Mayrah
Chapter 107 of 152
biyu don ina son ta dawo da wuri a fara mata gyaran jikin, in kuma za su mata can din to" Usman yace "Allah ya kai mu" Ammi tace "Ina son zuwa nan da kwana biyar a gama hada komai na lefen tunda kun ga kaduna za a kai masu kayan" Usman yace "A nan Abuja za a hada kayan?" Ammi tace "Eh da zan ma surkar Dr Khalil magana don muna gaisawa sosai da ita, Hajiya Safiya ma zata shigo Abujan sai su hada kayan tare kawai, Mariya kaga yau ta koma sai kuma biki zata dawo" Usman da yayi shiru yana kallon Ammi ya dan yi murmushi yace "But Ammi, Hajiya Amina dake kano ko ita ma zata iya hada kayan cause business dinta ne ba sai in involving outsiders ba" Kallonsa kawai Ammi take, can tace "To sai ka kwashi kudin ka tura mata ta hada" Usman yayi er dariya ya mike yace "Ni akwai inda zan je yanzu, sai na dawo" Ko kallonsa Ammi bata yi ba ya nufi kofa ya fita, Ammi tace "In nasa bikin ya tashi sai ya bata kudi ta hada masa kayan wannan kam bai isa ya gaya mana yanda za mu yi ba" Shi dai Maheer bai ce komai ba, can dai yayi murmushi ya mike, Ammi tace "Ka je ka ci abinci bawan Allah" Usman na fita ya yi knocking kofar dakin Mimi, Yana nan bakin kofar a tsaye har Maheer ya wuce sa ya sauka downstairs, Mayraah ta bude kofar dakin a hankali tana ganinsa tace "Yaya fita zaka kara yi?" Yace "Eh, fito ki ci abinci" Tace "Na ci abinci" Yace "Ammi tace baki ci da yawa ba" Shiru tayi bata ce komai ba, can tace "Yaya don Allah zan iya gaya ma Ammi ina son inje gidansu Ceo?" Usman yace "Ai ina jin Sunday za su tafi can kaduna, next week idan kinje kadunan za ki hadu da su a can" Bata sake cewa komai ba, yace "Fito ki zuba abincin?" Babu musu ta fito daga dakin suka sauka downstairs, ya zauna parlor yana jiran yaga ta zubo abincin kafin ya bar gidan, har ta nufi kitchen ta juyo tace "In zuba maka kai ma yaya?" Yace "Aa sai na dawo" Bata sake cewa komai ba ta nufi kitchen din, wani irin faduwa gabanta yayi bayan ta shiga kitchen din ta ga Maheer, lkci daya ta juya ta fito daga kitchen din fuska daure, Usman yace "Ina abincin?" Kin cewa komai tayi tana tahowa a hankali, yana ganin Maheer ya fito kitchen din da cup din coffee sai da abun ya basa dariya, shi dai Maheer bai kalli inda take ba balle Usman dake zaune ya nufi dakinsa, Usman ya mike kafin yace mata komai ta nufi sama, yace "Mimi" bata tsaya ba tayi wucewarta. Kamar yanda Ammi tace washegari da safe ta shirya ta tafi gidan surkar Dr Khalil bayan ta sanar ma Abba da ya koma kano jiya da yamma, Ammi bata bar gidan ba sai da ta tabbatar Mayraah tayi breakfast sanin bata son cin abincin.... Bayan azahar Usman zai fita Mayraah ta marairaice masa tace "Yaya kai ma fita zaka yi Ammi bata dawo ba" Ya kalleta da mamaki don makullin motarsa da ya bari jiya a dakinta ya shigo dauka yace "Akwai aikin da kika bani ban yi bane Mimi?" A hankali tace "To ni kadai fa a gidan" Yace "Bilkisu na nan ai, even Dr bai tafi aiki ba tukun ai sai da yamma" Bai jira cewarta ba ya nufi kofa, tace "Pls yaya zan rakaka" Sosai ta basa dariya, ya juyo yace "Ki rakani ina?" Ta sauke idonta tace "Inda za ka" Yace "Ni ai ba wani waje zan je ba Client ne ke jirana" Tace "Eh zan bi ka sai in jira a mota" Ya gyada kai yace "To je ki tambayi Dr" Tayi kasake tana kallonsa yace"Yea, in kina son bi na je ki fara gaya masa tukun" Tace "To saboda me?" Yace "Saboda ya kamata a gaya masa" Komawa tayi ta zauna alamar baza ta ba, Usman yace "Sai na dawo" Ta marairaice tace "Don Allah yaya" Ya wani hade rai yace "Ba ki ji abinda nace maki bane?" Shiru tayi tana kallonsa, ya fice daga dakin, a hankali ta mike ta dau gogaggen hijab dinta ta saka sannan ta fito, har zai fita parlon ta gansa da sauri tace "Don Allah ka jirani yaya" Ya juya yana kallonta, ita dai da ya bar ta ita kadai da Maheer a gidan gwara tayi abinda yace kawai, tana tafiya a hankali ta tafi dakinsa, kwankwasa kofar dakin ta yi sannan ta bude fuskarta babu yabo babu fallasa ta shiga, tana kallonsa tace "Wai ya Usman yace za mu fita ka kula da gidan ba kowa" Shi dai danna wayarsa kawai yake, bai daga kai ba balle ya kalleta, ta dinga kallonsa, can tace "Yaya magana nake maka" Jin bai tanka ta ba ta tura baki ta juya ta bar bakin kofar, ta koma ta samu Usman dake bakin kofa har sannan tace "Yaya na gaya masa" Yace "Me kika ce masa?" Tace "Za mu fita da kai" Usman yace "Client din ma sai gobe za mu hadu naji garin da rana..." Daga haka ya koma ya zauna kan kujera, ita babban takaicinta Maheer da yasa taje tayi ma magana gashi ko kula ta bai yi ba yayi mata banza, a hankali ta fara tafiya ta wuce sama, Usman ya bi ta da kallo yana murmushi.....
99
Yau ma dai kamar jiya Mayraah bata samu tayi baccin kirki ba da daddare, Allah Allah kawai take gari ya waye don tun a daren jiyan kafin su kwanta Ammi ta hada mata kayanta wai gobe za a kai ta kaduna, har cikin ranta tayi farin ciki da wannan tafiyar da zata yi don taji gaba daya bata son zaman gidan yanzu, bata jin gidan as her comfort zone anymore kuma sai yanzu taji zuciyarta ya gama amincewa da she is not longer a member of the family, don an nuna mata haka tunda har ake son ta auri Ya Maheer, shikenan sun cireta daga family dinsu, da asuba tana zaune saman darduma bayan ta idar da sallah, Ammi ma na zaune tana azkar dinta, karfe shidda da yan mintuna Maheer ya shigo dakin da sallama, Ammi ta daga kai bayan ta amsa sallamansa, ya karaso ciki ya zauna yana kallonta yace "Ina kwana Ammi?" A hankali Ammi tace "Lafiya lau, how was ur night?" Yace "Alhamdulillah" Ita dai Mayraah bata ko kalli inda yake ba kamar yanda shi ma bai kalli direction dinta ba, bayan wani dan lokaci ya mike yace "Ammi za mu shiga Niger state zuwa anjima, wani colleague dinmu lost his son za mu je masa ta'aziyya....." Ammi tace "Allah sarki, Allah ya gafarta masa" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga dakin, Ammi ta mike ta bi bayansa, har ya bude kofar parlor zai fita ya juya yana kallonta ganin ta fito daga dakin, ta kulle kofar dakin nata sannan ta tafi har inda yake tana kallonsa cikin kwantar da murya tace "Maheer amma nace maka yau za taje kaduna in ji Abban ku ko" Maheer dake kallonta a takaice yace "Eh haka kika ce" Ammi tace "To dama ba kai zaka kai ta ba?" Ko rufa baki bata yi ba ya girgiza kai da sauri yace "Aa ni gaisuwa za mu je, ba ga Usman ba" Ammi tayi shiru tana kallonsa, sai kuma a hankali tace "Ka fi kowa sanin halin Mimi Maheer, kayi hakuri da abubuwan nan da take yi, it is just a matter of time, she was taken unaware we shouldn't blame her" Maheer yace "I am not complaining and i will never complain, beside i was also taken unaware" Ammi tace "To ko baza ka kai ta kai kadai ba ku je tare da Usman din" Da mamaki yace "Ammi gaisuwa fa nace maki za mu je Niger" Ammi tace "Ae naga dai ba da sassafen nan nace maka za a kai ta kadunan ba, kwana za ku yi a Niger din in kun je, do what suit you Maheer" Daga haka ta juya ta bar wajen ya bi ta da kallo, juyawa yayi ya bude kofar parlon ya fita kawai.... Karfe sha biyu Mayraah ta gama shiryawa ta dau handbag dinta, tare suka fito da Ammi da ta tabbatar bata mance komai ba, ta bi ta har parking space, Usman dake tsaye kusa da motar ya karasa ya amshi akwatin hannun Ammi yana kallonsu yace "Da wannan akwatin kawai zata tafi?" Ammi tace "Eh" Bude booth yayi ya saka mata box din, sosai gaban Mayraah ya fadi ganin Maheer zaune gaban motar, ta sunkuyar da kanta Ammi ta bude mata back seat ta shiga, Usman na kallon Ammi yace "Toh sai mun dawo" A hankali Ammi tace "Allah ya tsare, ku yi addu'a" Sai da ya shiga motar sannan Maheer ya daga kai ya kalli Ammi yace "Sai mun dawo" Ammi ta gyada masa kai tace "Journey mercies in sha Allah" Tana tsaye har suka bar compound din.... The journey was silent don har suka bar garin Abuja babu wanda yace komai a motar, bayan wani lokaci Usman ya bar ma Maheer driving din, ita dai Mayraah daga karshe bacci tayi tun da ba wani bacci take samun yi da daddare ba, Sai da suka shigo garin kaduna ta farka daga baccin da ya dauketa, kallon gaban motar take ganin Usman ne ke kadai yana driving Maheer baya motar, saura kadan tace masa ina Yaya don har ta bude baki lkci daya ta rufe da sauri, Usman dake kallonta ta madubi yace "Weldone" Ta dan yi murmushi kawai bata ce komai ba, dai dai kofar gidan Alhaji Saminu yayi parking, Mayraah ta dinga bin unguwan da kallo kafin ta sauka daga cikin motar a hankali, bayan Usman ya sauka ya fiddo mata kayanta a bayan mota, tana tsaye absentminded har ya kawo mata akwatin kusa da ita, kawai ita dai ji tayi bakinta yace "Ina yaya fa" don sai da tayi shock jin tambayar da bakinta yayi, Usman ya daga kai yana kallonta yace "Yaya kuma, baya cikin motar ne?" Sai kuma ya bude motar da sauri yana duba ciki da mamaki a fuskarsa, Mayraah dake kallonsa ta zaro ido ganin facial expression dinsa tace "Ina yaje? Kai baka san sanda ya sauka ba dama?" Usman yace "Ohh oh na tuna, tun a hanya ya sauka ashe, haka ne a hanya ya sauka" Without any thinking tace "To me yasa? Kuma ina yaje?" Usman yace "I don't know too, in ba dai ki kira mana shi da wayarki mu tambayesa ba" Mayraah ta sauke idonta bata sake cewa komai ba, can ta duka zata dau akwatinta ya riga ta dauka suka nufi gate din gidan a tare, sai da Usman ya shiga har cikin gidan ya gaida Grandmum dinta da Aunty Halima dake gidan, ruwa kawai ya dauka cikin abubuwan da aka kawo masa sannan yayi masu sallama, Hajiya Ramatu tace "Me yasa baza ka sauka a nan ba? They are enough rooms ai" Yana murmushi yace "Ai Abuja zan koma ne yanzu don ina da aiki gobe Umma" Hajiya Ramatu tace "Allah sarki, to Allah Ubangiji ya tsare hanya Usman" Mayraah dake zaune parlor ita dai kallonsa kawai take, ganin ya nufi kofa ta ɗan kalli Hajiya Ramatu da Aunty Halima dake parlon, Aunty Halima tace "To ki je ku yi sallama mana Mayraah" Ita fa duk tunanin Aunty Halima Usman ne mijin, Mayraah ta sauke kanta sannan ta mike a hankali ta bi bayansa, bayan sun fito compound tana kallonsa tace "Yaya dama Abuja zaka koma?" Yace "In sha Allah" Ta ɗan yi shiru sai kuma tace "To a ina zaka samesa shi yanzu?" Duk da yasan wa take nufi sai yace "Wa?" Bata sake ce masa komai ba, ya ɗan yi murmushi yace "Wai Ya Maheer? zan ta duba hanya ko zan gansa, in ban gansa ba sai ya tafi tasha ya hau motar haya" Mayraah dai tayi shiru, yace "So now... Enjoy ur stay and be a good gal Mimi" Tayi murmushi ta gyada masa kai yace "Bye" Ɗaga masa hannu tayi ya juya ya nufi gate sannan ta koma cikin gidan tana tafiya a hankali, Hajiya Ramatu ta kai Mayraah nata Bedroom din da ba kowa ke ma zuwa bangaren ba, har cikin ranta take jin Mayraah, wani irin so take mata kamar yanda take ma Ubanta Abdallah, ta so ace sun samu daman rayuwa tare da Mayraah cikin su, kuma ta so auren nata ma ba yanzu aka daura ba duk don suyi creating bond din da babu tsakaninsu, but they are not in the righful place to tell Abba and Ammi tsarin da za suyi ma Mayraah, tunda aure suke son mata sun ga hakan ya dace ne, but Mayraah is their only grandchild a duniya ta so su ma sun kwatanta nuna mata gata kamar yanda su Abba da Ammi suka mata, suna shigowa dakin Mayraah ta gane dakin kakarta ne, Hajiya Ramatu na kallonta tace "Kin ce baki yi sallah ba, ga bandaki kije kiyi alwala kiyi sallahn, yanzu za a kawo maki abinci" Mayraah tace "Toh" Bayan Hajiya Ramatu ta fita Mayraah ta dinga bin babban dakin da kallo, bayan ta idar da sallah sai ga Hajiya Ramatu ta shigo mata da abinci iri iri ta ajiye gabanta, Mayraah felt loved, and she felt really at home, taji kuma tana son Hajiya Ramatu har cikin ranta, bata taɓa tunanin a rayuwarta akwai sanda zata ga wata a matsayin kakarta ba Hajja ba, ta taso tana ma Hajja kallon kakarta ne duk tsawon rayuwarta, a ranan kusan duk matan yan uwan kakanta Alhaji Saminu dake nan cikin garin kaduna suka zo yi ma Mayraah sannu da zuwa tare da yaransu, wasu sa'anninta wasu sun girmeta, wasu ta girmesu ga dai su nan, babban family ne sosai me cike da yara da jikoki, kowa kuma Mayraah yake zuwa gani, ba su suka bar gidan ba kuma sai bayan Magrib. Washegari sai kusan da rana Mayraah ta sauko downstairs don bacci kawai take ta yi tun dazu, Hajiya Halima dake zawarci a gidan tana gyara dankwalin kanta tace "Kin sakko kenan Mayraah" Mayraah ta ɗan yi murmushi ta karasa ta zauna tace "Eh" Kakarta dai sai kallonta take with love, Hajiya Halima ta mike ta dau handbag dinta tace "Dazu Abba ke tambayarki nace ai kina bacci" Sallama aka yi a parlon duk suka daga kai, Mayraah dai kallonsa take har ya shigo parlon kansa a kasa, Hajiya Ramatu tace "Har ka dawo kenan Daddy" Yace "Eh daxu da safe na dawo" Zaunawa yayi yana kallonta yace "Ina wuni Mama" Tace "Lafiya lau Dr, ya su Mami? Ya jikin nata? Ko da yake mun ma yi magana da ita ai dazu, tace min tana da bakuwa ko" Yace "Haka ne" kallon Aunty Halima yayi ya gaisheta ita ma, ta amsa tace "Baka koma aiki ba kenan Daddy?" Yace "Ina hutu, za ki fita ne" Tace "Wallahi kawata ce ke aurar da 'ya, har an gama biki jiya ban je ba, shine zan je in mata Allah ya sanya alkhairi" Yace "Ohk" Sallama tayi ma Hajiya Ramatu, sannan ta kalli Mayraah tace "Mayraah sai na dawo" Mayraah tace "Allah ya tsare" Sai a sannan ya kalli Mayraah, tana ganin haka ta sunkuyar da kanta, yace "Sannu Amarya" Ta sake daga kai ta kallesa duk yanda ta so kar ta hade rai kasawa tayi, saboda me zai ce mata amarya, amarya kuma kamar yaya, da kyar ta bude baki tace "Ina yini" Yace "Lafiya lau" Ya maida dubansa kan Hajiya Ramatu yace "Mama Baffa yana nan kuwa?" Tace "Bai jima da fita ba, yace min dai zaka kawo masa magunguna" Yace "Ehh na so in dubasa ne in ga ko there is need in canza maganin" Tace "Ai kam sai can magariba zai dawo" Yace "Toh Allah ya kai mu, ni zan koma, zan dawo bayan magrib din" Tace "Toh shikenan, kana ji Daddy, nayi waya da can iyayen Mayraah nace za a kai ta gidan yaron nan taje ta gaishesu, duk da ya zo dazu tana bacci, to amma dai ta je ta gaishesu, idan ya so daga can sai ku tafi gidanku ta gaida Mami, in zaka dawo da magrib ka taho da ita, bana son hadata da driver, na so Halima duk ta kai ta to jiya ni na tsayar da ita bata je bikin er kawarta ba zata je mata Allah sanya alkhairi yau, ita kuma Mayraah ban san kwanaki nawa iyayen suka deban mata tayi ba" MD yace "Toh shikenan Mama" Hajiya Ramatu ta kalli Mayraah tace "Baby je ki shirya kawunki ya ajiyeki gidan ɗan uwansa kin ji" Mayraah bata ce komai ba ta mike ta wuce sama ita ba fitan ne ma ya tsaya mata a rai ba gidansu MD din da aka ce har can a kai ta ne ya dameta, taje tayi me kuma a gidan nasu, zaunawa tayi gefen gado tasan kilan in aka ji shiru bata sauko ba kakarta zata biyota saman sai ta gaya mata ita dai bazata gidansu Musharraf ba, ai kam bayan kusan minti talatin sai ga Hajiya Ramatu ta shigo dakin, da mamaki take kallonta tace "Baby baki shirya ba?" Mayraah ta sauke idonta a hankali tace "Umma ni bana son inje can gidan nasu" Hajiya Ramatu ta karaso gefenta ta zauna tace "Wani gidan kenan? Ko gidansu Aliyu?" Mayraah ta gyada kai, Hajiya Ramatu ta dafata cikin kwantar da murya tace "Kin ga Mamin bata da lafiya, kuma tasan kin zo, ko da muka je Abuja ranan alhamis din nan da ya wuce kawai karfin hali tayi amma bata jin dadi, bayan mun dawo sai da aka mata ƙarin ruwa, banda zuwan da za muyi Abujan da ta koma kano tun last week sai ana sauran kwanaki biki zata dawo, kiyi hakuri kije sai ki mata ya jiki kin