Showing 450001 words to 452169 words out of 452169 words

Chapter 151 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

na dawo, in kina son wani abu Bilkisu na nan, zan ce ta dawo parlon ta zauna" Daga haka ta nufi kofa, Mama Ladi ta karasa gun Eeman ta kama hannunta tace "To ni na tafi Eemani, Allah Ubangiji ya baki lafiya kin ji, ki dinga daurewa kina cin abincin ko kadan ne, in kuma kunu aka baki shima ki daure ki sha, kema za ki fi jin kwarin jikinki" Eeman ta gyada mata kai, a haka Mama Ladi ta nufi kofa tana kallon Usman tace "Hala dai biyanka dreban nan yayi da ka addabemu tun dazu Usuman.... Shaidan fa aka sani da gaggawa" Usman bai tanka ta ba har ta fita daga parlon, karasawa gun Eeman yayi ya duka gabanta yana kallonta ya kamo hannunta yayi kasa da murya yace "Baby, u need anything?" Ta girgiza masa kai bata ce komai ba, yayi pecking forehead dinta yace "Za mu je raka Mama Ladi Airport yanzu" Nan ma kai ta gyada masa, yayi pecking din hannunta sannan ya mike ya fita daga parlon. Gaba daya yan gidan suka tafi raka Mama Ladi Airport banda Bilkisu da Eeman, Ammi ta rungume Mama Ladi bayan sun isa airport din cikin sanyin murya tace "Allah ya kai ku lafiya Mama, Allah ya...." lokaci daya hawaye ya cika idon Ammi ta kasa ci gaba, Murya na rawa Mama Ladi tace "Ameen Hajara, Allah Ubangiji ya kaddara saduwar mu, Allah ya maki albarka ya raya maki zuri'ar ki ya albarkace su, ki tayani yi ma Mamuda godiya, Allah Ubangiji ya saka masa da alkhairi da dawainiyar da ya dinga yi min, Allah ya hade kan zuri'arsa ya karesa sharrin masu sharri..." Ammi dai ta kasa cewa komai hawaye na zuba idonta, har cikin ranta ta fara jin kewan Mama Ladi tun bata bar kasan ba, Mama Ladi ta tafi ta rungume Mayraah dake jingine da mota tace "Kema Allah ya maki albarka ya sauke ki lafiya Mera, duk silar ki nake cin wannan arzikin, Allah ya baki zaman lafiya na har abada da mijinki ya raya maki zuri'ar ki, duk da bana jin Mashir ko kadan, don duk mun san wanene Mashir, Mashir mutum ne" Mayraah ta sauke idonta ta kasa cewa komai, Mama Ladi ta kama hannun Maheer dake murmushi tayi masa sallama ta sa masa albarka, tayi ma Usman dake rike da Aryaan shima haka, sannan Omar, tace "Kai ma Allah ya baka mace ta gari Umar, yanda ka gama karatun ka lafiya Allah ya kawo maka babban rabo da mace ta gari" Omar na murmushi yace "Ameen Mama" daga nan kanin Alhaji Ahmadu wanda shi ne sabon mijin Mama Ladi yayi leading dinta zuwa cikin airport da akwatunanta don shi ne zai mata rakiya zuwa UK din. Suna hanyar komawa gida Omar dake driving din motar yace "Amma shi Alhaji Ahmad din yana da mata ne Ammi?" Ammi tace "Ta rasu shekara takwas kenan wai" Omar yace "Allah sarki, amma yana da yara?" Ammi tace "Yaransa maza hudu, uku sun yi aure sai karaminsu dake masters dinsa a England, abokin Alhaji Saminu ne na kut da kut, a yanda ma yake gaya ma Mama Ladin Alhaji Saminun ya girmesa da shekara biyar" Omar ya girgiza kai yana murmushi yace "I am so happy for Mama Ladi, she deserves happiness too" A hankali Ammi tace "Haka ne" Daga haka ta amshi Aryaan dake kokarin dawowa gunta daga hannun Usman, Usman yayi dariya yace "Shi fa yaron nan ya zata kece Baabarsa tsakanin sa da Allah" Ammi na murmushi ta dora goshinta kan na Aryaan tace "Wai haka Aryaan?" Dariya ya fara yi mata ta rungumesa jikinta tana jin son yaron har cikin ranta, gaba daya son da take ma ubansa ne ya dawo kansa yanzu....
Bayan tafiyar Mama Ladi UK da wata biyu Mayraah ta haifo santala santalan 'ya yanta Maza biyu wanda aka mayar masu da sunan yan biyun Haseenah da suka rasu, farin ciki gun Ammi ba a cewa komai, wannan karon Mayraah sak ubansu ta haifo su kuma duk kama suke da twins din Haseenah, Ammi farin ciki biyu ne ya hade mata don ana gobe Mayraah zata haihu Aunty Mariya ta kira take sanar mata she is pregnant after 15 years of patient, farin ciki gun Ammi ba a cewa komai don babu sallan da zata yi da baza ta sa kanwarta a addu'a akan Allah ya bata haihuwa ba, Mayraah na gama wankan jego babu wata wata tayi family planning don bata son taking wani risk din kuma, wannan karan dama a gidan Maheer aka yi sunan twins din, wanda duk mutan kaduna sai da suka zo, har Alhaji Saminu sai da ya zo yi ma jikar tasa barka, Hajja ce ta zauna tare da Mayraah sai Bilkisu dake taimaka mata har aka yi 40 days sannan Hajja ta koma kano ta bar Bilkisu a gidan, kafin 40 days sau uku Badiyyah ke zuwa gidan don ita ma a Abujan take aure, kuma atamfa hudu ta kawo sanda aka yi suna tace inji mai gidanta da kishiyarta duk da kishiyar ma ta zo sunan. Ranan da Mayraah da babies dinta suka yi 50 days tana daki Bilkisu ta shigo tana sanar mata tayi baki a parlor, Mayraah ta kwantar da Shuraim dake hannunta tace "Su waye ne?" Bilkisu tace "Wasu mata da miji ne" Mayraah tace "Abban Aryaan ya fita ne?" Bilkisu tace "Aa yana parlon, tare suka shigo da baƙin yace in maki magana" Mayraah ta dau mayafinta ta fita zuwa parlon, ta ɗan yi mamakin ganin visitors din nata, ta karasa cikin parlon tana murmushi ta zauna tace "Sannun ku da zuwa" Jiddah na murmushi suka gaisa da Mayraah, sannan Mayraah ta kalli Musharraf ta gaishesa, ya amsa da fara'a yace "Sannu Maman twins, hope you are doing fine?" Tace "Alhamdulillah" Sai kuma ta kalli Jiddah tace "Ban ga baby ba, baku zo da ita bane?" Jiddah na murmushi tace "Wai Mimi, tana can kano gun Mami" Mayraah tace "Allah sarki" Mikewa tayi ta tafi dauko masu ruwa da drinks a kitchen, sannan ta koma dakinta with the help of Bilkisu ta kai masu twins din dake bacci parlon, ko minti ashirin basu yi a gidan ba Musharraf yace za su tafi, nan ya ajiye ma twins din 100k, Jiddah kuma ta ba Mayraah tsadaddun atamfa biyu, Mayraah was so happy, and she appreciated the gift so much, Maheer yayi masu rakiya har kofar gida yayi ma Musharraf godiya sosai. Within that period Ceo tayi ma Maheer hanyar aiki a US, at first he was reluctant about the offer don kwata kwata bai son nesa da Ammin sa, amma haka nan Ammi da Abba suka karfafa masa gwiwa akan ya karbi offer din, shi dai har a sannan bai gamsu ba cause he is well paid a inda yake aiki, amma bai ma iyayen nasa musu ba, farin ciki gun Mayraah kam ba a cewa komai don ko babu komai zata kara zama close da mahaifiyarta da dad dinta that are in the US, sai dai duk bata nuna ma Maheer haka ba, Ammi was really down ganin favorite Son dinta da family dinsa za su yi nisa da ita sosai amma bata bari damuwar nata ya fito fili ba tunda ita ce ke kara encouraging Maheer din. Maheer ya so a bar mata Aryaan ganin yanda suka shaku sannan bai saba da su ba sai ita da Bilkisu amma tace kawai su tafi da shi ba komai a hankali zai saba da su in ya ga babu ita da Bilkisun, bayan sun gama processing komai ana gobe zasu bar Nigeria Badiyyah ta zo gidan yi masu sallama, Ammi taji dadin yanda ta ganta, tun ma lokacin sunan twins, don kana ganinta kasan tana cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, ga dai shi tana da kishiya kuma gida daya suke, Ammi tace "Inji dai kina girmama abokiyar zamanki Badiyyah don naga matar na da hankali" Badiyyah na murmushi tace "Lafiya lau muke zaune Ammi, bata da matsala kwata kwata, na dauketa kamar yayata ne, yaranta ma duk suna girmama ni, duk da ta aurar da biyu, ni ce ma na yaye yaron first daughter dinta sai jiya na maida sa gun Mamansa" Ammi tace "To maa sha Allah, haka ake so ai, Allah ya ci gaba da hada kan ku...." Badiyyah tace "Ameen" nan Badiyyah ke ma Ammi da Mayraah gaisuwan Haseenah, Mayraah kasa cewa komai tayi tana kallon Badiyyah with shock, Ammi da ita ma sai da ta girgiza tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Haseenah ta rasu? a ina kika samu labarin nan Badiyyah?" Badiyyah tace "Cousin sis dinta naga ta dorata a status shekaranjiya, sai kuma naga wata kawarta ma ta dorata a facebook, ai ban san baku sani ba wallahi..." Ammi tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shekaranjiya kenan ta rasu, toh Allah Ubangiji ya ji kanta ya gafarta mata, rashin lafiya tayi ne?" Badiyyah tace "Ameen, nima haka na tambayi kawarta sai take ce min ai tunda tayi accident shikenan ta rasa lafiyarta kullum ana hanyar asibiti da ita, har Allah ya mata cikawa shekaranjiya" Ammi ta sauke ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace "To Allah ya gafarta mata, zan kira mahaifiyarta in mata gaisuwa kuwa don ina da numberta, Maheer ma ina jin bai sani ba da zai gaya mana, shi ma zan ce ya kira uwar yayi mata gaisuwa" Sosai jikin Mayraah yayi sanyi, a hankali tace "Allah Ubangiji yayi mata rahama, ya yafe mata kurakuren ta" Ammi da Badiyyah suka ce "Ameen" Badiyyah na kallon Ammi tace "Ammi kuna waya da Mama Ladi kuwa?" Ammi tayi dariya tace "To ko daxu da safe sai da muka yi video call da ita, ai in gaya maki Mama Ladi na can ta zama wata bukekiya tayi fresh abun ta, da Glasses ma take yawo yanzu" Badiyyah ta zaro ido tana dariya tace "To ya take operating Babban wayar?" Ammi tace "Kinsan Mama Ladi bata da duhun kai, wai ɗan mijin nata ke nuna mata yanda zata dinga amfani da wayar kan kace me har ta haddace, bini bini kya ga ta doka maka Video call, ta ce min ma jiya suka dawo daga New york da me gidan nata" Dariya Badiyyah ta dinga yi tace "Haka tace New york?" Ammi na dariya ita ma tace "Yu york tace min, ni kuma na fahimci me take nufi...." Sai da Mayraah tayi dariyar da bata yi niyya ba don tun da taji mutuwar Haeeenah jikinta ya mutu, Badiyyah ta dinga dariya Ammi na taya ta. Maheer da Mayraah sun bar Nigeria zuwa US da sati uku Eeman ta haifo yan biyunta kyawawa duk mata, kwana biyu ne tsakaninsu da Ihsaan da ta haifi santalelen ɗan ta namiji a Canada, labari na zuwa ma Mama Ladi cewar Ihsaan din Mendi ta haihu tace ma Attajirin me gidanta Alhaji Ahmadu a samar mata Bisan Canada, ai ko aka fara mata processing cikin gaggawa.....



*Littafin Mayraah na kudi ne ba free book ba, ayi kokari a sauke min hakkina don da ni da ku bamu san gobe ba.*

07087865788

Drop 8 concrete lessons of the book Mayraah, the best goes home with 10k
Drop via 07087865788

_ALHAMDULILLAH a nan na sauke littafin *MAYRAAH* darussan dake ciki Allah Ubangiji ya sa mu amfana da su, kura kuren ciki kuma Allah ya yafe mana..... I am thanking my fans Wholeheartedly for being patient with me from the beginning of the book Mayraah to the end, nasan kun min kokari sosai..._

Na kuma sadaukar ga littafin *MAYRAAH* zuwa ga Lovely Mom dina Hajiya Hajara with her ɗan auta Umar Farouk (Papi) 🥰 Allah Ubangiji ya dafa maki, ya jibanci lamarinki, ya raya maki mu cikin aminci.....
*Ya Allah ya Ubangiji kaji ƙan Abbana kayi masa rahama, ka Kyautata makwancinsa, ka yafe masa kurakuransa tare da duk sauran musulman da suka riga mu gidan gaskiya, ya Allah ka kyautata namu zuwan bayan nasu*😓


My special greetings goes to you Oga Barrister, thanks for always borrowing me little of ur time to do what makes me happy, Allah Ubangiji ya ci gaba da kara mana hakurin zama da juna,😂 Allah ya kara maka budi Ameen.


*To all Readers of Mayraah, thanks soooo much for patronizing me, Allah Ubangiji ya maku albarka ya raya maku zuri'a, marasa aure kuma Allah ya kawo babban rabo, Allah ya sa kafin karshen shekaran nan za ku aiko mana da cingam din sa rana...* 😁
********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 09017242889


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************


Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login