Mayrah

Chapter 91 of 152

ganin Mami ta fara welcoming dinta da fara'a, Mami ta karaso cikin dakin Ammi ta ajiye mata kujera tana mata sannu da zuwa, Mami sai da ta fara gaida Mama Ladi da tayi bake bake kan kujera, Mama Ladi na kallonta daga sama har kasa tace "Sannun ku da zuwa... Ai kun ma ci sa'a da aka barku ku ka shigo don lokacin ziyaran marasa lafiya ya wuce, duk da dai sun san wa enda suke raina ma hankali" Mami na murmushi tace "Ai kam da kyar suka bar mu Mama, ya me jiki?" Mama Ladi tace "Aa Alhamdulillah jiki yayi sauki, gashi har tana tashi zaune da kanta duk da maganar tata har yanzu sai an kasa kunne ake ji, da yake asibitin me tsada ne sun san kan aikinsu da karamin asibiti ne da yanzu gaisuwa ku ka zo ba dubiya ba" Mami tace "Gaskiya kam, Allah Ubangiji ya kara mata lafiya ya sa kaffara ne, Allah ya tsare gaba" Daga haka Mami ta karasa gun Ammi dake kallonta, da fara'a suka kara gaisawa Ammi na nuna mata kujera tace "Ki zauna Hajiya" Mami na murmushi tace "To nagode" Sai da ta fara karasawa kusa da gadon dakin tana kallon Mayraah cike da tausayinta tace "Sannu kin ji Mayraah, ya jikin?" A hankali Mayraah ta gaisheta, Mami ta amsa tace "Ya karfin jikin?" Mayraah ta gyada mata kai tace "Da sauki" Kallonta kawai Mami da ta dafa gadon take, don bata taɓa ganinta ba sai yau, ita dai Mayraah kanta na kasa, Mami kam bata fasa kallonta ba, Ammi ta amsa gaisuwar Musharraf da murmushi fuskarta tace "Ya hanya Musharraf?" Da ladabi yace "Alhamdulillah Ammi, ya me jiki?" Ammi tace "Jiki Alhamdulillah da sauki" Usman ya mike ya gaida Mami, sannan suka gaisa da Musharraf ya fita ward din, Umar ma ya gaishesu daga inda yake zaune, Musharraf ya karasa kusa da gadon yana kallon Mayraah dake kallonsa ita ma, Mami ta zauna kujeran da Ammi ta ajiye mata, Musharraf ya sauke wani ajiyar zuciya yayi kasa da murya yace "Ya jikin?" Ta sunkuyar da idonta ta kasa cewa komai, nan da nan hawaye ya kawo mata, shi ma ya sauke idonsa kasa, Ammi ta nufi MD da ta gani tsaye bakin kofa ya kasa shigowa, tayi kasa da murya tace "Don Allah ku yi hakuri Dr nasan ba haka ka'idar asibitin yake ba, amma su daga kano suke ne, in dubata zaka yi ka shigo kawai sai mu mu fita tunda su baki ne" MD ya sauke idonsa ƙasa ya kasa ce mata komai, Ammi ta koma cikin dakin zata ce ma Mama Ladi da Umar su ɗan fita su je reception, Sai a sannan Mami ta lura da MD a bakin kofa, tace "Oh ashe ka biyo mu Daddy" Bai ce komai ba ya karasa ciki, Mami na kallon Ammi tace "He is my son, he is working here" Da sauri Mayraah ta daga kai tana kallon MD kamar yanda Maheer har ma da Ammi ke kallonsa da mugun mamaki, MD ya sauke idonsa, Sai a sannan Ammi ta lura da mugun kaman da suke, ta ja kujera ta zauna da mamaki tana kallon Mami tace "Don Allah fa?" Murmushi kawai Mami tayi, Ammi na jinjina kai tace "Ji wani ikon Allah kuma" Mayraah dai ta kasa daina kallon MD babu ko kiftawa zuciyarta na wani irin bugawa, MD ya daga kai ya kalleta, da sauri ta sunkuyar da kai, ya juya ya fita daga ward din, Musharraf ya bi sa da kallo, Ammi da ta kasa daina mamaki tace "Allah me iko, ai kam ya mana kirki sosai, tun da aka kwantar da mu yake tsaye kan mu, always making sure she is better...." Musharraf ya maida dubansa kan Mayraah da jikinta yayi sanyi sosai ga tunani kala kala dake yawo a ranta infact ta ma rasa wani irin tunani zata yi, yayi kasa da murya yace "Ya jikin?" Ta gyada masa kai amma ta kasa cewa komai don duk a daburce take, a hankali Musharraf yace "Pls say something" Tayi karfin halin cewa "Alhamdulillah" Bai iya ya sake ce mata komai ba saboda yasan duk kallonsu ake a dakin barin Mama Ladi dake ta kallonsa tana kokarin tuna inda ta taɓa ganinsa. MD na komawa office dinsa ya zauna kan office chair dinsa ya tallabi chin dinsa looking so confuse zuciyarsa na bugawa da sauri da sauri, at the same time he was trying so hard to understand something, to a ina su Mami suka san Mayraah da family dinta kenan? Or are they family frnds? Kawai sai yayi convincing kansa da hakan wato they are just family frnds shine dai bai san da haka ba, ya kai minti sha biyar a yanda yake wayarsa da ke kan table ya fara vibrate ya sauke idonsa kan screen din a hankali ya ga Mami ce ke kiransa, dagawa yayi ya kai kunne murya can kasa yace "Mami" Tace "Na fito ward din yanzu, kana ina?" Ya sauke idonsa yace "Ina office, ai kin san office din Mami" Tace "Ohk gani nan zuwa" Mami ta kalli Musharraf da ya zauna reception don allura za ayi ma Mayraah shine yasa suka fito daga ward din har Mama Ladi da tace kora da hali kawai ake masu meye kuma za a ce su fita don za ayi mata allura kamar wasu bare, Mami tayi kasa da murya tace "Mu je office din Daddy Musharraf" Musharraf ya kalleta yace "Ki je ni zan jira a nan Mami" Mami tace "Saboda me? Wai kana da wani ɗan uwa da yafi Daddy ne a duniyar nan, me yasa ku ke haka Musharraf?" Shiru yayi bai ce komai ba, ganin yanda take kallonsa sai kuma ya mike, ta fara tafiya yana biye da ita har suka haura sama zuwa office din MD, Mami ta ɗan yi knocking kofar sannan ta bude ta shiga ciki Musharraf ma ya shiga, kallonsu kawai MD yake har suka karaso ciki sannan ya mike, Mami ta zauna kan kujera tace "Ka rage Ac din nan don Allah" Musharraf ya zauna ya dau remote din AC din dake kan karamin table dake gaban sofa din da suka zauna ya rage karfin AC din ya mayar da remote ya ajiye, MD ya nufi fridge dinsa ya bude ya dauko masu can drink biyu da goran ruwa biyu ya karasa ya ajiye kan table din, Mami tace "Kwanansu nawa kenan a asibitin yau?" MD ya tafi ya jingina da table din office din ya rungume hannunsa yana kallon Mami yace "Sati daya, amma a ina kika san su Mami? Ko family friends?" Mami tace "Wani family friends kuma? Ita ce fa yarinyar da Musharraf ya nema da aure aka fasa" Sai da MD ya dafa table din bayansa da sauri tsabar yanda zuciyarsa ya buga, Mami na kallonsa da mamaki tace "Are you okay?" Shi dai Musharraf idonsa na kan TV dake kunne a office din duk da yana sauraron conversation dinsu, MD ya dago da sauri yana girgiza kai ganin Mami ta mike yace "I'm fine Mami, just that tun safe muke wani aiki ne, i am exhausted..." Mami da ta tsaya tana kallonsa tace "To ko dai kwanciya zaka yi" Ya girgiza kai da sauri ya zauna kan kujeran dake kusa da shi ya jinginar da kansa jikin kujeran yace "I will be fine, it's just stress" Mami ta koma ta zauna tace "Sannu...." Sai a sannan Musharraf ya juya ya kallesa, Mami na kallon MD tace "I heard she was poisoned?" Gyada kai kawai MD yayi bai iya yace komai ba, Mami tace "Allah sarki, yarinyar nan na ganin jarabawa iri iri" Sai kuma da mamaki Mami tace "Wait... Amma ai da kai aka kai kudin auren nata Daddy ko ka manta ne? Ai zaka gane yayyinta maza da ma Abban nata...." Girgiza kai kawai MD that was speechless and confuse yayi yana kallon Mami amma ya ma kasa magana, Mami bata sake ce masa komai ba cause she can see he is tired don taga hakan a idonsa, bayan few seconds ya lumshe ido kansa na jingine da kujera zuciyarsa na ci gaba da bugawa, Musharraf ya dau can drink din gabansa ya bude ya fara sha, Mami kuma ta dau bottle water ta bude, Lkci daya MD ya bude ido bayan kusan minti biyu jin wayarsa na vibrate, yana dubawa ya ga Ceo ce ke kiransa, gaba daya yaji kamar an zare masa laka ne a jikinsa, Musharraf ya mike bayan ya kusa shanye drink din Mami na kallonsa tace "Zaka koma ward din ne?" Yace "I want to get something for her outside first" Mami tace "Ohk, amma kasan Flight dina na komawa Kano bayan magrib ne zaka yi using motar Daddy kayi dropping dina airport nan da minti talatin" Musharraf yace "Toh" Kallon MD da ke ta kallon kiran ceo yayi, gaba daya he is absentminded don hankalinsa ma baya kan kiran kawai kallon screen din yake babu ko kiftawa tunaninsa na wani wajen daban, Musharraf ya karasa kusa da shi yace "Zan yi amfani da motar ka" Sae a nan MD ya dawo duniyar tunanin da ya tafi ya daga kai da sauri ya kallesa, sai kuma ya daga kiran Ceo kafin ya katse, sanar masa tayi ta shigo asibitin tana office he should meet her, bayan sun gama magana MD ya katse wayar ya dauko makullin motarsa ya mika ma Musharraf ba tare da ya kallesa ba, Musharraf ya amsa ya nufi kofa, Mami dake ta kallon MD tace "Daddy are you sure you're okay?" Ya mike da sauri yana feigning smile yace "Mami na gaji ne fa, bari in je our Ceo is around ita ta kirani yanzu" Mami tace "Ohk" Yana tafiya a hankali ya fita daga office din. Har ya isa Office din Ceo hankalinsa baya jikinsa, ya sameta tana waya, ya sunkuyar da kai ya jira har ta gama, sannan yayi mata sannu da zuwa da ladabi, ta ajiye wayar hannunta tana kallonsa daga sama har kasa tace "Are you okay?" Ya gyada kai yana kirkiran murmushi yace "Sure Ma'am" Takarda ta dauka kan table dinta tayi rubuce rubuce sannan ta mika amsa tace "Magunguna da alluran da za a canza ma Mary Ann kenan, it should start from tomorrow morning pls" Ya amsa yace "Ok Ma'am" Tana kallonsa, bayan few seconds tace "You said the result will be ready today Aliyu" Yace "Sure Ma'am it's out, yana office dina ma..." Shiru tayi tana kallonsa, shi dai yana tsaye yana jiran next instruction da zata bada, Ajiye pen din hannunta tayi a hankali tace "Bring it to me" Yace "Alright Ma" Daga haka ya juya ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita. MD na komawa office dinsa ya zauna with confusion yana kallon Mami, calmly yace "But Mami ita wannan ai da iyayenta fa, har ma da yayyinta maza, warcen kuma ba cewa aka yi bata da iyaye bata da asali ba? Sannan ita wannan a nan Abuja suke zama...." Mami da ta ma rasa abinda zata ce masa tayi shiru tana kallonsa as if wanting to figure out something, ya girgiza kai yace "Gaskiya ina jin ko kamanni ne, ko kuma, kawai dai ba yarinyar bace....." He just realized he sounds stupid and he is not making any sense, ya kara girgiza kai ya mike ya dau envelope din result din genetic testing din da Ceo ta bada ayi, kofa ya nufa Mami ta bi sa da kallon mamaki har ya fita, yana komawa office din Ceo ya ajiye mata envelope din saman table yace "Here is it Ma'am" Kallon envelope din kawai Ceo take, yace "Is there anything again Ma'am?" A hankali tace "Just wait" Yace "Ohk Ma" Gefe ya koma ya tsaya, ta dau envelope din tayi unsealing dinsa gently ta ciro result din ciki, Shi dai MD kallonta kawai yake, Glasses dinta ta dauka ta saka sannan ta warware takardun tana dubawa, MD wondered why she was this nervous checking the result, ko da yake tace family issue ne, mikewa yaga tayi da sauri ta dafe table dinta, MD ya karaso da sauri kusa da table din yace "Is everything okay Ma'am?" Sai kuma yaga hawaye na sauka idonta ta cire glasses din idonta da sauri tace "I need privacy pls Aliyu" Yana kallonta yace "Alright Ma, take care pls" Daga haka ya nufi kofa yana waigota ya ga ta nufi dakin dake office din, shi dai ya fita ya kulle kofar, jingina yayi da bango ya lumshe ido zuciyarsa na wani irin bugawa, da kyar ya iya jan kafa ya bar wajen ya koma office dinsa, yana shiga office din Mami ta mike tace "Kar nayi missing Flight dina Daddy" a hankali yace "Okay Mami, Musharraf din ya dawo ne" Tace "Eh yana waje, mu je in fara masu sallama tukunna" Bai iya yace mata komai ba, suka koma ward din da Mayraah take, Mami ta karasa kusa da gadon Mayraah tace "Allah ya sauke Mayraah" Mayraah dai ta sunkuyar da kanta, kallonta MD yake babu ko kiftawa, Mami ta ciro 50k a jakarta ta ajiye gefen Mayraah tace "A siya maki fruits" Ammi tace "Har da dawainiya Hajiya, zuwan kadai ma ai ya wadatar wallahi" Mama Ladi ta kalli Ammi da sauri tace "Kul, ba a maida hannun kyauta baya, godiya kawai za kiyi mata kice Allah ya kara arziki haka ake yi" Murmushi kawai Mami ke yi tace "Lallai kam Mama gwara dai da kika gaya mata" Cikin sanyin murya Ammi tace "To Allah ya saka da alkhairi Hajiya, mun gode kwarai da gaske, Allah ya bar zumunci" Mami tace "Ameen ya Allah, ita kuma Allah ya bata lafiya ya tsare gaba" Ammi tace "Ameen" Mayraah ta ɗan daga kai ta kalli MD da bai fasa kallonta ba suka hada ido, kauda kanta tayi da sauri, Ammi da Mama Ladi suka fita raka Mami, Usman dai sai kallon MD dake kallon Mayraah yake.

*If you are reading this book without payment ki sani dari biyar dina na kanki har ko da yaushe, you better pay ki sauke burden*

Mayraah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah

Ur evidence via 07087865788

83
Har bakin mota MD ya rako Maminsa, tun da suka fito asibitin Mami ce ke ta magana shi kam yayi shiru kansa a kasa yana biye da ita ba tare da yasan ma me take cewa ba, bayan Mami ta bude back seat tana kallonsa tace "Take care of ur self Daddy" Yayi murmushin karfin hali yace "Sure Mami, Allah ya tsare" Tace "Ameen" Daga haka ya juya ta bi sa da ido har ya shiga cikin asibitin, gaba daya ta kasa gane dalilin wannan sanyin da jikinsa yayi lokaci daya, let it not be what she is thinking fa, tunanin hakan yasa taji hankalinta ya tashi, a sanyaye ta shiga bayan motar tana kallon Musharraf, sai da suka kusa Airport Mami tace "Where will u be spending the night Musharraf?" Yace "Hotel" Mami tace "Aa, kaje gidan yayanka.... kuma bana son musu" Musharraf ya kalleta ta madubi yace "Kin fa san halinsa Mami baya son sharing komai nasa da kowa, kawai bata min rai zai dinga yi mu samu issues a gidan nan, ni kuma i don't want to have any issues with him, " Mami tace "Baza dai kayi abinda nace ba kenan" Musharraf yace "To na ji" Mami tace "Yaushe zaka dawo?" Idonsa na kan titi yace "Ko gobe da safe in sha Allah" Mami tayi kasa da murya a hankali tace "Plss Musharraf bana son ka kara zura jiki zuwan ka Abujan nan don Allah, kaga u are yet to recover fully, kar kaje ka kara shiga wani damuwar bazan ji dadin hakan ba, you know what u went through da yanda ka fita hayyacin ka for the past few months, banda ma rashin lafiya ne kaga da bazan bari ka taho Abuja ba har ma in biyo ka, infact i will prevent anything da zai sake hada ka da yarinyar, amma rashin lafiya ya wuce komai, kuma dukkanmu musulmai ne..." Musharraf ya ɗan yi murmushin karfin hali a hankali yace "Mami ni yanzu tsakanina da Mayraah ai sai zumunci, i gave up long ago cause babu hope din aure tsakanina da ita, ta riga da ta min nisa, and with the way things are going bana tunanin za a bari outsider ya aureta, sai ki ga kilan daya daga brothers dinta za a hadata aure da tunda da aure tsakaninsu, so i will keep on nurturing my heart to forget about everything, in kuma rabona ce ita baxan ce bazan aureta ba i will gladly get married to her, amma da kamar wuya" Mami ta sauke ajiyar zuciya tace "Na ji dadin da ka fahimci haka, Allah Ubangiji yayi maka zabi mafi Alkhairi a rayuwar ka, idan ma ita din ce Allah ya baka ita cikin ruwan sanyi, in ko akasin haka Allah ya baka warce ta fi ta" A hankali Musharraf yace "Ameen" MD na komawa office dinsa ya zauna ya rike kansa da yayi masa nauyi duk ya rasa tunanin da zai yi, it was something he never saw coming, bude kofar aka yi ya dago da sauri, Dr Khalil ya shigo ya karaso gaban table dinsa yana kallonsa yace "Are you okay?" MD ya mike yace "Sure... Pls akwai patient ward 5, ka ɗan dubasa zan je office din Ceo ne" Dr Khalil yace "Ohk...." Juyawa yayi ya fita, MD ya dawo kan sofa din office din ya zauna ya tallabi chin dinsa, ya fi minti sha biyar zaune a haka, daga karshe ya mike duk jikinsa ba kwari ya nufi kofa yana tafiya a hankali har ya fita ya kulle office dinsa, yana isa office din Ceo yayi knocking gently, sau uku yayi knocking din jin bata yi responding ba ya juya ya bar wajen kawai... Dab da Magrib Musharraf ya shigo dakin da Mayraah take, ya ajiye fruits da ya siyo mata, Umar kadai

Download complete TXT · Novel page