Showing 189001 words to 192000 words out of 452169 words

Chapter 64 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

wanda bayan shi babu wani office a wajen, tana ta tsaye bakin kofar ta kasa knocking taji an bude kofar ta koma baya da sauri, wani dr ne ya fito ta gaishesa ya amsa da murmushi ya bar mata door din a bude ya wuce, a hankali ta saka kai ta shiga office din that was extra large, it was damn chill ga kamshin freshner da ya hadu da sanyin office din, everywhere was so organize and tidy, ya daga kai yana kallonta don bai san ta shigo ba, sosai gabanta ke faduwa ta kulle masa kofar kafin ta karaso cikin office din a takaice yace "get out and shut d door behind you....." mayraah ta daga kai ta kallesa, lkci daya ta ɗan hade rai ta juya ta fice daga office din ta kulle masa kofar. ko office din dr khalil bata koma ba balle ta gaya masa yanda suka yi, ta sauka downstairs kawai intention dinta tayi wucewarta gida a lkcn don ta riga tayi making din mind dinta bazata sake barin komai ya dameta a rai ba, gwara ta ci gaba da lallaba low bp din da ta samu all of a sudden, she will never allow anything weigh her down cause babu kuma abinda ya rage mata bata gani ba a rayuwar nan, zata tafi inda zata dau jakarta kenan wani dr ya ganta ya kirata zuwa theatre room, duk nurses din reception suka bi ta da kallo wasun su na kyabe baki, mayraah na shiga theatre din taga 2 nurses already a ciki, the theatre is already set for the surgery that was going to start soon, ta saka surgeon gown da hula tayi decontaminating hands dinta ta saka gloves with nosemask, bata dai san surgery din da za ayi ba, but she will just be assisting with surgical instruments don abinda likitan ya nuna mata kenan tun shigowar ta, after few more minutes tana juyawa taga md ya shigo theatre din gabanta yayi mugun faduwa ta dauke kai da sauri don ma dai fuskarta da nosemask, wani dr that will not be part of d surgery yayi assisting dinsa wajen saka protective wears sannan ya fita, md ya wanke hannuwan sa, ita dai bata yarda ta sake dago kai ba tayi facing din instruments dake gabanta. mayraah wished dr salim zata dinga mika ma instruments din gabanta not md, babu yanda ta iya don shine kan surgery din, though su ma da nasu part din da za su yi playing, fatan ta dai bazai gane ita bace duk da bata barin su hada ido take mika amsa duk abinda ya bukata babu ɓata lokaci, after working for long, tsabar yanda ta fara gajiya taje zata maida wani instrument ta dau wani kawai ya fadi a hannunta, da sauri ta durkusa ta dauka ta mayar cikin sauran yan uwansa, ba shi md ba har su kansu doctors dake wajen where took aback da abinda tayi, nan da nan tayi realizing mistake din gabanta ya fadi, maimakon tayi sterilizing wanda ya fadi sai kawai ta hada da sauran equipment din, contaminating them also, dole aka dauko wasu instruments din nan take don ta yi contaminating dinsu kenan, at last dai suka gama operation din successfully aka fitar da patient din zuwa ward, tana ta allah allah ta fita bayan ta cire gown din jikinta da gloves taji husky voice din md dake facing dinta yace "where is ur theatre hygiene?" wani dr ya mata alamar ta sauke nosemask dinta, tayi yanda yace a hankali tana kallon md din ba tare da tace masa komai ba, sai a sannan md yasan ita ce a theatre din, after looking at her from head to toes kawai ya fice daga theatre din zuwa office din dr khalil. maheer ya fito daga office din likita da takarda a hannunsa yana kallon ammi dake zaune da hajja a reception, ga badiyyah rungume jikin hajja tana ta mata sannu, hajja tace "wai ba gado za su bata bane maheer? tana jin jiki fa, nasan ba komai bane illa cizon sauron inda marasu tsoron allah nan suka kai ta" maheer yace "sun ce ba sai an kwantar da ita ba ya rubuta magunguna za a siya" hajja tace "to allurai fa" badiyyah ta marairaice da kyar tace "ni bana son allura" ko kallonta maheer bai yi ba yace "ku tashi mu tafi gida" hajja ta mike ta dago badiyyah, ammi zata riko badiyyan hajja tace "aa bar ta kawai ki ji da kanki tunda kema ba isasshen lafiyar gareki ba" a haka suka fita maheer na biye da su a baya, suna shiga motar hajja tace "gida kawai za ka kai ni, na sa mariya taje ta min share share ta daura girkin da zata kawo mana asibiti ban ma san baza su bamu gado ba" shi dai maheer bai ce komai ba, after 30 mins of driving ya iso gidan hajja yayi parking, hajja ta sauka tare da badiyyah ammi zata sauka yace "ammi we need to talk" ammi ta kallesa sai kuma ta koma motar, tuni hajja ta shige cikin gida da badiyyah tana mata sannu, maheer ya mika ma ammi takardan hannunsa, haka kawai ammi ta ji gabanta ya fadi, ta dinga kallon takardan kafin ta amsa tace "na meye" bata jira cewarsa ba ta fara warware takardan, sai kuma ta kallesa da sauri tace "ka gaya min na meye ni ba ganewa zan yi ba maheer" ya sauke idonsa kasa yace "she is pregnant.... 4 weeks pregnant" ammi da gabanta ya wani yanke ya fadi ta saki takardan ta jingina da kujeran motar tana zaro ido tace "innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ita badiyyar??" maheer dai bai sake cewa komai ba, nan da nan hawaye ya cika idon ammi ta dinga nanata innalillahi wa inna ilaihi raji'un jikinta na ɓari, gaba daya ta rikice a motar sai maganganu take daga karshe ta bude motar ta sauka kawai ta shige gidan hajja cikin tashin hankali, maheer ya ja motarsa ya kara gaba, ammi na shiga parlor ta tarar da hajja rike da badiyyah da ta kirba amai nan tsakar parlorn, hajja sai sannu take mata tana cewa "to nace a kwantar dake ance min ba haka ba, ya zan musu, tun dawowarku zuwa yanzu kinyi amai yafi a kirga gashi cikin babu komai" mama ladi dake zaune parlon sai yamutse fuska take tace "yanzu fisabilillahi ita yarinya ce ma da zata sako amai daga tsaye? ko yaro yaji amai ya san inda zai je yayi" a fusace hajja ta dakatar da mama ladi tace "ban gayyato ki gidana ba ladi? uban me ma ya kawo ki in ba neman magana ba, yaushe rabon da ki tako cikin gidan nan??" ammi ta fashe da matsanancin kukan takaici tace "kin cucemu badiyyah, kin cuce mu...." aunty mariya ta fito kitchen da sauri tace "lafiya ammi? me ke faruwa kuma" ita kanta hajja kasake tayi tana kallon ammi jin furucin da take ma badiyyah, mama ladi ta mike da sauri tace "auzubillahi wani satan ta sake yi kuma?" ammi na kallon aunty mariya cikin tashin hankali duk jikinta na rawa tace "mariya ciki ne da badiyyah har na sati hudu, mariya ki gaya min ta ina za mu fara mariya" wani ihu mama ladi tayi tace "ciki fa kika ce ammi? cikin ɗan mutum ko me?" ko rufe baki mama ladi bata yi ba suka ga hajja ta sulale kasa.
mayraah na fita daga asibitin bayan ta isa bakin titi inda zata je ta samu abun hawa taji wayarta dake jaka na vibrate, ta bude jakar ta ga khalil ne ke kiranta, ƙin dagawa tayi ta mayar da wayar tana duba cash din jakarta taga babu ma cash din sai dubu daya don kusan kullum idan ta fito tana siyan energy drink biyu wani lokacin har uku saboda low bp dinta sannan tana yin transport din komawa gida shi yasa cash din bai dade mata, nan ta hau dube duben atm card dinta bata gani ba a jakar sai na usman kawai, tunanin inda ta jefa nata ta fara yi, ko dai ta bar shi a daki ne can gidan ummi the last time da tayi using dinsa ko kuma ya fadi ne bata sani ba, tunanin faduwan yasa hankalinta ya tashi, ta rasa yanda zata yi gashi yau dama bata yi niyyar komawa gidan ummi ba suleja kawai zata wuce abun ta, can dai da ta gaji da tsayuwa ta ciro atm card din usman tana jujjuyawa tana nazarin tayi amfani da shi ko kar tayi a ranta, wani me adaidaita sahu ta tare tace masa inda zata cire kudi take son ya kai ta, tana shiga bayan sun yi tafiyar like 15 minutes yace "ga wani banki hajiya" ta kalli bank din tace "mu je dai, bana son cire kudi a wnn bankin din" haka yayi ta tafiya da ita suna ta wuce bankuna da dama sai tace su je wani, har dai mai adaidaita sahun ya gaji yace "hajiya kudin ki fa yawa yake, kar mu je muna wallahi tallahi a hanya" mayraah tace "ba damuwa mu je zan baka ko nawa ne" daga karshe dai bayan tafiya me tsayi tace masa ya tsaya, ta sauka tana kallonsa tace "amma zaka yi hakuri in cire kudin in dawo yanzu" ya wani hade rai yana kallonta, can ya kashe napep dinsa ya sauko yanda zai dinga ganinta da kyau yace "ina jira" shiga bank din tayi ta tafi atm machine din, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta saka ta fara cire dubu goma tukun, ai ko ya ciru, bayan nan ta sa 50k shi ma ta cire sannan ta maida atm card din cikin jakarta da sauri ta fito ta dawo gun mai adaidaita sahun ta shiga tace "mu tafi" yace "mu je ina?" tace "inda zan samu motar zuwa suleja zaka kai ni" yace "to bani kudin kawo ki nan da nayi tukun" dubu biyar ta kirga ta basa amma duk ta kagu su bar wajen, yana amsan kudin bayan ya ga nawa ne ya tada adaidaita sahun suka bar wajen, sai kusan magrib mayraah ta iso suleja a gajiye ga yunwa da take ji don har wani juya mata kanta yake, bayan ta sauka a daidaita sahun da ya kawota anguwan nasu don yace bazai shiga layin ba haka ta fara trekking zuwa cikin layin tana tafiya a hankali, tun daga nesa take kallon motar da ta hango anyi parking few houses before her's babu ko kiftawa. Har Mayraah ta isa dai dai inda aka yi parking motar bata daina kallon motar ba, as if tana son tabbatar da motar waye, kasa ci gaba da tafiya tayi zuciyarta na bugawa ganin an bude kofar motar alamar wanda ke ciki zai sauko, idonta na kansa har ya sauko ya kulle motar ya rungume hannu yana kallonta without blinking, ta wani hade rai ta ci gaba da tafiya kamar zata tashi sama, zata wucesa yace "Ilham" a mugun fusace ta juyo tace "Me yasa kake bibiyata? And how did u get here??" Yana kallonta directly yace "Saboda tun daga first day din da Ahmad ya kawo ki hospital baki da lafiya na gano da yawa daga maganganunki karya ne, nasan karya kike tun a sannan, u never called ur people that very night da Ahmad ya baki waya ki kirasu, wasu nambobi daban da kika san basa amfani kika yi dialing, don har yau i have the 2 numbers na karba gun Ahmad kuma ina kira inji a kashe, wacece ke? Why did u chose to say all sort of lies about so many things to me? Take a look at ur self, baki yi kama da warce tasan wani abu wai shi wahala ba a rayuwa, baki yi kama da warce ta fito daga gidan da sai an tara kudin admission kafin ki taho makaranta ba, sannan a ilimin ki da wayewarki bazan yarda cewar baki san anyi terminating admission dinki kika taho Abuja ba, show me the admission list kin ki, wani school ne kin ki fada min, ke da kika tsaya tara kudin makaranta da kyar ta yaya ma za kiyi lodging hotel me tsadan nan, har kiyi ikirarin zaki iya kama gidan dubu dari uku a Abuja, so many unnecessary lies, kin ce sunanki Mayraah kin dawo kince Ilham u think i forgot, and worst of all ke kadai kike zaune gidan da zaki shiga yanzu not with anybody kamar yanda kika yi claiming cewar gidan stepmom dinki ne, har briefing dinki labarin rayuwata nayi duk don ki zama relax and tell me a little about ur self amma kin ki, ban san mission dinki a Abuja ba, amma baki yi kama da warce ta fito daga gidan da ba tarbiya ba, you look decent and well brought up, as a medical Dr na hango depression a idanuwanki, damuwa na daga cikin abinda ke contributing na low bp dinki.... Nayi kokarin ganin kin fara aiki a hospital din ko zai canza maki thinking dinki akan abubuwa da dama da ya shafi rayuwarki amma naga ba haka bane, and kin nuna u are not even after the job, u are not desperate about it, sannan u don't mind being fired, that aside kina da enough cash a tare da ke" Mayraah ta kasa ci gaba da kallonsa nan da nan hawaye ya cika idonta, kasa daurewa tayi ta hade kanta da motar ta fashe da kuka sosai, shi dai kallonta kawai yake, can ya sauke ajiyar zuciya yace "Zan je masallaci, ana kiran sallah, ki shiga ciki kiyi sallah, idan na dawo masallaci i will call u out" Kai kawai ta gyada masa hawaye na sauka idonta ta wuce sa ta karasa gate din gidanta ta ciro makulli a jaka ta bude ta shiga ciki, sai a sannan ya dauke kai daga kallonta ya karasa masallacin da ya ji ana kiran sallah.

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda

Ur evidence via 07087865788

56
Mayraah na zaune kan darduma tun da ta idar da sallan magrib, har sannan ta kasa daina kuka don ya famo mata ciwon da ke cikin zuciyarta, bata taɓa sa wa a rai wai zata zauna ta gaya ma wani anything about her self ba, she just want to be, bata son tana tuna abinda zai dameta, juyawa tayi tana kallon wayarta dake vibrate, can ta jawo ta daga ta kai kunne, Dr Khalil yace "Ina jiran ki" Ta sauke idonta bata ce komai ba ya katse wayar, bayan few minutes ta mike ta linke darduman ta fita waje, tana tafiya a hankali ta karasa har gun motar yana zaune driver seat leaving the door open, hakan ya sa ta zaga ta bude front seat ta shiga ta zauna ba tare da ta kallesa ba tana fidgeting fingers dinta, shi dai kallonta kawai yake, can yace "Mayraah" Ta daga idanuwanta ta kallesa yace "Tell me who u are, me ya kawo ki garin Abuja" Nan da nan hawaye ya cika idonta, yace "Assuming i have any other intention toward u kinsan bazan kai ki gidanmu ba, ko ince gidansu matata, duk abubuwan nan da kika ga nake ta kokarin yi a kanki don bana son kije ki fada wani hali ne ba don komai ba, ni mutum ne me tausayi kowa ya sani so i have no bad intention toward u, don kin gaya min wacece ke iyaka idan naga da inda zan baki shawara sai in baki kuma bazan baki shawaran da zai cuce ki ba, idan kuma taimako ne da bai fi karfina ba sai in maki, trust me Mayraah" Ta goge hawayen dake sauka idonta ta gyada masa kai, a hankali tace "Sunana Mayraah Mahmud..." Ya gyada mata kai yana kallonta, tace "I was born and brought up in kano" Sai kuma ta fashe masa da kuka yace "Kin ga kiyi hakuri, be strong and tell me what u want to tell me" Nan ma kai ta gyada masa tana goge hawayen da ya ki tsaya mata.... Mayraah bata boye masa komai game da rayuwarta ba har zuwa ranan da ta bar garin Kano, she told him every single thing, shi dai Dr Khalil kallonta kawai yake cike da tausayinta, abu biyu kadai ne yaji tausayinta a kai a duk labarin nan da ta basa, na farko wa enda take kallo a matsayin iyaye tun tasowarta bayan shekaru 22 ta gano ba su ne iyayen nata ba, he can't imagine this great disappoinment, na biyu kuma fasa aurenta da aka yi saboda rashin sanin asalinta, shine kawai tausayinta da ya ji amma ita irin upbring din da ta samu ma mutane da yawa dake tare da iyayensu basu samu kwatankwacinsa ba, ta taso cikin gatanta da soyayya ta ko ina, she lived a comfortable life har zuwa sanda calamity din nan yayi befalling dinta, can ya tallabi chin dinsa yace "Mayraah" Ta daga jajayen idonta tana kallonsa yace "Ur story is not enough to leave home, baki ma Abbanki halacci ba, ita ma Ummin baki mata uzuri ba, da kin tuna irin soyayyar da ta maki tun baki san kanki ba na tabbatar babu abinda zai yi motivating dinki ki bar gida, sannan yayyinki maza su ma baki masu halacci ba" Cikin kuka tace "May be u are saying all this because u are not in the shoe, kowa zai dinga gani kamar it's easy but u promise u it's not, it's painful, i tried my best to be fine with them amma daga karshe kawai naga idan na ci gaba da zama zuciyata zata iya bugawa at anytime, i can't stand Ammi not talking to me a gidan bayan ba haka na taso take min ba, at the end su ma yayyin nawa avoiding dina suka fara yi ai, Abba did marry because of me...." Ta kasa ci gaba ta fara wani kukan, Dr Khalil yayi kasa da murya yace "Zaki koma gida Mayraah! dole za ki koma gida" Ta share idonta tana kallonsa tace "Bazan koma ba anytime now,

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login