Showing 222001 words to 225000 words out of 452169 words

Chapter 75 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar

sai gobe" Yace "Ohk..." Bayan ta gama zuba masa zata fita ya bi ta da kallo yace "Za mu yi magana ne idan na gama" Tace "Ka kirani in ka gama" Daga haka ta fita daga Parlon, duk kwanan nan ko zama part din nasa bata son yi unlike before, iyaka ta shigo ta basa abinci ta koma bangarenta, ko kwana ta daina yi a part din, yana gama cin abincin ya kirata, bayan ta dawo parlon ta zauna, yace "Duk kwanan nan ina lura kin maida bangaren nan baƙon ki" ta wani hade rai tace "Don Allah bana son wannan maganar... In wata magana ce ka min amma ba wannan ba" Ya ɗan yi murmushi yace "Ohk" Ajiye ruwan hannunsa yayi yana kallonta, bayan few seconds yace "Akan Usman ne...." Ammi ta maida hankali kansa tana sauraronsa, cikin few minutes Abba ya gaya mata maganar da Usman ya samesa da shi, Ammi sai kallon Abba take without blinking, can ta girgiza kai tace "I will prefer Maheer, don ya fi sa sanyin hali da sanin ya kamata, kuma nayi magana da shi akan hakan few days back, don haka ka bar maganar Usman" Abba dake ta kallonta da mamaki yace "But Usman showed interest first, saboda me za ki ce Maheer? Saboda me zan bar maganar Usman?" Ammi tace "Eh Maheer nace, saboda duk nasan halinsu ai, ita ma kuma nasan halinta da wanda zai iya hakuri da ita, ya kuma fi sanin ciwonta...." Abba yace "To tunda haka ne duk a bar zancen, daga Usman din har Maheer nayi cancelling maganar, tunda naga abun naki kamar son kai ne" Ammi tace "Babu batun son kai, future din yarinyata nake dubawa da inda zata samu kwanciyar hankali... Kuma duk yaran nan dai naga nawa ne babu wanda zai ce ya fini sanin halinsu gaba daya su ukun, kuma kayi hakuri zance dai baza a bar shi ba Yallabai, dama Maheer din ba wai yayi dacen mata bane, Mayraah kuma zata fi dacewa da shi don ina ga ko ni ban san halinta yanda Maheer ya sani ba" Mikewa Abba yayi ya bar mata parlon ya shige daki don baya son biye ta, ta kwashe warmer din abincin ta fita ita ma. Karfe tara na safe Mayraah ta sakko downstairs da jakarta, Hajiya Amina dake ta kallonta tace "Ko dai baki jin dadi ne, tun jiya naga you are not ur self, is anything wrong?" Mayraah tayi murmushin karfin hali tace "Ba komai Aunty, ciwon kai ne amma yayi sauki yau da safe" Hajiya Amina tace "Maheer din na waje ne" Mayraah ta gyada mata kai, Hajiya Amina ta dau ledan dake gefenta ta mika mata tace "Ga su nan turarruka ne, though they are not much" Mayraah ta risina ta amsa tace "Nagode Aunty" Hajiya Amina tayi mata murmushi tace "You are welcome, ki gaida Amminku da Mama" Mayraah tace "To za su ji in sha Allah" Daga haka ta nufi kofa ta fita, tana isowa kofar gida ta tadda Maheer a mota, ta karasa ta bude front seat ta zauna tana kallonsa tace "Ina kwana" Yace "Lafiya lau" A hankali tace "Yaya baza ka shiga ka gaisheta ba" Ya ɗan yi murmushi yace "Kin ga na makara, sai naje nayi dropping dinki sannan in tafi aiki" Mayraah tace "Just 2 minutes fa is enough yaya, kuma tasan kai ne ka zo daukata" Yace "Ohk i will do that next time in sha Allah" Bude motar tayi ta sauka tace "Ni dai sauko kaje ka gaisheta sai ka fito mu tafi" Shiru yayi yana kallonta, can ya kashe motar ya bude ya sauka ya zagayo, tana murmushi tace "Yauwa ko kai fa" Hancinta ya ja sannan ya shiga cikin gidan ta bi bayansa, har sannan Hajiya Amina tana zaune parlor tana kallo, Maheer ya karasa ciki bayan ta amsa sallamarsa, ya zauna sannan ya gaisheta ta amsa da fara'a tace "Ya aikin Dr" Yace "Alhmdlh" Tace "To maa sha Allah, ya su Ammi da Mama" Yace "Suna nan lafiya" Ta mike tace "Bari a hado maka breakfast" Yace "Aa i am okay, aiki zan tafi" Daga haka ya mike, Tace "Toh shikenan, Nagode kwarai, Allah ya tsare" Yace "Ameen" har balcony ta rakasa ya mata godiya ya sauka, Mayraah dake zaune inda ake shan iska ta mike ganin ya fito, ta jira har ya karaso inda take suka fita gate din a tare, suna barin anguwan tana kallonsa tace "Yaya" Ya juya ya kalleta sannan ya ci gaba da driving dinsa yace "Mimi" a hankali tace "You know what?" Yace "No Mimi" Tace "Kwanan nan naga u are somehow, is there anything wrong? You are not longer lively like before, baka magana sosai, you are always silent, why is that?" Maheer ya kalleta yace "Ba komai, i will be fine in sha Allah, stress din aiki ne" Mayraah tace "Ko har da na matarka?" Ya girgiza kai yace "Not at all, ai bana shiga harkanta, i have nothing to do with her, i am just waiting for time" Mayraah tace "To koma menene yasa kake zama silent kayi hakuri ka ji" Yayi murmushi yace "You are funny Mimi, ba komai kawai yanayin aiki ne" Murmushin tayi ita ma duk da nata damuwar da yayi mata yawa a zuciya ɗon ko baccin kirki bata yi ba jiya saboda tunanin Musharraf amma tun dawowarta gida bata jin dadin yanda ta lura Maheer bai cika son magana ba unlike before, she missed the old him, a haka har suka iso gida wanda in da ne ko bata basa labari ba shi zai dinga bata har su isa inda za su, bayan yayi parking kofar gida ta juya tana kallonsa tace "Take care of ur self" Yace "Toh Mimi" Bude motar tayi ta sauka ta dau jakarta a back seat sannan ta shiga cikin gidan, yayi reverse ya bar anguwan.
Abba na zaune parlon Ammi tare da Usman da Maheer, sai Ammi da Mama Ladi dake parlon su ma, Mayraah ce ta shigo karshe bayan Mama Ladi taje ta kirata a wajen Badiyyah, Mayraah ta zauna kasa kusa da Ammi wondering why she saw everyone sitted kamar ana meeting, Mama Ladi tace "To kai yanzu Mamuda a ina ka taɓa jin an bar ya mace tayi aiki? Ni dai tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin haka ba gaskiya, kyan ya mace ai dakin mijinta, sannan kace Habuja kana nufin mu sake sakinta kamar akuya ta koma Habujan kenan, abinda fa hankali zai dauka shi ake yi Mamuda, ya mace take faa" Maheer dake ta kallon Mama Ladi yace "Wa yace maki mace bata aiki?" Mama Ladi tace "Aa ba ruwana, ba a pamilyn mu ba wallahi, yanzu duk abun magana ai kamata yayi mu gujesa, har yanzu fa bamu gama farfadowa daga bakin fentin da Badiyyah ta goga ma pamilyn mu ba, in ku kun farfado ni ban farfado ba wllhi, tunda gashi har yau bana iya fita sai ina boye fuska kar a danganta ni da Badiyyah" Shi dai Usman bai ce komai ba, Ammi ma tayi shiru amma kana ganin mood dinta kasan batun aikin bai mata dadi ba ko kadan duk da Maheer ya mata maganar jiya, Abba ya sauke ajiyar zuciya yace "Duk abinda kika fada gaskiya ne Mama, amma dama ai baza ta fara aiki haka kawai bata da kowa a garin Abuja ba, duk sai da na gama tsarina da Usman sannan na tara ku a nan...." Ammi ta daga kai tana kallon Abba, Abba ya ci gaba yace "Babban asibiti ne kuma sananne a Nigeria, ba kowa ake bama aiki a asibitin ba, na taɓa wani aboki likita yayi aiki a asibitin shi ma kafin ya koma kasar waje, shi yasa naji bazan bari damar nan ta subuce ma Mayraah ba...." Mama Ladi tace "Naga abinda ya isheni, to me zata yi da aiki? Ba ci ta rasa ba, ba sutura ba, ba komai ba" Abba yace "Aa zata yi aikinta in sha Allah...." Mama Ladi tace "Toh aure fa? Kana ta maganar aiki kamar wasu kafurai, haka za mu sa ta gaba sai ta tsofe a gida mu shiga uku Mamuda, aure fa shine martabar ya mace ina tunatar da kai" Abba yace "Aure ai lokaci ne Mama, wuyarta lokacin ya iso za ayi, aiki kuma baya hana aure, mutane da yawa na neman aikin basu samu ba" Mama Ladi ta kyabe baki tana girgiza kafa alamar ita fa batun aikin bai gamsar da ita ba, Abba yace "Saboda haka na yanke shawaran Amminta zata koma Abuja da zama gaba daya, don har na siya gida a can an zuba komai, tarewa kawai ya rage, tun da idan nace a fara ginin filina dake can din zai iya daukar lokaci kuma Mayraah zata yi resuming aiki next week" Mama Ladi dake gwalo ido tace "Ka siya sabon gida a Habuja Mamuda?" Kabbara Mama Ladi ta saki cike da farin ciki sannan tace "Alhamdulillahi, dama ance mahakurci mawadaci, shikenan Ammi zata koma er Habuja duk me son ganinta sai ya shirya nan kuwa ko wani kare da doki shigowa yake, dama Allah na tuba anguwan nan in ba dole ba me mutum zai yi da shi duk ɗoyin ƙwata, duk lungun da ka bi warin ƙwata, kai maa sha Allah amma nayi farin ciki da wannan labarin kuma ka kyauta Mamuda" Abba ya ciro wayarsa dake ringing yayi picking call din abokinsa, Mama Ladi da farin cikinta ya kasa boyuwa ta mike ta lallaba ta tafi kusa da Maheer tace "Mashir a ina zaka samo min wani akwatin wallahi na gaji da wannan dama" Maheer yayi murmushi yace "Usman ne yasan inda ake siyarwa" Zata koma gun Usman taga Abba ya gama wayar da yake ta koma da sauri ta zauna tana washe baki, Abba ya ajiye wayarsa yace "Amma magana ta gaskiya Mama baza ayi tafiyar nan da Badiyyah ba, tun da can kadunan ance Hajjan ba lafiya to ina ga in zaki koma Karaye zaki koma can tare da ita kawai, don zuwa jibi za su bi jirgi in sha Allah, kayan sawansu kawai za su dauka..." Sake baki Mama Ladi tayi tana kallon Abba bata ko kiftawa.

67
Mama Ladi na gyara shimfidar da zata kwanta bayan ta ci kukanta ta gode Allah tace "Toh ma sai kace wata gantalalliyar tsohuwa mara makabuli ina ni ina bin ku wani Habuja, sai kace ban san me nake ba da zan kwashi kafa in bi ku kamar a garin gaba gaba, ai da wayo na kuma ni ba mahaukaciya bace nasan me nake, amma abinda yayi min ciwo har na zubda hawaye dalilin da zai sa Mamuda yace in dauki Badiyyah mu tafi karaye, a dubi girman Allah a gaya min me na hada da Badiyyah da Mamuda zai ce min haka? To wannan cin mutuncin da yayi min shi ya min ciwo har nake ta kuka amma ba wani abu ba" Ammi dai dake zaune parlon ta sauke ajiyar zuciya bata ce komai ba, Mama Ladi tace "Kuma a gaskiya ni ba a taba ci mun mutunci irin yau ba ma tunda uwata ta haifeni, wai in tafi da Badiyyah karaye ashe ma ni na mata cikin, to wallahi ki ja masa kunne ya fita harkata ya bar hada ni da Badiyyah, babu abinda na hada da ita haduwar bariki rabuwar bariki, kakarta ce fa yayata amma ko a lahira ni bazan ga Badiyyah ba, in zuciyata ta debeni sai in iya ja masu Allah ya isa daga
Mamudan har shegiyar Badiyyan da yake hada ni da"
Daga haka tayi kwanciyarta tana matsar wasu sababbin kwallan tace "Dama da asussuba Mashir ya zo ya kai ni tasha, maganina ma kenan da nayi ta zama nan kamar wata mara galihu" Ammi tace "Kiyi hakuri Mama Ladi duk bai kai..." A fusace Mama Ladi ta mike zaune tace "Rufe min baki, ke da kika ji yana cewa in koma karaye baki da bakin magana ne? Ni na cancanci Mamuda yayi watsi da ni? Da ba don ni ba ai gidansa fanko ya so komawa amma dan Adam me mance alkhairi, kullum fa sai an bugo min waya daga karaye ana tambayar Baaba ladi yaushe za ki dawo, da gata na kaca kaca a can, to kafin ku tattara ku koma Habujan ni gobe da Asuba zan bar gidan, kuma ki mayar masa da shegen kudinsa da ya bani bana bukata, ban rasa komai ba a karaye wallahi" Daga haka ta sake komawa ta kwanta tana matsar sabbin kwalla, Mikewa Ammi tayi ta shiga bedroom dinta don for almost an hour Mama Ladi ke ta mita da koke koke ita dai hakuri kawai take bata, wajen karfe sha daya da rabi ta sake fitowa paron rike da wayarta ta ga Mama Ladi kwance ido biyu, Mama Ladi da bata wuce karte tara da rabi da ta ci ta koshi take bacci, Ammi dai bata ce mata komai ba ta fita daga parlon ta sauka downstairs, Maheer ta ganin kwance kan 3 seater idonsa rufe, Ammi ta karasa kusa da shi ta tabasa tace "Maheer" Bude ido yayi, ya mike zaune tace "Baka tafi ka kwanta ba kake bacci a nan" Ya kalli agogo sannan ya mike zaune, Ammi ta zauna daga side dinsa tana kallonsa tace "Ka ci abincin ma kuwa?" Yace "Na ci" Sai kuma ya mike yayi mata sai da safe ya nufi kofa ta bi sa da ido har ya fita, Number Aunty Mariya ta fara dialing sanin mijinta baya gari, yana fara ring kuwa ta daga, tace "Baki yi bacci ba Ammi" Ammi tace "Ban yi ba" Aunty Mariya tace "To ya gidan? Ya su Mayraah?" Ammi tace
"Alhamdulillahi" Shiru Aunty Mariya tayi tana sauraren dalilin kiran Ammi don tasan tunda ta kirata by this time akwai magana ne, Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta sanar ma Aunty Mariya abinda ake ciki, Aunty Mariya tayi farin ciki da samun aikin Mayraah da kuma garin Abuja da za su koma, she was so happy, tace "To yanzu Ammi ya za ayi da Mama Ladi?" Ammi tace
"Mama Ladi? Badiyyah dai... tambaya za kiyi ya za ayi da Badiyyah tunda ita Mama Ladi tana da inda za ta, Shi kuma yace babu inda za aje masa da Badiyyah, i am confuse ban san ya zan yi ba kuma" Aunty Mariya tayi shiru, can ta sauke ajiyar zuciya tace "Amma dai Ammi shawaran da aka yanke tun farko shine a kai ta Bichi...." Ammi tace "To bari kiji tunda na kirasu na sanar masu abinda ke faruwa buden bakin shi yayan baban nata wai sun kwana biyu su basa Bichin sunyi tafiya, ita kuwa autars baban nata ita ma da na kirata bayan kwana biyu ce min tayi tana wajen mijinta a portharcourt yaranta ma na gun kakarsu, Kinga ai sun hada baki kenan, ni kuma gaskiya ban wani ga laifinsu ba, babu wanda zai karbi Badiyyah ko waye ma haka zai yi, ko don na bar zancen ban gaya maku ba? ita kanta Mama Ladi bata san yanda muka yi da yan Bichin ba ai har yau, to yanzu ga abinda Mai gidan yace i don't want to have any issues with him, don da farko cewa ma yayi Mama Ladi ta koma karaye da ita shine ta dinga rusa kuka wai an cuceta an hadata da Badiyyah" Aunty Mariya tace "Kinsan me zai faru Ammi, ai Hajjan yanzu jikinta da sauki don ko jiya naje gidan Baaba Yahanasun dubata don haka kawai ki tattara Badiyyar ki sa ta a mota ta koma can wajensu ai ta san gidan, kuma ba sai kin gaya ma kowa ba kawai su ganta, idan ya so ki kashe wayarki kawai, ni dai Hajja bazata fara cewa Badiyyah ta zo wajena ba tunda tasan yanda yanayin gidan nan yake, in kuma kince ba haka ba to ni kam ban san yanda za ayi ba kuma" Ammi tayi shiru tana nazari, Aunty Mariya tace
"That is the only way out fa, infact don ma mun samu Abbansu Maheer din ne amma wallahi ba ko wani namiji ne zai yi tolerating haka ba, ko mai gidana nasan bazai fara yarda Badiyyah ta zauna gidana ba, dama Mama Ladin ce dai dai tafiya da ita karaye ni ko nasan ko daura ma Mama Ladi Badiyyah aka yi a kafa sai ta kunceta" a hankali Ammi tace "To shikenan, zan sa Maheer ya kai ta tasha gobe ya saka ta a motar Kadunan tunda babu wani mafita bayan wannan" Aunty Mariya tace "Shine kawai magana, yanzu yaushe za ku koma Abujan?" Ammi tace "Ya ce jibi..." Aunty Mariya tace "Kai maa sha Allah, wallahi nayi murna sosai Ammi Allah ya sanya alkhairi, dama duk mahakurci bazai taba tabewa ba, sannan Ammi ina ta son zan maki magana akan matar Maheer, yanzu shikenan ana nufin haka zai ci gaba da zama da ita?
Wato ta ci bulus duk abubuwan nan da suka faru uwa uba ga bin bokaye da malamai, asiri har a dakinki?" Ammi tace "Mariya, the girl is pregnant" Sai da Aunty Mariya ta mike zaune daga kwancen da take, tace
"Pregnant kuma Ammi?" Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace "Har wata uku kuwa, shi dai yace bai san da shi ba, shine Abban nasu yace a jira ta haihu ayi DNA, wannan dalilin yasa muka hanasa sakinta tukunna, yanzu ma nasan kawai suna zaune under same roof ne babu yanda zai yi tunda kinsan baya ketare maganata amma ba da son ransa suke waje daya ba, ai ko da dan sa ne ni bazan i supporting ya ci gaba da zama da ita ba wallahi, for now dai we just have to be patient a fira ta hainu ayi DNA din, kinji dalilin da yasa take gidan nan har yanzu" Aunty Mariya jikinta yayi sanyi, a ranta kuwa har ta fara addu'a Allah sa Maheer have nothing to do with the baby, Allah ya rabasa hada zuri'a da irin Haseenah, can dai tace
"Amma Ammi an tabbatar kuwa, anje anyi scan ko kawai da baki ta fadi? Yarinyar nan fa makira

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login