Showing 180001 words to 183000 words out of 452169 words

Chapter 61 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

din, ko da ta iso parking space bayan ta mika masa laptop din yace "Ina za ki yanzu?" A takaice tace "Gida" yace "It's late ki ce zaki kama hanyar suleja yanzu, so kawai gidan Ummi....." Katse sa tayi da sauri tace "Aa ni bazan je ba gaskkya" yace "Saboda me?" Tace "Gidansu matarka ce fa" Yace "It's nothing, nace maki nima gidanmu ne, matata tasan wanene ni, ko dazu da muka yi waya da Ummi ta tambayeni ke, i told her anjima zaki je can cause nasan baki da inda zaki zauna nan Abuja yau din ma" it took more than 10 minutes kafin Dr Khalil yayi convincing Mayraah ya kai ta gidan surkarsa, duk jikinta a sanyaye ta shiga gidan kamar munafuka shi ko dama yana ajiyeta ya juya, Ummi na parlor da sister dinta Rabi'ah warce ita ma ranan ta zo, Mayraah ta zauna kasa ta gaida Ummi, Ummi ta amsa da fara'a tace "Ya aikin?" Mayraah tace "Alhamdulillah" Ummi tace "To maa sha Allah, yace min har yanzu baki samu wajen ba ko?" Mayraah ta gyada mata kai, Ummi tace "To in kin ga babu damuwa kiyi zamanki a nan mana sai ki dinga komawa gida weekend, ni dama da yace wai gida kike nema ki zauna hakan bai min ba kina 'ya mace, dama hostel ne cikin makaranta da sauki wannan, amma gida kam bai kamace ki ba" Mayraah dai kanta na kasa, Ummi tace "Sai ki ma iyayen naki bayani in sun gamsu ba wani takura sai ki zauna nan abun ki kina zuwa aikin ki, abinda in kin fita tun safe sai karfe shidda, weekend kuma sai ki je masu gida tun da naga Auxiliary nurses basu fiye aiki weekends a asibitin ba" Mayraah ta daga kai tace "Toh Nagode sosai, Allah ya saka da Alkhairi" Ummi tace "Ameen sai ki shiga kitchen ki debi abinci" Mayraah tace "Toh, nagode" Mikewa tayi ta nufi dakin da aka sauketa, Rabi'ah da ta bi ta da kallo tace "Ummi wacece?" Ummi tace "Bakuwa ce" Daga haka ta mike tace "Bari in je lokacin sallah yayi" Mayraah ta kai minti sha biyar tana nazarin zaman gidan da Ummi tace tayi, anya zata iya kuwa, though taga matar is very kind amma ita sai abun yayi mata wani iri a kai, shi ko tsoro baya jin kar su zargi wani abu ko ayi tunanin budurwarsa ce ita, kauda zancen tayi kawai a ranta daga karshe ta mike ta shiga bandaki. Da daddare Mayraah na daki Ummi ta shigo dakin tace "Ilham zo ki duba magungunan nan da Khalil ya bada aka kawo dazu bai bada prescription ba" Mayraah tace "Toh" Mikewa tayi ta bi bayanta suka fita zuwa wani daki, Wata tsohuwa ce zaune dakin kana ganinta kasan bata da lafiya, Mayraah ta zauna tana kallonta tace "Ina wuni kaka" Tsohuwar bata amsa ba, Ummi tace "Hajiya ba lafiya Ilham, duba magungunan ki ga" Da kyar tsohuwar ta bude baki tace "Kar ki sake sa ni a bakin duniya kice bani da lafiya Zuwaira, na kuma samu lafiyata babu abinda yake damuna yanzu, aniyar kowa ta bi shi" Ummi na kallon Mayraah tace "Ilham in kin bude maganin sai ki bata" Daga haka ta fita daga dakin, Tsohuwar na kallon Mayraah cikin rawan murya tace "Ke kiji rainin wayo, ita da 'ya yanta fa suka sa min guba yau sati uku kenan ina fama jiki yaki dadi, amma duk wanda ya zo sai tace masa Hajiya ba lafiyaa, sai terere take min" Tana kai wa nan ta fashe da kuka, Mayraah dai sai kallonta take ta ma kasa cewa komai, ta karasa buda mata maganin ta mike mata, hannu na rawa ta amsa ta dau cup din ruwa, Mayraah tace "Sannu, amma jikin da sauki ko?" Tsohuwar tace "Ke ba wani sauki, yanzu haka duk jikina ciwo yake er nan, banda yaron nan Halilu ɗan albarka ai da na mutu mushe a dakin nan, wai fa a haka an sa min gubar ban mutu ba sai ki ga ita wannan er figigiyar macen da suke ce ma Mimi tana lekoni tana raye raye da tafe tafe, su kuma yan biyun maza sai su zaga baya suyi ta buga kwallo kan windown dakin wai duk don kar in yi bacci, ke bari kawai abinda suke min a gidan nan wallahi kare bazai ci ba, Allah ya isa kawai, banda mutuwa me tonan asiri" Mayraah dai ta ma rasa me zata ce, Tsohuwar na matse kwallan idonta tace "Ga flask can ki tafi da shi ki dafo min wani ruwan zafin a kitchen ban yarda da wanda ke ciki ba tun dazu nake jiran shigowan Halilu ya dafo min wani ruwan shima shiru shiru gantalallen bai shigo ba yunwa nake ji kamar zan suma, ita ma munafukar me aikin gidan na daina yarda da ita duk bakinsu daya da yan gidan" Mayraah ta mike tace "Toh bari in dafo maki Kaka" Daga haka ta fita daga dakin, Tsohuwar tace "Gwara na kama bare kawai, in ma ta cuceni bazai min ciwo ba kamar na jikina" Mayraah na fitowa Ummi dake parlor da karime tace "Ikon Allah...." Karime ta kyalkyale da dariya tace "Ai kuma shikenan kun ƙulla da Inna tunda har ta yarda ki dafo mata ruwan shayi" Ummi tayi murmushi tace "To Allah shi kyauta, sai ki je ki dafo mata"
Hajja na kishingide bayan isha a parlor tana kallon Badiyyah dake kwance ko sallan la'asar bata yi ba balle Magariba ga isha har anyi, daga gefenta kuma plate din abinci ne da Hajjan ta ajiye mata har ta cinye ta bar mata plate din a wajen, Hajja tace "Ke yanzu fisabilillahi Badiyyah ina ta magana tun dazu kin ki tashi daga kan kujeran nan, ga salloli a kanki, kima je kiyi sallan mana sai ki dawo ki ci gaba da latse latsen wayar Badiyyah" Badiyyah tace "Kai na shiga uku, ke Hajja nace maki bazan yi sallan nan bane da kika dameni haka, ina fa sane, ki bari in gama abinda nake a wayar mana tukun" Hajja tace "Kina jin ai gorin da suka maki ranan babu dadin ji, amma ni ko a jikina tunda nasan ba su suke bada mijin auren ba, ita Ladi dama makwadaiciya duk inda galmi galmi yake nan take makalewa, cabdi ta zo nan tayi min me tasan ni ba me kudi ba, ai in ma ta zo wallahi koran kare zan ma er iskar makwadaiciya, tunda bata da zuciya tayi ta zama gidan Mamudan...." Ko rufe baki Hajja bata yi ba aka tura kofar parlon duk suka daga kai, wasu maza ne su hudu suka shigo parlon, Hajja ta mike zaune a firgice tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una me zan gani haka, daga ina ni Sadiya??" Badiyyah da ta gigice ta mike tsaye ita ma gashi babu daman gudu duk sun zagaye Parlon, Daya daga cikinsu ya sanar da cewa su yan sanda ne ya ciro ID card dinsa yana nuna masu sannan yace "Wata waya muka yi tracking muka gano tana cikin gidan nan" Badiyyah jiki na rawa tana nuna masa wayarta tace "Wallahi waya ta ce wannan ku duba ku ga" Wani ɗan sanda ya daka mata tsawa yace "Kar ki rena mana hankali ke, bayan wayar taki wani wayar ce a gidan nan kuma?" Badiyyah tana zare ido tace "Waya kuma? Sai ɗan karamin wayar kakata fa wllhi" Hajja dai salati kawai take ta kasa zaune ta kasa tsaye ko ina na jikinta na bari, Wani firgitattcen tsawa da police man din yayi ma Badiyyah sai da ta kusa sakin fitsari yace "Idan kika bari muka shiga muka dauko wayar da kan mu to baza ki ji da dadi ba" Nan suka sanar mata sunan wayar har da color din wayar Badiyyah ta hadiye wani abu da kyar ganin babu wasa fuskarsu ga wani har yana kokarin kai mata mari tace "Yana daki bari in dauko maku" Bin ta suka yi har zuwa cikin dakin ta dauko wayar wanda farashinta zai yi miliyan daya da rabi suka amsa a hannunta suka kado ta parlor, Hajja salati take har a sannan tana zaga Parlon babu wanda ya bi ta kanta aka saka Badiyyah dake rusa kuka a gaba suka bar gidan. Abba na zaune parlor tare da Mama Ladi dake cewa "Ni kaina Mamuda wallahi na gaji da koke koken nan da Ammi take ba dare ba rana kan yarinyar nan Mera, ka tambayi su Mashir babu abinda bana gaya mata don dai ta kwantar da hankalinta amma duk a banza, zuwa yanzu ya ci ace ko mutuwa Mera tayi Ammi ta sa ma ranta dangana kuma haka balle er banzan na can in an bibibiya hankalinta kwance tana sabgogin gabanta mu kuma ta bar zuciyoyinmu cikin walagigi, ni da ba don ma kar ku kullaceni ba da sai ince dama ance tsintattciyar mage bata mage, Mera ta nuna cewar lallai da gaske mu ba danginta bane shi yasa ta shiga duniya kanta tsaye ko duba irin kyakkyawan rikon da aka mata na shekara 23 bata yi ba duk ta mance wannan halaccin, to ni ko Allah ya isa na mata sai ya bi ta duk inda take wllhi, kuma haƙƙin Ammi bazai bar ta ba a dubi mugun damuwar da ta jefata ciki fisabilillah, to shine nake son baka shawara Mamuda anya baza ka dau Ammin nan ko Saudia ne ku je ku kwana biyu ba ko Allah zai sa ta samu salama a zuciyarta, ni wallahi tsoro nake kada ciwon zuciya ya kamata tunda dama tana da hawan jininta duk mun sani, kaga ban ma san zaka kawo min maganar ba ina ta son in samu lokaci in zaunar da kai ince maka gaskiya a duba lamarin Ammi ashe kai ma hakan na damunka bawan Allah" Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan Mama, shawaran da kika kawo ma yayi gaskiya, in sha Allah zuwa nan da sati daya sai mu tafi Saudi Arabia kawai" Mama Ladi tace "Yauwaaa Allah maka albarka Mamuda, daga nan sai ku saka er banzan yarinyar a addu'a Allah ya karkato da hankalinta gida, ai gantalin ya isa haka kuma, ni dai kafin ku tafi dama kar ka manta kajin firiji sun kare, er mantinar ma duk Ammi nake juye ma a kofi in zuba mata madaran gwangwani duk sun kare su ma, kasan kuma babu dadi a tafi a bar gida babu isasshen kayan abinci" Bude kofar Parlon aka yi duk suka juya, Hajja ta shigo tana rusa kuka tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mama Ladi ta mike tace "Mun shiga uku mutuwa Badiyyar tayi??" Cikin kuka Hajja tace "Yan sanda ne suka zo suka tafi da ita muna zaune parlor ba laifi ba komai, yaushe rabon ma da ta fita ko nan da gate Marainiyar" Abba da ya mike shi ma yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

MAYRAAH is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

INA MATA MASU AJI, BA ‘YAN RAKIYAR MATA NAKE NEMA BA. SHIN KINA DA LABARIN COMPANY DINNAN NA APHRODISIAC MA’ANA KAYAN MATA WATO *HONEYDROPS* DA KE GARIN *SOKOTO* SUNA DA INGANTATTUN KAYA DA BA SU DA NA BIYU WANDA SUKE DAWO MIKI DA MARTABARKI TA MACE KI DAWO TAMKAR BUDURWA ‘YAR SWEET 16, SUNA DA ZAFAFAN KAYA DA SUKA HA’DA DA *INFECTION FLUSHERS, BREAST FIRMING AND ENLARGEMENT PRODUCTS, HIPS AND BUTTS PRODUCTS, DIFFERENT TYPES OF WETNERS, VARIETIES OF SWEETENERS, VIRGINITY BACK PRODUCTS WATO TIGHTENERS *(MA’ANA AKWAI KALOLIN KAYAN QARIN NI’IMA, QARIN DADI, QARIN DANDANO DA KUMA MATSI NA BAN MAMAKI), SANNAN KAYANMU NA DA HADIN SINADARAN DA KE SAKA MALLAKA DA SOYAYYA A ZUCIYAR MIJI*

KAYANMU SUN HA’DA

*INFECTION FLUSHER*
*ORIGINAL SABAYA*
*ECHOES OF FOREVER*
*MOWA’S SECRET*
*HER ROYAL HIGHNESS*
*ETERNAL FLAME*
*SUGAR QUEEN* DA SAURANSU. KI HANZARTA SAVING LAMBATA KI KUMA YI MIN MAGANA DON SIYE KO SARI KO KUMA KASANCEWA CIKIN MASU SA’AR SAMUN KAYANMU A KYAUTA YAYIN DA MUKA YI GIVEAWAY. ZA A IYA TUNTUBARMU A LAMBOBI KAMAR HAKA 08167888934 KO KUMA 07026039714. KO A SHIGA LINK DOMIN MAGANA DA MU KAI TSAYE wa.me/+23481678888934

*MUNA MARABA DA KU, MUNA GARIN SOKOTO MUNA AIKE KOWANI GARI KOWACCE QASA CIKIN AMINCI*

53
Mama Ladi dake zaune Parlon Ammi ta maida cup din shayin gabanta gefe da sauran bread din da ya rage tana kallon Hajja da ta kasa daina kuka kamar ranta zai fita, ta marairaice tace "Yaya ki sa ma ranki salama don girman Allah, wallahi kukan nan naki ya sa na kasa nutsuwa in ci abinci in koshi duk hankalina ya rabu, tunda Mamuda ya ce zai yi duk iya bakin kokarinsa don ganin an sakota ai kema kinsan zai yi hakan, kwanaki da suka tafi dake ba waya kawai yayi aka sako ki ba ko kin manta ne...." A fusace Hajja tace "Ladi ki shiga hankalinki ki fita harkata kar ki sake cewa za ki min wata magana, ai da er ki ko jikarki aka shigo har gida aka dauke baza ki samu damar hada katon kopin shayi da bredi ki sa a gaba kina ci ba, rayuwa ce fa Ladi, kuma kowa yayi da kyau zai ga da kyau" Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "Ka ji yaya da wata magana dai, sai in ki cin abinci ina jin yunwa saboda yan sanda sun tafi da Badiyyah?? ayi magana fa ta gaskiya domin Allah? Shi ciki ina ruwansa da abinda ke faruwa shi dai ba kawai a fita hakkinsa a sallamesa ba, ita kanta Badiyyar yan sandan baza su bar ta haka ba sai sun bata abinci a celf balle ni da nake gida, kaji fa yaya da wata magana jama'a, shi ciki meye nasa a wannan lamari da za a tauyesa?" Ammi dai dake Parlon zaune sai kallonsu kawai take bata ce komai ba, a fusace Hajja tace "Ga ki ga abinci Ladi... Kiyi ta ci ba komai rayuwa ce" Mama Ladi ta mike ta dauke shayinta da sauran bredi ta nufi dakin Ammi tana cewa "Ji min dai fadan rashin gaskiya kiri kiri wai kar in ba cikina haƙkinsa don an tafi da Badiyyah, a ina aka taɓa haka, ba sai mutum ya ci ya koshi zai samu karfin jajanta lamarin ba, ni dai ba ruwana" Daki ta shige don har Hajja ta bata mata rai, murya can kasa tace "Ina ruwana da wata Badiyyah ma dai tukun, ban da dai neman magana irin na Hajja, Mera ma da bamu san inda take ba bai sa mun hana cikinmu abinci ba balle wata Badiyyah da muka san inda aka kai ta" Ammi na kallon Hajja cikin sanyin murya tace "Kiyi hakuri Hajja, tun da yace zai yi duk yanda zai yi in sha Allah a daren nan za a gama komai ta dawo gida, ki kwantar da hankalinki don Allah" Hajja na kuka tace "Toh Allah ya sa Ammi, Allah ya dubi maraicin yarinyar" Abba na zaune parlonsa Maheer ya shigo ta dalilin kiransa da Abban yayi, ya zauna kan kujera Abba na kallonsa yace "Wayar wani babban mutum fa yarinyar nan taje ta dauka babu batun bail yanzu haka, anya kuwa yarinyar nan kanta daya bata da wani mental problem?" Maheer yayi shiru yana kallon Abba yana jinjina abinda Badiyyah tayi a ransa, Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Gaskiya an ɓata rayuwar yarinyar nan kawai, abun nata sai gaba yake, ya kai har da dauke dauke yanzu take, ko kwana goma ba ayi ba taje gidan matarka tayi mata sata wanda ya kai su ga fada har ta fasa mata kai, yanzu kuma wayar mutane taje ta dauko me tsada aka yi tracking, wannan wace irin rayuwa ce?" a ran Maheer tunani ya shiga yi don ma Abba bai san duk adadin gurmin da ta hada a yan watannin nan ba, iya wanda kawai ake gaya masa ya sani, wanda da zai san har da sa hannunta wajen barin Mayraah gida da ma fasa auren Mayraah da ko bin ta kan case din nan bazai yi ba, dama shi tun da yaji an zo an tafi da ita ko bin ta kan issue din bai yi ba don abinda ya damesa ma ya ishesa, duk inda ma za a kai ta a kaita for all he cares ba kuma abinda zai tofa a lamarin, Abba ya kara sauke ajiyar zuciya yace "Sai dai zuwa gobe da safe kuma mu ga abinda hali zai yi, amma wannan ba karamin case bane gaskiya, don sun ce sai me wayan ya zo yana Abuja, to wa yasan sanda zai zo" Maheer yace "Allah ya kyauta" Abba yace "Ameen" Wayarsa dake ring ya dauka ya ga Hajiya Amina ke kiransa, Maheer ya mike ya fita daga Parlon, this past days kawai karfin hali yake yi, rashin Mayraah ba karamin taɓa sa yake ba, it's weighing him down sosai ba kadan ba, dare daddaya ne baya mafarkinta idan ya kwanta, downstairs ya dawo ya zauna ya jinginar da kansa da kujera ya lumshe ido missing his lil sis, he misses her so badly, ya fi minti sha biyar zaune parlon ya ji muryar Mama Ladi ya bude ido yana kallonta, Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ya ake ciki, inji dai Mamuda bai samesu a wayar ba su yan sandan" Maheer ya gyara zama a hankali yace "Wayar wani babban mutum ta dauke, ba ma batun bail yanzu maganar da ake" Mama Ladi ta gwalo ido tace "Wayar babban mutum? Eh lallai Badiyyah ta shahara sauran kawai ta fara yawo da makamai, nan ko kakar tun dazu ta ishi kunnemu da kuka wai da kyar ba sharri aka laka ma Marainiyar ba ni ko a raina ina ta tunanin anya Hajja ba bakinsu daya da Badiyyah ba kuwa? Da kyar fa in ba ita take kai ma kayan satan ta ajiye mata ba, sannan don girman Allah kai dai ka ja bakinka kayi shiru kar ka wani ce ma kowa ance babu beli wllh hanamu bacci tsohuwar nan zata yi daren yau don gaskiya yanzu haka ma bacci nake ji kada a shiga hakkina akan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login