Showing 231001 words to 234000 words out of 452169 words
Chapter 78 - Mayrah Complete By Khaleesat Haydar
office din zuwa office din MD, a long pavement din saman ya samesa ya fito daga office din CEO walking towards his office, Dr Khalil ya jirasa
har ya iso MD yace "3 nurses, 5 Dr's for tomorrow's workshop, zaka yi booking flight din yau, 10 ticket in all" Dr Khalil dai na biye da shi har suka shiga office dinsa, MD ya zauna letting out a sigh yace "Yanzu zaka ga ta sake biyo ni nan" Dr Khalil yayi dariya yace
"Amma ana gama workshop din zata koma ne?" MD bai ce masa komai ba ya mike ya dau tea cup dinsa ya tafi ya wanke ya dawo ya zauna yace "Nan da sati biyu ne Conference din da tace a England ai, or is it even US, na dai manta" Har ya bude flask din sai kuma ya sake kallon cup din ya mike ya tafi ya kara wankewa ya dawo, Dr Khalil yace "Ohk ku biyu za ku yi attending Conference din kenan?" MD yace "No pls... Dr Balogun should go" Dr Khalil yace "Kai ma kasan she can't do without u in anything ai" MD ya kalli wayarsa dake ring ya dauka yayi picking call din ya kai kunne, cikin minti biyu ya gama wayar ya ajiye, ya kalli Dr Khalil yace "What were u saying?" Dr Khalil ya kalli agogon office din saboda theatre da za su shiga he is cautious of time, MD ya sake tashi ya tafi ya wanke tea cup din hannunsa ya dawo, kiran Ceo ne ya shigo wayarsa ya zauna ya daga yana sauraronta, sai kuma yace "Ohk ma, i will bring them in 30 mins time" Bayan ya katse wayar ya tashi ya sake wanko cup din ya dawo, Dr Khalil ya tabe baki ya mike yace "Are you ready? Za ta shigo interview din yanzu, cause she is around" MD ya daga kai ya kallesa, sai kuma ya hade rai yace "Waye haka?" Dr Khalil yace "You insisted she should come for the interview last week, so she is around today" MD yace
"Ohh shine yasa CEO ke tambayana ita da naje office dinta yanzu kenan, ashe ta ganta ne, ita dai ta dage lallai sai tayi aiki a asibitin nan, ko dai mayya ce yarinyar nan?" Dr Khalil yace "Ga dai ta nan with her credentials kamar yanda ka bukata, so i will send her right away, don ni zan shiga theatre" Ko tankasa MD bai yi ba ya sake tafiya ya dauraye cup da zai sha coffee, kafin ya dawo har Dr Khalil ya fita daga office din, yana komawa nasa office din ya kalli Mayraah yace "You can go to his office, but piss Mayraah be a good girl, kiyi abinda ya kamata he is our boss, and he is employing you, speak to him with respect and calmness, kalmominki kar su wuce Yes sir, Ok sir, sorry sir, thank you sir" Murmushi Mayraah tayi tana kallonsa ta rasa dalilin da zai dinga cewa she should be a good gal in zata je gun jarababben mutumin can, to tayi kama da bad girl ne? Ta sunkuyar da kai tace
"Toh Dr" Yace "You can go now, yana jira" Mikewa tayi ta dau jakarta da Envelope din takardunta, ga cire glasses dinta zata saka a jaka, Dr Khalil yace "Me yasa kika cire, ki maida abun ki" Mayraah ta kallesa yace "Ki sa mana, ai ya maki kyau" Dan murmushi tayi ta maida glasses din sannan ta nufi kofa, har ta rike handle din sai kuma ta juyo tana kallonsa a hankali tace "But do u have any idea akan abinda zai tambayeni" Dr Khalil yace "Ki kwantar da hankalinki and be calm, ba wani tambayar da zai maki na sani, kawai zai duba takardunki sai kuma ya tambayeki informations dinki to be imputed, yana ganin result din ki ma nasan sai ya rasa tambayar da zai maki don mamaki.... So just go" da murmushi ya kare maganarsa, Mayraah ta sauke idonta kasa ta juya ta fita daga office din, last floor ta tafi zuwa office din MD, gently tayi knocking kofar har sai da ya amsa sannan ta bude ta shiga, Coffee dinsa yake sha bai kuma daga kai ba balle ya kalleta, ta karasa har gaban table dinsa ta tsaya calmly tace "Good morning sir" Dago kai yayi, kiris ya rage ya saki cup din coffee din hannunsa don har sai da ya dan zube masa a white shirt dinsa, mikewa yayi da sauri ya ajiye cup din yace
"Kee, why will u just badge into my office are you okay? Ance maki kasuwa ne nan?" Bai jira me zata ce ba ya shige Bedroom dinsa dake office din, Mayraah ta bi sa da kallo, can ta tabe baki a ranta tace kilan dai Dementia garesa, cause sai da tayi knocking ya bata permission din shigowa kafin ta shigo, tana ta tsaye har ya fito bayan minti biyar with another white shirt, ya wani daure fuska kamar bai taba ko murmushi ba, ita dai bata yarda ta kallesa ba har ya karaso table dinsa ya dau cup din coffee din ya tafi ya zubar ya dawo, still yaki kallonta yace "Me kike jira har yanzu?" Calmly tace "I came for the interview u ask me to come for, here are my credentials" Bata jira me zai ce ba ta ajiye envelope din kan table dinsa sannan ta koma gefe ta tsaya, yace "Ohk shi Khalil din ne yace maki kina zuwa ki ajiye CV din kan table dina?" Mayraah bata ce komai ba, ta dau envelope din ta nufesa ta tsaya a gabansa tana mika masa while looking at him, kin yarda ya kalleta yayi may be he wasn't expecting that, kawai taga ya bar wajen ya koma seat dinsa ya zauna, ta juya tana kallonsa still ya ki kallonta, kwankwasa office din aka yi, ya mike da sauri duk tunaninsa Ceo ce, Dr Balogun ya bude office din ya shigo da wani file, yana ganin Mayraah yace "Ohh Madam, where have u been all this while?" Mayraah ta gaishesa da ladabi, ya amsa da hausansa irin na yoruba yace "Kwana biyu baki zo aiki ba, ina kika tafi?" Mayraah ta dan yi murmushi tace "Ya ce in zo interview ne tukunna kafin in ci gaba" Dr Balogun ya kalli MD that was unnecessary clearing stuffs off his table, Dr Balogun yace "Ohk MD in je in dawo kenan after the interview, dama akan aikin da za mu yi da daddare ne..." Sai a sannan MD ya daga kai a takaice yace "You can interview her Balogun, i am a bit busy..." Dr Balogun ya kalli Mayraah yace "Are you with ur CV?" Ta gyada masa kai ta mika masa Envelope din hannunta, zaunawa yayi kan kujera ya nuna mata kujeran dake kallon wanda ya zauna yace "Sit..." MD yace "Why should she sit? She should take off those glasses we are not doing fashion here" Dr Balogun ya kalli Mayraah da ta cire glasses din idonta, sai kuma ya fara fiddo da takardun, Mayraah ta wani harari MD dake kallonta ta gefen ido, Statement of result dinta Dr Balogun ya fara dubawa, sai kuma ya kalleta da sauri yace "Waow, first class from this prestigious university? It's my alma mater also, nasan lecturers dinku sosai" Mika ma MD yayi, MD dake kallonsa yace "First class in Botany or what?" Dr Balogun ya zaro ido yace "Nursing Science Malam, ina jin fa department din nan rabon da a fita da first class zai kai shekara sha biyar ko ma ya fi, and she just graduated" MD dake ta kallonsa yace "Nursing Science?" Dr Balogun yace "Gashi ka duba" MD ya girgiza kai yace "Wani makaranta ne?" Dr Balogun ya gaya masa, MD yace "That's a lie" Da mamaki Dr Balogun yace "Ka taba ganin anyi forging result a makarantar nan?" MD ya dau wayarsa yace "I have a frnd that is a Lecturer in the department, i will confirm it now" Shiru Dr Balogun yayi yana kallon MD da ya amshi result din yana dubawa sannan ya dau wayarsa ya fara dannawa, Ita dai Mayraah ko kallon inda yake bata sake yi ba, har cikin ranta bata taba jin ta tsani mutum irin yanda take jin tsanar mutumin nan ba, she detest him with passion, ji take kamar ta fice daga office din amma bazata yi haka ba sbda Dr Khalil, tana ta jiran taji ya kira wayar sai kuma bai vi ba, ya maida wayar ya ajiye yace "I will confirm that later, Dr Balogun you can leave, we will discuss the issue at hand later" Mikewa Dr Balogun yayi, har sannan kallon Mayraah yake don ko kadan bai ji shakkan result dinta ba, bayan fitar Dr Balogun ya jawo laptop dinsa after some minutes ba tare da ya kalleta ba yace "Ur name?" Sai a sannan Mayraah ta kallesa, a takaice tace "Mayraah Mahmud". Ya hade rai ya kalleta yace "Kee sunanki zaki gaya min ba sunan gayunki ba, ko an gaya maki wajen wasa ne nan?" Tace "U can check the name in my result for ur self" ita kanta bata san sanda ta gaya masa haka ba, ya dinga kallonta, kawai ya rufe laptop dinsa yace
"Get out" Bude office din aka yi Ceo ta shigo, ya mike da sauri yace "U need something Ma?" Karasowa ciki tayi tana kallon Mayraah cikin sanyayyen muryarta tace "Hello, how are you, i just asked of u not long ago" Mayraah ta gaisheta da ladabi, MD dai kallonsu kawai yake, Ceo tayi mata side hug, sosai gaban Mayraah ya fadi, Ceo na kallonta with calmness tace
"Why are you not on scrub?" Mayraan ta kasa kallonta tace "I..." Sai kuma ta rasa me zata ce, Ceo ta kalli MD tace "Is there anything?" Da sauri yace "No, not really, just adjusting some mistakes in her data....
She is not on duty today" Ceo tayi murmushi tana kallon Mayraah a hankali tace "If he is done, Come make me coffee in my office Mary Ann" Mayraah ta gyada mata kai tace "Ok Ma" Daga haka ta ajiye takardun hannunta ta juya ta nufi kofa, Mayraah ta bi ta da kallo babu ko kiftawa, juyawa tayi suka hada ido da shi, Ikci daya ya mike ya dau wasu textbook zai kai Library dinsa na office din, tace "Can i take my leave?" Wani shegen kallo ya jefa mata, hakan yasa ta fara kokarin tattara takardunta yace "Hey get out" Juyawa tayi ta bar takardun ta fita daga office din.....
70
Mayraah na fitowa office din MD ta nufi office din Dr Khalil, zai fita suka hadu da shi a bakin kofa, yana kallonta yace "Har kun gama?" Mayraah ta taɓe baki tace "Ni dai in kaje office din ka dauko min credentials dina pls" Dr Khalil na jin haka yasan an samu matsala, yace "Tell me, ya ku ka yi da shi?" Tace "Ni yanzu na fara masa uzuri gaskiya, kamar fa ba shi da lafiya ne, but seriously bai kamata ana bari yana fitowa gida a wannan yanayin ba, his parent are not doing him good" Dariya Dr Khalil yayi ba tare da ya shirya ba, Mayraah ta sauke ajiyar zuciya ta koma gefe ta tsaya, har a zuciyarta ta fara tunanin da gaske MD na da problem may be in his brain or so, to ko dai karatu ne ya fara taɓa masa ƙwaƙwalwa, Dr Khalil that was just laughing ya dake yace "Amma dai ya maki tambayoyin da zai maki?" Mayraah ta daga kai ta kallesa tace "He was just talking gibberish and finding fault where there is no fault...." Dr Khalil na murmushi yace "Za ki jira har mu fito theatre?" Mayraah tace "Zan je office din Ceo ne yanzu, i am dropping my handbag in ur office" Dr Khalil yace "Kun hadu da ita ne?" Ta gyada masa kai tace "Ta shigo ne ta gan ni" Dr Khalil na murmushi yace "I love this bond that is forming gradually between u and Ceo, i like it, kuma fa bata da yarda matar, ke kuma gashi kamar taku ta zo daya, ko office dinta in ba MD din ba sai kilan Dr Ajay babu me zuwa, out of bound muke kiran wajen, you know she is so confidential...." Mayraah dai bata ce komai ba, ya mika mata makullin hannunsa yace "Idan kin ajiye jakan sai ki kulle min office" ta amsa tace "Ohk" Yana barin wajen ta shiga office dinsa ta ajiye jakarta sannan ta fito, ta kulle kofar ta tafi sama zuwa office din Ceo, Dr Elliana Alfred... Haka Mayraah ta fada a zuciyarta bayan ta ga sunan manne jikin kofar office din, ta kai hannu zata yi knocking kofar kenan taga an bude, ido hudu suka yi da MD, ita ta fara sauke idonta ta bi ta gefensa ta shiga cikin office din ta bar sa nan tsaye, kasa fita daga office din yayi, did he just open the door for this brat to come in? Kawai ya fice daga office din ya kulle kofar. Mayraah ta karasa har kusa da couch din da Ceo ke zaune da magazine a hannunta, har ta karaso kuma kallonta matar take, matar ta nuna mata inda zata tafi don making mata coffee din da coffee maker dake office din tace "The coffee maker is over there" Mayraah ta karasa wajen sai taga ba coffee powder a nan, dawowa tayi ta gaya mata, Ceo ta ajiye magazine din hannunta tace "Ki je office din Dr Aliyu ki amso, i took it home the last time i was here...." Mayraah tace "Ohk Ma" Daga haka ta juya ta fita, office din Dr Khalil ta tafi duk da tasan bazata gansa ba amma she wish he was there yaje ya dauko coffee din da kansa a wajen MD, ita dai bata son encounter da mutumin nan kwata kwata, avoiding dinsa ma ya kamata ta dinga yi don ta fara masa kallon mahaukaci, ganin babu wani alternative ta sake komawa sama zuwa office din MD din tunda babu yanda zata yi, tsaye tayi bakin kofar tayi knocking, taji yace "Who is there?" kawai ta bude office din a hankali ta shiga, tsaye ta samesa gaban table dinsa yana duba statement of result dinta, wasu takardu yayi saurin dauka a kan table din ya daura kan result din nata cikin few seconds, and she saw that, ta dai karasa cikin office din ba tare da ta bari ta kallesa ba tace "Ta ce wai ka bada coffee powder..." Shi ma without looking at her yace "Naga kamar kina nema ki dinga kawo min reni, don me za ki shigo min office kai tsaye kamar dakin ki? Are you okay?" calmly tace "I knocked first" ya kalleta a karo na farko fuska a daure yace "And who gave u the permission to come in?" Ita ma kallonsa take taki cewa komai, sai kuma ta hango coffee powder din da ya hada dazu a kan table dinsa, zagayawa tayi ta tafi zata dauka, ya bi ta da kallon mamaki, bayan ta dauka zata bar wajen bata lura da laptop dinsa da ke caji ba kawai kafarta yayi tangling wayar chargern, force din ya jawo tsadadden laptop din tun daga kan table din har kasa, komawa baya tayi ta dinga kallon laptop din a tsorace, lokaci daya gabanta ya wani fadi, ta durkusa da sauri ta daga laptop din tana duddubawa, bayan few seconds ta mike tana kallonsa cike da karfin hali tace "I am.. am sorry...." Sai kuma ta ajiye laptop din tare da makullin hannunta ba tare da tasan tayi hakan ba kawai ta dau coffee powder din ta nufi kofa ya bi ta da kallo, tana fita ta kulle office din ta sauke wani ajiyar zuciya har sannan gabanta na faduwa, ko dai bai ga abinda tayi ma laptop din bane, da sauri ta bar wajen ta koma office din Ceo, cikin minti kadan ta gama making mata coffee din, duk inda ta bi sai Ceo ta bi ta da kallo ta ma daina karatun magazine din da take, daga karshe Mayraah ta kai mata coffee din a Tea cup da saucer dinsa, Ceo ta nuna mata table din gabanta, Mayraah ta duka ta ajiye a hankali, Calmly Ceo tace "Thank you dear" Mayraah ta ɗan yi murmushi tace "You are welcome Ma" Ceo tace "Are your parent here in Abuja?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Yes Ma" Ceo tace "Mary Ann every movement of urs reminds me of my late friend, it's been long i felt heartbroken this way, har na koma England kina raina ban san me yasa ba, i think i asked Aliyu about you twice or so" Mayraah ta sauke kanta kasa, wani bugawa zuciyarta yake da ita kanta bata gane dalilin sa ba, Ceo ta dauki cup din shayin tace "You can take your leave, thank you dear" Mayraah ta kasa barin wajen, har sai da Ceo ta daga kai ta kalleta, sunkuyar da kanta tayi tace "But ma, kin ce za ki hada ni da relatives din friend din taki" Ceo ta ɗan yi murmushi tace "Sure i will, i am kinda busy now, gobe za mu je workshop Lagos, in 2 days time zan koma England ina da aiki a can" Mayraah ta gyada mata kai tace "Toh Nagode" Ceo tace "You are welcome" Daga haka Mayraah ta juya tana tafiya a hankali ta nufi kofa, matar ta bi ta da kallo babu ko kiftawa. Gaba daya Mayraah ta mance da batun makullin Dr Khalil har sai da ta sauko second floor ta lura she is not holding the key, nan hankalinta ya tashi don bata san inda ta bar makullin ba, ko a office din MD ko na Ceo, hango kofar office din tayi kamar a bude, hakan ya bata mamaki sosai ta dai karasa tana kallon kofar that was slightly opened, tura kofar tayi taga MD tsaye gaban table din Dr Khalil with her handbag in his