Showing 321001 words to 324000 words out of 452169 words

Chapter 108 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

dariya Jiddah tayi MD ya jefa mata wani kallo, ya ajiye ledan maganin a kasa ya mike ya fita daga parlon, Mami tace "Atoh, ka ban magani yana ta wujijjiga ni tun shekaranjiya, wnn kuma gashi tun safe da na sha lafiya lau" Jiddah ta mike tana murmushi ta fita daga parlon, ba a dau lokaci ba sai gata ta dawo rike da tray din ruwa da lemo ta ajiye ma Mayraah, ita dai Mayraah bata sake yarda ta kalleta ba, Jiddah ta koma kan kujera ta zauna, Mami na kallon Mayraah tace "Ya su Amminki da Abba?" A hankali Mayraah tace "Duk suna lafiya, suna gaisheku" Mami tace "To maa sha Allah" Haka Mayraah tayi ta zuba ido taga MD ya zo ya maidata gidan kakanninta amma shiru har six, kana ganinta kasan a takure take a parlon, abincin da aka kawo mata ma bata ci ba, tana ganin Magrib ya gabato taji hankalinta ya tashi, gashi ta kasa ce ma Mamin ai ance ta dawo gida kafin magrib, a haka dai taje tayi alwala tayi sallah a Parlon, tana zaune kan darduma aka bude kofar parlon ta daga kai da sauri ya shigo da sallama, Mami tace "Wai fita kayi dama" Yace "Aa ina Chalet" Kallon Mayraah yayi sannan ya kalli Mami yace "Mami zan maida ta gida" Mami tace "Da Magariban nan zaka maidata gida? Ina laifin gobe da safe" Mayraah taji gabanta ya fadi, MD yace "Umma cewa tayi in maidata da magrib" Mami tace "Aa bai kamata ba, tomorrow is another day in sha Allah, zan kira Maman" Mayraah ji tayi kamar ta rusa ihu a parlon hankalinta yayi mummunan tashi, MD yace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga parlon, sai ga Jiddah ta shigo, Mami na kallonta tace "Jiddah ki bata kananun kaya ta canza na jikinta" Jiddah ta kalli Mayraah tace "Ohk" Mami tace "Bi ta ku je Mayraah" Mikewa Mayraah tayi tana tafiya da kyar tabi bayanta suka fita daga parlon Mami. Har isha Mayraah na makale a dakin, abinci ma sai kawo mata daki aka yi, bata taba shiga takura irin haka ba a rayuwarta, ji take kamar a ƙaya take, Jiddah dai sai harkar gabanta kawai take alamar dai ita ma bata sakewa da stranger, Mayraah sai dai tayi ta satan kallonta, wajen karfe tara Mayraah dake zaune dakin ita kadai ta mike da kyar ta dau tray din abincin da aka kawo mata zata fitar da shi kar abun nata yayi yawa, don Jiddan ce ma ta kawo mata abincin, kar ta ga kamar jira take ta fitar da tray din, gidan kuma da alama babu me aiki, a hankali ta bude kofar dakin ta fito corridor, walking slowly ta nufi hanyar da zai kai ta main parlor din gidan, sosai gabanta ya fadi jin dariyar Musharraf tun kan ta karasa cikin parlon, ita tama taba ganin yana dariya haka kuwa? Ai sai dai murmushi, zaune yake tare da Jiddah a parlon, giving her a look that can melt heart, ita kuwa Jiddah taki yarda ta kallesa sai danna wayarta kawai take duk da ba waje daya suke zaune ba amma basu da wani nisa da juna, a hankali ya matso da kansa kusa da ita ko me yake ce mata oho, ta ɗan matsa daga wajen ba tare da ta kallesa ba tana ci gaba da danna wayarta tana ɗan murmushi, gaba dayansu babu wanda ya lura da Mayraah, a hankali ta juya zata koma inda ta fito taga MD ya fito daga Parlon Mami, yace "You want something?" Bata yarda ta kallesa ba ta girgiza kai da sauri tace "Aa zan kai kitchen ne" Ya amshi tray din a hannunta, sai ya ga hawaye idonta, shiru yayi yana kallonta, can ya fita parlon ita kuma ta wuce daki da sauri, nan tsakiyar parlon ya ajiye tray din yana kallon Jiddah yace "Take it to the kitchen" Jiddah ta daga kai tana kallonsa, yace "Sai kuma ki bar bakuwa ita kadai a daki?" Jiddah ta ɗan buda manyan idanuwanta tace "Yaya nima fa jiya na zo, am i not also a stranger?" Musharraf dake kallon MD yace "Do we have visitor?" MD yace "Kaje ka tambayi Maminka" Daga haka ya bar parlon, Ya kalli Jiddah yace "Bakuwa Mami tayi ne?" Jiddah ta daga kai ta kallesa a karo na farko tun shigowarsa parlon, kasa daina kallonta yayi baya ko kiftawa, don tun dazu yake fama da ita ta dago kai taki, cikin sanyin muryarta tace "Eh, dazu ta zo, naji Mami na ce mata Mayraah...." Musharraf yace "Oh Mayraah, ta zo kenan, she is my cousin's daughter" Jiddah tace "Eh haka Mami tace min" Yayi kasa da murya yace "Toh kin ci abincin Baby?" Sauke idonta tayi tace "Eh" Yace "Wait for me kar ki shiga ciki pls, bari in je mu gaisa da ita" Daga haka ya mike ya bar parlon ta bi sa da kallo babu ko kiftawa, don bata iya kallonsa sai dai a sace, Musharraf na shiga wajen Maminsa yaga Mayraah bata nan, hakan ya sa ya dawo dakin da take yayi sallama, tana zaune kasan carpet, MD kuma na tsaye jikin kofar yana mata magana ganin Musharraf yayi shiru, komawa gefe yayi ya basa hanya ya shigo, Musharraf na shiga dakin da fara'arsa yace "Amarya ya kike, ashe kin zo gidan mu, i just got to know now, ya kika baro yan Abuja" Ta ki kallonsa da kyar tace "Lafiya" da murmushi yace "Toh you are welcome amarya" Daga haka ya juya ya fita daga dakin, duk yanda Mayraah ta so controlling kanta ta kasa ta fashe da kukan da bata shirya ba wanda kuma bata san dalilinsa ba, MD ya zauna kan kujeran dake dakin yana kallonta yace "What's ur problem Mayraah? Meye na kuka" Girgiza masa kai tayi cikin kuka tace "Sir amma Umma fa tace ka dawo dani gida da Magrib" Yace "Ke ni babanki ne ba Sir ba, don't sir me again" Ta daga kai tana kallonsa hawaye na sauka idonta, Ya ɗan sauke ajiyar zuciya yace "Kamar yanda nake gaya maki yanzu you can see for ur self ya nuna maki he has moved on, to ke meye damuwarki? Beside in ma auren ne kin rigasa ai, don ranan da za ayi bikinki shi za a daura nasa auren, accept this is the best for you Mayraah, i promise you it's the best, ke matar aure ce yanzu" Tace "Ni ka daina ce min matar aure" Ya ɗan buda ido yace "To matar me zance maki" Tana Girgiza masa kai cikin rawan murya tace "Yayana fa ake cewa an aura min, how will i cope with this plss, ta yaya zan iya zama da shi as my husband, isn't it weird? wallahi ina masa kallon wanda muka fito ciki daya ne, all my life a haka muka taso da shi, why all of a sudden zai zama mijina kuma" Kuka take sosai, MD ya ɗan yi murmushi yace "Ba dai wannan Calm gently Dr din ba da na sani? To u are very lucky Mayraah, just our few encounters together in hospital when u were sick na lura shi mutum ne me kirki da saukin kai da sanin ya kamata, bai dauki kansa komai ba, imagine he was also a Dr but he was patient har sai sanda aka basa izinin shiga wajenki a ICU yake shiga, unlike that other one, har number Maheer ina da shi yanzu haka kuma muna magana, i was a bit relieved da naji shi ne mijinki, but i know it will be hard for u kasancewar kun taso gida daya kina masa kallon wanki as you've said, kinga Jiddan nan few years back an so in aureta but i decline don ina mata kallon warce muka fito ciki daya tunda a gidansu na tashi since when i was a toddler, ina gidan aka haifeta ta girma as my lil sis shi sa ni kallon jinina sosai nake mata, but in ur on issue ga yanda situation ya juya at the end, amma i am assuring you u will be proud of this one day one time, Allah ya riga ya rubuto mijinki ne shi din, nothing can change that Mayraah, kiyi hakuri" Ita dai hawaye kawai take tana kallonsa, yace "Don haka ina baki shawaran ki cire duk wani abu dake ranki, ke matar aurece ko tunanin Musharraf kika kawo ranki sai Allah ya tsine maki, nima kawai don babanki ne yasa na zauna nan ina maki magana if not bazan ma fara zama dake ba, kin dai ga shi harkan gabansa ma kawai yake yana jiran ranan aurensa eagerly, ke kuma da naki auren a kai kin zauna kina masa kuka, to kukan me? Kukan kina sonsa har yanzu ko me?" A hankali ta girgiza masa kai, yace "Toh kiyi hakuri and say Alhamdulillah in every situation" Goge idonta tayi a hankali bata ce komai ba, ya ɗan yi murmushi yace "I now see ta inda kika samu first class din da kike daga mana shoulder da shi a hospital, haba an gaya maki first class a nursing science child's play ne" Hade rai tayi tana kallonsa tace "Zaka iya tambayarsa, tun da na fara course din nan every semester da first class nake fita tun ma bai san ni ba, ni ba abinda ya min, and it was my first class that attracted him to me, ko dashing mark baya yi ma student shi in gaya maka" MD yayi er dariya yace "Ko duk jikina kunnuwa ne...." Bai jira me zata ce ba yace "Hope you will take all my advice?" A hankali ta gyada masa kai, yace "Good, if there is anything that bothers you ko a wajen Maheer ne you can get my number cause I will be going back to Canada soon" Hade rai tayi don bata wani son ana danganta ta da Maheer har ranta, ita ce masa tayi ta amince zasu zauna da Maheer as husband and wife ne, Kauda zancen tayi tana kallonsa tace "Kai yaushe zaka yi auren" Gyara zama yayi, sai kuma yayi murmushi yace "Tunda kanena da daughter na sun yi auren ai shikenan, Musharraf, Jiddah, and you" Tace "Ni naka auren nake tambaya" Yace "Babu budurwa ae" Ta ɗan buda ido tace "To in maka budurwa?" Yace "In dai bata da rashin kunya da rainin wayo kamar ki" Bata san sanda tayi dariya ba tace "Ai ko i have a new girlfriend for you" Yace "Really?" Tana gyada kai tana murmushi tace "Yea, Maleeha is her name" Yana gyada kai yace "That's sweet.... Maleeha" Da sauri ta jawo wayarta tace "Bari in kirata" Nan da nan ta shiga contact dinta ta nemo number Maleeha ta kira, tasan bata da wnn number nata, yana fara ring Maleeha ta daga cikin calm voice dinta tayi sallama, Mayraah ta amsa tace "Maleeha" Daga daya bangaren Maleeha tace "Mayraah? What happened to ur line pls? Nayi ta kiranki bana samun ki" Mayraah na murmushi tace "Did you ask Yaya Usman about me?" Tayi er dariya tace "Haba ai bama communicating ne da shi shiyasa, but naji yayana yace min ai kun koma Abuja" Mayraah tace "Ehh haka ne, kina kano ne?" Maleeha tace "Wallahi mun zo bikin cousin sister dinmu ne muna kd" Mayraah ta zaro ido tana kallon MD dake sauraron conversation dinsu, tace "Da gaske, wani anguwa?" Maleeha tace "Unguwar Dosa" Mayraah tace "Kai haba nima fa ina kd, bari inji wani anguwa nake i will get back to you" Daga haka ta katse wayar tana kallon MD tana murmushi, ya gyada kai yace "She's got a cute voice" Mayraah tayi dariya tace "Don Allah ina ne unguwan Dosa?" Yace "Nan anguwan take" Mayraah tace "Lahhh da gaske" Sai kuma ta mike ta dau Hijab dinta tace "To don Allah mu je sai in kirata ta turo mana address din gidan da take" Buda baki MD yayi yana kallonta yace "Kamar fa baki da hankali" Tsayawa tayi tana kallonsa, yace "Da auren naki zaki fita gantali? Ko dai kin zata auren wasa aka maki" Nan da nan mood dinta ya canza, yace "Kirata ta turo maki address din, i will get her for you tomorrow kafin in maida ke Malali" Komawa tayi ta zauna a sanyaye, ya ciro wayarsa yace "Give me her number" Sai a sannan ta ɗan yi murmushi tace "Sai ma ka ganta yaya, soo pretty and cute, idonta ma fa ba irin namu bane wllhi" Shi dai kawai yayi murmushi, nan ta fara karanto masa number yana dialing a wayarsa, tace "Kaga kawai sai ka koma Canada da ita...."

*To fatee shanono sai a dau na annabawa, Allah bai kaddara za a canada da MD ba, Parrot ta samar maki wani MDn a kano*😂😂😂😂

100
Mayraah taji ta samu relieve sosai bayan fitar MD daga dakin, ta mike ta koma saman gadon dakin tana danna wayarta, number Usman tayi dialing yana fara ringing ya daga a hankali tace "Yaya ina yini" Yace "Lafiya lau Mimi, how are you?" Tace "I am fine" Shiru tayi, sai kuma tace "Kun je gida lafiya yaya?" Usman yace "Sai yanzu kika tuna ko mun je lafiya ko bamu je lafiya ba Mimi" Ta ɗan buda ido, a nan tayi realizing ashe tun jiya ai ya kamata ta kirasa taji ya hanya, sai ta langwabar da kai cikin sanyin murya tace "To na manta ne" Yace "Good, ni ai ban tafi jiya ba na tsaya yin wani abun ne, i left for Abuja today in the evening...." Shiru tayi jin abinda yace, lokaci daya tace "To shi yaya fa?" Usman yace "I don't know, I can't reach him..." Da mamaki tace "Baka tambayi Ammi ba?" Yace "Ke me ya hanaki tambayarta?" Bata sake cewa komai ba, sai kuma a hankali tace "Sai anjima" Yace "Ohk Mimi" Daga haka ta katse wayar, kwanciya tayi bayan ta ajiye wayar, cikin mintuna kadan bacci ya dauketa, ko awa daya bata yi ba tana baccin ta farka kamar warce aka tada, ta mike zaune sai kuma ta jawo wayarta tana kallon agogo taga karfe goma da yan mintuna, number Ammi tayi dialing, Ammi na dagawa tace "Baki yi bacci ba dota?" Mayraah ta sauke idonta cikin sanyin murya ta gaisheta, Ammi tace "Lafiya lau, ya gida?" Tace "Alhamdulillah" Ammi tace "Ya su Hajiya?" Mayraah tace "Lafiya lau.... Ammi yaya ya dawo gida ne?" Ammi tace "Eh ya dawo dazu" Rasa abinda zata ce tayi don ita ba Usman take tambaya ba, can dai tayi karfin halin cewa "Ya Maheer?" Ammi tace "Ohk jiya shi ya dawo, you want to speak to him?" Zaro ido Mayraah tayi tana girgiza kai da sauri tace "Aa dama kawai na manta ban kira bane in ji" Ammi tace "Ohk, they are back Mimi" Da sauri tace "To sai da safe Ammi" Ammi tace "Alright dear, kiyi addu'a kafin kiyi bacci...." A hankali Mayraah tace "Toh" Daga haka ta katse wayar ta koma ta kwanta, bayan ta kwanta da kamar minti sha biyar sai ga Jiddah ta shigo dakin, Mayraah tayi kasa da idonta da sauri kamar me bacci, Jiddah ta karaso daya side din gadon ta ajiye wayarta ta cire Hijab din jikinta ta linke, kayan baccinta ta dauko sannan ta shiga bandaki, Mayraah dai bata dago idanuwanta ba balle asan ba bacci take ba, Jiddah na shiga banɗaki wayarta dake gefen gado ya fara ring, sai a sannan Mayraah ta daga kai tana kallon wayar, Yaya M... ta gani jikin screen din ta dinga kallon digit din ganin na Musharraf ne, wanda yayi blocking dinta, a hankali ta mayar da kanta daya gefen, bayan wani lokaci Jiddah ta fito tayi shirin bacci ta karaso ta zauna side din gadon ta dau wayarta, duk da kiran nasa da ta gani sai bata kirasa ba, tana kwanciya sai gashi ya kara kira ta daga.... har kusan karfe sha biyu waya suke da Musharraf, Mayraah dake jin duk conversation dinsu kawai ta mike zaune daga karshe cause the phone call is disturbing her ears kuma bacci take so tayi, sauka tayi daga kan gadon, ta nufi kofa ta fita daga dakin, Jiddah ta bi ta da kallo don ta zata bacci take, parlor Mayraah ta tafi duk da babu wani haske ta karasa ta zauna 3 sitter tana kallon direction din da hasken da ya ɗan haska parlon ke fitowa, Mikewa yayi bayan ya ajiye textbook din hannunsa ya shigo parlon ya kunna wuta yana kallonta, sunkuyar da kanta tayi, yace "Ba ki yi bacci ba?" Tayi shiru bata ce komai ba, yace "Kilan ta dameki da waya ko?" Gyada masa kai kawai tayi, yace "Mu je ki kwanta a wani dakin" Ta mike ta bi bayansa tana tafiya a hankali, ya kai ta har wani daki ya bude mata kofar dakin ya kunna fitila yace "Good night" Shiga cikin dakin tayi tace "Nagode" Ya kullo kofar ya bar wajen, bin dakin ta dinga yi da kallo wanda da alama nasa ne, ta karasa ciki sae da ta fara rage Ac din dakin sannan ta kashe wutan ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa. Washegari da safe Mayraah na gama breakfast ta dinga baza idon inda zata ga MD ya maida ta gida don ita har ta shirya, ashe jiya da ya koma can gidan kakaninta da magrib sae da Hajiya Ramatu ta basa kayanta a karamin jaka ya tafi mata da shi, da safe tana wanka dama Mami ta kawo mata jakan har dakin da take, Allah Allah kawai take ta bar gidan ba tare da ta sake haduwa da Musharraf ba, don tun da gari ya waye bata gansa ba bata kuma fatan ta gansa. ita babban takaicinta da tuno yanda yayi blocking dinta kawai, wato shi yana ma da babban dalilinsa na blocking dinta at once, sai kuma yanda yayi ta avoiding dinta farkon zuwansu Kaduna gidan Grandparent dinta yaki barin su hadu balle tayi masa magana, kasa daurewa Mayraah tayi ta mike ta tafi bangaren Mami, Mami na kallonta tace "Kinyi breakfast

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login