikin damuwa yace "Aunty me ya faru kuma? Why is Ammi crying?" Aunty Mariya ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Usman Pls tell me ur opinion akan auren Mayraah da wannan saurayin nata, tell me all what u think about it" Usman yace "Amma dai kukan me Ammi take Aunty? I want to know first pls" A hankali Aunty Mariya tace "She is crying because of how things later turn out, idan Mayraah ta auri yaron nan Musharraf kaga ai tayi nisa da ita ta koma dangin ubanta gaba daya, sai sanda kuma Ammi ta ganta" Usman ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, a hankali yace "Is that why she is worried?" Aunty Mariya tace "Da bata son Mayraah bazata damu ba Usman, kun fi kowa sanin irin son da take ma Mayraah, motherly love take mata, she feel za a rabata da ita ne na har abada" Usman dai bai ce komai ba, Aunty Mariya tace "What do u have to say Usman?" Ya sauke wani ajiyar zuciya yace "Ban san me zan ce ba Aunty" Aunty Mariya bata sake cewa komai ba har bayan minti biyar a dakin, Usman dai yayi nisa tunanin da yake. Bayan isha Mayraah na zaune parlon Abba tare da Ammi sai Maheer da Usman, wanda Abba ne duk yayi kiransu parlon nasa, Abba ya daga kai yana kallon Ammi da ta fada duniyar tunani yace "Hajiya...." Ammi ta daga kai da sauri ta kallesa, Yace "Kin dai san abinda ya kamata shi ake yi ko?" Ammi dai kallonsa kawai take, Abba ya jinjina kai yace "Ya kamata Mayraah taje gidan Ceo tayi masu ko kwana uku ne, don ranan Alhamis Alhaji Saminu yace min za su shigo don jin matsayar mu akan maganar aurenta, and today is Saturday, kinga ranan Wednesday da yamma sai either Maheer or Usman wani yaje ya daukota, if they are not available ma Drivernta zai iya zuwa ya dawo da ita, even though nasan CEO din ma zata sa a dawo da ita in lokacin dawowar nata yayi" Sosai gaban Mayraah ya fadi bayan taji abinda Abba yace tana kallonsa, Ammi dai kanta na kasa bata ce komai ba, Abba yace "Kin fahimci abinda nake nufi?" Ammi ta daga kai a hankali tace "Na gane" Abba yace "Hakan ya kamata, don haka Usman ko Maheer za su iya dropping dinta tomorrow in the afternoon" Ammi dai bata sake cewa komai ba, Abba yace "Kiran kenan dama" Mayraah na tsaye kitchen that same night tana dafa ma Ammi shayi ganin bata ci abinci ba taji an bude kofar kitchen din, juyawa tayi tana kallonsa har ya karaso cikin kitchen din yace "Are you making tea for Ammi?" Mayraah ta gyada masa kai, yace "Ohk, take ur time..." Juyawa yayi zai fita ta bi sa da kallo tace "Me zaka yi yaya?" Ya juyo yace "I want to make coffee" Tace "Okay let me make you" Yace "Thank you..." Kokarin fara making masa coffee din take, shi dai kallonta kawai yake, ta juya ta kallesa ya ɗan buda ido yace "Alas baki ci abincin nan ba dai Mama Ladi ta ci" Ta ɗan ɓata fuska tace "Ba nace ka kawo min daki ba ka ki kawo min" Yayi murmushi yana shafa beard dinsa yace "Bayan masifar da kika min na tashe ki bacci" Buda baki tayi tana kallonsa, ya karasa ya kashe gas din da shayin da take yi ma Ammi yake kai, ta nufesa tace "Yaya yaushe na maka masifa?" Ba tare da ya juyo ba yace "Cikin mafarki, har da murguda min baki" Daga haka ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita kitchen din ya kullo kofar, haka dai ta zuba ma Ammi shayin a karamin flask, sannan ta gama yi masa coffee din, zata fita kitchen din Usman ya shigo tana kallonsa ta mika masa flask din hannunta a hankali tace "Yaya pls ka ɗan taya ni kai ma Ammi upstairs" Yana kallon coffee din hannunta yace "Wancan kuma na waye?" Tace "Yaya" Yace "Ke bakya differentiating yayas din, which of the Yaya" Murmushi tayi tace "To kace in maka coffee ne? Beside ai kai baka shan coffee ai naga" Ya ɗan buda ido yace "Sai kice min Doctor" Daga haka ya amshi flask din hannunta ta fita daga kitchen din, ya dau cup ya tafi sama zuwa bangaren Ammi dama daga can din yake, Mayraah na zuwa kofar dakin Maheer tayi knocking a hankali, sannan ta bude kofar ta shiga, har ya sa Pajamas dinsa zai kwanta ta karasa ta ajiye masa Mug din tace "Gashi Yaya" Yace "Ohk thank you" Ta daga kai tana kallonsa sai kuma ta marairaice tace "Yaya yaushe na murguda maka baki?" Maheer ya ajiye wayar hannunsa yace "Kin kai ma Ammi shayinta?" Ta turo baki tace "Ai ba ruwan ka da wannan kuma" murmushi yayi yace "Tunda haka kika ce let me go and check for my self" Yana fadin haka ya mike ya nufi kofa ta bi sa da ido, tana ta durkushe inda take bayan fitar sa, can ta mike ta dau Coffee din da ta ajiye masa ta fita daga dakin ta koma kitchen ta zubar a sink ta wanke mug din ta kife sannan ta fita daga kitchen din ta wuce sama, a stairs ta hadu da shi yana saukowa, taki kallonsa zata wuce ya ɗan bi ta da kallo, can yace "Mimi" Ta ki juyowa balle ta tsaya, hakan yasa ya kamo hannunta yace "Are you angry?" Kamar jira take ta fashe da kuka, ya zaro ido yace "Me kuma ya faru Mimi?" Taki cewa komai tana kuka sosai, ya jawota kusa da shi yana bin ko ina na stairs din da kallo, sai kuma ya daura kanta saman kirjinsa a hankali yace "Ohk, i am sorry...." Muryarta na rawa tace "Ni yaushe na maka masifa na murguda maka baki?" A hankali yace "A dakin ki mana, yanzu ma a dakina ai kin min" Ta daga kai hawaye na zuba idonta tana kallonsa, ya ja dogon hancinta yana murmushi yace "Baki san kin yi ba ko?" Sauke idonta tayi tana tunani, sai kuma ta fara sabon kuka tace "To me nace maka ka tuna min" Getting her more closer to himself yace "Shikenan, ya wuce...." Muryar Usman suka ji duk suka juya da sauri, Mayraah ta matsa daga kusa da Maheer, yana tsaye jikin rail din stairs din supporting himself with his hands yace "Ammi's wrapper or Aunty Mariya's Wrapper?" Maheer that was confuse yace "Wrapper?" Usman yace "Eh, wai ka goyata yanda zata ji lallashin da kyau mana tunda bata da aiki sai kuka" Turo baki Mayraah tayi tana kallonsa kamar zata fashe da kuka, Maheer dai ɗan murmushi kawai yayi ya fara sauka downstairs, Usman yace "Silly gal" Daga haka ya juya ya bar wajen, Mayraah ta bi Maheer da kallo sai kuma ta bi sa downstairs da sauri tace "Yaya na fa shanye coffee din sai dai in maka wani" Ya juya yana kallonta yace "Kin dai zubar Mimi" Ta zaro ido tana kallonsa, sai kuma da sauri tace "Ba wani nan, let me make u another one in just 2 minutes" Yana ci gaba da tafiya yace "Tun da kika zubar kawai kije ki kwanta don't bother ur self" Ta marairaice tace "Plss ni dai bari zan je in maka wani" Still bai juyo ba yace "Kwanciya zan yi, kawai ki bari tun da kin zubar" Tsayawa tayi ta bi sa da kallo har ya wuce dakinsa ya kulle, a hankali ta juya ta wuce sama lkci daya duk jikinta yayi sanyi, sai tayi da ta sanin zubarwan da tayi. Washegari da safe wajen karfe goma da rabi Ammi ta shigo dakin Mayraah, ta zauna gefen gado tana kallonta a hankali tace "Mimi ki hada kayan naki, in kin gama sai ki zo in gyara maki gashinki" Mayraah ta sunkuyar da kai ta kasa cewa komai, Ammi ta mike tace "Be careful kar ki manta komai" Daga haka ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo har ta fita, nan da nan hawaye ya cika idonta, sai bayan kusan minti talatin ta mike ta fara hada kayan nata a akwati, bayan ta gama ta fita, tana tafiya a hankali ta nufi part din Ammi, sai kusan azahar Ammi ta gama yi mata gyaran gashin, Ammi na kallonta tace "Kije ki fara cin abinci sai kiyi wanka kiyi sallah...." Mayraah tace "To Ammi" Mikewa tayi ta nufi kofa, Ammi ta kalli Usman da shigowarsa kenan a hankali tace "Wa zai kai ta?" Usman yace "I will drop her" Ammi tace "Ohk, zuwa karfe uku sai ku tafi" Yace "In sha Allah" Kamar yanda Ammi tace karfe uku Usman suka bar gidan tare da Mayraah, ko sallaman kirki Ammi bata iya tsayawa sun yi ba ta shiga dakinta, tun da suka baro gidan Mayraah ke hawaye, lkci lkci Usman ke kallonta yana driving dinsa, can ya ɗan yi murmushi a hankali yace "Ke da za ki yi aurenki ki koma Familyn Dad dinki shine za ki fara kuka tun yanzu" Mayraah ta kallesa da idanuwanta da suka yi ja bata taɓa tunanin akwai ranan da zai zo a kira wani ba Abba ba da Dad dinta, Usman yayi kasa da murya yace "Mimi zaki yi aure kiyi nesa da Ammi da mu kanmu gaba daya, may be say once in a blue moon za mu dinga ganin ki" Mayraah dai sai kallonsa take, Calmly yace "Gradually bond din mu zai ragu, daga karshe ma ya zama tarihi.... that beautiful bond of 22 years.... gradually za ki mana nisa and we will have no lil sis to look upon, Ammi will have no daughter to show to the world anymore" Mayraah na share hawayen dake zuba idonta ta ɗan yi murmushi tace "You think so yaya?" Shi dai bai ce mata komai ba, ta girgiza kai cike da karfin hali kar ta fashe da kuka tace "Har cikin zuciyata nasan bani da familyn da za su fi min ku a duniya, a cikinku na taso na ga kaina, nothing can ever change the fact that ku ne family members dina a ko da yaushe, and i am sorry to say any other family member will only be a counterfeit" Usman yace "I need a favor from you Mimi, nasan tunda mu ke ban taɓa tambayarki wani abu ba sai dai ke ki tambayeni ko?" Mayraah ta juya tana kallonsa, haka kawai taji gabanta na faduwa ta rasa dalili, yace "Bazan samu favour din ba kenan" Ta hadiye abu da kyar tace "Zaka samu in sha Allah" Yace "Ohk bari in samu waje in tsaya sai mu yi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login