Showing 201001 words to 204000 words out of 452169 words

Chapter 68 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

iya haka ta mike tsaye, wani takaici ya tokare mata wuya, she was trying her best kar ta bari hawaye ya taran mata a ido, daukan kayanta tayi ta shiga bandaki ya bi ta da ido, sai a sannan hawaye ya fara sauka idonta ta jingina da bangon bandakin bayan few minutes ta saka kayan ta fito ta dau Hijab dinta ta saka, ta dau handbag dinta with her charger and phone, duk yana ta bin ta da kallo, without looking at him tace "I am done" har suka fita compound din gidan a motarsa Mayraah bata yarda sun hada ido ba, kamo hannunta yayi yana kallonta yace "or should we go for the hotel we met first?" Ta gyada masa kai kawai, yace "Ohk, but do u have an international passport?" Duk da tana da shi haka ta girgiza masa kai tace "Nop" Da mamaki yace "Why? Big gal kamar ki ace baki da International passport" Ta yi feigning murmushi bata dai ce komai ba, yayi kasa da murya yace "I will get you one if u don't mind, sai a maki visa ko na Uk ne don zaman kasar nan baya wani cire ma mutum damuwa a rai ga sa ido irin na malam bahaushe, u need to be far far away, i think next week zan koma i will try and see if we can make it together" Mayraah tace "Thank you" All through the ride shi yake ta surutunsa, ita kam tayi nisa tunanin da take suna isa hotel din kafin ya shiga ciki ta kallesa tace "Zan ɗan amso abu a mart din can na gaba, wait for me" Yace "Me za ki amso?" Tace "Chewing gum" Yace "Oh ok, bari in amso maki" Ta masa murmushi tace "Ai baka san irin wanda nake so ba" Yace "True" Bude motar tayi ta sauka ta kulle masa tana kallonsa tace "Not every girl that left home is a bitch, not every girl that left home is useless, don kaga na baro gida ba yana nufin ni er iska bace, kuma hakan ba yana nufin bani da tarbiya bane, i chose leaving home because of my mental health..." Tana kai wa nan tayi tafiyarta, sai a sannan wasu hawaye masu zafi suka dinga sauka idonta tana jin zuciyarta na mata zafi, ko waiwayawa bata yi ba har tayi nisa daga hotel din, tana isowa main road ta tare adaidaita sahu ta shiga ta gaya masa inda zai kai ta, har suka iso bata san sun iso ba don tayi nisa tunanin da take ga hawayen da ke ta saukan mata, sai da mai tricycle din yayi alerting dinta sannan ta sauka tana goge idonta ta basa kudinsa, tana shiga gate ta nemi kujera ta zauna, sai da tayi kukanta me isarta sannan ta ciro wayarta, missed calls din Musharraf ta gani ya fi goma, tayi dialing number Dr Khalil yana fara ringing ya daga, gaishesa tayi a hankali, ya amsa yace "Ya kike, ya gida?" Tace "Alhmdlh, are you at work?" Yace "Yeah ina night duty, Why do u ask?" Tace "Aa just want to be sure" Yace "Are you okay?" Wasu hawaye ne suka cika idonta kawai ta katse wayar, mikewa tayi taji ya sake kiranta bata daga ba ta shiga cikin asibitin, sau uku yana kiranta bata daga ba, tana shiga reception ta gaida nurses da ta gani ta haura sama zuwa office dinsa, wata nurse fa'iza ta mike da sauri ta tafi inda jakarta yake ta ciro wayarta ta fara kiran Zainab. Dr khalil na zaune still calling her line ta shiga office din ko knocking bata yi ba, yana ganinta ya mike yana kallonta, bata yarda sun hada ido ba ta zauna kan kujera, ya zagayo yace "Mayraah are you okay?" Bata san sanda ta fashe da kuka ba, ya iso gabanta da mamaki yace "Lafiya? Talk to me, me yake faruwa?" Duk da tambayoyin nan da yake jefo mata hankalinsa kawai ya tafi kan kila Zainab taje ta sameta ne a gida don not long ago ya kira Ummi tace masa tana gidan biki, ganin taki basa amsa sai kuka take ya duka gabanta yace "Plss talk to me Mayraah, an maki wani abun ne?" Bude office din aka yi duk suka juya, MD ne ya shigo, Dr Khalil ya mike yana kallonsa, Mayraah ta kauda kanta da sauri, tunda ya kallesu sau daya bai sake kallonsu ba ya ajiye files din hannunsa yana kallon Khalil yace "See me off" Dr Khalil yace "Ohk" fita yayi office din Dr Khalil na kallon Mayraah yace "I will be back right away" Daga haka ya fita daga office din ta bi sa da kallo tana goge hawayen dake sauka idonta. Dr Khalil na kallon MD bayan sun fita reception yace "Drivern ya iso ne?" MD yace "Ban kirasa ba, just drop me" Dr Khalil yace "Ni fa da na ga kayi dare na zata u will pass the night here MD" MD na mika masa makullin hannunsa yace "Ka taba ganin na kwana asibiti in ba dole ba?" Dr Khalil bai amshi makullin nasa ba yace "Sae dai mu je a motata ka bar naka a nan, tunda zan dawo asibitin" MD yace "Mu tafi a nawa sai ka dawo da shi, bazan iya jira sai kaje sama ka dauko key ba" Yana fadin haka ya bude front seat ya shiga, Dr Khalil ya zaga ya shiga driver seat, sai da suka bar asibitin Dr Khalil yayi dialing number Mayraah, tana dagawa yace "Nan da 30 minutes zan dawo in sha Allah, ki jirani" yana gama fadin haka ya katse wayar, MD dake kallonsa yace "Wato ita wannan mannerless teenager din budurwarka ce shi yasa ka dage sai ta samu aiki a asibitin nan ku jone salon ka daina maida hankali a aikin ka ko, sannan ita wannan er mitsitsiyar yarinyar har yaushe aka haifeta tayi degree? thank God ba aikin za a bata ba, kuma baza a taɓa bata ba as far as i remain the MD in here, sannan on a serious note bana son sake ganinta a asibitin nan, she is neither a staff nor a patient don haka ban ga dalilin da zata dinga shigowa ba, i will talk to the securities not to let her in from henceforth" Dr Khalil dai bai tankasa ba driving dinsa kawai yake. Bayan tafiyar Khalil da kusan minti arba'in Mayraah dai na zaune office dinsa ta jinginar da kanta jikin kujera tayi nisa tunanin da take taji an bude kofar office din ta juya duk tunaninta shi ne ya dawo, sosai gabanta ya fadi ganin Zainab ta shigo office din fuska a murtuke kamar an jefota, Mayraah ta sauke idonta daga kallonta, lokaci daya jikinta yayi sanyi, Zainab ta karaso har gabanta tana kallonta da kyau tace "Ke don kaza kazanki duk fadin garin Abuja baki ga maza yan iska mara mafada karuwai irinki ba sai mijina za ki makale ma? Baki ga matsiyata masu zaman kansu kaman ki ba sai mijina? To wai ma ke uban wa yace maki Khalil ɗan iska ne? ko kuma ance maki shi ma daga sama ya fado bashi da iyaye kamar ki? Don in har kina da iyaye ban jin zaki dinga irin wannan kazamin rayuwar da kike kamar sakakkiyar akuya a garin Abuja, baki can baki nan, baki gidan mutane, baki asibiti, baki hotel, baki Suleja da kika kama gida kike zaman kanki ko ance maki duk ban bincika ba? to bari ki ji wallahi wallahi ina ja maki kunne da babban baƙi ki fita harkar mijina, i am warning u ki fita harkar khalil, stay away from my husband kada inyi maki abinda baki taɓa zato ba a rayuwarki don wallahi ba mutunci ne da ni ba, ba ni da kirki wallahi, sannan in ba zina iyayenki suka yi suka haifeki ba to ki bar min gidan uwata ki kama gabanki ki je can ki ci gaba da rayuwar zaman kai da kike a suleja, mu gidanmu gidan tarbiya ne, sai ki wani dinga yawo da hijabi sumi sumi kamar ta kirki nan kuma lalata mazan mutane kike yi cikin Abuja, i am cutting you this first and last warning idan kuwa ba haka ba nace maki duk abinda na maki ke kika ja ma kanki, banza kawai karuwa me zaman kanta" Zainab na kai wa nan ta fice daga office din kamar zata tashi sama, Mayraah ta jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune. Sai bayan awa daya Dr Khalil ya dawo asibitin, Mayraah na zaune yanda Zainab ta fita ta bar ta ya shigo office din, ya karaso yana kallonta bayan ya ajiye makullin motar MD kan table dinsa yace "Ki gaya min me ya faru Mayraah, why are you crying?" Shiru tayi har sai da ya dawo gefenta ya zauna leaving enough distance tsakaninsu yace "Pls say something, an maki wani abu ne kika shigo kina kuka daxu?" Mayraah ta kallesa sannan a hankali tace "Dama idan mutum ya bar gidan su yaje wani waje sai a fara masa kallon yana iskanci?" Tana masa tambayar hawaye ya cika idonta, Dr Khalil yayi shiru yana kallonta, ta fashe da kuka ba tare da tasan tayi hakan ba, tace "Ko dai nayi kama da warce take iskanci ne?" Dr Khalil ya sauke ajiyar zuciya yace "Gaya min me ya faru?" Tace "No! answer my questions first" Dr Khalil yace "Mayraah, in our society today da kuma al'adan mu na hausa fulani duk macen da ta bar gaban iyayenta for whatsoever reason dole zata yi facing fiye da haka a rayuwa, kin ga wasu za su mata kallon warce tafi karfin iyayenta, wasu su mata kallon er iska warce idonta ya bude tunda an san dai tafi karfin iyayenta ne ya sa ta shiga duniya, don babu iyayen da za su ba ma er su go ahead ta tafi tayi zaman kanta, wasu za su mata kallon warce ke karuwanci, bazan boye maki ba Mayraah at first da na ga take taken ki nayi maki kallon warce ta zabi ta shigo Abuja tayi rayuwar shashanci ne, even the hotel u lodged in na sa maki question mark a lokacin, but at the same time u look innocent" Goge hawayen dake sauko mata tayi tana kallonsa, yayi kasa da murya yace "Tell me what happened" Cikin rawan murya tace "Shi yasa Ahmad yake min kallon er iska har yake tunanin zan iya bin sa hotel mu kwana?" Khalil ya zaro ido yana kallonta, yace "Ahmad??" Ta fashe masa da kuka sosai, mikewa Khalil yayi ya ma kasa ce mata komai gaba daya jikinsa yayi sanyi Ahmad bazai taɓa canzawa ba kenan, bayan few seconds ya sauke wani ajiyar zuciya ya duka gabanta yana kallonta a hankali yace "Only this is enough for you kiji hankalinki ya koma gida Mayraah, mace in ba gaban iyayenta take ba kowa ma kallon da yake mata kenan to be frank.... You have given dem enough space na sati biyu yanzu, nasan duk hankalinsu ba a kwance yake ba na rashin ki" Mayraah tayi murmushin takaici tana share idonta bata son tace masa komai game da abinda matarsa ta shigo tayi mata bayan fitarsa, bazata so ta dalilinta happy family din su samu issues ba, tunani ne iri iri a ranta a lokacin, daren ranan a nan asibitin Khalil ya sa ta kwana, with d hope that as early as possible kafin zuwan MD zai je yayi dropping dinta, amma sai suka tashi da wani aiki da asuba tare da sauran likitocin asibitin, zuwa karfe tara Mayraah ta gama shawaran abinda zata yi a zuciyarta, tun cikin dare take tufka da warwara a ranta ko baccin kirki bata yi ba sai bayan sallahn asuba ta samu bacci ya dauketa, yanzu kuwa tana tashi ta tafi bandakin office dinsa ta wanke bakinta da mouth wash ta wanke fuskarta sannan ta fito ta dau Handbag dinta ta nufi kofa ta fita har sannan kuma su Dr Khalil basu fito theatre ba, tana sauka stairs tayi ido hudu da MD da shigowarsa reception din kenan da wasu turawa biyu sai bakin fata daya duk sanye da suit, a tare da su wata dattijuwa ce warce bata da maraba da halfcast coporately dressed in black suit with skirt da iyakarsa gwiwa, dai dai nan su Dr Khalil ma suka fito theatre da likitoci kusan hudu, gaba daya nurses gaida matar suke da ladabi, har ma da Dr's din tana amsa su cikin fara'arta da turancinta me cike da phonic, MD gaba daya attention dinsa na kan Mayraah bayan ya wani hade rai kamar bai taɓa dariya ba da ya hangota, wato a asibitin ma ta kwana kenan, Mayraah ta karasa saukowa downstairs ita ma ta gaida matar, Matar ta sakar mata murmushi tace "Helloo" Har tayi gaba ta sake juyowa tace "Are you a staff here young lady?" Mayraah ta ɗan kalli MD da ya kafeta da ido, a lkci daya ta kalli Dr Khalil taga ya nodding mata kai alamar ta ce eh, da sauri ta gyada ma matar kai kamar kadangariya, matar ta kalli baƙin mutumin dake cikin fararen fatan tace "Dr Yemi, you remember my Late moslem frnd Hajiya Amina?" Yace "Oh yes, Late Professor Amina, exactly i remembered Ma" Matar ta nuna Mayraah tace "Her replica, she just reminded me of her, may her soul rest in peace" Duk suka amsa da "Ameen" Matar tace "Ba don nasan yaranta ba kuma bata da karamar yarinya da nace ke yarinyar ta ce..." Mayraah dai sai murmushin karfin hali take tana kallon kyakkyawan dattijuwar don bata taɓa zaton tana jin Hausa ba sai gashi tayi hausa, amma Hajiya Amina da tace take replicating ya tsaya ma Mayraah cak a rai, to ko dai she is related to the Hajiya Amina tunda tace suna kama, MD na kallon Ceo din tasu da ladabi yace "Ma, You've stood for so long"
Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda

Ur evidence via 07087865788

60
Da ido Mayraah ta bi su har suka haura sama da sauran Dr's din dake biye da ita za su rakata office dinta, Ceo din na hawa second stairs ta kara juyawa ta kalli Mayraah, sai kuma ta kalli MD dake bayanta tace "What is that her name again?" MD ya girgiza kai da sauri yace "I have no idea Ma'am" Ta kalli Mayraah tace "What did u say ur name is?" Mayraah da gabanta ke faduwa tace "My name is Mayraah" Ceo ta bude ido tace "Mary Ann?" Dr khalil yace "She is Mayraah Ma'am" Daga likitocin har nurses duk kallon Mayraah suke, MD dai bai sake kallon downstairs din ba, Ceo na gyada kai tace "She should meet me in my office, in 30 mins time" Tana fadin haka ta ci gaba da tafiya sauran likitocin na biye da ita, Dr Balogun yayi ma Mayraah thumbs up ya wuce sama yana amsa gaisuwan da take masa, Dr Khalil ya nufo ta ya mata murmushi yace "Good morning" Tace "Ina kwana?" Yace "Har kin tashi baccin?" Ita dai bata ce komai ba, yace "Kije office dina ki jira tunda tace ki sameta nan da minti talatin" Mayraah tace "Toh" Sama ta wuce, few of the nurses suka bi ta da kallo with enviousness and jealousy. Dr Khalil ya bude office dinsa kenan zai shiga wayarsa ya fara ring yana dubawa yaga MD ke kiransa, ya kalli Mayraah dake zaune office din ya karasa ciki yace "Yanzu za a kawo maki breakfast" Tace "Toh Nagode" Fita yayi daga office din zuwa office din MD, tsaye ya samesa office din yana jiransa, MD ya nufesa cikin fada yace "Kasan implications din da kake kokarin ja min kuwa yanzu Khalil? How on earth will i explain to the CEO that this silly gal isn't a staff here?? I told u bana son sake ganin yarinyar nan a asibitin nan you are taking me for granted, saboda tsabar bata da kunya an tambayeta if she is a staff tayi nodding kanta, waye yayi employing dinta? Wa ya bata aikin? Ko ka fara bada aiki ne a asibitin nan ban sani ba?" Dr Khalil ya nemi waje ya zauna yace "To avoid the complications u are talking about kawai kayi imputing data dinta a system yanzu MD a wuce wajen" a fusace MD yace "Never!! Bazan taɓa bata aiki a asibitin nan ba like i have already said, ko dole sai tayi aiki a nan? Ba ga asibitoci iri iri da zaka iya samar mata aiki ba, all my thought was that u will be contented with Zainab amma ashe ba haka bane, ka makale ma er cikinka kasa duk ta rainamu ko aikin bata samu ba, baza kuma ta taɓa samu ta wajena ba, watch and see" Yana kai wa nan ya fice daga office din, Khalil ya bi sa da kallo yana murmushi. Ceo na zaune babban office dinta wanda mutum sai yayi tunanin a kasar waje ne tana stamping wasu files MD ya shigo, tana ci gaba da abinda take tace "I won't be able to go round the hospital today because i will be leaving in an hour time, i have a meeting to attend, and when did u say the next workshop is in Lagos?" Da ladabi MD yace "In 2 weeks time Ma'am" Tace "Ohk, i think zan koma UK nan da kwana biyu saboda exams da yaran nan za su fara, I will be back before the Lagos workshop, Send me the names and details of all our staffs i have a little token for them, and lest i forget there will be a medical conference in the US, za mu je da staffs biyu...." Bata jira ya bata amsa ba tace "Where is the Lady i asked to meet me in 30 mins time? Did she hear me right?" Yayi kasa da kai yace "Erm... Ma'am, but" Daga kai tayi ta kallesa don duk wannan maganar da take kanta na kasa tace "Is there anything Aliyu?" Ya girgiza

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login