Showing 192001 words to 195000 words out of 452169 words

Chapter 65 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

idan kuma kace zaka takurani i am leaving Abuja.... i promise u" Da mamaki yake kallonta, can yace "To ke yanzu halaccin da zaki masu kenan? Kika san halin da suke ciki bayan barin ki gida?" Tace "Ba halaccin da zan masu ba kenan, i will never forget their good deeds and they still remain my parents har ko da yaushe, bani da kowa sama da su, kawai dai ina son in bada space ne zuciyar kowa yayi sanyi... Ina son komai ya dawo dai dai a family din, tunda ta dalilina kaga yanda abubuwa marasu dadi suke ta faruwa, i am the caused of everything, tun daga sanda aka fasa aurena abubuwa ke ta faruwa, i am blaming my self for everything" Dr Khalil yayi shiru kamar me nazari, can yace "Ya ma kika ce sunan yayan naki that is a Medical Dr?" Ta wani kallesa tace "I don't think that is necessary" Ya ɗan yi murmushi wanda iyakarsa lips yace "Ohk then, kin samu labarin fitowar result dinku na makaranta?" Ta girgiza kai a hankali tace "Bani da contact din kowa yanzu" Ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan" Bai sake cewa komai ba ita ma haka, and they were silent for almost 3 minutes kowa da tunanin da yake a ransa, A hankali tace "It's getting late, kuma zaka koma Abuja" Gyara zamansa yayi ya sauke ajiyar zuciya yace "Haka ne, amma don Allah ina son kiyi hakuri ki daina dawowa Sulejan nan kwata kwata saboda ke macece bai kamata ki kama gida ke kadai ki dinga rayuwa ciki ba, don't forget everyone is watching u, za a maki fassaran me zaman kanta...." Mayraah ta kallesa tace "How did u find out nan da nake?" Yace "Nace maki tun farko dama ni ban taɓa yarda dake ba ko na second daya, though confidently kike karyanki but facial expression dinki ke exposing dinki, ina me baki shawara next time ki daina karya bai yi fitting dinki ba kuma za a gano ki cikin few minutes...." Ta sunkuyar da kanta, yace "I came here through ur neighbor's Husband, yarinyar da ta rasu kwanaki a hospital, i had to trace the man's number, don ranan da za su zo daukar gawan yarinyar yayi ta kirana ban daga ba ina aiki, sai yayi min text message, so sai da nayi tracing text message dinsa sannan na samu number" Mayraah ta wani hade rai tace "To banda sa ido irin na mutane shine har yace maka ni kadai nake rayuwa a gidan nan?" Yace "Aa bai ce haka ba, ce min yayi according to his wife ke student ce a jami'a, weekend kawai kike dawowa yi a gidan" Mayraah bata sake cewa komai ba, Dr Khalil yace "And lastly yanzu idan na bar nan zan je gidan MD, i will beg him on ur behalf cause dazu bayan tafiyarki ya shigo har office ya sameni, ke da nace kije ki basa hakuri sai kika ki basa kika yi masa kerere a bakin kofa, why Mayraah..." Da sauri ta wani hade rai tace "Ta yaya zan basa hakuri bayan yace in fita daga office dinsa" Dr Khalil ya ɗan yi murmushi yace "Ai yana cewa ki fita baxa ki fita ba zaki fara basa hakurin cikin ladabi, not to just walk out don yace ki fita" Mayraah ta kauda kai, Dr Khalil yace "Ba aikin kike bukata ba sbda ke ba shi ne ma a gabanki ba shi yasa u won't mind ko kin rasa aikin da thousand of people ke nema, but i wont allow that happen sbda bana son ki sake zama Sulejan nan, ban ga alamar an maki tarbiyar da zaki zama me zaman kanta ba" Ita dai bata ce komai ba, yace "Ki shiga gida sai da safe, gobe ki shirya ki taho asibitin" A hankali ta bude motar ta sauka, sai da ya ga shigarta gidan sannan ya bar layin a ransa yana nanata sunan Maheer da ta ambata masa a labarin da ta basa, sai kusan karfe tara saura ya shigo Abuja, yana parking bakin gate din gidan MD wayarsa ya fara ring, yana dubawa yaga Zainab ce, murmushi yayi, yayi silencing wayar don yasan taga bai dawo bane yasa ta kirasa, ya lura da ita duk kwanan nan she is acting insecured akansa, ya gaisa da mai gadin gidan ya shiga, a parlor ya tadda MD with different textbooks a gabansa da laptop, Dr Khalil yace "Mun kusa fara ce maka professor fa mutumin nan" MD ya daga kai ya kallesa, Murmushi khalil yayi ya zauna yana facing dinsa yace "To ya ake ciki?" MD ya rufe laptop din gabansa yace "Next week fa zata shigo, ina ga her plan is to meet the workshop" Dr Khalil ya bude ido yace "Really, i tot kace makarantar da take lecturing za su yi commencing exams" MD yace "To haka dai ta ce min" Dr Khalil yace "Kace akwai ƙura kenan" MD ya daga kafada yace "Ita da Dr Ajay kenan, yaushe rabona da asibitin, ai ta sani" Dr Khalil yace "Lallai kam, MD alfarma na zo nema don Allah" MD ya kallesa, nan da nan ya hade rai yace "Ba dai maganar fitsararriyar yarinyar nan ya kawoka gidana ba" Dr Khalil ya girgiza kai yace "Wallahi kayi misperceiving dinta ne MD, she is so good sannan ta iya aiki" MD ya girgiza kai yace "Ban ga alama ba, wai ba ita bace ta kasa ba ma yarinya common injection ba a ward ranan, sannan muna aiki a theatre tayi contaminating mana equipments, how is she good, don Allah do not spoil my mood Khalil, kai ma kasan bamu da vacancy" Dr Khalil yace "Na sani, shi yasa nace alfarma pls" da mamaki MD yace "To ko dai budurwarka ce yarinyar nan?" Dr Khalil yayi dariya yace "Kai ma kasan daga Madam dita ai babu kari" MD ya ɗan yi tsaki yace "Wallahi i hate dealing with rude human beings, zaka takurani Khalil" Dr Khalil yace "Ka dai yi hakuri don Allah" MD ya kara jan tsaki, bayan few seconds yace "Ina CV dinta?" Khalil ya shafa kansa yace "Za a kawo" MD yace "Till then" Khalil yace "Don Allah kafin su Madam su shigo kasar nan ka bata aikin nan, kasan in suna nan it will be hard wllh" MD yace "Ka ma maida ni ban san abinda nake ba Khalil, ta yaya zan bada aiki babu CV?" Khalil yace "Ko Hafsat ba sai daga baya aka kawo ba, kuma me wuyar dama mutum yayi graduating ko" MD yace "Don Allah lokacin kwanciya na yayi, in dai yarinyar nan ne bazan bata aiki babu takardu ba, apart of takardu sai nayi interviewing dinta, kuma idan naga she is not fit for the job Billah sai dai kayi hakuri bazan bata ba kaji har na rantse, even after the interview idan tayi passing kenan she will be starting as an Enrolled nurse" Khalil yayi shiru yana kallonsa, can a hankali yace "Enrolled nurse kuma MD" MD ya fara tarkata textbooks dinsa da nufin barin parlon, Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Toh shikenan ba matsala, amma a fara interview din tukunna pls" MD yace "Then she should come together with an apology letter in 2 days time, gobe bani da lokacinta haka ma jibi, sai ta bari on Sunday kenan idan Allah ya sa na shiga Asibitin" Yana gama fadin haka yace "I will be going to Bed Khalil" Khalil ya ɗan yi murmushi ya mike yace "To shikenan, thank you sir, Allah ya tashe mu lafiya" Daga haka ya bar parlon. Maheer dake zaune dakin Usman sai kallonsa yake har ya rufe hand luggage dinsa, can Maheer yace "When did u see the debit alert?" Ba tare da Usman ya kallesa ba yace "Not long ago" Maheer yace "To yanzu ina za ka?" Usman yace "I contacted my account officer ya sanar min a Abuja ta cire kudin" Da mugun mamaki Maheer yace "Abuja?" Usman dai bai ce masa komai ba, Maheer yace "Yanzu Abujan zaka tafi da daddaren nan?" Usman yace "Yeah" Maheer yace "But... Ta yaya za ka fara tracing nata a garin Abuja that is wide??" Usman yace "Watch and see, i have been waiting for this day dama" Maheer ya sauke wani boyayyen ajiyar zuciya, tun da Usman ya kirasa ya sanar masa Mayraah ta cire kudi a account dinsa yaji wani kwanciyar hankali ya zo masa don the silence is too much, shirun ne yasa duk hankalinsa ya tashi, but tunda har ta cire kudi ya nuna she is fine and doing well kilan kudin account dinta ya kare kenan, Maheer yace "But ya kamata ka fara zuwa gidan Hajja ka dubata har yanzu she is not saying anything, she is really shock" Usman ya kallesa yace "Wani abu ya faru ne da zan je dubata?" Buda baki Maheer yayi yana kallonsa don sarai yasan abinda ke faruwa duk commotion din nan da aka yi throughout yau yana sane amma yaki tofa nasa, Maheer ya mike ya dafa shoulder dinsa yace "Saboda Ammi zaka yi Usman, ni ma ba don Ammi ba i won't involve my self in this, yanzu haka can zan tafi, kayi hakuri mu je tare" Usman bai ce masa komai ba suka fita gidan a tare. Maheer ne ya fara shiga parlon Hajja da sallama Usman na biye da shi a baya, Hajja na kwance an sa mata drip sai bin kowa take da ido tana numfashi sama sama, Mama Ladi na gefenta sai fifita take mata ta tsuke baki, Ammi da idanuwanta yayi jajir ita ma tana zaune kasa har a sannan bata daina kukan da take ba, Aunty Mariya dai tayi tagumi, Abba ma na zaune parlon don ko minti biyar bai yi da shigowa ba su Maheer suka zo, Maheer ya karasa kusa da Hajja yana dubata, Mama Ladi ta fashe da kuka tace "Mashir ni dai da kawai a tafi asibiti a duba min er uwa da kyau, naga kamar karkacewa bakin nata yake kokarin yi, ita kenan gareni a rayuwar nan fa ka rufa min asiri mu tafi asibiti" Maheer yace "Ko mun je asibitin abin nan da nake shi za a mata, in sha Allah zata samu sauki" Shi dai Usman na tsaye bakin kofa, Abba ya sauke ajiyar zuciya yana kallon Ammi for the first time yace "Ina Badiyyar?" Mama Ladi tace "Er iskar na daki in gaya maka Mamuda, wa ma zai bi ta kanta muna kokarin ceton ran er uwata wallahi ko sanin halin da take ciki bamu yi ba yanzu haka, kawai yanzu tunda zaratan mazan nan sun shigo kamata yayi su risketa a dakin da duka ta fadi uban da yayi mata ciki duk mu ji, tun dazu nake ce ma Ammi da Mariya su shiga su tambayeta cikin waye sun ki hankalinsu na kan lafiyar uwarsu" Abba ya sunkuyar da kai yace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai ga hawaye na sauka idon Hajja, Mama Ladi ta fashe da kuka tana goge mata hawayen da dankwali tace "Tun dazu a haka take, sai dai kawai mu ga hawaye na bin gefen idonta ni dai na shiga uku na lalace Badiyyah ta cucemu" Abba na kallon Maheer yace "Kira min ita" Maheer bai so wannan aiken na Abba ba, don shi kansa tun dazu bai sa Badiyyah a ido ba bai kuma tambayi isilinta ba ya ma zata ta gudu ta bar gidan, amma bai ma Abba musu ba ya mike ya tafi zuwa dakinta, bude kofar yayi ya shiga ya ganta kwance kasa kamar warce ta yi wata uku tana jinya da alama har yanzu ko ruwa bata samu ta kai baki ba, tana ganinsa ta rushe da kuka ta mike zaune da kyar tace "Yaya don girman Allah ka rufa min asiri ka bani magani in cire cikin nan" bata rufe baki ba ya sauke mata lafiyayyen mari yayi ball da ita yace "Ni kike ce ma in baki magani ki cire ciki?" Bude kofar yayi fuskarsa a murtuke yana nuna mata waje yace "Fita ki je ki gaya masu who is responsible kar in kakkarya ki" Jikinta na rawa ta fara rarrafe zuwa bakin kofar don ko tashi bazata iya ba, rakubewa tayi jikin pillar dake corridor din tana kallon mutanen parlon hawaye na sauka idonta, Abba da Mama Ladi sai Usman kawai ke kallonta, don Ammi kauda kai tayi haka ma Aunty Mariya da zuciyarta ke tafarfasa, Mama Ladi na nunata da yatsa tayi mitsi mitsi da ido tace "Allah ya isa tsakaninmu da ke Badiyyah, kaf zuri'a ba a taɓa dauko mana abun kunya ba sai a kanki, Allah ya isa bamu yafe ba, yanzu da wani ido za mu kalli yan ubanmu?" Sai kuma ta rushe da matsanancin kuka tace "Ba don mun zama daya da Mamudan ba shi kansa da wani ido za mu kallesa wannan abun kunya haka a pamily dinmu" Abba na kallon Badiyyah calmly yace "Who is responsible?" Ta kara makalewa jikin pillar tana zazzare ido kamar me nazarin abinda zata ce, Abba ya sake jefo mata tambayar still looking at her, ta daga kai a hankali ta kalli Maheer.

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788
*Wato idan kina neman turaruka masu musulmin kamshi, irin turaren nan da komin bacin rai dole ya narke yabi ruwa🫠 kiji kamar kinyi bargo da gajimare. Toh ki nemi Scentmania_by_sana by sana 07065525409 kawai kice ta baki 'The Empress combo'. Irin turaren dake sa maigida ya nemi shiri cikin gaggawa. In kinason kiyi activating din inner gimbiyarki👸🏽instantly wannan combo din shi ya dace dake.*

57
Maheer ya wani hade rai ya daka mata tsawa yace "Baza ki bude baki kiyi magana ba kina bata ma mutane lokaci" Ta fashe da kuka a hankali tace "Wallahi Haseenah ce ta hada ni da shi ni ban san shi ba" Daga Ammi har Aunty Mariya basu san sanda suka juya da sauri suna kallon Badiyyah ba, Mama Ladi da ta gwalo ido tace "Wacece haka? Sunan fa matar Mashir naji ta kira ko dai kunnena ne jama'a? Sanisa dai da duka muka sani?" Cikin kuka Badiyyah tace "Wallahi ita ce ta hada mu, Malaminta ne shi yake mata aiki a Zaria" Salati Mama Ladi ta saki bayan ta ajiye maficin hannunta tana tafe hannu cikin kidimewa tace "Malaminta kuma?" Maheer kam kallon Badiyya kawai yake babu ko kiftawa kamar yanda Abba da Usman dake tsaye bakin kofa ma suke kallonta, Cikin rawan murya Badiyyah tace "Dama bayan an fasa auren Mayraah nace mata ina son Musharraf din ya dinga kulani, shine ta hadani da malamin wai ya iya aiki, shikenan mu ka fara waya da shi na fara tura masa dubu hamsin sai watarana yace in je Zaria zan amshi wasu turarruka da zan dinga amfani da shi, ni kuma sai nayi ma Hajja karya zan je Bichi sai na tafi Zaria wajensa" Tana kai wa nan ta kara rushewa da kuka, Mama Ladi dake ta zare ido tace "Sai aka yi yaya?" Cikin kuka sosai Badiyyah tace "Wallahi ni ban taɓa iskanci ba Haseenah ce ta hadamu da shi, kuma yace min shi ne ma yayi mata aiki har ta auri Ya Maheer, sannan ya bata asiri da ta kai dakin Ammi wai don Ammi taji ta tsani Mayraah, ita ma kuma ai tana zuwa wajensa a zaria sai da tayi aure ne ta daina zuwa wajen sa" Mikewa Mama Ladi tayi ta dafe gwiwa tana kallon Hajja da hawaye ke sauka ta gefen idonta tace "To Allah ya sa dai kunnuwanki basu samu matsala ba kina jin duk abinda marainiyar ki ke cewa, mu dai sai dai mu ce Allah ya isa lalata mana zuri'a da za ayi da shege, yau ga dai Badiyyah da cikin boka" Sai kuma ta fashe da matsanancin kuka ta rike kanta, Ammi ma kukan take sosai wani bakin ciki da takaici na taso mata a zuciya, ita dai Aunty Mariya shock ya sa ko motsi ta kasa yi a inda take zaune sai kallon Badiyyah take, shi kansa Abba kallon Badiyyah kawai yake ko kiftawa babu, can ya girgiza kai ya mike kawai ya fita daga parlon, Usman ya juya ya bi bayansa, Maheer ya kusa minti biyar tsaye parlon da tunani iri iri a ransa, can ya nufi kofa ya fita shi ma, Ammi ta mike ta bi bayansa da sauri har a sannan tana kukan takaici, tsayawa yayi har ta karaso inda yake cikin rawan murya tace "Yanzu Maheer ta yaya za ayi a cire cikin nan? Ya za mu yi yanzu ya fita Maheer?" Da mamaki Maheer ke kallonta yace "A cire fa kika ce Ammi?" Ta fashe da kuka tace "To me zance Maheer? da wani ido za mu kalli duniya? Wannan abun kunyar har ina Maheer? Badiyyah ta cuce mu, ta cuce mu wllh" Maheer ya girgiza kai yace "Ai in ma wani ya kawo shawaran a cire cikin ke me hanawa ne Ammi" Muryar Mama Ladi suka ji da karfi tana cewa "Ashe baki da kai Ammi? Ina maki kallon me ilimi ashe ba haka bane? Wani cikin za a cire? So kike Allah yayi fushi da kaf zuri'ar mu? Ga laifin zina sannan ga na zubar da ciki, to wallahi babu ruwana sai inyi ta kaina in fita daga zuri'ar nan in shiga duniya kamar yanda Mera tayi, babu zunubin shegiyar da zai shafeni ban ji ba ban gani ba, ai tunda taje ta yo cikin dole sai ta haifesa a ba Hajja ko kuma a baki ku yi raino don nasan Mariya bazata amsa ba, ni ma kuma ba ruwana wallahi, da ana canza ma tuwo suna wallahi a yau din nan da na canza pamily bakina alekum na koma wani pamilyn, yanzu zancen da nake maki wllh kunyan Mamuda nake ji tun dazu na kasa hada ido da shi" Ammi dai kuka take ta kasa cewa komai ta nemi dakali ta zauna, Maheer ya fita daga tsakar gidan kawai, a kofar gida ya tadda Abba tsaye

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login