Mayrah

Chapter 120 of 152

tayi, ko da taje gaida Abba a bangarensa bata dade ba on like before ta dawo bangaren Ammi ta zauna, duk Ammi na lura da ita abun ma dariya yake bata, tana gama cin abincin ta mike zata fita da plate din Ammi tace "Ya isheki?" Gyada mata kai tayi, sai ga Bilkisu ta shigo da sallama, plate din ta amsa hannun Mayraah sannan ta dau warmers din abincin ta fita. Karfe takwas da yan mintuna Abba na zaune parlon parlon Ammi, sai Haseenah dake kan carpet ta sunkuyar da kanta, daga kusa da Ammi Mayraah ce zaune sai Maheer da Usman da su ma duk suna parlon, Ammi dai fuskarta babu yabo babu fallasa a parlon don ko kallon Haseenah taki yi, da Haseenar ma ta gaisheta a takaice ta amsa mata babu yabo babu fallasa without looking at her, da ta tuna irin wahalan da Mayraah ta sha sai taji they have nothing to do with Haseenah, cikin jikinta ma kawai fata take kar ya kasance na Maheer, don sam bata son su hada zuri'a da irin Haseenah, duk kawaicinta da hakurinta tunda har ta kasa yi ma Haseenah wnn kawaicin to ba karamin kullatar ta tayi ba a ranta, Abba yayi gyaran murya cikin nutsuwa ya fara magana yace "Da farko dai nasa an daukaka karan wannan yarinya ne ba don komai ba sai don albarkacin juna biyun da take dauke da shi, sannan Allah ma muna masa laifi mu nemi gafararsa ya yafe mana, ko ma ba don haka ba iyayenta mutanen kirki ne, duk da suna da damar daukan lauya da zai kareta tun farkon shari'a amma basu yi hakan ba, they neva supported her deed, sai ta dawo kamar mara galihu a lokacin, anyway all that aside, ban sa a daukaka karar nan don yarinyar ta dawo cikin rayuwarmu ba, Aa ina son mu yi considering condition dinta, sannan Maheer is suppose to take her responsibilities har zuwa sanda Allah zai sauketa lafiya, in ta yarda zata shayar da yaron it's left for her, idan kuma bazata shayar ba shi ma it's okay" Ammi dake ta kallon Abba zuciyarta na tafarfasa tace "So yanzu me kake nufin zai faru?" Abba ya kalleta, shi dai Maheer kansa na sunkuye bai taba jin zai bijire ma umarnin parent dinsa ba amma wnn umarnin kam baya jin zai iya because he have nothing to do with Haseenah, ko ganinta ma bai son yi har cikin ransa yaji yana mugun tsanarta, Abba ya katse masa tunaninsa ta hanyar cewa "Abinda zai faru, kawai wajen da zata zauna har zuwa sanda zata haihu Maheer zai samar mata a cikin garin nan, ko da self contain ne, sannan zai dau duk wani responsibilities nata tun daga ciyarwa har zuwa magani da abubuwan bukatan yau da kullum" Ita dai Haseenah kanta na duke hawaye na ta sauka idonta, A takaice Ammi tace "Na ga dai duk wannan responsibilities din da kake fadi za a iya mata a ko ina ba lallai sai an samar mata waje a Abuja ba, don't she have relatives? Ta tafi wajensu mana, sai lallai tana nan ne za ayi taking responsibilities dinta" Abba dai kallonta kawai yake, Haseenah ta fashe da kuka muryarta na rawa tace "Don girman Allah Ammi kiyi hakuri ku yafe min, wallahi ban san inda zan je ba kuma daga nan, Mum dita ta koreni kuma ta hanani zuwa gun yan uwanta gaba dayan su, dangin babana duk yan Nijar ne, bayana ciwo yake min bazan iya zaman motar zuwa can ba wllh, don Allah ku rufa min asiri ku tausaya min..." Tana kai wa nan ta fashe da matsanancin kuka, Abba na kallon Maheer yace "Get her a self contain apartment, zan tura maka kudin" Abba na kai wa nan ya mike, Ammi ta bi sa da wani irin kallo, har ya kusa kofa ya sake juyowa yace "Kafin a samu gidan, ka biya mata hotel ko na 3 days ne ta zauna a can, so in za ku tafi gida sai ku tafi tare da ita ka samar mata hotel a hanya ka ajiyeta" Bude kofar parlon Abba yayi ya fita, Ammi da ranta yayi mugun baci ta mike ta wuce dakinta, Sai a sannan Mayraah da gaba daya mood dinta ya canza ta dago kanta a hankali sannan ta mike ta nufi kofa ta fice daga parlon Maheer ya bi ta da kallo, Usman ya mike shi ma ya fita daga parlon, Haseenah na kuka ta hade hannunta biyu tana kallon Maheer cikin rawan murya tace "Don girman Allah ka yafe min Maheer, wallahi nayi nadamar duk abinda na aikata, son zuciya ne ya kai ni ga aikata abubuwan da nayi, ka dubi girman Allah in ci albarkacin cikinka da nake dauke da shi ka yafe min ko zan samu sukuni a rayuwata..." Kuka take yi sosai kamar ranta zai fita, Maheer da ko kallonta bai yi ba ya mike ya wuce dakin Ammi, Ammi na zaune gefen gadon ranta a bace, Maheer ya zauna kan kujeran dakin a hankali yace "Ammi this time around i am sorry zan yi abinda ban taba yi ba a rayuwata, which is ignoring Abba's order, gaskiya bazan iya yin duk abubuwan nan da Abba ya lissafa ba don i can't withstand the sight of her" Ammi dake kallonsa ta kwantar da murya tace "Hakuri zaka yi kawai Maheer, yanzu yana ganin ka kiyi cewa zai yi ni ce na zugaka barin yanda yaga nayi reacting a parlon, don haka kawai kayi hakuri kayi abinda yace, kai din me biyayya ne na sani, kuma baza ka taɓa tabewa ba, ba dai nan da sati shidda bane zata haihu, Allah ya kai mu lokacin, in ta haihu sai ayi DNa test din da aka ce" Shi dai Maheer bai ce komai ba amma sam ransa bai so haka ba, wani mugun tsanar Haseenah yake ji har cikin ransa, Ammi ta katse masa tunanin da yake tace "Dare nayi baza ku tafi gida ba?" Yayi kasa da murya yace "We will be spending the night here" Yayi hakan ne don baya jin zai iya daukan Haseenah a motarsa, Ammi tayi shiru tana kallonsa, can tace "Tsoron yarinyar nan fa nake ji Maheer, bamu san da wani kulalliyar ta zo ba kuma, don duk wanda zai iya sa ma mutum guba a abinci yaci don ya kashesa to babu abinda bazai iya aikatawa ba, sam zuciyarta babu alkhairi a cikinsa, gwara dai a kai ta can hotel din" Maheer yace "Babu abinda zai faru in sha Allah Ammi... Gobe da safe idan muka fita zan kama mata hotel din sai ta tafi can" Ammi tace "Toh gaskiya sai dai a bude mata Chalet taje can ta kwana, don ni hankalina bai kwanta da ita ba" Maheer bai sake cewa komai a dakin ba, ita ma Ammi tayi shiru, da ta tuna irin wahalar da Mayraah ta sha a hospital sai taji wani sabon tsanar Haseenah a ranta, mikewa Maheer yayi daga karsh ya nufi kofa, Ammi ta bi sa da kallo har ya fita ya kulle mata kofa, bai ga Haseenah a parlon ba alamar ta sauka parlon downstairs, walking slowly ya nufi dakin Mayraah, a hankali ya bude kofar dakin ya ganta kwance kan gado, ya shiga ciki ya kulle kofar gently sannan ya karasa kusa da ita ya zauna yana kallonta, ita dai bata yarda ta kallesa ba, ya kamo hannunta yace "Are you okay?" Shiru tayi bata ce komai ba, Yace "Mimi" Ta daga manyan idanuwanta ta kallesa suka hada ido, sosai gabanta ya fadi don har ta mance rabon da ta hada ido da shi, Ya daura forehead dinsa kan nata as if counting his words yace "Should we spend the night here or we should go home?" Kokarin mikewa zaune take hakan yasa ya dagota ta sauke kafafuwanta daga kan gadon tace "I want to take my bath" Ya bi ta da kallo har ta tashi tsaye ta nufi bandaki, tana shiga ta kulle kofar ta jingina da bango ta fashe da kuka a hankali, wanda ita kanta bata san dalilin kukan ba, Maheer ya fi minti goma zaune dakin kafin ya mike tsaye da kyar ya fita daga dakin ya sauka downstairs, Bilkisu ce tsaye kan Haseenah bayan ta bata sakon Ammi kan cewar ta je Chalet ta kwanta, Bilkisu ta kara da cewa "Kinsan duk anyi occupying dakunan nan, zaki fi sakewa a can bangaren idan kin je" Cikin sanyin murya Haseenah tace "Toh, amma bayana ya rike bazan iya tashi yanzu ba sai zuwa anjima, kafafuwana ma sun min nauyi sabda benen da na hau, ki bani makullin idan naji dama dama sai in je can" Bilkisu tace "Toh" Mika mata makullin tayi, Maheer da ko kallon inda suke bai yi ba ya wuce dakinsa. Wajen karfe goma Mayraah ta sauko kasa sanye da hijab har kasa don kayan bacci ne jikinta, Bilkisu na zaune parlon har sannan tana jiran fitan Haseenah sannan ta kulle kofa kamar yanda Ammi ta umarceta, Lkci daya kamshin Mayraah ya zagaye parlon bata kalli direction dinsu ba ta wuce kitchen, Ta shiga kitchen ba dadewa Maheer ya fito daga dakinsa, bin parlon ya dinga yi da kallo as if trying to figure out something, can ya nufi kitchen Haseenah dake sauke numfashi a hankali ta bi sa da kallo, Har sannan bata san da auren Mayraah da Maheer ba, Mayraah ta juya jin an bude kofar kitchen din, ganin shi ne ta maida dubanta kan abinda take yi, ya karasa har bayanta ya tsaya, leaning against her, zuciyarta ya fara bugawa da sauri, as if whispering yace "Har da ni shayin?" Kai ta gyada masa da sauri don tsoro ma take kar wani ya shigo ya gansu a haka, still a hankali yace "To a kawo min nawa daki idan an gama" nan ma kai ta gyada masa, ya juya ya fita daga kitchen din, wani ajiyar zuciya ta sauke jin kafafuwanta sun mata nauyi ta juya ta jingina jikin cabinet din kitchen din. Mayraah na kai ma Ammi shayinta ta dawo ta dau nasa ta fito zata kai masa, har a sannan Bilkisu na zaune parlon tana jiran sanda Haseenah ta fita, Haseenah ta bi Mayraah da kallo har ta dau hanyar dakin Maheer, Mayraah bata kulle kofar ba gaba daya ta karasa ta ajiye masa shayin, gani tayi ya sauka ya tafi ya kulle kofar har da sa makulli, ta zaro ido gabanta na faduwa tace "Yaya wllhi Ammi fa na jirana zata sa ni wani aikin..." Yace "Na wa aikin ai ya fi na Ammi lada yanzu" Marairaice masa tayi tana komawa baya.... Ashe dama ba shayin zai sha ba don at the end they ended up spilling the whole cup of tea a kasan tiles din dakin.... Wajen karfe biyun dare Mayraah ta bude idanuwanta da suka mata nauyi sbda bacci, duk da baccin bai isheta ba haka ta zame jikinta a hankali from his, ta sauke kafafuwanta kasa, sai da ta laluba inda zata ga ribbon dinta kan gadon bayan ta gani ta dauka ta daure gashinta.... After dressing up ta dau hijab dinta ta saka sannan ta nufi kofa, har wani rurrufewa idonta suke sbda bacci, a hankali ta bude kofar dakin ta fita ta kullo masa, ido hudu suka yi da Ammi da saukowarta parlon kenan, Mayraah ji tayi kamar ta nutse a wajen, nan da nan baccin ya bace idonta, Haseenah dake zaune idonta biyu don bata iya yin bacci, sai kallon Mayraah take bata ko kiftawa, Bilkisu kuma bacci ya ɗauketa kan kujera a parlon, Ammi dai tun da ta kalli Mayraah sau daya ta dauke kai tace "Mimi baki yi bacci ba dama" Mayraah da ta kasa kallonta tana kame kame tace "Eh Ammi, yanxu na sauko kasa, ina kallo ne a laptop" Daga haka tayi saurin barin wajen ta wuce sama ba tare da ta jira me Ammi zata ce ba, bandaki Mayraah ta shiga tayi wanka sannan ta shige cikin duvet dinta amma ta kasa bacci sai juye juye take, ta rasa me yasa moment din dazu ya makale mata a rai haka, daga karshe ta rufe har kanta bayan ta takure kusa da second pillow dinta, a haka ta samu bacci ya ɗauketa.

113
Washegari da asuba Mayraah na idar da sallah ta tafi bangaren Ammi don gaisheta, Ammi dai kallonta kawai take bayan ta amsa sallamarta, har ta zauna kan carpet kanta a kasa tace "Ammi ina kwana?" Ammi tace "Lafiya lau Mimi, how was ur night" Tace "Alhamdulillah" Ammi tace "Maa sha Allah" Daga haka Mayraah bata sake cewa komai ba a dakin, ko minti 5 bata yi da shigowa ba Maheer ya shigo dakin da sallama, Ammi ta amsa masa sallaman, zaunawa yayi yana kallon Ammi yace "Ina kwana" Ammi tace "Lafiya lau, an tashi lafiya?" Yace "Alhamdulillah" Mayraah ta ɗaga kai suka hada ido da shi, sunkuyar da nata kan tayi tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" Bata sake ce masa komai ba, Ammi na kallonsa tace "Likita za a kira ne ya dubata ko asibitin zaka kai ta?" Maheer bai ce mata komai da farko ba, can yace "Ba ga driver ba Ammi, sai mai aikinki ta rakata su je asibitin kawai, zan bata number na if there is anything idan sun je ta kirani" Ammi dai tayi shiru tana kallonsa, Mayraah dai kanta na kasa tana jin conversation din nasu, Ammi tace "To it's better su tafi da wuri" Mikewa Mayraah tayi, Ammi ta kalleta tace "Za ki je ki kwanta ne Mimi?" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "Eh" Ammi tace "Toh kiyi kwanciyar ki a nan mana" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Zan je dakina" Ammi tace "To je ki" Ta nufi kofa Maheer ya bi ta da kallon gefen ido har ta fita. Tuni Ammi ta sauko downstairs don sanar ma Bilkisu ta shirya ta raka Haseenah asibiti, don tun wajen karfe ukun dare Haseenah ke fama da ciwon ciki har asuba kuma bata yi bacci ba, Ammi na kallon Haseenah da ta samu bacci a parlon, sannan ta tafi kitchen... Bilkisu dake aiki a kitchen din ta juya ta gaisheta da ladabi, Ammi ta amsa tace "Yaushe tayi baccin?" Bilkisu tace "Tun da ya bata magani bayan wani dan lokaci bacci ya dauketa" Ammi tace "To idan ta tashi driver zai kai ku asibiti, zan baki number Maheer din idan da wani abu sai ki kirasa" Bilkisu tace "Toh Hajiya" Juyawa Ammi tayi ta bar kitchen din Bilkisu ta ci gaba da abinda take. Har gari ya waye Mayraah na kwance dakinta, ɗan baccin safen da take yi ma ta kasa yin sa ta rasa dalili, tashi tayi daga karshe ganin karfe tara saura ta shiga bandaki don yin wanka, ta fito daga wanka tana shiryawa Ammi ta bude kofar tana kallonta tace "Mimi kin yi breakfast ne?" Mayraah ta girgiza mata kai tace "Ban yi ba" Ammi tace "Toh ki je sai ki hada har na yayanki ki kai masa" a hankali Mayraah tace "Toh" Juyawa Ammi tayi ta fita daga dakin, Mayraah ta gama shiryawa ta fita zuwa downstairs, Haseenah ce zaune a Parlon da shayi a gabanta ta jinginar da kanta da kujera, da alama tayi nisa tunanin da take don bata ma san Mayraah ta sauko downstairs ba, Mayraah tayi wucewarta kitchen ta fara hada ma Maheer breakfast, tana gama hada masa breakfast din ta dauka ta fito daga kitchen din ta nufi dakinsa, har a sannan Haseenah da ta jinginar da kanta da kujera bata sani ba, bayan kusan 10mins Bilkisu ta shigo parlon daga dakinta tana kallon Haseenah tace "Aunty baki gama shan shayin ba har yanzu? Dreba na ta jiran mu a waje" Haseenah ta sauke numfashi a hankali tace "Ciwon cikin ma ai ya lafa min bilkisu, kawai ruwan lipton zaki taimaka ki kawo min na kasa shan shayin...." Bilkisu ta juya ta tafi kitchen ta bude flask ta tsiyaya mata ruwan lipton sannan ta kai mata, kadan Haseenah ta sha ta jawo maganin da Maheer ya bata jiya tana dubawa, sai kuma ta kalli Bilkisu tace "Ya ma yace zan sha maganin nan?" Bilkisu tace "Biyu yace ki sha ai" Haseenah tace "Anya, kinga fa uku ne babu a jiki, gwara dai in tambayesa" Bilkisu dai bata ce mata komai ba tana kallonta, da kyar Haseenah ta dafa kujera ta mike tsaye ta fara tafiya shi ma da kyar don kafafuwanta sun mata nauyi sun kumbura, dakin Maheer ta nufa, Bilkisu ta bi ta da kallo kawai ta tafi ta ci gaba da abinda take, Haseenah na isa kofar dakin nasa kafin ta bude taga an riga ta bude kofar, komawa gefe tayi ganin Mayraah, daga sama har kasa Mayraah ta kalleta sannan ta bar wajen, Haseenah ta kalli cikin dakin, Lkci daya Maheer ya murtuke fuska ganinta yace "Ke wai baki da hankali ne ko kuma kin fara hauka ne? That was how u barge into my room earlier this morning, are you alright?" Haseenah ta sukunyar da kanta bata ce komai ba, bayan few seconds ta juya ta bar bakin kofar dakin.... Mayraah na zaune parlon Ammi Maheer ya shigo da sallama, Ammi na kallonsa tace "Bilkisun ta kira ka?" Yace "Aa" Zaunawa yayi, Ammi dai kallonsa kawai take ganin he is moody, amma tayi tunanin kawai saboda Haseenah ce da yake tunanin ta karfi da yaji ana cusa masa ita, Mayraah dai idonta na kan TV, mikewa yayi Ammi tace "Ko da wani abu ne?" Ya girgiza mata kai yace "Aa babu" Kofa ya nufa Ammi ta bi sa da kallo tace "Night shift gareka ne yau?" Yace "Eh" Daga haka ya fita, Bayan fitarsa da some minutes Ammi ta mike ta fita daga parlon ita ma. downstairs ta sauka ta gansa zaune a parlor shi kadai, Ammi ta zauna tana kallonsa tace "Me yasa kake son saka ma kanka damuwa ne Maheer? Nobody is trying to bring Haseenah back to ur life in haka kake

Download complete TXT · Novel page