Showing 312001 words to 315000 words out of 452169 words
Chapter 105 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
ta karaso cikin dakin, bata taba jin kunyan Ammin nata ba irin yau, Ammi ta zauna gefenta ta dafa kanta tace "Dota kin dawo shine kika yi zamanki a daki?" Mayraah dai ta kasa dago kai ta fara kame kame, Ammi dake ta kallonta can kasan ranta kuma sai ta fara tunanin to ko dai abinda Mama Ladi ta fada haka ne don ita ko da wasa bata yarda da zancen Mama Ladi ba amma reaction din Mayraah ya sa ta fara zargin ko dai haka ne, Ammi tace "Ya kika baro yan can gidan?" Mayraah tace "Sun ce in gaishe ku" Ammi ta dan yi murmushi tace "To muna amsawa bari in je kitchen Abbanku na hanya yau" Ita dai Mayraah bata ce komai ba Ammi ta mike ta nufi kofa Mayraah ta bi ta da kallo, sosai Ammi tayi mamakin jin Mayraah bata ce bari ta zo ta taya ta ba as usual, though notice she is so uncomfortable. Maheer ya bi Ammi da kallo bayan ta sauko downstairs, ita dai kallo daya tayi masa tayi hanyar kitchen, yace "Ammi kuyi ignoring din Mama Ladi kema kin san kawai sharrin ta ne fa" Ammi dai ta tabe baki bata kallesa ba balle ta ce komai ta yi shigewarta kitchen. Bayan magrib Maheer yayi mamaki ganin Mayraah bata fito daki ba har sannan, sama ya tafi ya bude kofar dakinta ya ganta zaune saman darduma ya karasa ya zauna gefen gado yace "Baki sakko kin ci abinci ba Mimi" Tace "Aunty Bilkisu ta kawo min ai" Tana fadin haka ta nuna masa abincin, whereas Ammi ce ta sa Bilkisu ta kai mata abincin har dakin ganin taki fitowa, Maheer yace "Ohk then" mikewa yayi ya fita daga dakin. Karfe tara Mayraah tayi plugging wayarta a caji zata kwanta kenan aka yi knocking kofar dakin, ta kalli kofar sannan ta karasa ta bude a hankali, Usman ta gani tsaye ta sunkuyar da kai, yace "Ke baki san Abba ya dawo bane, ko zuwa zai yi ya gaisheki?" Ta daga kai tana kallonsa sai kuma ta marairaice tace "Yaya kaga abinda Mama Ladi ta min ko?" Da mamaki yace "Me ta maki?" Kamar zata yi kuka tace "Kana wajen fa" Ya ɗan buda ido yace "Ohh that? Kin san an taba mata aiki a ido har sau uku, probably it's making her to see things very close to each other" trying hard not to laugh ya karasa maganar keeping a serious face, Mayraah ta zaro ido tace "Da gaske" Yace "Go and greet Abba" Daga haka ya bar bakin kofar, Mayraah ta dau hijab dinta har kasa ta saka sannan ta fita zuwa bangaren Abba... A hankali ta bude kofar bayan tayi sallama ta shiga, Ammi da Abba ne kadai zaune parlon, ta karasa ta zauna saman carpet ta gaida Abba, Abba yace "How are you dear, kin dawo lafiya?" A hankali Mayraah tace "Alhamdulillah Abba, sun ce suna gaishe ku" Abba yace "To maa sha Allah" Ita dai Ammi kallon Mayraah da kanta ke kasa kawai take, Bayan some seconds Abba yace "Gobe yan Kaduna za su iso in sha Allah" Sai da gaban Mayraah ya fadi duk da tasan goben za su zo amma tana ta kauda tunanin hakan a ranta, still dai bata dago kanta ba kuma bata ce komai ba, Calmly Abba yace "Do you have anything u want to discuss with us daughter akan batun aurenki da Musharraf? Feel free ki fadi duk abinda ke ranki kin ji" Mayraah tayi murmushin karfin hali ta girgiza kai a hankali tace "Aa babu komai Abba" Abba yace "Are you sure ba wani abu Mimi?" Ta gyada masa kai, ita dai bazata taɓa cewa ga yanda suka yi da Musharraf a waya ba, he should speak for himself that tomorrow, or his relatives should speak for him, amma ita kam bazata ce komai ba, Abba ya katse mata tunaninta yace "Toh shikenan Daughter, we pray it's the best for you in sha Allah" Ita dai kanta na kasa, Abba yace "You can leave, Allah ya maki albarka" Da kyar tace "Ameen" Daga haka ta mike ta nufi kofa tana tafiya a hankali, Ammi ta bi ta da kallo hawaye cike idonta har ta fita, Abba na kallon Ammi bayan Mayraah ta fita yace "Look Madam, bana son kowa yayi kokarin canza mata ra'ayinta in anyway, nasan ki, nafi kowa saninki, nasan this isn't ur wish for Mayraah saboda wani dalilinki na daban a ranki, adalcin da za mu yi ma yarinyar nan bai wuce supporting dinta ta auri heart desire dinta ba bayan duk abinda ta fuskanta a watannin baya, shirun da tayi yanzu yana nuni da she still loves him and want to be with him, beside yaron nan ni dake mun shaida yana sonta, so na tsakani da Allah, wanda duk abubuwan da suka faru a baya shi bai gujeta ba dai dai da rana daya, don haka laifin iyayensa bai kamata ya shafesa ba in anyway, sannan so far so good yaro ne shi nutsattse ga hankali, muna kuma da yakinin zai rike mana ita da amana duba da irin son da yake mata, ina ce wannan shine babban burin ko wasu iyaye a kan er su idan aurenta ya tashi? and beside ga yanda Allah yayi lamarinsa shi Musharraf din ma ɗan uwanta ne na jini, don haka mu yi masu fatan alkhairi kawai, i think that's all" Ammi ta share hawayen dake zuba idonta tace "Amma kuma kayi saurin judging dina Yallabai, ko last week da muka yi magana da Mariya na gaya mata farin cikin Mayraah shi ne nawa, don haka ni bazan tauyeta ba, babu wanda zai canza mata ra'ayi" Abba yace "Better, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu baki daya... Da can ba Musharraf din muka yarje mata ta aura ba banda ƙaddarar da ta gifta, so now also we should support her, yaron nan ba laifinsa bane, Ko ke a shekarun baya kin taɓa tunanin hada auren Mayraah da daya daga cikin yaranki?" Ammi ta ɗan yi murmushin karfin hali ta girgiza masa kai tace "Ban taɓa ba gaskiya, don a sannan they are all same a cikin zuciyata" Abba yace "Ohh yanzu they are not same kenan?" Ta fashe da kuka tana kallonsa tace "This i never bargained for, yanzu ba ni daya ke da Mayraah ba i have to accept that, an riga da an dasa min a rai cewar rikonta kawai nayi ban haifeta ba wanda a baya ban taɓa mata kallon warce nake riko ba, a yanzu ba tawa bace ita ni kadai, Gradually kuma zata koma gun righful owner dinta, ni da ita dama sai dai hange daga nesa" Abba yace "Ke kike ganin haka har ya tsaya maki a rai" Ammi bata sake ce masa komai ba ta mike tana goge idonta ta fita daga parlon Abba ya bi ta da kallo yana jin tausayinta har ransa... Aunty Mariya na zaune dakin Usman tana kallonsa tace "Don girman Allah ka ajiye wannan laptop din magana nake maka Barrister" Ya mayar da laptop din gefe yace "Aunty na fa ce maki let leave Mayraah, i don't want it to look like mu muka canza mata ra'ayi muka sa ta yin abinda bata yi niyya ba a ranta, let just pray this is just the best, Mayraah is not a kid, kuma da Ammi ta saka a rai cewar tana aure zata mata nisa dama ai shi aure babu inda baya kai mutum, ya kai mutum kasar waje ma balle just within Nigeria, i believe Mimi bazata mance halacci ba that is just it, at the end of the day ma ni sai nayi regretting me yasa nayi mata maganar da kika ce, even the Dr da na samesa da maganar maida ni clown yayi a compound" Aunty Mariya tace "Clown as in how?" Usman na kallonta yace "He isn't taking me or the issue serious, kamar it's funny to him wai taya don Mayraah tayi aure far away zata mance Ammi, daga karshe kuma yace min shi bai ma kawo wannan tunanin a rai ba, kinga ni da ke ne kawai muka kawo hakan a rai, shi yasa kawai naga mu bar ta with her choice, mun ma yi magana da Abba shi ma yace min haka...." Aunty Mariya tace "To ai shikenan, Allah ya sa hakan shine mafi Alkhairi gare mu baki daya" Yace "Ameen, ai Musharraf din na sonta har yanzu, ita ma haka, that is the most important of all" Jawo laptop dinsa yayi ya ci gaba da abinda yake, Aunty Mariya ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo masa kofar. Washegari tun sassafe Aunty Mariya da Ammi da Bilkisu suka shiga kitchen domin fara girkin varieties na abincin da za su tari grandparent din Mayraah da shi, Mama Ladi na zaune kan kujeran dinning a bakin kofar kitchen din tace "Ai in kun kula tun jiya wasan er buya take da ni a gidan...." Aunty Mariya ta juya tana kallonta tace "Don girman Allah ki rufa mana asiri da wannan maganar da yaki ci yaki cinyewa tun jiya Mama Ladi, kuma ni wallahi tallahi nasan ba haka bane kece kilan dai kika juya lamarin a haka" Mama Ladi ta saki baki tana kallonta, can tace "Toh ki hutasshe da kanki ki ce min Ladi makaryaciya mana Mariya" Aunty Mariya dai ta ci gaba da abinda take, kilan in ba haka ta ma Mama Ladi ba wannan magana bazai taɓa mutuwa ba har Abba sai ta iya cewa zata gaya masa, don dai babu yanda za su yi da ita ne amma ita wallai bata so ma ace tana gidan Grandparent din Mayraah da iyayenta za su zo ba kar taje ta kunyata mutane kawai, Mama Ladi tace "Mutuniyar banza kawai da na haihu ai 'ya yana baza su zuba maki ido kina min wannan fitsara haka ba, ko da yake kema din dai gashi har yau shiru shekara sha uku da aure, haka nan lokacin bikin Mashir kika ce a koreni ga Ladin kauye ta zo biki...." Sai kuma ta fashe da kuka, Ammi ta kalli Bilkisu tace "Bilki kije in da wani abu zan kira ki" Bilkisu tace "To Hajiya" Daga haka ta fita daga kitchen din, Ammi ta kalli Mama Ladi cikin kwantar da murya tace "Don Allah kiyi hakuri ki rabu da Mariya Mama Ladi, baki ma tambayi wasu baƙin za mu yi ba yau muke ta girke girke" Mama Ladi tace "Yo shawara ku ke da ni da zan tambayi wasu baƙi za ayi ku gwaleni, kawai don ni Allah bai taɓa bani haihuwa ba sai in zama banza a gidan duniya...." Ammi na ɗan murmushi tace "Haba Mama Ladi, ai ke uwar mu ce halaq malaq, To iyayen Mayraah ne za su zo yau, dama so nayi ki ga hakan a ba zata shi sa nake ta boye maki" Mama Ladi ta saki baki tace "Iyayen Mera kuma? Su waye iyayen Mera da na sani banda ku?" A hankali Ammi tace "Iyayenta na asali da suka haifeta, dalilin tafiyar mu kaduna kenan satin da ya wuce, dama cewa nayi kawai sai dai mu yi ma Mama Ladi ba zata" Mama Ladi tace "Ni ai kin rikita ni, iyayenta da suka ya da ita cikin kwata a kwali ko kuma wasu iyayen kike nufi?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Bari in maki bayani yanda za ki fahimta Mama" Nan Ammi ta fara dauko ma Mama Ladi bayani tiryan tiryan sai dai yawanci duk kwaskwarima tayi ma labarin don bata gaya mata Ceo ba musulma bace, sannan bata gaya mata Ceo bace ta yada Mayraah ta dai ce wata makiyiyarsu ce a gidan tayi hakan saboda tana jin haushin Aaria, sannan still ta boye yanda Abdallah ya auri Aaria cikin sirri don iyayensa where against the marriage, bata kuma gaya mata dangantakar Mayraah da Musharraf ba don kar ma labarin yayi tsayi, haka dai tayi fabricating labarin yanda Mama Ladi bazata samu abun fade ba na har abada, Mama Ladi da ta mike tsaye ta dinga salati tana tsine ma matar da ta yasar da Mayraah, Aunty Mariya dai aikinta kawai take ta yi, Ammi tace "Kakanta sananne ne a kasar nan ma" Mama Ladi ta zaro ido tace "Waye shi?" Nan Ammi ta gaya mata sunansa, Mama Ladi ta saki sabon salati tace "Yo ai na sha zuwa kofar gidansa a Adamawa in amso abincin sadaka in kai gida wajen Hajja, don wallahi wani lokacin sai naje na bi layin karban sadaka muke samun abincin da za mu ci ku duk baku wani girma ba, kinsan babanku sai yayi tafiyarsa ya kwashe wata da watanni bamu gansa ba, haka za muyi ta wahala, sannan shi kakan nata wajen ubansa ya gaji uban dukiyar nan tasa har yayi Gwamna a Adamawa, Innalillahi wa inna ilaihi raji'una yanzu daga wannan tsatsson Mayraah ta fito?? Mahaukacin kudi fa gare kakanta ban dai san uban nata ba, matar kakar tana nan ana ce mata Hajiya Ramatu mata me kirki da faram faram da jama'a, duk sai ta tabbatar mun samu abincin sadaka a wancan lokacin in mun bi layi, kuma ai ɗanta daya tak a duniya bata sake haihuwa ba bayan shi, to ban dai san ko Alhaji Saminun ya kara wani auren ba ko uba Meran ɗan kishiyarta ne" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Wannan ɗan nasa guda dai shi ne mahaifin Mayraah" Mama Ladi ta koma ta zauna tana gwale ido tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, ita Meran? Yau mun shiga uku mun lalace Allah ya so bamu taɓa cutarta ba" Ammi bata sake ce mata komai ba ta ci gaba da aikinta ta bar ta tana ta salallami. Karfe goma Mayraah ta fito daga dakinta, tun da gari ya waye bayan ta gaida su Ammi ta koma daki bata sake fitowa ba, Breakfast ma Bilkisu ce ta kai mata, downstairs ta sauko tana tafiya a hankali, tana hango Mama Ladi zaune bakin kofar shiga kitchen duk ta cika muryarta a parlorn, ta juya da sauri tun kan ta ganta ta koma sama tana zaro ido, sai kuma ta nufi bangaren Ammi, ta bude kofar gently tana leka cikin Parlon, Maheer ne zaune da pepper soup a gabansa da bai fara ci ba, suna hada ido ta juya ta bar wajen ta koma jikin bango ta tsaya, shi dai ya ci gaba da danna wayarsa, har ta fara tafiya sai kuma ta tsaya, ta juyo a hankali ta koma bakin kofar parlon tana makale jikin kofa without looking at him tace "Yaya ina kwana" Shi ma bai kalleta ba yace "Lafiya lau, sai yanzu kika tashi kenan" Sunkuyar da kanta tayi ta karasa ta zauna kasan carpet ɗan nesa da shi tace "Aa" Bai sake cewa komai ba, ita ma tayi shiru, bayan wani lokaci tace "Baka je aiki ba?" Yace "Sai da yamma" Tace "Ohk" Mikewa tayi tana tafiya a hankali ta nufi kofa ta fita sannan ta kullo kofar. Karfe sha daya da rabi su Alhaji Saminu suka iso gidan Abba, kuma kusan tare ma suka iso gidan da Ceo da Aaria, Mayraah dai na kwance dakinta bata ma san duk sun iso ba, gaba daya ta rasa me ke mata dadi ga shi sai faduwa gabanta ke yi wanda ta kasa gane dalilin hakan, Bude kofar dakinta aka yi ta mike zaune da sauri tana kallon kofar, Usman ne ya shigo dakin ta dinga kallonsa har ya karaso yana kallonta yace "Me yasa kika makale a daki tun safe, ko saboda Mama Ladi?" Tayi murmushin karfin hali ta sunkuyar da kanta tace "Aa, bacci nayi na tashi" Yace "Hope you've taken ur bath?" Ta gyada masa kai yace "Our visitors are around" Sosai gabanta yayi mugun faduwa ta daga kai da sauri tana kallonsa....
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788
98
Mayraah na kwance dakin Ammi wajen karfe biyun dare a exact position din da ta kwanta tun karfe taran dare, ko motsin kirki bata yi a inda take kwance, kuma tun da ta kwanta ko gyangyadi bata ji ba idonta a bushe yake, ashe a baya duk ba tashin hankali ta shiga ba yanzu ne take jin ta cikin asalin tashin hankali wanda baya mitsaltuwa, gashi ko digon hawaye ya ki zubo mata ko zata dan ji sanyi a ranta, har a sannan kuma maganganun Abba sun kasa daina yawo a kunnenta, ko tsabar shock din ne yasa ta nemi hawaye ta rasa ita kanta ta kasa ganewa, a hankali ta juya ta kalli Ammi dake daya side din tana bacci, ko da Ammi ta shigo zata kwanta dazu wajen karfe sha daya pretending tayi tana bacci don kulle ido tayi, a hankali ta mike zaune ta sauke kafafuwanta daga saman gadon, sosai taji kanta yayi mata nauyi ga wani ciwo da kanta yake mata, ita tayi mamakin ma da Asthma dinta bai tashi ba yau, Ammi ta juya tana kallonta don slightest motsi ke farkar da ita bacci ta dau wayarta ta kunna fitila, da sauri Mayraah ta fara murza ido kamar a lkcn ta farka, Ammi ta mike zaune tace "Ya aka yi daughter? Kina son wani abu ne?" Bata san sanda ta girgiza kai tace "Ruwa zan sha" Sai kuma ta mike tsaye da kyar tana jin kamar jiri na dibanta, Ammi ta kunna wutan dakin tace "To ki duba parlor ko akwai ruwan, Allah ya sa Bilkisu ta kawo ruwan dazu" Mayraah ta nufi kofa ta fita daga dakin, a hankali tayi switching fitilar parlon tana bin ko ina da kallo, amma tunanin da ya tsaya mata a rai daban, muryar Ammi taji a bayanta tace "Kin samu ruwan" Mayraah ta girgiza kai da sauri tace "Zan je in dauko yanzu" Daga haka ta nufi kofa Ammi ta bi ta da kallo, bayan ta fita Ammi ta bi bayanta ta bude kofar parlon, Mayraah na jin Ammi ta bude kofa ta nufi downstairs da sauri don da tsayuwa