Showing 225001 words to 228000 words out of 452169 words
Chapter 76 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
ce babu abinda bazata iya aikatawa ba wilhi, sai ta iya forging cikin ma ko a asibiti" Ammi tace "Kin manta shi likita ne Mariya? Anyi scan, ai shine nace maki har wata uku with few days" Aunty Mariya ta tabe baki tace "Ai shikenan, amma what if the DNA result comes out negative after still keeping her for 7 months Ammi?" Ammi tace "Ta cuci kanta ba mu ba" Aunty Mariya ta girgiza kai tace "Allah Ubangiji ya shirya mana zuri'a" Ammi tace "Ameen, sai da safe" Sallama suka yi
Ammi ta katse wayar ta wuce sama zuwa part dinta, har a sannan Mama Ladi bata yi bacci ba, Ammi ta kalli agogo da mamaki tace "Baki yi bacci ba Mama Ladi?" Banza Mama Ladi ta mata, Ammi ta karasa cikin bedroom dinta. Washegari da sassafe Ammi ta kira Maheer ta sanar masa yanda suka yi da Aunty Mariya kan cewar ya dau Badiyyah ya kai ta tasha, shi dai yayi shiru yana kallonta, tace "Ko ya ka ga Maheer?" Maheer yace "To ya za ayi dama, tunda relatives din babanta na denying dinta and they are not to be blamed, kawai hakan shine mafita" Ammi tace "Dama nima ban yi blaming dinsu ba" Maheer bai sake cewa komai ba, Ammi tayi kasa da murya tace "Da zaka taimaka ma tunda yau Saturday da kayi dropping dinta a kadunan saboda situation dinta"
Maheer yace "Ai yau din ma ina zuwa aiki Ammi, kawai dai ina dawowa da wuri ne" Ammi tayi shiru, sai kuma tace "Toh shikenan" Yace "In ba dai Barrister za ki ma magana ba tunda yana nan" Ammi ta rike haba tace "Wani Barrister din?" Maheer yace "Usman mana, shi da ya maida zuwa kaduna kamar zuwa cikin gari" Ammi ta tabe baki tayi murmushi kawai bata ce komai ba, Maheer ya mike yace "Ko ni sai inje in masa magana yanzu" Ammi tace "Ka dai san dama ba Badiyyah bace, amma ko me zaka ce masa in dai
Badiyyah ce bazai je ba" Usman ne ya sauko downstairs zai je kitchen ya hado shayi, Ammi ta bi sa da kallo, ya karaso ya gaisheta ta amsa, ya kalli
Maheer yace "Bonjour" Maheer ya daga kai ya kallesa yace "Morning" Zai tafi kitchen Ammi tace "Usman zaka je kaduna ne yau?" Ya juyo ya kalleta yace "Eh"
Tace "Kamar yaushe?" Yace "Zuwa karfe goma in sha
Allah" Ammi tayi kasa da murya tace "Dama wai taimakawa zaka yi ka ajiye Badiyyah a gidan Baaba Yahanasu" Kallonta Usman ya tsaya yi, can yace "Duk da dai ban tabbatar da tafiyar ba tukunna" Ammi ta dan kalli Maheer da yayi murmushi kawai, Ammi tace
"Toh shikenan" Juyawa Usman yayi ya shiga kitchen,
Maheer yace "Zan dau excuse wajen aiki sai in ajiyeta in sha Allah" A hankali Ammi tace "Allah maka albarka, sai ku je da Mayraah to keep u company, kafin yamma kun dawo in sha Allah, amma sai kun fita da wuri" Karfe tara Maheer ya shirya ya yafi bangaren Ammi, tuni Ammi ta kira Mayraah ta sanar mata tafiyar da za su yi Kaduna, jikin Mayraah yayi sanyi don tausayin Badiyyah take har cikin ranta, Ammi ta sa taje ta hada mata kayanta duk a akwati, Mayraah na hada kayan Badiyyah dake ta bin ta da kallo tace
"Me yasa kike hada kayan Mayraah?" Mayraah ta kasa kallonta, har sai da Badiyyah ta sake mata tambayar, ba tare da Mayraah ta kalleta ba tace "Za mu je kaduna ne?" Badiyyah ta mike zaune da kyar tace "Kaduna kuma? Wajen wa a kaduna?" Mayraah tace "Nima ban sani ba, Ya Maheer ne zai kai mu" Shiru Badiyyah tayi amma haka nan taji hankalinta ya tashi sosai, cikin karfin hali tace "Har da Ammi?"
Mayraah ta girgiza kai tace "Aa" Daga haka ta mike ta fita daga dakin, tana share hawayen da ya makale idonta ta kulle kofar ta jingina jiki, Usman ne ya fito daga dakinsa ta juya ta kallesa sai kuma ta sunkuyar da kai, har ya karaso inda take tsaye bai daina kallonta ba, jin bai ce komai ba ta daga kai ta kallesa, a hankali tace "Ina kwana?" Yace "Why are you crying?" kamar jira take ta fashe da kuka, ya bi wajen da kallo sannan ya matso kusa da ita ya kamo hannunta da mamaki yace "What happened?" Cikin rawan murya tace "They are taking Badiyyah to kaduna, Yaya idan taje can babu wanda zai kula da ita and she needs care in this her condition, this is her destiny we are not suppose to neglect her.." Usman yace "Is that why u are crying?" Ta gyada masa kai, yace "Did anyone help u carry ur own destiny with you? I mean... did anyone partner with u in all what u went through this pass months?" Mayraah ta dinga kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "So she should carry her cross alone" Yana fadin haka ya kai fingers dinsa yana share mata hawayen fuskarta, Mayraah couldn't stop looking at him, she doesn't even understand if she is surprise or Shock at his action, kuma bai fasa kallon kwayar idonta ba while wiping away her tears. Ammi ce ta fito daga part dinta, tunda ta kallesu sau daya daga nesa bata sake kallon direction din ba, Mayraah ta matsa daga kusa da shi da sauri, har dai Ammi ta karaso tace "Kin gama hada kayan ne Mayraah?" Mayraah ta gyada kai tace "Na gama" Ammi ta kalli Usman da ya juya zai sauka downstairs tace "Kai kayi breakfast din ne?" Ba tare da ya juyo ba yace "Na yi" Ammi ta maida dubanta kan Mayraah tace "Shiga ki fito da akwatin ki kai motar yayanku, yana waje yana jiranku" Mayraah ta bude kofar dakin ta shiga, Ammi kuma ta koma part dinta, Mayraah na sauka downstairs da akwatin Usman yace "where are you taking it to?" Tace
"Motar ya Maheer, Ammi tace shi zai kai mu" Usman ya gyada kai without saying anything, tana jan akwatin ta fita compound, Maheer na jingine jikin motarsa ya hango Mayraah, ya nufeta ya amshi akwatin, tace "Yaya ina kwana?" Yace "Lafiya lau, how was ur night?" Tace "Alhamdulillah" tare suka karasa gun motarsa ya bude booth ya saka akwatin yace "Ina take?" A hankali Mayraah tace "She is inside" Daga haka ta juya ta koma cikin gidan, duk Haseenah na lekosu ta window with so many thoughts running her mind, can ta dan yi murmushi ta juya ta bar bakin windan. Ammi ta shiga dakin da Badiyyah take, ta sameta zaune kana ganinta kaga tashin hankali a fuskarta, a takaice Ammi tace
"Maheer zai kai ki Kaduna, za muyi tafiya da Abba, kinga babu kowa gidan, Mama Ladi kuma zata tafi karaye, mai aikin zata tafi garinsu, Mayraah ta samu aiki a Abuja she will be traveling too" Badiyyah ta fashe da matsanancin kuka tace "Ammi ko ni kadai ce don Allah a bar ni zan zauna wallahi, don Allah ku rufa min asiri" Ammi tace "Kulle gidan za ayi, haka zaki hakura ki tafi kadunan sai sanda Allah yayi mana dawowa gaba daya" Tana kuka sosai tace "Ammi wajen wa a Kaduna?" Ammi tace "In an je za ki gani, ki dauko hijabinki ki fito lokaci na wucewa" Daga haka Ammi ta bar dakin, Badiyyah ta tashi tana kuka sosai ta dau hijab ta saka ta fito, dubu ashirin Ammi ta bata ta amsa tana kuka har suka sauko downstairs, har sannan Usman na zaune Ammi ta raka Badiyyah bakin kofar parlon, Mayraah ta dinga kallonta cike da tausayi har ta karaso parking space ta bude mata mota ta shiga ta kulle sannan ta tafi front seat don Maheer na cikin motar a zaune, babu bata lokaci suka bar gidan. Hira Mayraah take ta yi ma Maheer dake sauraronta bayan sun dau hanya, Badiyyah dake zaune a baya tayi nisa cikin tunanin da take gaba daya bata ma cikin hayyacinta bata san me suke cewa ba duniya ta mata zafi, after an hour drive Mayraah ta sauke ajiyar zuciya tana kallon Maheer tace "Ni kadai nake ta labarina" Yace "No, ina jin ki mana Mimi, what were you even saying?" Kin cewa komai tayi ta hade rai tana kallon titin gabansu, ya dan yi murmushi yace "So now sai monday zaki amshi statement of result dinki kafin ku tafi Abuja?
Since u will be going for interview on Tuesday..." Mayraah ta gyada masa kai kawai, yana murmushi yace "C'mon Mimi, i am sorry" Ta dan turo baki, yace
"Baxa ki hakura ba" Tace "Na hakura but yaya ni tsoron interview din nake, MD din bashi da mutunci kwata kwata wallahi, yana da anger issues, sannan he is rude and arrogant, infact he is so loud for my liking komai masifa da jaraba" Maheer na gyada kai yace
"Duk shi kadai?" Mayraah tace "Wallahi, just my few days in that hospital the experience was horrible, har bana son tunawa, wilh he is rude Yaya" Maheer na gyada kai yace "I trust you idan ya maki interview din ma you will only leave him with mouth agape, did u know that ur intelligence is extra ordinary lil sis? I am always amazed with ur intelligence, you graduated with first class, nursing science, ai shima sai yayi mamakin result dinki wallahi, shi kansa ba lallai yayi graduating da first class ba idan nursing science yayi...." Mayraah dai sai murmushi take saboda kodatan da yayan nata yake, kafin su isa kaduna Badiyya tayi amai yafi a kirga, suna isa kofar gidan Yahanasu Badiyyah ta fashe da kuka a galabaice, Maheer dai ya sauka ya fiddo mata akwatinta ya kira almajiri, jikin Mayraah yayi sanyi ta kasa sauka daga cikin motar, nan da nan hawaye ya cika idonta, Maheer ya bude ma Badiyyah bayan motar yana kallonta yace "Sauko" Saukowa tayi tana kuka sosai tace "Yaya don girman Allah ku taimakeni ku rufa min asiri, bani da kowa...." Maheer ya katseta yace "Ва Ammi tace maki tafiya za su yi ba, in kin shiga ciki sai ki gaya masu, duk sanda ta dawo sai ki koma kanon ai" Daga haka ya kulle motarsa ya zaga ya shiga driver seat, hawaye kawai Mayraah take tana kallon Badiyyah dake kuka kamar ranta zai fita, Maneer ya ja motarsa ya bar kofar gidan.
68
Sai kusan karfe hudu Mayraah suka iso kano daga kaduna, Mayraah ta kalli Maheer tace "Alhamdulillah for journey mercies" Kai kawai ya gyada mata, tace
"What should I cook for u idan muka isa gida, kaga kai baka ci abinci ba, ni kuma ka siya min a Zaria" Ya dan kalleta yace "Baki gaji ba?" Er dariya tayi tace
"Bayan ba nice ke driving din ba, i slept all through fa" Ba don yayi missing girkinta ba da bazai bari tayl girkin ba but he is craving her cooking, jin yayi shiru yana driving dinsa tace "Ko baka so?" Yace "Gani nake za kiyi stressing kanki after this long journey, kamata yayi muna komawa gida yanzu kiyi wanka kiyi sallan Asr ki kwanta ki huta" Mayraah ta dan vi murmushi bata ce masa komai ba, ya juya ya kalleta jin tayi shiru, sai kuma ya maida dubansa kan titi yace
"Ko ba haka ba Mimi?" Tayi wani murmushin tace
"Naga kamar u are avoiding me this days, baka son muna magana da yawa, i don't know! u are just being unusual, we weren't like this before" Maheer ya buda ido sosai, babu abinda ya fado masa rai sai lokacin da ita ma ta dinga kokarin avoiding dinsa 3 months back after finding out they are not blood, yasan she is talking about kafin su san matsayinsu ne, yana murmushi yace "Avoiding my lil sis? Kema kin san hakan bazai yiwu ba..." Tace "Then if u are not avoiding me kana da damuwa ne da baka son ka gaya min?" Ya dan kalleta yayi murmushi yace "You caught me" Tace "I definitely know there is something, yaya na fa san ka nasan halin ka, i know there is something bothering you, amma shine kake boye min whereas before baka boye min komai" A hankali yace "I will tell u Lil sis, but yanzu ina bukatar in huta na gaji" Tace
"Tohm shikenan, and again yaya me yasa baza ka dau transfer ba kai ma ka koma Abuja, naga kuna da Branch a can ai" Maheer yace "Kin manta daga
Abujan na nemi transfer na dawo kano, it will be a bit hard to get another transfer back to Abuja" A hankali tace "Try yaya, we will miss u idan muka tafi ba tare da kai ba, kaga shi Ya Usman dama yafi aiki a Abuja and kaduna, nasan he is going back to Abuja too" Maheer yayi murmushi yace "I will try" The rest of the journey was silent har suka iso gida, bayan yayl parking tace "Idan nayi sallah zan maka girkin" Yace
"Toh Nagode Mimi" Tayi murmushi ta bude motar ta sauka ta nufi cikin gidan. Mayraah na shiga parlon Ammi ta tadda Mama Ladi kwance ta lullube da bargo, Mayraah ta karasa kusa da ita ta duka tana kallonta da mamaki tace "Baki da lafiya ne Mama?" Mama Ladi tayi kasa da murya tace "Ae tun asuba da na tashi naji kafafuwana sun kasa daukata nasan da matsala, to ilai kuwa gashi" Mayraah tace "Ayya, to Allah ya sauwake, kin sha magani?" Mama Ladi tace
"Wa zai bani er nan? Ai yanda kika gan ni a nan tun dazu a haka nake" Mayraah tace "To zuwa anjima sai in fita in amso maki maganin idan nayi sallah" Daga haka Mayraah ta mike ta karasa dakin Ammi, kaya ta sameta tana ta hadawa a akwatuna, Ammi tace "Ya hanya Mimi?" Mayraah tace "Alhamduillah, ina yini Ammi" Ammi tace "Lafiya lau, ina yayan naki?" Mayraah tace "Kamar ya shiga gida" Ammi tace "Toh kiyi sallah ga abinci can na maku ki duba kitchen" Mayraah tace "Toh Ammi" Ta juya ta nufi kofa Ammi tace "Ki fito da kayanki gaba daya daga press din dakin ki ajiye kan gado, zan jera maki a akwati, amma sai kin ci abinci in kinyi sallah" Mayraah tace "Toh Ammi" Daga haka ta fita daga dakin, tana komawa dakinta tayi wanka sannan ta dauro alwala, bayan ta idar da sallah ta sauka downstairs ta shiga kitchen, duba abinda Ammi ta girka masu tayi, sai kuma ta fita ta koma ta dauko wayarta ta dawo parlon ta zauna tayi dialing number Maheer, yana fara ring Maheer dake kwance ya mike zaune ya daga yace "Mimi" Tace "Yaya me kake son ka ci?" Yace "Koma me kika girka zan ci" Tace "Ohk" Daga haka ta katse wayar, Haseenah dake kitchen din dake Chalet zata zubo masa abinci duk da tasan ba ci zai yi ba, tana jin wayar da yayi da Mayraah ta dan yi wani murmushi ta mayar da abincinta cikin warmer ta fito daga kitchen din ta wuce daki, dama girkin da Ammin tayi ne taje kitchen ta debo ba wai ita ta girka ba, Mayraah na kitchen tana ma Maheer girkin da tasan ya fi so wajen karfe biyar da wani abu aka bude kofar kitchen din ta juya, suna hada ido tace "Ina yini Yaya" Yace "Lafiya lau" Karasawa cikin kitchen din yayi yace "Babu abincin ne?" Tace "Aa akwai, Ya Maheer nake ma girki" Ya gyada kai ya dau plate zai debi abinci tace
"Ko zaka ci wannan da nake yi" Yace "Aa akwai me shi ae" Tayi dariya tace "Ai zan iya tsam maka kadan a ciki" Bai sake kallonta ba ya debi abincin da zai diba ya fita daga kitchen, Ammi na shigowa kitchen zata hada ma Mama Ladi shayi tace "Mimi baki son abincin ne?" Mayraah ta kalleta tace "Aa Ammi yaya nake girka ma favorite dinsa" Ammi tace "Tohh ai shikenan nawa bai yi dadi ba kenan" Dariya Mayraah tayi tace "Aa ko dandanawa bai yi ba fa Ammi, kawai favorite dinsa nake masa saboda nasan ya gaji" Murmushi kawai Ammi tayi, ta hada shayin da ya shigo da ita ta fita daga kitchen din, Mayraah na gamawa ta fito parlor ta dau wayarta tana kallon Usman dake zaune kan kujera yana kallo a laptop, Maheer ta kira ta sanar masa ta gama, a hankali yace
"Ki kawo min nan Chalet Mimi" Ta dan buda ido tace
"Chalet kuma? Aa yaya kawai ka daure ka zo ka amsa" Yace "Na gaji ne" Ta dan yi shiru, sai kuma yace "Ki bar shi kitchen din idan na shigo zan dauka" Tace "Bari in kawo maka yaya" Daga haka ta ajiye wayar ta nufi kitchen, Usman ya bi ta da kallo, daukan abincin tayi ta dawo parlor tace "Yaya kace baza ka ci ba ko?" Yace "Eh" Kofa ta nufa ta fita zuwa Chalet, tana knocking kofar yace "Come in" Ta bude ta shiga sannan ta karasa inda yake kwance, tun da Haseenah ta ji yayi waya da Mayraah ta kawo masa abinci ta sake fitowa Parlon ta zauna, Mayraah bata yarda ta kalli direction dinta ba balle har hakan yasa sai ta gaisheta, she pretends bata ma san tana wajen ba a zaune, tana ajiye masa abincin tace "Ga abincin yaya" Yace "Thank you Mimi" Tayi murmushi ta mike ta nufi kofa ta fita, Haseenah ta bi ta da ido. Ko da Mayraah ta koma sama ta tarar Ammi na ta hada mata kayanta cikin set din akwatunanta, Mayraah tace "Ammi ki bari in karasa" Ammi tace "Aa bar shi ai na kusa gamawa kije kiyi alwala kawai, it's almost Magrib" Bandaki Mayraah ta shiga don yin alwala.... Da daddare Ammi na dakinta tare da Mayraah, Mama Ladi kuma na kwance har sannan cikin bargo Maheer ya shigo parlon, ya zauna ya gaida Mama Ladi ta gyada masa kai kawai, yace "Mama ba lafiya ne?" Mama Ladi tace "Ai tunda na tashi da asuba na ji jikina na rawa nasan da magana, to ilai ga ni nan rai a hannun Allah" Maheer yace "Subhanallah, to kin sha magani?" Mama Ladi tace "Mera ta samo min wani gantalalle na hadiya dazu, amma ba sauki" Maheer yace "Zuwa