Mayrah
Chapter 124 of 152
a gayyato ni Habuja, matar da ta wargaza mana pamily ta sa ma Mera guba a abinci ta ci, ai ko don wannan bai kamata ma ku bari ta haihu a gabanku ba, uwar da ta haifeta ta mutu ne? In ma uwar ta mutu bata da dangin uwa da na uba ne a duniya? yarinyar da ta tafka mana lafiyayyen barna amma ace duk mun manta sai nan nan ake da ita don ta haifo maza biyu? Ko da yake ku dai ku ka manta amma ni ban manta ba wallahi, kuma daga yau ma bazan sake ma yaran wanka ba ke ki dinga masu tunda jikokin ki ne, kece dolensu" Mama Ladi na huci ta sake kallon jikin yaran tace "Wannan dai da kyar in ba izaya ta dinga masu da abu me zafi ba a jiki tunda ba imani ne da ita ba duk mun sani, to meye bazata aikata ba in har zata iya saka ma mutum guba a abinci ya ci, wallahi Hasinu ba abar yarda bace er jikar firauna ce" Daga haka Mama Ladi ta fice daga dakin ta koma gun abincin ta, duk wannan abun Haseenah dake ban daki na jin Mama Ladi don ba a hankali take maganar ba, gabanta sai faduwa yake jin maganganun Mama Ladi na karshe, tunanin abinda zata yi ta dinga yi a bandakin, Maheer dai kallon Ammi kawai yake, Ammi ta sake kallon jikin babies din.... Bayan wani ɗan lokaci Haseenah ta fito daga bandakin tana rike da cikinta ta karaso ta durkusa kan carpet ta sunkuyar da kai tana yarfe hannu hawaye na zuba idonta, Ammi dake ta zaune tana jiran fitowarta tace "Lafiya?" Da kyar tace "Cikina ke ciwo sosai" Da haka Haseenah ta samu tayi distracting din su daga tabon dake jikin babies din don kuka ta dinga yi kamar ranta zai fita tana durkushe a dakin, Shi dai Maheer fita yayi kawai daga dakin ya bar Ammi dake bin ta da sannu, Mama Ladi na ganin fitowarsa tayi masa alamar ya zo, ya nufi inda take ya zauna, Tayi kasa da murya tace "Yanzu fisabilillahi Mashir nan ya kamata yarinyar nan ta zauna tayi jego? Bata da pamily ne? Mu fa ba yan iska bane Mashir, kuma me hali bai fasa halinsa, iyakar kokarin da za ayi mata a gidan nan an mata tun da har gashi an bari ta haihu a nan, to sai kuma ta koma pamilynta su ma su yi dawainiya da ita ai hannunsu bai rubewa su yar, kuma don ta koma pamilynta hakan ba yana nufin duk abinda kai da uwarka ya kamata ku yi mata baza ku mata ba a can, don haka ni a gaskiya ban goyi bayan zamanta a gidan nan ba, in kuma Meran er banza ku ka mayar da ita ne to sai in ji, don ko domin abinda ta aikata ma Mera na kisan gilla bai kamata ko gate din gidan nan ta sake shigowa ba" Maheer dake ta sauraron Mama Ladi ya sauke ajiyar zuciya yace "Dama Ammi tace kawai kwana arba'in zata yi ta koma gun iyayenta" Mama Ladi tace "Wato har sai tayi kwana arba'in kafin nan ta kara tafka mana wani tsiyar ko? Da ace ita Ammin ce ta ci guban da Mera ta ci ai bazata fara cewa Hasinu tayi kwana daya a gidan nan ba balle kwana arba'in, kun dai mayar da Mera er banza, yarinyar nan fa gata gareta kaca kaca ta ko ina, ko kakanta Alhaji Saminu yaji wnn abun da ku ka yi sai ya kullace ku wllh, kun nuna bara da balu kenan, duk mutumin da zai iya yunkurin kashe wani fa babu abinda bazai aikata a duniyar nan ba, ina ta fada kun sake fahimtata amma ba komai" Maheer ya jinginar da kansa da kujera yace "Ba gidan nan zata zauna ba Mama, nan da kwana bakwai zata koma can gidan da aka kama mata, a can za su yi arba'in din" Mama Ladi tace "Oho dai ni ba ruwana duk abinda zai je ya dawo ni dai nawa ido..." Kallon agogo dake nuni da karfe biyu saura Maheer yayi sai a snn ya tuna lunch da yace zai siya masu shi da Mayraah, mikewa yayi ya bar parlon, Mama Ladi dai ta taɓe baki, ta mike ta tafi tayi sallah. Ammi zata fito daga dakin da Haseenah take kenan Maheer ya bude kofar, hanya ya bata bayan ta fita ya shiga dakin, Haseenah na kwance ta rufe ido kamar me bacci amma ba baccin take ba, Ya karasa kan gadon yana kallon jariran dake bacci, kasa kasa Haseenah ke kallonsa yanda bazai gane ba bacci take ba, ya fi minti uku yana kallon yaran and she could see their love in his eyes, daga karshe ya mike bayan ya gyara masu lallausan blanket din dake jikinsu sannan ya nufi kofa ya fita ya kullo, ɗan murmushi Haseenah tayi adding more hope to her self. Karfe uku saura Maheer ya isa gida, tun da ya shiga parlon gabansa ke faduwa don bai ma san me zai ce ma Mayraah ba, shi dai yasan ko da wasa bazai ce mata daga gida yake ba, ya ajiye takeaway din abincin hannunsa a hankali, yana tafiya slowly ya isa kofar dakin Mayraah, sai kuma ya kasa bude kofar, after standing for a while a bakin kofar ya bude a hankali yana kallon cikin dakin, bin dakin ya dinga yi da kallo ganin bata ciki, ya fito ya duba dakin dake kusa da nata nan ma yaga bata ciki, mamaki ne ya cikasa, komawa yayi parlor ya tafi kitchen ya duba nan ma bata ciki, duk da yasan baza ta shiga dakinsa ba still dai haka ya tafi dakin nasa nan ma yaga bata ciki, he became confused at once, ya fito ya tafi master bedroom nan din ma bai ganta a ciki ba, compound ya sake fita da sauri ya nufi mai gadi, yana kallonsa yace "Don Allah ta dade da fita gidan ne??" Mai gadi dake kallonsa yace "Aa gaskiya bata fita ba, ina jin ko ta zaga can baya ne, amma ina nan ban ga fitar ta ba" Maheer ya sauke wani ajiyar zuciya sannan ya zaga bayan gidan, zaune ya ganta a garden din wajen tana danna wayarta, ya nufeta yace "Mimi" Ta daga kai ta kallesa sai kuma ta ci gaba da abinda take, a takaice tace "Good evening" Zaunawa yayi gefenta yace "Baki ci abinci ba har yanzu ko?" Tace "Aa na ci" Ya ɗan buda ido yace "Kuma gashi na siyo maki abinci a eatry" Tace "Sai ka ci, don ni na riga na ci abinci" Yayi shiru yana kallonta, after few seconds a hankali yace "Kinsan har ina muka je yau kuwa?" Mayraah tace "Aa how will i know" Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "I am so exhausted, inda muka je da nisa sosai, yanzu ki tashi mu je ki kara cin abinci, sai mu shirya mu je can gida, Ammi har ta fara kira tana tambayar me yasa ba mu zo ba yau" Sai a sannan Mayraah ta daga kai ta kallesa, ya sakar mata murmushi ya ja dogon hancinta yace "Yes, ko kuma ni in zauna ke kadai ki je gidan kiyi representing the 2 of us, dama na gaji sosai bacci nake son in yi.. " Mayraah dai bata ce komai ba ya mike ya dago ta, yana rike da hannunta suka bar wajen, da kansa yaje kitchen ya dauko masu plate ya juye masu abincin, ita dai tana zaune tana kallonsa.... Bayan La'asar Maheer na dawowa masallaci yace "Let me order a bolt da zai kai ki can gidan Mimi, cause ina son inyi bacci ne i am so tired, idan na tashi ko zuwa 6 ne sai in je in dauko ki mu dawo gida..." Maheer bai jira opinion dinta ba ya tashi ya shiga dakinsa, bayan ya sauke ajiyar zuciya ya dau wayarsa don mata ordering bolt din, sai dai fatansa Allah sa garin maganganun Mama Ladi bazata ce ma Mayraah ai yaje gidan da safe ba, haka nan Mayraah ta tafi dakinta ta shirya ba don ranta ya so ba, after some minutes Maheer ya shigo dakin nata don ganin ko ta gama shirin cause Bolt din na kofar gida, kallonta ya dinga yi ta madubi baya ko kiftawa, don wani kyau na musamman tayi cikin tsadadden atamfar jikinta, she look so beautiful and stunning, daga dankunne har tsarka da zobunan hannunta gold ne, ita dai tun da ta kallesa sau daya ta ci gaba yafe gyalenta, ya karasa har bayanta ya tsaya, hakan yasa ta juyo amma taki kallonsa, ya lumshe ido ya rungumeta jikinsa, yayi kasa da murya yace "You look so cute wife" dukawa yayi ya mata Light kiss a lips dinta, ta ɗan yi murmushi still bata bari sun hada ido ba, ba karamin kashe masa jiki murmushin nan nata yayi ba, a haka ya rakata har bakin gate yana rike da handbag dinta cikin rashin kuzari, ya bude mata back door yana kallonta har ta shiga sannan ya ajiye mata jakarta, ya daga mata hannu cikin sanyin murya yace "Till i come later Dear" Sai a sannan ta daga kai suka hada ido, still smiling at him ta daga masa hannu, kallonta ya dinga yi babu ko kiftawa har sai da motar ya bar wajen.... Mayraah na isa gida wajen karfe biyar saura ta gaida securities dake bakin gate ta shiga cikin compound, tana isa entrance din parlor ta bude kofa ta shiga, dai dai sanda Mama Ladi ta fito kitchen rike da kettle din ruwan zafi, Mama Ladi ta kalleta daga sama har kasa tace "Wacece wannan kuma kamar dai Mera" Mayraah na murmushi ta karasa har kusa da ita ta gaisheta, Mama Ladi tace "Wannan ai sai ki sa Mashir din ya dinga rashewa kugunki yaki tabuka abun arxiki a rayuwarsa, irin wannan kwaliyya haka kamar wata jikar sarki, ko da yake meye banbancin Alhaji Saminu da sarkin, shime sarki ne a fadarsa ai" Mayraah dai murmushi kawai take zata amshi kettle din hannunta Mama Ladi tace "Aa bar shi kawai mu je dakin, ruwan zafi ne zan ma wa en can jariran er iskar matar can wanka, duk da ance na toyesu dazu da safe, amma dai albarkacin ubansu bazan ki masu wanka ba don Mashir mutumin kirki ne duk duniya mun shaida" Mayraah tace "Ammi tana sama ne Mama?" Mama Ladi tace "Wani sama? matar da ji take kamar za a gudu mata da jikokin nan nata idan ta matsa daga wajensu, ke dai mu je ki bude min kofa kawai" Mayraah na tafiya a hankali har suka iso dakin da Haseenah take ta bude kofar, Mama Ladi ta fara shiga sannan ita ma ta shiga ta kulle kofar, kallonta Haseenah ta dinga yi ko kiftawa babu don da farko bata ma gane ta ba, Mayraah dai tun da ta mata kallo daya ta dauke kai, Ammi na ganin Mayraah tayi murmushi, Mayraah ta karasa har inda take ta zauna sannan ta gaisheta, Ammi ta amsa tace "Ya gidan Mimi?" Mayraah tace "Alhamdulillah Ammi, ya twins" Ammi ta dauko mata daya babyn ta mika mata, Mayraah ta amshesa tana kallonsa, har sannan Haseenah bata daina kallon Mayraah ba lkci daya duk mood dinta ya canza ga hawayen dake kokarin cika idonta, Mama Ladi ta ajiye ruwan zafin hannunta tana kallon Ammi tace "Ni fa da farko ban gane Mera bace ta shigo parlor, lallai Mashir ya iya kiwo, kuma da kyar in ba sabon ciki ne da ita ba wannan tsantsan kyan da tayi haka, shi ma Mashir din naga yayi kiba, haskensa ya kara fitowa alamar yana cikin kwanciyar hankali Mera na kula da shi sosai yanda ya kamata, bawan Allah sai yanzu zai san yayi aure amma da ai wahala yake bai san dadin aure ba" Haseenah ta sunkuyar da kanta cikin dubara take goge hawayen da ya cika idonta, Ammi dai jin maganganun Mama Ladi sun fara fin karfinta ta mike ta shiga bandaki don dauko baff din babies din, Mama Ladi ta kalli Mayraah da ta sunkuyar da kai tace "To ina Mashir din?" Mayraah ta daga kai a hankali tace "Yana gida yana bacci" Mama Ladi tace "Ahaf, da ina ya samu kwanciyar hankalin yin bacci miko min yaron in cire masa kaya" Mayraah ta mike ta mika ma Mama Ladi jaririn hannunta.
117
Bayan magrib Mayraah na zaune parlor tare da Mama Ladi dake cin abinci Maheer ya shigo gidan da sallama, idonsa na kan Mayraah har ya karaso cikin parlon ya gaida Mama Ladi, Mama Ladi ta ajiye cokalin hannunta tana kallonsa da kyau tace "Dazu da safe kiri kiri kai da uwarka ku ka titsiyeni wai na toya yara da ruwan zafi, to wallahi dazu da zan masu wanka ni da Ammi muka kare ma jikinsu kallo da kyar in ba abu me zafi makirar uwar ta dauka ta dinga dangwala masu a jiki ba, hankalin Ammi ma yafi nawa tashi, wajen duk yayi jan taɓo alamar ƙuna dama ga su farare sol, ai kuwa muka sa muguwar a gaba ta fada mana abinda tayi ma yaran in gaya maka shaidaniyar ba sai ta sakar mana kuka ba wai ta yaya zata cutar da yaran da ta haifa a cikinta, to wai ma wanda yayi niyyar kashe mutum menene ma bazai yi ba Mashir? Tsaf haushinmu da take ji zai sa ta kashe yaran nan biyu mu shiga uku wallahi, sam babu imani a tattare da lamarinta, sabili da hakan nace ma Ammi tun da sauran mutuncinmu a idonta mu dauketa mu maida ta gida gun iyayenta, yaran kuma a bar su gun Ammi ta dinga basu madaran jarirai, ga madaran ma har an siyo za su saba da shi a hankali, in sun yi wayo kuma a daukesu a ba Mera ta rike maka su, wannan shine kawai mafitar mu, yanzu haka Mamuda nake jira..." Mayraah dai kallon Maheer dake kallon Mama Ladi kawai take, Mama Ladi ta kalleta tace "Wallahi Mera da ya zo da safe shi da uwarsa cewa suka yi na toye yaran da ruwan zafi wajen wanka, abun ya min ciwo sosai don sai da nayi kukan bakin ciki suka sa abincin da nake ci ya fita raina" Maheer na kallon gadon yaran dake parlor ga kuma gwangwanin madara da Feeders yace "Ina yaran suke yanzu?" Mama Ladi ta gyara zama tace "Ahaf, shi fa jini mugun abu ne Mashir, dazun nan Ammi ta fita a gigice da dreba bayan taga taɓon jikinsa ta je babban shago ta siyo masu madara me shegen tsada, wai aka kada madaran a feeder da ruwan zafi aka ba yaran nan suka ki sha, sai tsala mana ihu suke a parlon nan, banda sun kwaso munafurci da mugun halin uwarsu yaushe aka haifesu da za su iya banbance Nono da madaran kanti? In gaya maka haka suka kunyata mu tsamo tsamo yanda uwar zata ji dadin mana dariya, dole dai muka sa Bilki ta kai ma uwar ta basu Nono, tun da aka shiga da su tsit kake ji, to tun fa ba aje ko ina ba kenan sun iya munafurci da makirci" Shi dai Maheer shiru yayi bai ce komai ba yana kallon formula din da Ammi ta siyo masu, after a while ya sauke ajiyar zuciya, ya ɗan kalli Mayraah dake kallonsa, sauke kansa yayi ya zauna kan kujera, Mama Ladi ta kalli Mayraah tace "Tashi ki shiga dakin ki dauko masa yaran daya bayan daya" Mayraah bata ce mata komai ba kuma bata tashi ba, Mama Ladi ta rike haɓa, can tace "Ba shakka" Sai kuma ta kalli Maheer tace "Haka fa dazu nace taje dakin ta dubo min wayana sai yarinyar nan Bilkisu ce taje ta dubo min, ilai nayi alwala zan yi magariba nace taje ta dauko min shijabi na da na bari a dakin inyi sallah amma yarinyar nan taki tashi tayi kamar bata ji me nace bata, kai ko ta ga tayi aure ta shigo layin manya tasan komai, bari ta sabunta rashin kunyanta...." A hankali Mayraah ta mike tsaye fuskarta babu walwala, ko kadan bata son Mama Ladi na aiken ta dakin nan, babu yanda ta iya tana tafiya a hankali ta nufi hanyar dakin, Mama Ladi tace "Kawai don dai kakanki Alhaji Saminu mutumin kirki ne kuma ina jin kunyarsa amma da wallahi kema tattara lamarinki zan yi in watsar a kwandon shara, naga kamar tsohon halin Badiyyah kike son ara ki yafa a kanki, ita kuma ga ta can ta koma sak ke lkcn da kike budurwa, Badiyyah ta dawo ba sawa ba hanawa gwanin ban sha'awa, duk tayi sanyi ta dawo mutuniyar kirki sallah baya wuceta, har na fara mata sha'awar Usuman, ina ta son ya dawo in samesa mu yi shawara" Maheer bai san sanda ya juya da sauri ya kalli Mama Ladi ba, dariya sosai ta basa, ita dai ta ci gaba da cin abincin ta, Mayraah na shiga dakin da Haseenah da twins dinta suke, Haseenah ta wani kalleta fuskar nan nata a daure, Bilkisu dai na zaune a dakin bayan Ammi ta umarceta ta zauna tun sanda ta shigo da su Haseenah ta basu Nono, sau uku Haseenah na attempting koranta daga dakin amma cikin dubara, Bilkisu da ta ganota taki fita tunda ga abinda Ammi ta ce mata, Mayraah bata ko kalli Haseenah ba ta nufi gun babies din dake kwance kan gado, tun kan ta dauki wanda ke gabanta Haseenah ta daukesa da sauri fuskarta a murtuke tana kallonta a walakance tace "Ke kika haifa min su? Kema ki haifi naki gobe mana in gani" Bilkisu dai sake baki tayi tana kallon ikon Allah, Haseenah ta ja wani dogon tsaki ta jawo daya babyn ma, Mayraah ta gyara tsayuwa tana mata kallon cikin ido tace "Kema naga ai ba daga zuwa kika haifesu ba, me kike ci na baka na zuba? in my own case daga ni har jaririn uban zai so tamkar