Showing 309001 words to 312000 words out of 452169 words

Chapter 104 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

"But da bakinsa yace ya hakura ai ko?" MD yace "He is frustrated Ma'am, amma nasan yana sonta har yanzu kawai ya rasa yanda zai yi ne, it's now left for her and her parent to do him justice" Ceo tace "To kudin aurensa da kace za a kai fa?" Yace "Ma'am that is a decision between our mother and him, uncle dinmu ai shi yanzu jiran feedback din iyayen nata yake idan sun zo ranan alhamis" Ceo na gyada kai a hankali duk da ita fa ba haka ta so ba, tace "Ohk then, i will speak to her about him, kai kuma zaka iya zuwa Canada ko wata biyu ne kayi since that is what you want, Dr Wale and Dr Ajay suna nan ai, either of them will take ur Seat kafin ka dawo" Shi dai kansa na kasa, can ya dago ya kalleta a hankali yace "Thank you Ma'am" Tace "You are welcome" Daga haka ta mike ta bar wajen ta koma cikin gida. Da daddare Ceo ta shigo dakin Aaria, da mamaki take kallonsu Mayraah na mata kalaba da dogon gashinta wanda yake har kusan bayanta, Aaria da bazaka taɓa convincing dinta ka mata kitso ba wai sai ga Mayraah na mata kitso, Ceo ta karasa tace "Kitso ku ke ta yi kenan" Mayraah na murmushi tace "Mun ma gama ai" Ceo tace "Good, in kin karasa ki zo zan sa ki wani aikin a parlor na" Mayraah tace "To" Daga haka Ceo ta fita, Bayan Mayraah ta gama tana kallon Mahaifiyarta da kyawunta ya kara fitowa tana murmushi tace "You look cute Mom" Murmushi Aaria ma tayi tana kallonta a hankali tace "Thank you my love" Mayraah ta tafi bandaki ta wanke hannunta sannan ta dawo dakin, Aaria dai sai bin ta take da kallo, ta dauko mata magungunanta da ruwan gora ta bata, sannan ta gyara mata shimfidarta, har bayan minti ashirin Mayraah bata bar dakin ba sai da taga uwarta ta fara bacci sannan ta fita zuwa gun Ceo, kujera CEO ta nuna mata, Mayraah ta zauna tana kallonta tana jiran jin aikin da zata sa ta, Ceo tace "Tell me the truth Mary Ann, har yanzu a ranki kina jin zaki iya auren brother din Aliyu that was ur fiance before?" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Ma'am mun yi waya da shi dazu yace min shi ya riga ya hakura da ni, beside yayansa ai yace mana za a kai kudin aurensa" Tana magana amma bata san har hawaye ya cika idonta ba, Ceo dai sai kallonta take, Mayraah tayi karfin halin cewa "Saboda haka nima na hakura da shi, he told me in my ears we shouldn't deceive our selves anymore, kilan ya riga ya samu wata warce yake son aure tunda gashi har za a kai kudi don haka nima i am not interested any longer, Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi" Ceo ta girgiza kai calmly tace "You are not saying this from ur heart Mary Ann, i can see it, kina sonsa har yanzu" Mayraah ta goge idonta tace "Da gaske nake Ma, ni na hakura da shi wallahi, i am not getting married to him, i assume don yana da wata ne yanzu shi yasa ya gaya min haka, if not ai bai jira ranan da aka ce za su zo ba yaga ko zan yi denying dinsa kawai ya yanke hukunci, since he isn't patient enough to wait for that day it's fine dama yana da wata da ya saka rai zai aura bayan mun rabu, i believe haka ne, Allah ya sa hakan shine mafi alkhairi gare mu baki daya" Ceo dai kallonta kawai take don bata san haka take da bakin magana ba, bayan few seconds ta sauke ajiyar zuciya tace "Me yasa baza ki masa uxuri ba?" Mayraah tace "He didn't even give me a listening ear Ma, kawai ya riga ya gama deciding and he was eager to cut off the call a lokacin, beside Ma'am yayi blocking dina fa ta wayana, ta wayar brother dinsa na samu muka yi magana, kinga assuming he is still interested bazai yi blocking dina ba" Da mamaki Ceo tace "Blocking dinki kuma?" Mayraah ta gyada mata kai a hankali, Ceo tace "To ki kyalesa, ki rabu da shi kawai, may be kamar yanda kika fada ya samu wata ne if not da sai ya jira yaga ko zaki amince da auren nasa ko baza ki amince ba, just leave him" Mayraah dai ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba wasu sabbin hawayen na taruwa idonta, Ceo tace "I think kamata yayi a bar zancen auren nan haka gaba daya har Allah ya kawo maki wani zuwa wani lokaci, duka duka shekarunki nawa, marriage is not something to rush about, you are still young, probably idan Parent dinki suka ji stand din Brother din Aliyu su ma za su bar zancen auren" Mayraah ta daga kai tana kallonta a ranta kuwa taji dadin wannan maganar da tayi, don ita kanta zata zo a bar zancen auren nan zuwa wani ɗan lokaci zuciyarta ya huta from all this stress of few days ago, she need rest, yanzu kawai jira zata yi taga abinda zai faru idan Uncle din su Musharraf suka zo, Ceo bata sake cewa komai ba nan kuwa ita ma wani tunanin ne daban a ranta, Bayan wani ɗan lokaci Ceo ta sauke ajiyar zuciya tace "Zaki iya tafiya ki kwanta, do not stress u self anymore pls, ki kwantar da hankalinki kin ji?" Mayraah ta gyada mata kai a hankali tace "Thank you Ma'am" Daga haka ta mike ta nufi kofa, Ceo ta bi ta da kallo har ta fita ta kullo mata kofar. Kamar yanda Ceo tace ma Mayraah ta kwantar da hankalinta haka ta kwantar da hankalinta sosai ta cire duk wani damuwa a ranta tana harkokin gabanta, ta maida attention dinta gaba daya kan uwarta tana kula da ita tayi mata girki ta gyara mata daki ta hada mata ruwan wanka, duk wani abu dai da Farida ke ma uwarta duk ta dauke mata ita ke yi, yini take tare da mahaifiyarta a dakinta tana mata hira ko kuma su fito parlon dake sama, ita kanta bata san zata yi saurin sakewa da mahaifiyarta haka ba ta dinga jin ta har ranta don at times sai Ammi ta fado mata zata yi maza taje ta kirata a dakinta, Abba dai tun zuwanta sau biyu tayi waya da shi, Maheer bai kirata ba ita ma bata kirasa ba. Ranan laraba da yamma misalin karfe biyar Mayraah na hada kayanta a akwatinta da ta dawo da shi dakin uwarta gaba daya, duk jikinta a sanyaye ta ke hada kayan har ta gama ta kulle box din, Aaria dai na zaune gefen gado tana ta kallonta bata ko kiftawan kirki, bayan wani ɗan lokaci Mayraah ta daga kai tana kallonta, mikewa tayi tana tafiya a hankali ta isa kusa da ita ta zauna gefenta tayi mata side hug ta jinginar da kanta jikin shoulder dinta cikin sanyin murya tace "Momy kiyi hakuri, ai zan dawo in sha Allah, i will be back soon" Aaria da hawaye ya cika idonta ta sauke kai bata ce komai ba, Mayraah duk jikinta yayi sanyi bata san sanda ta rungumeta ba a hankali ita ma hawaye cike idonta, muryarta na rawa tace "I promise you i will be back soon, i have cook all ur favorite na sa maki a freezer, microwaving dinsa kawai Aunty Farida zata dinga maki kinji?" Aaria ta gyada mata kai kawai hawaye na zuba idonta bata iya ta ce komai ba, a haka Ceo ta shigo dakin ta samesu don Driver na jiran Mayraah tun dazu, juyawa tayi ta fita daga dakin kawai ita ma duk jikinta yayi sanyi, Mayraah tayi pecking din mom dinta a goshi ta kara rungumeta tightly tace "Sai na dawo in sha Allah" Daga haka ta mike tana goge idonta ta tafi ta dau akwatin ta, ta juya tana murmushin karfin hali tace "Momy baza ki rakani bakin mota ba?" Girgiza mata kai kawai Aaria tayi, Mayraah ta ja box din ta nufi kofa, bata yarda ta juyo ba saboda hawayen dake sauka idonta har ta fita daga dakin ta jawo kofar a hankali, a parlor ta tadda Ceo a zaune, Ceo na kallonta a hankali tace "Kin ce mata zaki dawo?" Mayraah ta gyada mata kai, Ceo tace "Zan kira ki da layinta sai ki dinga kiranta frequently kin ji?" Cikin sanyin murya Mayraah tace "Toh...." Mai aikin Ceo ta kai uban shopping din da Ceo ta sa aka yi ma Mayraah da akwatinta har bakin tsadadden motar da zai yi dropping dinta a gida, Ceo na rike da hannun Mayraah suka fita har zuwa parking space din, har cikin ranta take jin kewar mahaifiyarta tun bata bar gidan ba, yanzu shikenan ita kadai zata yi ta zama a daki don da alama ko zaman parlor bata so, Mayraah ce ke jan ta su fito parlor, Ceo tayi pecking hannunta tace "Take care of ur self daughter" Mayraah ta gyada mata kai tana murmushin karfin hali, Ceo tace "Ki gaida min parent din ki da brothers din ki" Mayraah tace "Toh za su ji" Har Mayraah zata shiga mota sai kuma ta tsaya tana kallonta cikin sanyin murya tace "Ma'am ai za ki zo gobe, pls ki zo tare da ita" Ceo ta ɗan yi murmushi tace "Ohk i will my dear" Daga haka Mayraah ta shiga bayan motar ta ɗan ji ta samu relieve don gobe alhamis Ceo zata zo gidan nasu saboda Uncles din su Musharraf that will be around, Ceo ta kulle motar tana daga mata hannu har suka bar babban compound din. Mayraah na isa dai dai gate din gida taga Usman tsaye bakin gate din shi da Security alamar magana yake masa amma tun da yaga motar ya maida attention dinsa kan motar waiting to see who is inside, Tuni Drivern motar ya sauka ya bude mata motar kafin ta ankare, ta ɗan buda ido cause bata yi expecting haka ba, can dai ta sauko daga cikin motar, er dariya Usman yayi bayan ya ganta, ita kam murmushi kawai tayi ta nufesa tana tafiya a hankali, yace "Ni ai na zata er wani governor ce ta shigo estate din namu za ayi dropping dinta gidan kawarta or so, ashe dai Mimin mu ce" Mayraah bata san sanda tayi dariya ba tace "Kai yaya" Yace "Irin wannan mota haka Mimi" Ta marairaice tace "Yaya Allah bana so" Yana murmushi yace "Tohm an daina, welcome back home" Ta sauke idonta a hankali tace "Thank you, good evening" Usman yace "How are you?" Tace "Alhamdulillah" Security din gidan ne ya amshi kayanta gun driver din da ya kawo ta, Usman na kallonta yace "Ko dai sai an bude maki gate din gidan ne?" Bai jira me zata ce ba ya bude mata gate yanda drivernta ya bude mata mota, Dariya tayi tace "Don Allah yaya ka bari pls" Yace "Shiga dai an bude maki naga kamar haka kike jira" Shiga gidan tayi tana murmushi tace "Thank you" Yace "Ya kika baro yan can gidan?" Tace "Suna gaisheku" Yace "Muna amsawa" Tafiya ta fara yi zuwa main entrance din gidan ta bar masu kayan nata gaba daya, tana isa kofar shiga Parlon ta bude a hankali sannan ta shiga da sallama, Maheer ne kwance 3 seater a parlon yana kallon kwallo, yana jin sallamarta ya kulle ido as if yana bacci, ta gefen ido take kallonsa da ta shigo parlon can ta dauke idonta har ta fara tafi hanyar staircase sai kuma ta juya ta kallesa sake rufe idonsa yayi ruff kamar me bacci, juyawa tayi bayan komai yayi escaping mind dinta, lkci daya ta koma cikin parlon ta zagaya ta inda kansa yake ta sakalo kanta tana kallonsa a hankali tace "Stop pretending Yaya" Still dai bai bude ido ba, dukawa tayi ta kai fuskarta dai dai nasa har yana jiyo saukan numfashinta tace "Allah nasan ba bacci kake ba da yamman nan" A hankali ya bude ido suka yi ido hudu da shi, a gigice suka ji muryar Mama Ladi da ta fito daga kitchen da kwanonta cike da shinkafa da miya tace "Auzubillahi ni Ladi, sumbatar sa kike Mera?" Mayraah ta dago kanta da sauri ta tashi tsaye, shi kuma ya mike zaune, Mama Ladi dai ta saki baki tana kallonsu da idanuwanta kamar za su fito alamar ta gigice, Can tace "Usuman wallahi tallahi abinda na gani kenan, kai in na masu sharri kar Allah ya bani cin gobe da na jibi, ashe kai ma dai kana tsaye jikin kofa kana kallon ikon Allah, ace gubar lafiya Mera ta ci?? Sumbatarsa fa take, Aa ba ruwana wallahi" Mayraah ta juya da sauri ta kalli bakin kofa taga Usman dake dariya har ya juya ya fita daga parlon ya bar mata kayanta a bakin kofar, Mayraah ta maida dubanta kan Mama Ladi da sauri ta marairaice tace "Sumbata kuma Mama? Wallahi kawai...." Mama Ladi taki tsayawa balle ta saurareta irin taga abinda ya fi karfinta din nan tayi hanyar stairs kawai da sauri, Mayraah ta kalli Maheer hankali a tashe kamar zata yi kuka tace "Yaya shine zaka yi shiru?" Ya gyara zama yace "Nima ba farkawa nayi naga kamar kina hakan ba"

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

97
Maheer yayi murmushi ganin how shock Mayraah was looking at him, ya dan buda idonsa yace "To ke me zai dameki? Ko dai kin yin ne gaya min gaskiya Mimi...." Ko kallonsa bata sake yi ba ta juya ta nufi stairs da sauri, ya bi ta da kallo yace "Mimi" Juyowa tayi tana kallonsa, ganin yanda yanayinta ya canza ya mike yana kallonta da mamaki yace "Kuka za ki yi?" Kawai ta fashe da kuka kamar jira take , ya buda baki sai kuma ya nufeta da sauri yace "C'mon Mimi, wasa fa Mama Ladi ke maki, ke baki san wasa ba" Cikin kuka tace "Wallahi ba wasa take ba she was very serious kuma kayi shiru kana kallonta, yanzu zata je ta dinga ta fada a gidan nan, what if Ya Usman ma ya yarda da abinda tace" Sai ta kara rushewa da kuka, dariya sosai ta basa sai dai bai yi ba ya kamo hannunta yace "To yi hakuri Mimi" Tana goge hawayen idonta tace "Ni dai mu je kace mata ba haka bane" Yace "Me zan ce mata ba haka bane?" Ta masa wani kallo, yayi keeping serious face yace "Tell me mana" kwace hannunta tayi zata bar wajen ya sake rikota yace "Toh mu je in gaya mata kema sai ki sake mata bayani da kanki" Stairs suka nufa tare yana kallonta ganin da gaske ita hankalinta fa ya tashi, murmushi yayi har suka haura sama zuwa dakin da Mama Ladi take, ba a rufe kofar dakin sosai ba Mayraah taji muryar Mama Ladi tana cewa "Wallahi wallahi idan na masu sharri Ammi kar Allah ya ban ikon cin abincin nan lafiya, ni na fito kitchen kenan shi kuma wannan mutumi Usman ya shigo parlon, tsabar yanda shi ma ya gigice wllh sai makalewa yayi jikin kofa ya kasa shigowa, to in son Mashir din take uban me kuma ake jira? Magana ta gaskiya fa tunda Mera ta ci guba ta fara fin karfin mu a gidan nan, dama guban har da iskanci yake sakawa ko dai irin wanda ita ta ci ne hka?" Mayraah da wasu hawayen suka cika idonta ta juya tana kallon Maheer da ya juya mata baya nan kuwa kokarin danne dariyarsa yake, juyawa tayi ta bar wajen ta nufi dakinta da sauri, bin bayanta yayi har zuwa dakin nata, Mama Ladi na fifita da dankwalinta tace "A gaskiya ba ruwana, naga ma kamar kun mayar da ni ban san abinda na gani nake fada ba duk kun min shiru ga Ladi er iska, shi fa Mashir din nan dama can ya taba aure, sarai yasan meye aure, idan ta ci gaba da yi masa haka wataran biyeta zai yi barin an fasa masu kwan cewar ba muharramarsa bace, lamari ne kawai zai lalace daga ni har ku mu shiga uku, mu kuma kenan ace pamilyn mu daga wannan sai wannan, to ko dai iyayen nata da suka jefar da ita cikin kwata sun hada jibi da turawa ne, kunsan su basu dau Sumbata a bakin komai ba da yake kafurai ne" Ammi dai idonta na kan TV dake aiki Aunty Mariya kuwa danna wayarta kawai take kanta a kasa, Mama Ladi tayi kwafa ta jawo abincinta ta fara ci. Maheer ya kulle kofar dakin yana kallon Mayraah da ta zauna gefen gadonta ta hade kai da pillow tana rusa kuka, karasawa yayi ya zauna kusa da ita ya dagota yace "Ke fa bush gal ce Mimi" Cikin kuka sosai tace "Su Ammi fa taje tana gaya ma yaya, wayyo Allahna na shiga uku" Shi dai kallon bakinta kawai yake, can ya sauke idonsa a hankali yace "Kiyi hakuri, zan je in ce masu bayanin ba haka bane" Yana fadin haka ya fara goge mata idonta da hannunsa yace "It's okay lil sis" Ta daura kanta a shoulder dinsa tana sheshekar kuka, yayi kasa da murya yace "Baza ki daina kukan ba?" Cikin rawan murya tace "Yaya sharri fa ta min" patting bayanta yayi yana murmushi yace "Ai duk mun sani" Sai da yaga ta daina kukan gaba daya sannan ya dago kanta yace "Let me go and meet them" Gyada masa kai tayi a hankali, ya mike ya nufi kofa ya fita daga dakin ya kulle mata kofar, downstairs ya sauka yana murmushi ya tafi ya ci gaba da zamansa a parlon. Mayraah dake ta zaune dakinta har wajen karfe shidda saura ta kasa fitowa balle taje ta gaida Ammi, bude kofar dakin aka yi ta juya da sauri, Ammi ce ta shigo dakin Mayraah ta kasa kallonta har

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login