Mayrah

Chapter 150 of 152

in sha Allah u will get better very soon" Ta fashe masa da kuka sosai tace "Saboda ba kai kake wahala ba ko?" bude kofar dakin aka yi ya juya da sauri, Ammi ce ta shigo dakin da cup din kunu, every few minutes take shiga dakin to check on Mayraah, Maheer ya mike tsaye Ammi tace "Idonta biyu ne?" Ba tare da ya kalli Ammi ba yace "Eh" Ammi ta karasa kusa da ita, shi kuma ya juya ya fita daga dakin. Wajen karfe goma na dare Mama Ladi ta lallaba ta sauka downstairs zata je kitchen ta hado shayi ta tafi dakinta ta sha, tana bude kofar kitchen din ta ga Usman tsaye at the far end of the kitchen kusa da store yana facing din Eeman da ta makale jikin bango taki hada ido da shi tana wasa da yatsunta kana ganinta kasan she is uncomfortable a wajen, Usman ya juya ya kalli Mama Ladi sai kuma ya dauke kansa yana kallon Eeman da kanta ke kasa, Mama Ladi dai tace "Dama ni ruwa na sauko dauka kada in je cikin dare kishin ruwa ya hanani sukuni, ita kuma Ammi na can yaro ya hanata zaman lafiya, duk wani wahala in aka tarkato ita ake dora ma, ga renon me laulayi ga renon jariri" Tana fadin haka ta dau ruwanta ta fita daga kitchen din, direct bangaren Ammi ta nufa, Ammi na goye da Aryaan dake kuka, duk kwanan nan ya koyi kuka abinda bai da shi, Mama Ladi ta ajiye goran ruwan hannunta tace "Yanzu dai yaushe naji ance za a kai Eemani katsina?" Ammi ta zauna kan kujera bayan ta sauke Aryaan zata kara basa abinci tace "Zuwa gobe in sha Allah" Mama Ladi tace "Wa zai kai ta katsinan?" Ammi tace "Maheer ne zai kai ta, amma za su tsaya kano don tare da Mariya za su tafi katsinan" Mama Ladi tace "To gwara dai haka, kar aje ayi aika aika a gidan nan mu shiga uku mu lalace" Ammi ta dinga kallon Mama Ladi alamar bata gane abinda take nufi ba, Mama Ladi tace "Atoh, tunda ni dai nasan me na gani" Mikewa tayi ta dau goran ruwan da ta dauko tace "Yau wai saura kwana nawa ne bikin ma?" Ammi tace "Wata daya in Allah ya yarda" Mama Ladi tace "Toh Allah dai ya kai mu da lafiya, shegu ba dai sun ga yaran sun samu daukaka ba tun ba aje ko ina ba, shi yasa suke son su lallaba su jawo su jikinsu ta yanda su ma za su dinga cin arziki, har da wani cewa a katsina za ayi biki a kai masu yarinyar, basu son duk mazajen yaran ba kanwan lasa bane, shi Mendi dama ba da uban kowa yake dariya ba, ba kuma ko wani shege yake sakar ma fuska ba, sabgar gabansa kawai yake, ni da farko ma na zata soja ne sai kuma daga baya naji ana kiransa likita, wani sa'in kuma ace masa Daddy, shi kuma mijin dayar dama suna kawo masa wargi zai lafta masu sammaci ba mutunci garesa ba, sam bai daukar nansense, mu kan mu ya muka kare da shi balle ace su kawo masa iskanci a gidansa, ai tijara ma zai masu, ba gwara Mendi ba ma a kansa, Mendi sai yayi dariya sau uku shi wnn bai yi sau daya ba, ai Usuman ba kyau, shi sa na kama kaina bana barin komai ya hadamu tunda ya zageni haihuwar wannan yaro a asibiti, ita kanta Eemanin naga a tsorace take da shi yanzu ta dena shige masa kamar da, mu dai Allah ya nuna mana ranan auren lafiya kawai" Ammi tace "Ameen" Mama Ladi tace "Sai kuma magana ta karshe, tun kan a fara biki a gidan nan saboda bakin mutane gwara a nemar ma Mera er dattijuwa su koma can gidanta dattijuwar ta dinga yi mata komai, bakin jama'a masu zuwa biki nake gudu, wani sam bakinsa bai da kyau, kowa ya ganta kwance shame shame yasan laulayin ciki take kuma an san ko wata shidda yaronta bai karasa ba, don haka gwara ta tattara su koma gidanta sai a bar mana ɗan kawai, bayan biki in ma za a dawo da ita nan din ne sai a dawo da ita, Mama Ladi na kai wa nan ta fita daga parlon. Washegari da safe Ammi ta shigo dakin Mama Ladi dake linke kayanta da Bilkisu ta wanke mata da hannu don tace bata son washing machine kar kayanta su kode, a nutse take linkin kayan sai ka rantse iron din su tayi, bata barin kowa ya mata linkin kayanta, daga kasa kuma ga tray din breakfast din da ta gama, don sai da taci tayi nak ta fara linkin, Ammi ta zauna tana kallonta tace "Sannu da aiki Mama" Mama Ladi tace "Yauwa, ina jikan naki?" Ammi tace "Yana kasa gun Bilkisu" Mama Ladi tace "Dama ita za a bar ma renonsa ranan bikin Usuman ta yanda zaki tarbi baƙin ki cikin nutsuwa ki basu kulawan da ya kamata, baza mu bi ta tasa ba ranan don naga wani sabon rigima ya koya yanzu, da har ina cewa yaro shiru shiru kamar ubansa sbda hakuri ga kuma fara'a, ko da yake cutarsa aka yi aka rabasa da Mama ko wata shidda bai yi ba kinga baza mu ga lefinsa ba gaskiya" Ammi dai murmushi kawai take, bayan few seconds tace "Mama Alhaji Saminu ne ya kira Abba jiya ya bada sako wai a sanar maki" Mama Ladi ta ajiye zanin hannunta tace "Sakon me kuma?" Ita dai Ammi bata dena murmushin da take ba, Mama Ladi ta nemi waje ta zauna tace "To ina ji sakon menene? Kudi ya bada a bani?" Ammi ta girgiza kai tace "Aa ba kudi bane Mama" Mama Ladi tace "Toh menene?"

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah
Ur evidence via 07087865788

143
Shirye shiryen bikin Usman da Eeman kawai ake a gidan Abba, duk da tun bikin na sauran wata daya Eeman ta koma katsina, kamar yanda Mama Ladi ta ba Ammi shawara haka nan aka yi Mayraah ta koma gidanta tare da sabuwar mai aikinta da aka daukar mata don kula da ita, ita kanta Mayraah taji ta ma fi son ta koma gidanta don sam bata son hayaniya, shima Maheer hakan ya masa saboda lkcn cikin Aryaan duk bata wani samu kulawarsa ba don kasa zuwa gidan yake, yanzu kam he will take good care of his wife fully, Ammi kuma ta ci gaba da kula da Aryaan da taimakon Bilkisu, tuni Aryaan ya warware ya maida jikinsa, a sati yake shanye gwangwanin madarar sa wanda Usman ke siya masa, ana saura wasu yan kwanaki bikin Mama Ladi suka tafi kai lefen Eeman can Katsina gun dangin mahaifinta, kaya na gani na fada aka yi ma Eeman kamar dai yanda aka ma Twin sister dinta, Mama Ladi suna dawowa daga kai lefen Ammi ta shigo dakinta ta sameta tana murmushi, ta ajiye mata abincin da ta kawo mata tace "Sannu Mama, ya gajiyan hanya?" Mama Ladi ta rike haɓa tace "Huhuhu, ashe dai matsiyata ne dangin uban nasu, in gaya maki wallahi wasu yaku bayi muka kai ma lefen dai, yarkace yarkace da su haka nan dai muka mika masu lefen, ke kinga ɗan kuturin gidan da muka kai lefen ma kuwa? Ni dai wallahi jikina sanyi yayi, ko ruwa na kasa sha a gidan, sai yanzu na fahimci me yasa suka danne gadon marayun bayan rasuwan ubansu suka handame, kuma dai gashi ban ga sun yi abun kirki da gadon ba tunda har yau suna nan a tsiyace kamar en iska, Allah dai yaji ƙan Amina duk da mugun halinsu da talaucin da suke fama da shi bata taɓa nisanta yaran da su ba, don kinga ai suna can katsinan ma tayi hatsari ta rasu, mata me son zumunci, Allah dai yaji ƙan ta, ya gafarta mata, in sha Allahu marayun nan da ta bari sai sun samu daukaka ta yanda duk bama zato a duniya, sam bana jin Mendi, saura mana kawai mu zaunar da Usuman mu kulle kofa mu sake jaddada masa hukuncin wanda ya cuci maraya ko ya walakanta sa, don ko Eemani marainiya ce gaba da baya, in yaci amanarta to Allah zai saka mata tun a gidan duniya ya daidai ce, kawai abinda ya rage mana kenan mu yi don ni dai a tsorace nake da Usuman" Ammi dai sai kallon Mama Ladi take, Mama Ladi tace "Allah kuma ya basu zaman lafiya da zuri'a dayyaba ya dora su kan mazajen nasu, ita kuma Mera Allah Ubangiji ya sauketa lafiya" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Ameen" Har aka gama bikin Eeman aka watse Mayraah bata san me ake ciki ba tana fama da kanta, ashe laulayin Aryaan ya zo mata da sauki bata sani ba, don wannan kam ji take kamar bazata yi rai ba, ta rasa ina zata sa kanta taji dadi, roban drip kuwa ta sha yafi a kirga, ga mai aikin da aka daukar mata mai hankali da nutsuwa, don sosai take kula da ita kamar er ta, bini bini zata shigo dakin ko da wani abu da zata yi mata, wani lkcn har ta zauna dakin tana ɗan mata hira wai kar kadaici yayi mata yawa, bayan biki da kwana biyu, wajen la'asar Aisha mai aikinta ta shigo dakin ta duka gabanta tace "Hajiya kin yi baƙi suna parlor" Mayraah ta bude ido da kyar tana kallonta amma ta kasa tambayarta waye don ko magana bata so, Aisha da tasan bata fiye son magana ba tace "Wannan tsohuwar da ta zo kwanakin baya ce, ita da wata bakuwar" Mayraah ta riga ta gane Mama Ladi ce ta zo, don kafin biki ta zo gidan dubata ita da Omar har sau biyu, Mayraah ta mike zaune da kyar ta dau hijab dinta ta saka, tun da ta fito parlon Aunty Mariya ke kallonta cike da tausayinta ganin wani mugun raman da tayi, Mama Ladi tace "Ai kuma shikenan, ciki dai sai kace na jaraba Allah na tuba, kina haife masa wannan dama maza kiyi ta kanki kiyi tsarin iyali, wannan wahala har ina haka?" Mayraah ta zauna kan kujera Aunty Mariya na mata sannu, Mama Ladi tace "Ko da yake ita ma uwar taku haka tayi ta wahala duk ciki sai tayi wata biyar a kwance ni da Hajja ke mata wahala, to gashi kin biyo kafarta dai, cikin Umar ma duk mun zata mutuwa zata yi" Mayraah dai tun da ta gaishesu a parlon bata sake cewa komai ba kanta a kasa, Aunty Mariya ta kalli Mama Ladi tace "Tunda an watse biki lafiya ba gwara ta koma can gidan ba Mama?" Mama Ladi tace "Wani gida? Kema dai da taya bera bari kike Mariya, ba fa cikin farko bane wannan, kuma da Ammin bata kusa da ita fa? Iya renon ma da aka bar ta da shi na jaririn yaron nan ai ya isa haka, shikenan sai sun sa baiwar Allahn ta tsufa saboda wahala hankalinsu zai kwanta, ai kamata yayi yanzu ace Ammi ta samu hutu kuma ai, ta gama bautan yaranta ta dawo kan jikoki kuma" Aunty Mariya dai bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Nan da yan watanni zata dawo dai dai, tunda ga mai aikinta na kula da ita kawai tayi zamanta a gidan mijinta da ya dora mata wahalan....." Ita dai Mayraah ta jinginar da kanta da kujera don har ta gaji da zaman, kwanciya kawai take son yi, ko minti talatin su Aunty Mariya basu yi da shigowa gidan ba Ihsaan ta shigo parlon da sallama, Mama Ladi ta daga kai tana kallonta tace "Ke kuma ba yau aka ce jirgin naku zai tashi ba? Ko kun fasa tafiyar ne" Ihsaan na ɗan murmushi ta ajiye ledan hannunta tace "Sai karfe takwas in sha Allah" Mama Ladi ta kalli agogo tace "Atoh da sauran lokaci" Ihsaan ta zauna kan carpet ta fara gaida su Mama Ladi sannan ta kalli Mayraah dake kallonta ta gaisheta, murmushi kawai Mayraah tayi mata ta gyada mata kai, Ihsaan tace "Ya jikin Aunty?" A hankali Mayraah tace "Alhamdulillah" Mama Ladi tace "Bikin er uwarta ta zo tun bikin bai karaso ba, kilan shi ne mijin zai ce ta zo ta duba ki kafin su koma kasar ta su" Mama Ladi ta kalli Ihsaan tace "To ina Mendin?" Ihsaan ta sauke kanta tace "Yana cikin mota" Mama Ladi tace "Toh me ya hanasa shigowa? Ba gidan er sa bace?" Ihsaan na murmushi tace "Yace in gaisheta da jiki" Mama Ladi tace "Aa, je ki ce masa Ladi tace ya shigo" Ihsaan ta mike ta fita daga parlon, Mayraah ta wani daure fuska tana kallon Mama Ladi, ba a dau lokaci ba Ihsaan ta dawo parlon ta zauna kasan carpet, bayan some minutes sai ga MD ya shigo parlon da sallama, Mayraah dai ta sunkuyar da kanta, ya zauna suka gaisa da Aunty Mariya da Mama Ladi, Mama Ladi tace "Ai in kai ma ka shigo duba jikin nata zata ji dadi tunda kai ubanta ne Mendi, kasan kowa da yanda laulayin ke zuwa masa ita kam tana jin jiki, sai dai mu ce Allah Ubangiji ya bata lafiya" Mayraah dai kanta na kasa tana wasa da hijab din jikinta, MD na kallonta yace "How are you feeling Mayraah?" Da kyar tace "Alhamdulillah, ina yini?" Yace "Lafiya lau, Allah ya sauwake, gradually u will get better in sha Allah" Kai kawai ta gyada masa, Mama Ladi tace "Ga ɗan nasu na fari ma sai yanzu yayi wata shidda, ni ko nace dama ma'aikatan lafiya na yarda su yi gwarne? naga shi likita ita Nas amma kuma ace anyi gwarne saboda Allah" Aunty Mariya ta dinga kallon Mama Ladi rai bace, MD dai murmushi kawai yayi yace "To Mama ai duk yanda Allah ya tsara hakan ne zai faru ko" Mama Ladi tace "Sai dai haka kuma, to Allah ya raba lafiya dai" Mikewa MD yayi yana masu sallama, ya ajiye ma Mama Ladi 50k yace "Naga ke da Aunty a kaduna ku ke, sai ku yi kudin mota" Mama Ladi tace "Toh Allah ya maka albarka Mendi, Allah Ubangiji yasa ka fi wan ubanka wato Alhaji Saminu, Allah ya daukaka mana kai Mendi" Yana murmushi ya kalli Mayraah yace "Allah ya kara lafiya Mayraah" Sai a sannan ta daga kai ta kallesa ta ɗan yi murmushi ta gyada masa kai, MD yayi ma Aunty Mariya ma sallama sannan ya fita daga parlon, Ihsaan ta dau abun da suka siya ma Mayraah ta kai gabanta ta durkusa ta ajiye tana kallonta tace "Allah ya baki lafiya Aunty" Mayraah na mata murmushi a hankali tace "Ameen Ihsaan, Allah ya kiyaye hanya" Ihsaan tace "Ameen" Daga haka ta mike tayi ma su Mama Ladi ma sallama sannan ta fita daga parlon ta bi bayansa, Mama Ladi ta fara matsar kwalla tace "Duk sun yi dacen mazaje wallahi, yanzu ki ga yanda yake kula da yarinyar nan ta dawo kamar ba ita ba, ta zama wata er gayu, kuma sanin er yarinya ce kinga ai har yanzu bai yarda tayi ciki ba sai ya gama renonta yanda ya kamata, ita kanta Eemani muna kyautata zaton Usuman zai zame mata uwa da uba a duniya, amma fa zance na gaskiya duk Mera ta fi su dacen miji, don a nan duniya dai kafin a samu me hali sak na Mashir to sai an tona wllhi, Mashir ba sa wa, ba hanawa, ga gudun bacin rai, ga kunya, ga kawaici, ga biyayya, ita kanta Ammin ace yau ta rasa Mashir Al-qur'an sai tayi karamin hauka...." Mayraah ta dinga wa Mama Ladi wani kallo jin furucinta na karshe, ita kanta Aunty Mariya wani kallon take ma Mama Ladi, Mama Ladi ta sauke ajiyar zuciya tace "Allah dai yayi masa albarka, ya basa 'ya yan da za su masa biyayya yanda yake mana, tun yanzu Aryaan din nan na lura hakuri ke garesa kamar ubansa, da wuya kaga yayi kuka in ba ko bai da lafiya ba, shi yasa yaron ya shiga raina wallahi..." Babu dae wanda ya tanka Mama Ladi a parlon. Mama Ladi ce zaune parlon Ammi tayi kicin kicin da fuska kamar bata taɓa dariya ba, Aunty Mariya na gefenta zaune a parlon, Ammi kuma na goye da Aryaan dake bacci a bayanta, rai bace Mama Ladi tace "Tun a sannan fa nace a bar wannan batu ni babu ruwana, meye kuma yanzu za a sake tado min da wannan zance fisabilillahi idan ba neman magana ba" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Banda abun ki Mama tunda ance yau zai zo ai da kin jira ya iso in bai maki ba sai a san abun yi kuma, ai dama ba ace lallai dole ba" Aunty Mariya tace "Wallahi haka na gaya mata kafin ki shigo Ammi" Mama Ladi tace "To wai akan wani dalili ma zai zo min tukun? In fa yayi gigin zuwa inda nake zan daddana masa ashar wallahi tallahi, Da girmana a kawo min wani batu na aure banda rashin tsoron Allah, da fa na haihu da ina da jika kamar Meran ki yanzu, a bar ganina ina da kyan jiki ayi zaton shekarata hamsin a duniya, shi kuma Alhaji Saminun kaf danginsa ya rasa warce zai hada da abokin nasa sai ni Ladi? Wato ga Ladi er iska ga Ladi er kauye tunda nace masa a karaye nake, In kin bibiya fa irin abokan nan ne tun na kuruciya wa enda aka yi wasan ƙasa tare, shi Alhaji Saminu sai Allah ya daukaka sa a cikinsu yayi kudi su kuma suna nan da talauci amma suna makale da shi suna maula, to fa ina ga shine a cikinsu wani shegen zai ce ai aure yake so amma bashi da halin yi bai da ko sisi, ni kuma gani er kauye sai in fado ran Alhaji Saminu sai yaga bari kawai ya hadani da shi mu karata, banda haka ai kaf abokansa da suke harkokin arziki tare

Download complete TXT · Novel page