Showing 360001 words to 363000 words out of 452169 words
Chapter 121 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
Mayraah, Ammi ta kalleta tace "Mimi kun yi sallama da yayan naki" Ɗan murmushi tayi tace "Eh Ammi" Mikewa tayi ta amshi hand luggage dinsa ta nufi kofa ta fita, tana tsaye a parking space din taki yarda ta kalli Haseenah dake zaune back seat, Bilkisu kuma tana jikin motar a tsaye, Maheer da Ammi na isowa parking space din Mayraah ta sa hand luggage dinsa a booth, ta ɗan kallesa tace "Allah ya kiyaye hanya" Yace "Ameen" Ammi na kallon Bilkisu tace "To ki shiga bayan motar ke ma, zai fara kai ku gidan ne, kafin driver ya kai sa Airport" Bilkisu tace "To Hajiya" Bude back seat tayi ta shiga ta zauna gefen Haseenah, Juyawa Mayraah tayi ta bar wajen, Maheer ya bi ta da kallo, har ta shiga cikin gidan, zagawa yayi kamar zai shiga front seat sai kuma ya dawo yace "I think ban dauko power bank dina ba" Daga haka ya bar wajen da sauri ya nufi entrance din shiga gidan, direct sama ya tafi zuwa dakin Mayraah, ya ganta zaune gefen gado ta daura fuskarta kan pillow, tana jin an bude kofa ta dago kanta da sauri tana goge hawayen idonta, karasawa yayi ya zauna kusa da ita da damuwa yace "Mimi" ta sauke kanta wasu hawayen na zuba idonta, rungumeta yayi jikinsa, kamar jira take ta fashe da kuka, kasa ce mata komai yayi yana jin kukan nata har cikin ransa, cikin sanyin murya yace "I am spending just 4 weeks in Lagos Mimi, 4 weeks is just like tomorrow" Ita dai gyada masa kai kawai tayi hawaye na zuba idonta, a hankali yace "I will miss you so much" Ya dago kanta yana goge mata hawayen fuskarta da hannunsa, ita dai kallonsa kawai take, yayi kasa da murya yace "Ko dai mu tafi tare ne?" lumshe ido yayi giving her a deep snog..... Tun da Maheer ya tafi Mayraah ta fara kirga kwanakin da yace mata zai yi a Lagos, ita kanta ta kasa fahimtar irin kewarsa da take duk da a rana ya kan kira ta sau uku, sai dai sbda yanayin aiki basa dadewa a wayar, gaba daya gani take kamar kwanakin basa gudu, duk da Ammi tayi vowing ko inda Haseenah take bazata je ba amma saboda zuciyar musulunci kasa yin hakan tayi, don kuwa duk bayan kwana uku ta kan bi Bilkisu su je gidan da aka kama mata ta dubata, Mayraah bata taɓa cewa zata je gidan ba, Ammi ma bata taɓa ce mata ta shirya su je ba, daga karshe Ammi kawai ce ma Bilkisu tayi ta debi kayanta a akwati ta koma gidan gaba daya ganin yanda Haseenah bata iya yin komai sbda nauyin ciki, kayan babies kuwa babu wanda Ammi bata siya ba, har abubuwan da ake bukata na haihuwa ta siya..... Mayraah na zaune parlorn Ammi bayan isha tana kallo, Ammi kuma tana can bangaren Abba, wajen karfe tara Ammi ta dawo bangarenta, ganin fruits din da ta bar ma Mayraah bata sha ba tace "Me yasa baki sha fruits din ba Mimi?" Mayraah tace "Na koshi ne Ammi" Ammi ta zauna tace "Dazu wai hiran me Usman ke maki a parlor daga ganina yayi shiru?" Mayraah tayi er dariya tace "Ammi wannan ai secret ne between us" Murmushi Ammi tayi tace "To in ke da shi baku gaya min ba ai Abbanku ya gaya min yanzu" Dariya Mayraah tayi tace "To me Abba yace maki?" Ammi tace "Oho" Murmushi kawai Mayraah ke yi ta kuma ki gaya ma Ammi maganar da suka yi da Usman. Washegari friday Bilkisu ta bugo ma Ammi waya kan cewar Haseenah bata da lafiya tun jiya, Ammi tace "Ko dai nakuda take?" Bilkisu tace "Ina kyautata zaton haka" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Toh zan taho yanzu, in haihuwan ne sai mu tafi asibiti" Babu bata lokaci Ammi ta sa driver ya kai ta gidan da Haseenah take, ko da taje taga ba labor bane amma ganin condition dinta haka ta sa driver ya maido su gida gaba daya..... Mayraah da Ammi suna kitchen ranan lahadi da yamma, Mayraah na assisting din Ammi dake ma Abba girki, Bilkisu ta shigo kitchen din tana kallon Ammi tace "Hajiya ina jin fa nakuda take" Ammi ta fito daga kitchen din ta karasa kusa da Haseenah dake duke a parlor tana yarfe hannu don azaba, Ammi ta kamata tana kallon bilkisu tace "Maza ki kira Driver mu tafi asibiti" Mayraah dai na tsaye bakin kofar kitchen tana kallonsu, da azaba yayi ma Haseenah yawo bata san lokacin da ta kwala wani ƙara ba ta kankame Ammi, Bilkisu ta tafi dakinta da sauri ta dauko wayarta don kiran driver, Ammi dai sai sannu take ma Haseenah, dai dai nan Maheer ya shigo parlon, da Mayraah ya fara hada ido a parlon, amma ganin condition din da Haseenah ke ciki kawai sai ya nufesu, Ammi ta kallesa tace "Ka dauko Makullin motarka mu tafi asibiti labor ne" Dakinsa ya nufa da sauri, Mayraah ta bi sa da kallo cikin few seconds ya dawo parlon da car key dinsa ya fita don starting motarsa, Ammi ta daga Haseenah da taimakon Bilkisu suka tafi parking space da ita, Ammi na kallon Bilkisu bayan sun taimaka ma Haseenah ta shiga mota tace "Ki dauko akwatin kayan haihuwan nata" Babu bata lokaci Bilkisu taje ta dauko sannan suka dau hanyar asibiti, Suna isa asibiti ko 30 mins ba ayi ba Haseenah ta haihu.
114
Maheer na tsaye bayan isha yana kallon yaran dake kwance kan gadon jarirai a wani ward, it took some times kafin aka samu yaran suka yi kuka bayan an haifo su, kallon babies din yake daya bayan daya baya ko kiftawa, sai ga wata nurse ta shigo tare da Ammi dake biye da ita, Ammi ta karasa kusa da gadon jariran, ta fi minti daya tana kallon yaran, tun da aka haifosu kusan awa daya kenan sai yanzu aka bari Ammi ta shigo inda suke bayan likitoci sun tabbatar they are fine, ita duk tunaninta ma ko sun mutu ne jin shirun yayi yawa, Ammi ta kalli Maheer sai kuma ta sake kallon yaran sannan ta duka ta dau daya daga jariran tana gyara baby blanket da aka yi wrapping dinsa da shi tana murmushi tace "Maa sha Allah, Allah ubangiji ya raya mana ku bisa tafarkin addinin musulunci, Allah yayi maku albarka" Mika ma Maheer yaron tayi tana kallonsa har sannan murmushin fuskarta bai gushe ba, sauke idonsa yayi ya amshi yaron daga hannunta, Ammi ta duka ta dau daya jaririn shi ma ta masa addu'a.... Haseenah na kwance ita kadai a ward din da aka kwantar da ita hawaye na sauka idonta, ita ma ba a dade da kawo ta ward din ba don tun da ta haihu ta shiga unconscious state, bayan ta dawo hayyacinta aka maido ta ward, sai kuma taga shiru shiru ba a shigo mata da babynta ba gashi Ammi dake kusa da ita bata ce mata komai akan babyn ba, sai sannu kawai take mata, hakan yasa ta fara tunanin ko ya mutu ne yaron, daga karshe ma Ammi barin ward din tayi wannan yasa ta dinga kuka ita kadai babu me rarrashinta. Bude kofar ward din da aka yi yasa ta juya da sauri, Ammi ta shigo rike da one of the baby, ta karasa har kusa da Haseenah dake kallonsu, Ammi ta kwantar mata da shi a gefenta tana kallonta tace "Sannu Haseenah, Allah ubangiji ya raya, ke kuma Allah ya baki lafiya" Haseenah dai goge hawayen idonta kawai take tana kallon yaron, dai dai nan Maheer ya shigo ward din ta daga kai tana kallon second baby dake hannunsa, ya karasa ciki ya kwantar da shi kusa da dan uwansa, Haseenah ta dinga kallon Babies din that are so identical, sai kuma ta ɗaga kai ta kalli Maheer dake kallonsu shi ma, a takaice yace mata "How are you feeling?" Ta gyada masa kai a hankali tace "I am okay" Abba ne ya shigo ward din da sallama tare da Usman, ko wannensu ya dau each of the babies Abba yayi ma Haseenah barka tare da addu'an samun lafiya..... Bayan tafiyar Abba da Usman da kusan minti sha biyar Bilkisu ta shigo rike da basket din kayan shayi ta ajiye tana kallon kyawawan jariran tana washe baki tace "Alhamdulillah, Allah ubangiji ya raya su, yayi ma rayuwarsu albarka, ke kuma Allah ya baki lafiyar shayar da su" Ammi tace "Ameen nayi ta kiranki ince ki taho mata da kayan sa wa baki dau waya ba" Bilkisu tace "Wallahi Hajiya wayar na daki ai ko dakin ma ban shiga ba ina tafasa ruwan zafi na dauko kayan shayin muka juyo kawai da dreba" Ammi tace "Mayraah fa?" Bilksu tace "Naje har sama nayi mata sallama don in sanar mata da haihuwar amma kamar ina jin tayi bacci ne" Ammi ta hada ma Haseenah shayi me kauri da kanta sannan ta mika mata, after some minutes Ammi ta mike tana kallon Maheer tace "Zaka kwana a nan ko?" Maheer yace "To put an eyes on the babies" Ammi tace "Toh shikenan zan dawo da asuba in sha Allah..." Daga haka ta kalli Bilkisu tace "Mu je Bilkisu" Bilkisu tace "To Hajiya" Daga haka suka nufi kofa suka fita, Sai a sannan Haseenah ta daga kai tana kallon Maheer, a hankali muryarta na rawa tace "Don girman Allah Maheer kayi hakuri ka yafe min for the sake of this babies" Maheer ya dakatar da ita a takaice yace "Look kar ki dameni... Concentrate on ur health ki bar ni da wnn maganar, i am not interested" Shiru tayi tana kallonsa bata sake cewa komai ba.... Ammi na komawa gida tayi knocking kofar dakin Mayraah sannan ta bude ta shiga ciki, kwance ta sameta kan gado, ganin bacci take Ammi ta juya ta fita. Wajen karfe goma da rabi Maheer ya fito daga ward din da Haseenah take bayan tayi bacci ita da yan biyunta, reception ya tafi ya zauna yayi dialing number Mayraah, har ya gama ringing bata daga ba, ya sake kiranta nan ma bata daga ba, mikewa yayi ya koma ward din da ya fito ya zauna. Washegari da asuba Mayraah na zaune dakin Ammi bayan ta gaisheta Ammi ke sanar mata Haseenah ta haihu, Mayraah tace "Maa sha Allah, Allah ya raya baby, ita kuma Allah ya bata lafiya" Ammi tace "Ameen" Mayraah ta daga kai ganin kallonta Ammi take tace "Ammi Baby boy ne ko Girl?" Ammi tace "Yan biyu ne maza" Mayraah ta sauke kanta tace "Maa sha Allah, Allah ya raya mana su, ya albarkace su" Ammi tace "Ameen" Mikewa Ammi tayi tace "Bari in je in ga ko Bilkisu ta karasa abinda take yi a kitchen, zuwa karfe bakwai za mu je asibitin, ki je ki shirya" a hankali Mayraah tace "Toh" Ammi na fita daga dakin Mayraah ta mike ta bi bayanta ta koma dakinta. Kamar yanda Ammi tace karfe bakwai ta shirya bayan sun gama hada ma Haseenah breakfast da za a kai asibiti, dakin Mayraah ta shigo ganinta kwance tace "Baki shirya bane Mimi" Mayraah ta girgiza mata kai a hankali tace "Cikina ke ciwo Ammi" Ammi tace "Subhanallahi, tun yaushe?" Mayraah tace "Da daddare, amma da sauki" Ammi tace "To kin sha magani?" Ta girgiza kai tace "Aa zan sha idan nayi breakfast" Ammi tace "To sauko ki hada shayin ki sha, sai ki hadiyi magani ki kwanta" Mayraah ta sauko daga kan gadon a hankali suka sauka downstairs da Ammi, tana zaune parlor har Ammi da Bilkisu suka tafi asibiti wajen karfe bakwai da yan mintuna. Karfe daya da rabi Mama Ladi ta iso gidan bayan Ammi ta sanar mata da haihuwan, sama ta tafi da sabon akwatinta, jin gidan tsit ta tafi bangaren Ammi nan ma ba kowa, ta dawo corridor tace "Ikon Allah, to dama babu kowa gidan aka sa na biyo hanya ko kumallon kirki ban yi ba, tarewa pamilyn suka tafi suka yi a asibitin kenan saboda Hasinu ta haihu" Dakin da take sauka ta kai akwatinta sannan ta fito tace "Toh ni yanzu ya zan yi da yunwan cikina ni Ladiyo" Karasawa tayi ta murda kofar dakin Mayraah, Mayraah dake zaune kan darduma ta daga kai ganin Mama Ladi tace "Sannu da zuwa Mama" Mama Ladi tace "Au da kina ji na kika yi shiru Mera?" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Wallahi ban ji ba Mama, sallah ma nake, yanzu na idar...." Mama Ladi tace "Toh ina yan gidan gaba daya?" Mayraah tace "Suna asibiti" Mama Ladi tace "Kaji wani taya bera bari, ita Hasinun matar kirki ce da za su je asibiti su tare saboda ita, banda ma Pamilyn namu akwai zuciyar musulunci in wasu pamilyn ne yaushe ma za a kalleta, ba fa aure tsakaninta da Mashir din amma ki ji yanda ake hidima da ita, Allah dai yasa tagwayen nasa ne" Mayraah dai kallonta kawai take bata ce komai, Mama Ladi tace "Al-qur'an bazan je asibiti ba inyi ta warin izal, zamana zan yi a nan har ranan da za a sallamesu su, tashi ki samar min abinda zan ci" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta linke darduman da tayi sallah ta ajiye, Mama Ladi tace "Ba dai ki da rabon kishi da er iskar, don duk me bin boka da malamai ɗan iska ne, Maheer mijinki ne ke kadai ba wata shegiya" Mayraah ta sunkuyar da kanta ta fita daga dakin ta sauka downstairs, tun safe she was just moody and weak ta rasa dalili don ko breakfast din kirki ta kasa yi, amma words din Mama Ladi na karshe yasa taji strength dinta ya dawo, she felt relieved with those words, sai dai ita kanta bata san me yasa taji hakan a ranta ba. Mama Ladi na biye da ita suka sauka downstairs, dai dai nan Bilkisu ta shigo parlon rike da basket din abinci da wasu kaya a hannunta, Mayraah na ganin haka ta shige kitchen bata tsaya a parlon ba, Mama Ladi na kallon Bilkisu tace "Daga asibitin kike kema" Bilkisu tace "Eh Mama, an ma sallame mu, sannu da zuwa Mama" Sai ga Ammi ta shigo parlon rike da baby daya, Haseenah na biye da ita, sannan Maheer dake rike da second twin din shi ma ya shigo parlon, Mama Ladi ta nufi Ammi da sauri tana kallon jaririn hannunta tace "Barka barka, ashe dai banda rabon wahala don yanzu nake shirin zan je asibitin sai ga ku, sauka ta kenan wllhi ko zama ban yi ba" Sannu da zuwa Ammi tayi mata tana mika mata jaririn, Mama Ladi ta rike haba tace "Allah mai iko, ki ji ɗan kamar uban yayi kaki, ko ke baki ga haka ba Ammi??" Ammi dai mika mata yaron hannunta kawai take, Mama Ladi ta amshesa tana kare masa kallo kawai ta saki kabbara tace "Wallahi Kamar Mashir sanda kika haife sa, iko sai Allah" Da sauri ta karasa gun dayan Babyn dake hannun Maheer tana kallonsa tace "Yau ni naga abun mamaki, yo wannan ai babu zancen wani gwaje gwaje ko makaho ya shafa fuskar yaran nan yasan na Mashir ne, kawai sai dai muyi fatan Allah ubangiji ya raya mana su bisa imani, fargaban mu daya nonon da zata ce zata basu, kun dai san babu abinda yaro bai dauka a nonon uwarsa, don haka hakuri kawai Mashir zai yi ya tanadi kudin madaran gwangwani don mu ba sai ta shayar mana da yaran ba mun yafe" Dakin da Ammi ta sa Bilkisu ta gyara aka shimfida zanin gado ta nuna ma Haseenah, Haseenah dake kallon Mama Ladi a sanyaye, ta juya tana tafiya a hankali ta karasa cikin dakin da aka gyara mata. Duk Wannan abun da ake Mayraah na jin su a kitchen don kofar kitchen din a bude yake, ta gama zuba ma Mama Ladi abinci ta fito parlon, dai dai sanda Maheer ya sauko downstairs bayan ya haura sama zuwa dakinta bai ganta a ciki ba, bata yarda ta kalli direction dinsa ba ta nufi dakin da take jin muryar Mama Ladi fuskarta a daure, ta shiga da sallama ta ajiye mata abincin hannunta, a takaice tayi ma Haseenah barka without looking at her in the eyes, Mama Ladi ta mika mata one of the twin tace "Amsa yaji duminki ku fara sabawa tun yanzu" Mayraah ta amshi cute baby din wanda truly replica din ubansa ne, kallonsa kawai take bata ko kiftawa, Mama Ladi na washe baki ta amshesa ta kwantar sannan ta dauko dayan ta mika ma Mayraah shi ma, Mayraah ta karɓe sa shima tana kallonsa don ba a iya banbanta sa da ɗan uwansa banda shaidan da aka yi using a asibiti to differentiate them, Mama Ladi tace "To gwara tun yanzu ki fara sabawa da su, su ma su saba da duminki, don da kyar in ba ke zaki rike ma Mashir su ba tunda babu aure dai tsakaninsa da tambadaddiyar uwarsu, saki uku yayi mata" Daga kai Haseenah tayi tana kallon Mama Ladi jin abinda take cewa, sai kuma ta kalli Mayraah, har a sannan Haseenah bata san da auren Maheer da Mayraah ba, to tana fitowa prison kwana daya kacal tayi gidan Abba washegari aka kama mata gida aka kai ta can, duk iya bugan cikin da ta ke ma Bilkisu dake zuwa wajenta don ta samun hint din abubuwan dake faruwa a family din Bilkisu taki bata hadin kai, da alama kuma Ammi ce ta kwabeta, hatta Badiyyah sai da ta tambayi Bilkisu inda take, amma Bilkisu tace mata bata ma san ta ba, don haka Haseenah knows nothing na gidan, har tafiyar da Maheer yayi ma bata sani ba duk da babu ranan da zai wuce da bazata tura masa text na ban hakuri ba amma baya responding, kira kuma dama ya sa ta a busy.... Mayraah dai bata ce ma Mama Ladi komai ba, after few more minutes ta mika mata yaron tace "Zan je in karasa aikin da nake yi Mama" Daga haka ta fita daga