Showing 198001 words to 201000 words out of 452169 words

Chapter 67 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

tun shekaranjiya fa kike nan ko mutuwa aka yi ya ci ace kin koma dakinki barin ma ga Hajja har ta fara tashi zaune ga kuma shayi tana sha, nima zuwa anjima in sha Allahu zan taho sai Mariya ta zauna tayi jinyar Hajjan da me laulayin can, don gaskiya bazan iya jure ƙarnin aman da Badiyyah take kirba mana ba, in tayi aman ƙarnin har nan malam, to a kan me, ɗa ba ɗan sunna ba ta dinga cutar mu da ƙarni, bazan iya ba wallahi" A karo na farko Hajja ta bude baki a hankali tana girgiza kai tace "A fitar min da ita daga gidana dama jira nake in gama shan shayin inyi magana, a tafi da ita duk inda za aje da ita, in ko ba haka ba in bi Mariya mu tafi kaduna ta sauke ni gidan yahanasu" Tana magana ne hawaye na sauka idonta, Mama Ladi ta saki baki tana kallon Hajja da mamaki, can tace "A fita da ita a kai ta ina Hajja? Ko dai baki gane wa nake nufi ba, Badiyyah fa nake magana, Badiyya guda fa taki" Hajja na gyada kai wani bakin ciki na kara tokare mata makogwaro tace "Ita Ladi, bazata kwanar min a gida yau ba ta tafi duk inda za ta, ni ma kaduna zan tafi gun yahanasu" Ammi tayi kasa da murya tace "To ina za ta Hajja? Da dai kin yi...." Dakatar da ita Hajja tayi cikin rawan murya tace "Wallahi tallahi bazan kwana da Badiyyah gidan nan ba yau kun ji har na rantse, dama ina ta addu'ar in samu karfin yin magana tun jiya Allah bai bani iko ba sai yanzu, to Allah ya isa tsakanina da ita, Allah ya isa, Allah ya isa wannan abun gorin da ta ja min har karshen rayuwata, duk soyayyar da na nuna mata saboda tausayin maraicinta duk jan ta jiki da nayi don kawar mata da maraici a rayuwarta sakayyar da Badiyyah zata min kenan, da haka zata saka min? ta cuce ni, ta ja min abun kunya, ta ja min abun magana, ta ja min abin gorin da har in koma ga mahaliccina...." Kasa ci gaba tayi saboda tarin da ta fara kamar zata shide tana gwalo ido, Mama Ladi tayi saurin mikewa tana kallon Ammi tace "Kin ga tun da tace a fitar mata da ita daga gidan nan bazata kwanar mata ba to gaskiya ki shiga ki temaka mata ta hada kayanta a akwati a dora ta motar Bichi ta tafi wajen dangin ubanta, haka kawai bakin cikinta bazai kashe min yayata ba in shiga uku, maza a fita da ita ba ruwana, ko kuma ni in je in hado mata tsummokaran nata da kaina" Hajja na kuka tana tari tace "Ku fita da ita ko ni in tafi, ku fitar min da ita nace" Mama Ladi ta nufi dakin Badiyyah da gudu tana cewa "Daga wannan tarin fa wani ake zare ran, wallahi ba ruwana Badiyyah ta zo ta tafi kar in rasa yayata" kwance Mama Ladi ta tarar da Badiyyah shame shame a kasa kamar mara galihu, ko bin ta kanta bata yi ba tana toshe hanci ta bude inda kayanta suke ta dinga kwaso su tana zubawa cikin akwatin da ta bude, Badiyyah sai bin ta take da ido tana sauke numfashi a hankali, tun shekaranjiya babu me bi ta kanta a gidan sai Ammi dake ajiye mata kunu a bakin kofar dakinta tayi tafiyarta, ji take kamar mutuwa kawai zata yi, komai ya dena mata dadi a rayuwar, Mama Ladi na gama cusa kayan cikin akwati tana kallonta tace "Tashi ki fita a samar maki adaidaita sahu ki tafi can gun dangin ubanki su yi jinya, mu ba yan iska bane duk ta sunna aka same mu, don haka baza mu yi jinyan cikin shege ba Allah ya tambayemu" Badiyyah ta mike zaune da kyar tashin hankali karara a kan jemammen fuskarta tace "Mama Ladi wallahi basa so na, ko a baya ba jin dadin zaman can garin nake ba don Allah ki rufa min asiri Mama Ladi" Mama Ladi bata sake sauraronta ba ta fito parlor da akwatinta, Ammi na tsaye tana kallon Hajja dake kuka hade da tari ta dage a fitar mata da Badiyyah daga gidan, Mama Ladi tace "To ni dai bani da karfin dagota Ammi ki je ki fito da ita ga akwatin nata na fito da shi, ko shatar adaidaita sahu ne sai a dauko mu biyasa ya kai ta har Bichi" Sai ga Badiyyah ta shigo parlon da rarrafe ta fashe da kuka tace "Don girman Allah Hajja ki ce ma Mama Ladi a bar ni nan bazan iya zaman Bichi ba basa sona ke ma kin sani" Wani rikicewa Hajja tayi ganin Badiyyah ta dinga tari da karfi tana nuna alamar a fitar mata da ita, Dole haka Ammi ta fita da Badiyyah compound don Hajja ta dena ganinta, Mama Ladi ta dauki akwatin Badiyyah ta bi su da shi, Badiyyah ta rike kafar Ammi tana kuka sosai tace "Don Allah Ammi kema kinsan bani da inda zan je, basa sona a Bichi, don Allah ku yi min rai Ammi" Ammi dai na tsaye ta kasa cewa komai, Mama Ladi na ajiye masu akwatin ta koma gun er uwarta Hajja tace "An fitar da ita yanzu za a daura ta a mota ya kai ta Bichin don Allah ki kwantar da hankalinki yaya" Hajja dake ta sauke numfashi da kyar Aunty Mariya na durkushe gabanta ta rike hannayenta biyu, cikin sarkewar murya tace "Mariya ki kai ni wajen yahanasu kawai" Aunty Mariya ta kwantar da murya tace "Hajja yamma yayi mu kama hanyar kaduna yanzu, ki yi hakuri gobe da sassafe sai mu tafi in Allah ya yarda" Mama Ladi ta zauna gefenta tace "Tafiyar yamma babu dadi yaya, gobe da asuba har ni sai mu je Kadunan in hankalinki zai kwanta da haka, idan ya so idan nayi kwana biyu sai in bar ki tare da yahanasun ni in dawo" Kai kawai Hajja ke gyada masu tana sauke numfashi, Ammi dai an bar ta tsaye da Badiyyah da akwatinta a tsakar gida ta rasa yanda zata yi, Aunty Mariya ta kira da wayarta dake hannunta, ba a dau lokaci ba Aunty Mariya ta fito tsakar gidan, ko kallon Badiyyah dake kwance ƙasan compound din tana rusa kuka bata yi ba ta karasa gun Ammi da ta koma gefe tana jiranta, Ammi na kallon Aunty Mariya cike da damuwa tace "Yanzu ya za mu yi Mariya?" Aunty Mariya tace "Ya za mu yi me Ammi?" Ammi tace "To ina za a kai yarinyar nan yanzu?" A takaice Aunty Mariya tace "Aa, ba dangin ubanta na Bichi ba, ko kin manta ne Ammi" nan da nan hawaye ya cika idon Ammi tace "Kar ki manta Mariya yau ace Rukayya na da rai...." Kasa ci gaba tayi saboda kukan da ya taho mata, Aunty Mariya dai tayi shiru nan da nan ita ma hawaye ya cika idonta, cikin rawan murya Ammi tace "Hannunka baya rubewa ka yanke ka yar, ko mun ki ko mun so Badiyyah ta mu ce, er uwar mu ta jini ce ta haifeta gashi bata doron kasa yau ga halin da er ta ke ciki, kuma Allah ya gani mun yi bakin kokarinmu kan Badiyyah, i tried my best Mariya, my children tried their best also, ke za a ce ba a garin kike ba, Amma Allah yasan kokarin da nayi kan Badiyyah" kasa ci gaba Ammi tayi, Aunty Mariya ta goge hawayen idonta tace "Yanzu ya za mu yi yaya?" Ammi na hawaye tace "Wallahi ban sani ba, kin ga tace bata son ganinta ni kuma yanzu ba ɗa bane a gidana, i don't have that power anymore, ban san ko Mahmud zai amince Badiyyah ta koma can ba" Aunty Mariya ta sauke ajiyar zuciya tace "Ni kuma kin san family house nake, bazan dau Badiyyah da ciki in fara kai ta gidana ba ya zame min abun gori gun facalolina da dangin mijina" Ammi na gyada kai tace "Haka ne, kawai yanzu daukarta zan yi mu tafi gida sai in ga yanda za mu yi da Mamuda" Aunty Mariya tayi kasa da murya tace "In har ya nuna bai amince ba ko jayayya kar kiyi da shi Ammi, ki nemi izini kawai ki kai ta Bichi gobe, nima goben za mu tafi da Hajja kadunan tunda tace baxata zauna nan ba, ga Mama Ladi tace za ta bi mu" Ammi tace "Toh shikenan" Aunty Mariya ce ta fita ta samo masu adaidaita sahu, aka saka akwatin Badiyyah a ciki, Ammi ta daure fuska tana kallon Badiyyah dake kwance a kasa tace "Tashi ki fita" Da rarrafe Badiyyah ta karasa gate din ta lallaba ta shiga adaidaita sahun, Aunty Mariya tayi ma Ammi sallama tana tsaye har adaidaita sahun ya juya ya bar layin sannan ta koma cikin gida. Ammi na isa gida dab da magrib ta sauka ta ba me adaidaita sahun kudinsa sannan ta sauko da akwatin Badiyyah ba tare da ta bi ta kanta ba ta shiga cikin gidan, Badiyyah ta sauko da kyar tana biye da ita a baya tana maida numfashi, Ammi taga motar Abba a garage alamar yana nan, Haseenah ce ta fito daga Chalet sanye da Hijab bayan ta leko compound jin an bude gate taga Ammi ce, ta sauka kasa ta karasa gun Ammi tace "Ammi sannu da zuwa" Ko kallonta Ammi bata yi ba tace "Sannu" Zata amshi akwatin hannun Ammi, Ammi ta ki sake mata tace ta bar shi kawai, tun shekaranjiya Haseenah ke gidan bayan an sallameta daga asibiti kamar yanda Abba ya umarce Maheer ya kawo ta gidan don tana ma gidan Badiyyah tayi wannan tonan sililin a parlon Hajja, kamar ance Haseenah ta juya taga Badiyyah ta shigo compound wujiga wujiga duk ta rame tayi baki, nan da nan Haseenah ta hade rai ta kauda kai, Badiyyah dake fama da kanta ko bin ta kan Haseenah bata yi ba ta shige cikin gidan da sauri don kwanciya kawai take son yi ga amai da ke taso mata, Haseenah ta ɗan yi jim, sai kuma ta bi bayansu zuwa main building din gidan ita ma, a parlor ta tadda Badiyyah ta kwanta, Ammi kuma ta haura sama, Lokaci daya ta ga Badiyyah ta mike da gudu ta shige bandakin dake parlor tana kakarin amai, bude baki Haseenah tayi da mamaki bayan ta bi ta da kallo, a hankali tace "Amai kuma??" Can dai ta juya da sauri ta fita daga parlon ta koma Chalet din da take. Ammi tayi shiru tana kallon Abba a sanyaye don maganganu kawai yake cikin fada inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, har ya kai aya, can ta sauke kanta kasa cike da karfin hali tace "Shikenan Yallabai kayi hakuri... kayi hakuri, goben sai in kai ta Bichi idan Allah ya kai mu" A takaice Abba yace "Da dai ya fi don bazata zauna a gidana ba i stand my words" Daga haka ya mike ya shige Bedroom dinsa Ammi ta bi sa da kallo wasu hawaye na sauka idonta, duk ya canza kamar ba shi ba, Abba da ko ɗaga mata murya baya yi idan yana mata magana a baya, abu ko bai masa ba idan tace haka take so to haka nan zai yi don baya son bacin ranta kwata kwata amma yanzu duk babu wannan, duk hakan na neman zama tarihi daga yan watannin nan da suka shude, he is now a changed person, tunanin hakan ya kara breaking heart dinta sosai, ta mike ta fita daga parlonsa ta koma bangarenta ta ci kukanta ta gode Allah.....
Mayraah na kwance dakinta bayan isha Karime ta shigo da sallama tace "Hajiya Ilham ga can kwan na soya maki a kitchen sai ki yanki bredin da zai isheki ki debi ruwan shayi a flask ki bar ma yallabai sauran, ni zan shiga gidan makociyarmu in duba jikin er ta ta kone a kafa, to duk yau ban shiga ba" Mayraah ta gyada mata kai tace "In zan ci zan je in dauka" Karime tace "Toh sai na dawo" Mayraah ta bi ta da kallo sae kuma tace "Amma ba dadewa za ki yi ba ko?" Karime ta juyo tace "Toh akwai dae wani pim din hausa da ake yi duk ranan juma'a, wani lokacin in Ummi ta shiga ta kwanta da wuri na kan je gidan in kalla, kinsan duk an rufe tashoshin gidan nan saboda yan biyun nan maxa da yarinyar nan Mimi da basu son maida hankali su yi karatu sai kallo, to yallabai duk ya rufe tasoshin ba a kallon finafinai a gidan nan, ke baki ga tun da kika zo sae dai ki ga an kamo tashan labarai ba" Mayraah tace "Yanzu dai kallo za ki je yi kenan" Karime ta kyalkyale da dariya tace "Baxan boye maki ba shi zan je inyi gaskiya, karfe goma ake gama pim din, ana gamawa zan dawo in sha Allah" Mayraah tace "Toh... Shikenan, sai kin dawo" Karime tace "Toh kar dai ki bar kwan ya sandare" Daga haka ta fita daga dakin.

59
Mayraah ta sauko daga kan gadon da take kwance bayan tafiyar karime da kusan minti sha biyar, wayarta ta dauko ta bude second sim din da ta kashe tun dazu, ta zauna gefen gado tana ta kallon wayar as if contemplating to call him again or not to, after many minutes of thinking ta ajiye wayar a hankali ta mike ta shiga bandaki, wanka tayi ta fito, tana cikin dauko daya daga dogayen rigunan bacci da ta siya a Suleja cikin jakarta taji wayar ta na vibrate, ta dauko kayan baccin ta mike tana gyara daurin towel din jikinta ta karasa kusa da wayar tana duba me kiranta, sai da gabanta ya fadi ganin number Musharraf, ta zauna gefen gadon a hankali ta dau wayar tana kallo, har ya katse bata daga ba, ya sake kira nan ma bata daga ba har ya gama ringing, sake kira yayi this time around sai ta daga ta kai kunne tayi shiru, daga daya bangaren ta ji yace "Pls who is this?" Ai bata san sanda ta zamo kasa ta zauna ba, she just realized she missed him so very much, ta kasa cewa komai zuciyar ta na bugawa, daga daya bangaren yace "I know u can hear me, pls say something...." Mayraah ta jinginar da kanta da gado a hankali tace "Good evening" Musharraf ya mike tsaye daga zaunen da yake yace "Mayraah" Shiru tayi bata ce komai ba, ya marairaice mata yace "Plss tell me kina ina Mayraah?" A hankali tace "Ina lafiya" Trying all best to be calm yace "I know, yes i know, amma plss ki gaya min inda kike trust me, tell me pls Mayraah, just trust me pls" Lkci daya ya birkice mata, Ta langwabar da kai tace "You don't worry about that" Yace "Nooo pls, Mayraah kin san halin da kika tafi kika bar ni ciki kuwa, not only me, ur brothers, ur parent, haba Mayraah, pls i am begging u ki gaya min inda kike, Baby don't u trust me?" Mayraah ta lumshe ido ta bude tace "I am somewhere far away, kar ka damu tunda ka ga na kira ka i am fine, and i just wanted to say hi...." A hankali yace "Mayraah" bude kofar dakin taji anyi ta juya da sauri taga Ahmad, kallonsa ta dinga yi don duk tunaninta idan ya ga yanayin da take zai fita sai taga ba haka ba, instead he is even walking in, dauke kanta tayi zuciyarta na bugawa tace "I will call you back" Bata jira cewar Musharraf ba ta katse wayar wondering dalilin da zai sa ya shigo mata daki duk da yanayin da ya ganta, she just tied a towel, gefen gadon ta ji alamar ya zauna, lkci daya ta juya ta kallesa tace "I am sorry, i want to dress up" Ya ɗan yi shiru yana kallonta, sai kuma ya buda mata hannu alamar what is there? Kasa motsawa tayi daga inda take zaune with shock amma taki nuna hakan a fuskarta, ko hijab dinta ta kasa yunkurin daukowa don dole sai ta tashi zata yi hakan, banda faduwa babu abinda gabanta yake gaba daya ta rasa wani tunanin zata yi a lokacin, silencing kiran da Musharraf yake ta yi mata tayi ta ajiye wayar a gefenta, kawai gani tayi ya dawo gabanta ya durkusa yana kallon idonta as if counting his words yace "I understand what u are going through Mayraah, Khalil briefed me earlier, it's sad and i get kin fito ne ki samu relieve by chilling away ur worries right? i love ur courage and braveness" Mayraah ta fara matsawa jikin gadon a hankali tana kallonsa babu ko kiftawa, a hankali tace "You are drunk" Buda ido yayi sosai yana gyada mata kai yace "Not much though, but how did u know? Ko kema kina sha ne?" Tayi murmushin da iyakarsa lips tace "Yeah" ya kara buda ido yace "Really?" Ta gyada masa kai tace "I won't mind some" Ya karyar da kai yace "Unfortunately I can't bring that home because of my Ummi, i drink only outside" Sosai gaban Mayraah ya fadi a tunaninta zai ce bari yaje ya dauko mata ne tasan na kwatanci, nan da nan hankalinta ya tashi, yayi kasa da murya holding on to her hand yace "Would u mind us spending the night somewhere...." Ta dake tace "Somewhere like??" Yace "Hotel, club, guess inn... And what have you" Tayi saurin gyada masa kai tace "Ohk, let me get dressed" Yayi kasa da murya yace "Thank you...." Bata yarda ta mike ba a gabansa, gaba daya idonsa na kirjinta, da sauri tace "Can u excuse me in shirya?" Yace "C'mon meye in kin shirya while am here" Daga ta zai yi ta wani fizge hannunta tace "Stop it" Ya mike yace "Ohk then" Jikin window ya koma ya tsaya ya rungume hannunsa yace "Ki shirya" Babu yanda ta

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login