Showing 366001 words to 369000 words out of 452169 words
Chapter 123 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
"Says who?" Ko rufe baki bata yi ba ya daga rigar jikinta sama gaba daya, er kara tayi ta durkusa kasa tana zaro ido, ji tayi kamar ta nutse don kunya, ta bata fuska kamar zata yi kuka tace "Ni dai wallahi bana so yaya, wannan ai iskanci ne" dukawa yayi gabanta yana kallonta kamar me rada yace "Kuma gashi Allah yana kallonmu ko?" Rufe fuskarta tayi da sauri tana turo baki at the same time tana murmushi, yana murmushin shi ma yace "Toh tashi kiyi wanke wanken ki" Ta ki bude fuskarta don kunya tace "Ni dai ka fita plaa" Yace "Aa tare za mu yi wanke wanken ai" Kasa tashi tayi tsabar kunya ga shi yasa ta zama uncomfortable da kayan jikinta, ya mike ya dagota tana nonnoke masa, yace "Zan fa cire rigar in ajiye gefe kiyi wanke wanken a haka" Zaro ido tayi ta mike ta juya masa baya ta ci gaba da wanke wanken ta yana tsaye bayanta, gaba daya ta kasa nutsuwa jin sa a bayanta, daga karshe ta wanke hannunta ta marairaice tace "Ni dai sai anjima zan ci gaba wllhi" Kamar jira yake kawai taga ya dauketa suka bar kitchen din, bai ajiyeta a ko ina ba sai master bedroom din gidan, kamar dai dazu da asuba haka nan Maheer ya kyale Mayraah yanzun ma without achieving his goal, lallashinta ya dinga yi yana rungume da ita cike da tausayinta, daga karshe ya samu ta daina kukan tana sauke ajiyar zuciya, bayan few mintues ya dago kanta yana kallonta da idanuwansa da suka canza launi, sauke idonta tayi don har a lkcn a tsorace take, ya lumshe ido ya kai bakinsa kunnenta murya can kasa yace "I will get us a Lube, to make it easier, you won't be hurt with the Lube..." Rufe fuskarta tayi a kirjinsa zuciyarta na bugawa sosai, idan ta tuna first and second experience dinta with him sai taji gabanta yayi mugun faduwa, ko tunawa ma bata son yi, ga shi yanzu taga alamar dole sai ta ji irin azaban da taji a karonsu na farko da na biyu in har zai tara da ita, wayarsa ne ya fara ring ya juya yana kallon wayar sannan ya dauka ganin Mama Ladi ke kiransa yayi picking ya sa a handsfree, ita dai Mayraah kanta na kirjinsa idonta a lumshe tana jin bugun zuciyarsa, muryar Haseenah suka ji tace "Hello Maheer, the babies are developing serious fever, kuma Ammi da Mama Ladi sun fita kasuwa za su karo masu kayan sa wa...." Lkci daya Mayraah ta bude ido bayan ta ji abinda Haseenah tace, Maheer wish ba a handsfree ya sa wayar ba, don da ace ba a handsfree bane kawai katse call din zai yi bakinsa alekum ba tare da Mayraah ta ji komai ba, a hankali Haseenah tace "Are you there pls Maheer, their temperature is so high" Maheer ya dake yace "Ammi ya kamata ki kira ki gaya ma ba ni ba...." Daga haka ya katse wayar ya ajiye, a hankali Mayraah ta zame kanta daga jikinsa without looking at him tace "Zan je inyi wanka" Daga haka ta jawo rigarta after covering her body ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga part din ta kulle kofa, jawo wayarsa yayi ya sake dialing number Mama Ladi, yana fara ring Haseenah ta daga, yace "Ban gane suna developing fever ba, weren't they given the medicine i got for them yesterday?" Haseenah tayi kasa da murya tace "Wallahi an basu, kawai yanzu ne naji jikin nasu na yin zafi, shi kuma dayan da ya sha nono sai ya dinga sarkewa, ai yayi a gaban ka jiya ka gani da daddare, he did it thrice this morning...." A takaice yace "Ina zuwa" Daga haka ya katse wayar ya sauka daga kan gadon ya shiga bandaki, Haseenah ta ajiye wayar hannunta da sauri ta mike ta dauko flask din ruwan zafin da aka ajiye mata a dakin ta bude flask din sannan ta dauko towel, ta manna towel din bakin flask din ruwan zafin, sai towel din yayi absorbing tiriri sosai sannan ta cire ta dinga manna towel din sama sama jikin twins din dake bacci kan gado, wanda zafin towel din duk ya tada su daga baccin da suke suna mutsu mutsu, haka Haseenah ta dinga yi, yaran har da kukansu amma bata fasa ba ita a lallai sai jikinsu yayi zafi kafin Maheer ya karaso. Mayraah na gyara bedroom dinta bayan tayi wanka Maheer ya shigo dakin, daga sama har kasa ta kallesa ta ci gaba da abinda take, a hankali yace "Mimi i want to go get something in dawo yanzu" Ba tare da ta kallesa ba tace "Ohk" Ya sunkuyar da kansa yace "What are you cooking for us this afternoon?" A takaice tace "I am not in the mood"
116
Maheer yayi shiru yana kallonta, ita dai gyara gadon ta kawai take without looking at him, bayan few seconds yace "Ohk should i get takeaway for us while coming back?" Still not looking at him tace "Ohk" juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo mata kofar, sai a sannan ta zauna gefen gado hawaye cike idonta, tana jin fitar motarsa daga gidan ta zamo kasa a hankali hawaye wasu na bin wasu a fuskarta taji zuciyarta na mata zafi, bata san sanda ta fashe da kuka ba ta hade kanta da gwiwa. Maheer na isa gida ya shiga dakin da Haseenah take da yaran, tana zaune gefen gado ta kifa daya babyn a cinyarta tana jijjigasa a hankali, daya kuma tana rike da shi a kafada shi ma tana shafa bayansa a hankali, har a sannan kuka yaran suke, tuni dama ta maida flask din inda yake ajiye a dakin, karamin towel din ma taje ta shanya shi inda Mama Ladi ta shanya a banɗaki bayan tayi masu wanka da asuba, sai dai fa hankalinta ya tashi sosai ganin duk inda ta dosana masu towel din a jikinsu sai da yayi ja sosai, dama gasu farare kal, ko don fatarsu yayi laushi da yawa ne yasa wajen yayi ja haka oho.... Maheer ya karasa cikin dakin yana kallon yaran, ta daga kai ta kallesa da damuwa cikin sanyin murya tace "Tun dazu suke ta kuka, na rasa me ke damun su haka, jikinsu har yanzu da zafi, na basu nono sun ki amsa" Ya amshi babyn dake kafadarta yana kallonsa, tayi kasa da murya tace "Ko dai asibitin za mu maida su ne?" Sosai gabanta ya fadi ganin ya daga rigar babyn, sai kuma taga ya tsura ma jikin babyn ido, da sauri tace "Shi ma dayan haka jikinsa yayi wallahi, bari ka ga" Daga haka ta juyo da jaririn hannunta ta daga masa rigarsa tana nuna masa, Maheer was a bit confuse ya dinga kallon jikin babies din, ita dai gabanta sai faduwa yake don da ace tasan haka fatarsu zai yi bazata fara sa masu towel me zafi a jiki ba, ya daga kai ya kalleta yace "When did u notice this in their body?" Ta gyara zama a hankali tace "Not long ago, shi yasa ma na kira ka" Yace "Wa ya masu wanka yau?" Gabanta na faduwa tace "Mama Ladi ce, amma da ta masu wankan gaskiya ni ban ga haka a jikinsu ba don ina dakin ta masu wankan, amma ina jin ruwan wankan ne ya masu zafi da yawa don da take masu wankan ma jikinsu sai tiriri yake suna tsala ihu" Maheer bai sake cewa komai ba sai kallon jikin yaran kawai yake, ita dai kallonsa take don da alama ya yarda da abinda tace, har cikin ranta ta ji dadin ɗan maganar nan da Maheer yayi da ita, after few minutes cikin sanyin murya tace "Ko dai mu maida su asibitin ne kawai?" Ya daga kai yace "Ba a basu magungunan su bane?" Tace "Tun asuba da ta basu bayan ta masu wanka ba a sake basu ba" Yace "Yaushe suka fita?" Tace "Wajen tara suka fita kasuwa" Mikewa yayi ya tafi ya dauko magungunan a inda suke ajiye yana rike da daya babyn a hannunsa, Haseenah dai sai bin sa da kallo take bata ko kiftawa, bata taɓa jin ta samu hope kan Maheer zai iya yafe mata ba sai yau, dubi wai Maheer ne yake mata magana in a calm way, definitely this babies might be the only reason da zai sa ya yafe mata har ma kilan su dawo su zauna tare as husband and wife for the sake of the babies, don taga alamar har cikin ransa yana son yaran nan, bayan ya gama ba babyn hannunsa maganin ya kwantar da shi kan bed dinsa, ta mika masa na hannunta tana kallonsa, ya amshe sa ya basa maganin shima, duk idonta na kansa ta kasa daina kallonsa, daukan babyn da ya ajiye tayi ta daurasa kan kafadarta kamar yanda taga yayi ma dayan, after few minutes yaran duk suka koma bacci.... Sai wajen karfe daya su Ammi suka dawo daga kasuwa, har sannan kuma Maheer na gidan bai tafi ba, a parlor Mama Ladi ta jefar da gyalenta ta baje tana kallon Bilkisu tace "Ke zubo min abinci ko bai dahu ba" Bilkisu ta tafi kitchen don kawo mata abincin, Ammi kuma ta shiga dakin da Haseenah take da jariran, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Tirrr, akan wata er iska shegiya za ayi ta gantali da ni cikin azababben ranan Habuja kamar mara makabuli, dubi yanda na ƙode kamar ban taɓa haske ba a rayuwata, to akan me? Kai ko matar kirki ce Hasinun ai kayan da aka siyo mata tun na farko ya isa ba sai an ce za ayi cacan wasu kudaden a karo wasu kayan ba, balle duk mun san er iska ce shaidaniya mara tsoron Allah, in na sake bin kowa kasuwa shegiya nake wallahi, amma dai mu je zuwa in ta sake tafka masu wata tsiyar ni dai ina kaduna kuma ko jaje wallahi, don ta haifo en biyu sai a rufe ido a shashantar da mugun abun da ta aikata a pamily, gashi nace kar a bari ta basu nono mu siyo Madara amma anki saurarata an maida ni er banza sai dirka masu nononta mara tsarki take, to su suka jiyo in yaran suka kwaso mugun halinta ni dai ba ruwana ina Kaduna, Mera dai ce abar tausayi, don hadata da uban nasu za su yi ta yi ya dinga jin haushinta" Tuni Mama Ladi ta gyara zama ganin Bilkisu na tahowa da babban plate din abinci da kwalin lemo... Ammi ta dinga kallon jikin twins din da Maheer ya nuna mata, ita dai Haseenah kanta na kasa, Ammi ta kalli Haseenah tace "Yaushe jikin nasu yayi haka?" Haseenah ta dago kanta a hankali tace "Tun bayan da Mama Ladi ta masu wanka ta shirya su" Maheer dai kallon Ammi kawai yake, Haseenah ta mike daga kan gadon ta dau pad ta wuce bandaki, Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Zan mata magana yanzu, ruwan wanka ya masu zafi da yawa ne" Maheer dai bai ce komai ba, Ammi ta kwantar da babyn kan gado sannan ta mike ta nufi kofa har ta fita sai kuma ta dawo tana kallon Maheer tace "Ina Mayraah?" Yace "Tana gida" Ammi tace "Ohk" daga haka ta fito parlor ta tadda Mama Ladi dake cin abincin da aka kawo mata, Ammi ta zauna kan kujera tana kallonta tace "Dreban bai shigo da kayan ba" Mama Ladi dai sai tura abincin gabanta take bata dago kai ba balle ta kalli Ammi, cikin kwantar da murya Ammi tace "Mama ina jin fa ruwan da kike ma yaran nan wanka da shi ya masu zafi da yawa" Mama Ladi ta daga kai ta kalleta, can tace "Haka yaran suka buda baki suka gaya maki?" Ammi ta ɗan yi murmushi tace "Aa nunawa yayi a jikinsu, duk jikin nasu yayi tabon ja" Mama Ladi tace "Kamar ya?" Ammi tace "Gama cin abincin sai ki gani Mama" Mama Ladi ta maida abincin gefenta ta mike tace "Aa mu je dai in gani, sai kace yau na saba yi ma jarirai wanka za ace ruwan yayi masu zafi, a takaice dai so ake ace na kone su, ina ce har ubansu na yi ma wanka ban kona sa ba balle su" Ita dai Ammi bata ce komai ba, dama tasan dole sai Mama Ladi ta juya zancen nan, ganin Mama Ladi ta nufi dakin da Haseenah take Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta mike ta bi bayanta, Mama Ladi na shiga dakin ta nufi kan gado ta daga kayan jariran tana kallon jikinsu, can tace "Ikon Allah, shi kuma ruwan wankan saboda neman magana sai yayi masu dabbara dabbara a jiki maimakon duk jikin nasu gaba daya yayi ja, to ko Mariya da bata taɓa haihuwa ba bazata ce ruwan wanka ne yayi ma yaran nan tabo a jiki ba balle ke me yara uku ga Mera ta hudu, wato ga Ladi er banza da bata san abinda take ba ko? to wllhi ku tuhumi makirar uwarsu ita kadai tasan me ta masu jikinsu yayi wannan tabon, kada wani shege ya sa ni a bakin duniya sai in tattara sabon akwatina in koma kaduna tunda ba kanwar uwata bace ta haihu, ban da ma zuciyar musulinci ina ruwana da abinda Hasinu ta haifa da har za a gayyato ni Habuja, matar da ta wargaza mana pamily ta sa ma Mera guba a abinci ta ci, ai ko don wannan bai kamata ma ku bari ta haihu a gabanku ba, uwar da ta haifeta ta mutu ne? In ma uwar ta mutu bata da dangin uwa da na uba ne a duniya? yarinyar da ta tafka mana lafiyayyen barna amma ace duk mun manta sai nan nan ake da ita don ta haifo maza biyu? Ko da yake ku dai ku ka manta amma ni ban manta ba wallahi, kuma daga yau ma bazan sake ma yaran wanka ba ke ki dinga masu tunda jikokin ki ne, kece dolensu" Mama Ladi na huci ta sake kallon jikin yaran tace "Wannan dai da kyar in ba izaya ta dinga masu da abu me zafi ba a jiki tunda ba imani ne da ita ba duk mun sani, to meye bazata aikata ba in har zata iya saka ma mutum guba a abinci ya ci, wallahi Hasinu ba abar yarda bace er jikar firauna ce" Daga haka Mama Ladi ta fice daga dakin ta koma gun abincin ta, duk wannan abun Haseenah dake ban daki na jin Mama Ladi don ba a hankali take maganar ba, gabanta sai faduwa yake jin maganganun Mama Ladi na karshe, tunanin abinda zata yi ta dinga yi a bandakin, Maheer dai kallon Ammi kawai yake, Ammi ta sake kallon jikin babies din.... Bayan wani ɗan lokaci Haseenah ta fito daga bandakin tana rike da cikinta ta karaso ta durkusa kan carpet ta sunkuyar da kai tana yarfe hannu hawaye na zuba idonta, Ammi dake ta zaune tana jiran fitowarta tace "Lafiya?" Da kyar tace "Cikina ke ciwo sosai" Da haka Haseenah ta samu tayi distracting din su daga tabon dake jikin babies din don kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita tana durkushe a dakin, Shi dai Maheer fita yayi kawai daga dakin ya bar Ammi dake bin ta da sannu, Mama Ladi na ganin fitowarsa tayi masa alamar ya zo, ya nufi inda take ya zauna, Tayi kasa da murya tace "Yanzu fisabilillahi Mashir nan ya kamata yarinyar nan ta zauna tayi jego? Bata da pamily ne? Mu fa ba yan iska bane Mashir, kuma me hali bai fasa halinsa, iyakar kokarin da za ayi mata a gidan nan an mata tun da har gashi an bari ta haihu a nan, to sai kuma ta koma pamilynta su ma su yi dawainiya da ita ai hannunsu bai rubewa su yar, kuma don ta koma pamilynta hakan ba yana nufin duk abinda kai da uwarka ya kamata ku yi mata baza ku mata ba a can, don haka ni a gaskiya ban goyi bayan zamanta a gidan nan ba, in kuma Meran er banza ku ka mayar da ita ne to sai in ji, don ko domin abinda ta aikata ma Mera na kisan gilla bai kamata ko gate din gidan nan ta sake shigowa ba" Maheer dake ta sauraron Mama Ladi ya sauke ajiyar zuciya yace "Dama Ammi tace kawai kwana arba'in zata yi ta koma gun iyayenta" Mama Ladi tace "Wato har sai tayi kwana arba'in kafin nan ta kara tafka mana wani tsiyar ko? Da ace ita Ammin ce ta ci guban da Mera ta ci ai bazata fara cewa Hasinu tayi kwana daya a gidan nan ba balle kwana arba'in, kun dai mayar da Mera er banza, yarinyar nan fa gata gareta kaca kaca ta ko ina, ko kakanta Alhaji Saminu yaji wnn abun da ku ka yi sai ya kullace ku wllh, kun nuna bara da balu kenan, duk mutumin da zai iya yunkurin kashe wani fa babu abinda bazai aikata a duniyar nan ba, ina ta fada kun sake fahimtata amma ba komai" Maheer ya jinginar da kansa da kujera yace "Ba gidan nan zata zauna ba Mama, nan da kwana bakwai zata koma can gidan da aka kama mata, a can za su yi arba'in din" Mama Ladi tace "Oho dai ni ba ruwana duk abinda zai je ya dawo ni dai nawa ido..." Kallon agogo dake nuni da karfe biyu saura Maheer yayi sai a snn ya tuna lunch da yace zai siya masu shi da Mayraah, mikewa yayi ya bar parlon, Mama Ladi dai ta taɓe baki, ta mike ta tafi tayi sallah. Ammi zata fito daga dakin da Haseenah take kenan Maheer ya bude kofar, hanya ya bata bayan ta fita ya shiga dakin, Haseenah na kwance ta rufe ido kamar me bacci amma ba baccin take ba, Ya karasa kan gadon yana kallon jariran dake bacci, kasa kasa Haseenah ke kallonsa yanda bazai gane